Noor Albi

NOOR ALBI 11

Umma Jamila kasa nutsuwa tayi ta ringa addabar Haj Karima Saida suka sako Kawu saidu da Kira Kan Kira ya shiryo ya taho sbd matuqar ba yana garinba Turaki yazo yatafi to fa Babu wata maganar aure bayan sukam tuni suka hau Shirin aure gadan gadan batareda lissafin komaiba ko tunani irin na masu shekaru,

Koda Kawu saidun ya iso daga nijar ya sauka a dakin Abba sosai yashiga mamaki da takaicin ganin halinda Laylah ke ciki sbd shikam kallo daya yayi Mata bayan Sa’adah takawota sun gashesa ya fahimci batada isashiyar lafiya Dan kuwa ko dagowa ta kallesa bataiba kanta a qasa ta gaidasa.

Abinci kawai yaci yayi salloli ya wuce asibiti gurin Dan uwansa yabar gidan
Yana fita kuwa saiga Alhaji Atiku da Umma Jamila sunzo gurinsa Basu tarar dashiba Dole suka koma da niyar dawowa gobe Dan subarsa yau din ya huta.
A asibiti kuwa tunda yayi ido biyu da Dan uwansa take jikinsa yayi Sanyi Dan baiyi zaton Jikin yayi Munin hakanba take qwallar tausayi Dan uwa taciko idanuwansa ya hadiye Yana jinjina Kai Yana sauraron bayanin yanda Abban yaketa fama da jikin duk tsawon lokacin Nan daga Abdullahi…

Shiru Abdullahin yayi yanason sanarda kawun wasiyar Abban na bawa AB TURAKI auren Laylah ko bayan ransa Yana shakkar Shiga zancen sbd sanin maganace Mai girman gaske tunda aure ake magana
Auren Kuma da mutum kamar Turaki,
Shi daza’a basa auren Laylah dinma da wlh Yanaso ya karba.

A asibiti Kawu ya tarewarsa Bai sake komawa gidanba ya zauna jinyar Abban Abdullahi yasamu hutu duk da kullum da daddare saiya leqo asibitin kawowa Kawun abinci duk da Babu wata wata daga gidan umma Jamila ake kawo Masa abincin safe Rana dare Kuma abincin Alfarma lafiyayye Wanda tun Kawun Bai kawo tunanin komai aransaba yafara tunanin akwai dalilin hakan Dan Haka ya zuba musu ido yaringa cin abinda Dan yasan Umma Jamila batada Tausayin bawa Dan uwan Mahmoud ko abunda bataso matuqar ba babban daliline garesuba Mai matuqar mahimmanci.

Ganin dai Kawun baida niyar dawowa gida bare suzo ayi magana dashi yasa Suka yanke shawaran haduwa dashi a asibiti Dan Haka yau da daddare Yana zaune bayan yadawo daga masallacin asibitin sallar ishai yaci tuwon semo da miyar kubewa da gandar da aka kawo Masa tareda fruits
Gamawarsa kenan Yana kokarin amsa Kiran Mai dakinsa daya shigo wayarsa saiga Alhaji Qarami tareda Alhaji Atiku da umma Jamila sai Haj Karima data iso a jiya sunshigo sanye cikin shigar Alfarma,

Miqewa yayi cikin sakewar fuska Yana cewa”

Marabanku da zuwa,
Alhaji Qarami bismillah ku qaraso daga ciki,
Alhaji Atiku barka da zuwa
Sannunku sannunku
Yanzu da Daren Nan kuke shigowa.
Haj barkanku da zuwa Bismillah ku shigo,
Hannu ya miqa musu sukai msabaha Yana sake gaidasu cikin mutuntawa duk dai ya girmesu saidai kasancewarsu manyan mutane yasa shine yafara gaidasu din Suma cikin mutuntawa fuska asake suke gaidasa tareda maida kallonsu Kan Abba cikin alhini suke tambayar jikinsa,..

Allah yakawo sauki da afuwa yasa kaffarane.

Amin Amin ya Allah,

Alhaji Atiku Naga hidima anatayi damu
Allah ya Sanya alkhairi yabada Lada
Ana kokari sosai wlh
Ngd Sosai Haj Jamila.

Bakomai Kawu saidu ai duk yiwa Kaine musamman kaida kabaro iyali kazo nesa gashima bamu samu lokaci anyi maganar datai dalilin zuwan naka.

Gyara Basu gurin zama Kawun yayi Yana zama shima kafin ya nutsu Yana kallon Alhaji Atikun yace”

Eh wlh to nazo na tararda jikin na Mahmoud ba sauki ba sauyi shine hankalina duk ya koma kansa Amma ai tunda maganar aurece ba wata damuwa duk lokacinda magabatan yaron suka tsaida ranar zuwa sai a sanar Dani naje saimu taru a tattauna din….

Kallon Alhaji Qarami sukayi sbd shi Basu fada Masa ainihin gskiyar zancenba Dan bazai taba yarda da hakan ba
Haj Karima ta karbe zancen da cewa”

Aure Kam ai magana na hannunka Dan kaine Wanda zai tunkari Wanda aka bawa auren da maganar auren kasancewar Kaine tamkar uba agareta tunda Kaine tamkar uba ga mahaifin nata Dan Haka komai a hannunka yake.

Murmushi Kawu yayi Yana jinjina Kai yace”

Hakane,
Inshallah Allah wannan aiba wani matsala bane,
Auren ne manemin Bai tashiba kokuwa?sai anemesu muyi mgn dasu….

Alhaji Qarami ne ya gyara zama Kai tsaye cikin nutsuwa yace”

Alhaji Mahmoud ne kafin Allah ya sako Masa wannan jarabawa a kwanakin baya yabar wasiyar bada auren Sa’adah ga Aminsa AB TURAKI Wanda kasani,
To ita yarinyar yanzu akwai masu neman aurenta da har mun amince anbasu saigashi Kuma Haj Karima takirani akan a dakatar da waincan din sbd yarinya mahaifinta yariga yabada ita ga Amininsa shinefa Muka dakatar da waincan sbd Afaraji ga Turakin idan ya amsa shikenan sai adaura aure abawa waincan hakuri
Idanma akasin hakan aka samu kaga dai anfita haqqin wasiya sai abawa waincan dama sukuma fitowa sai ayi dasu wannan shine taqamaimai dalilin kiranka Alan kazo Dan kuwa Babu Wanda yafi cancanta yabada aurenta Kamar Kai
Hakama Kaine kafi cancantar neman AB TURAKI da maganar sbd ba huruminmu bane mu dangin uwa.

Shiru Kawu saidu yayi Yana jinjina Kai cikin Dan mamakin zancen Yana juya zallar tazara dakuma banbancin rayuwar Dake tsakanin AB TURAKI da Sa’adah din
Saidai tunda Allah Bai haramtaba ba illa bane face qarfafa tare dakuma bawa yarinyar rayuwa Mai kyau a gaba duk da Laylah ce tafi cancanta da hakan ko Dan maraicinta dakuma shaquwar Turakin da mahaifiyarta zaifi Mata riqo na gaske sbd uwarta.

Numfashi ya sauke ahankali Yana sake jinjina Kai ya dago yace”

Babu illa Inshallah zanyi magana dashi saikuyi hanyar da zata hadani dashi din sbd Baya daukan waya sai dace.

Wannan ba matsala bane Inshallah zamu saka lokaci saimuje gabaki daya can Abuja har gidansa sai ayi maganar sbd Inshallah Ana saka ran shigowarsa gobe.

Kawu dai zancen yazo Masa wani iri Amma tunda maganar aurece zaije din bakomai bane dama shine Kamar waliyin su Sa’adah din yanzu tunda mahaifinsu ga yanda Allah yayi dashi.

Da zasu tafi kudi sosai suka bawa Kawun Amma yaqi karba yace bazai karba ba hidimar abinci kawaima da akeyi dashi ya isa.

Haj Karima da umma Jamila sai Alhaji Atiku dasukasan gskiyar lamarin zukatansu cike suke da farin ciki da qaguwa har suka Isa gidajensu
Kawu kuwa dayake mutum ne Mai maimaicin zancen bayan tafiyarsa zaunawa yayi yanata sake juya lamarin har Abdullahi yazo Nan yasake bayyanarda zancen ya Dora da cewa”

Ina shakkar son abun duniya irin na zuriar Zainab idan basune sukeson ingizani Kai zancen wasiyar da babu ba mutuncina da Turaki yake gani ya zube
Dan kuwa Ina mamakin Ta yanda Mahmoud zai bawa Amininsa daya Isa haihuwar yarsa so dubu aurenta batareda laakari da komaiba
Hakama tayaya yake tunanin Turakin zai karba auren Shi Dana mazauniba,hakama baya haihuwa…….

Shiru Abdullahi yayi Yana sauraron Kawun yanason magana Yana Hana kansa
Jin dai Kawun nata nanacin zancen yasashi bude Baki a natse yace”

Dan bada Aure kam Abba yabada aure ga Turaki Kuma yace wasiyace acikamasa ita Amma dai Kam ba Sa’adah ba……

Kawun Bai gama gane qarshen zancen Abdullahin ba yace”

To Allah yasa Turakin yasan da zancen Dan zaifi sauki da mutunci akan nine zanfara tunkararsa da zancen,
Tabbas nasan Akwai alqawarin hada zuria a tsakaninsu saidai ta ‘yaya waya sani Ashe ba yayansu zasu hadaba Matar Turakin ce zata fito ta tsatson Aminin nasa,
Wannan da Laylah ce amaimakon Sa’adah da sainace Rabon aurensa da itane yasa ya tsaya tsayin dakan auren uwarta da ubanta harma shine ya biya sadakin.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button