JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

Malam Muddasir na shirin magana Jariri yace, “Kawai hango idanuwanta nake lokacin da na maƙaleta a moto nace mata sai na sha mama.” Jariri ya kuma fashewa da dariya sannan ya kalli Inno yace, “Yooooo ban da abin ta gwada ta fa nake Allah na tuba me zan? Wa ya ga tafiyoka” yana faɗar haka yana kuma fashewa da dariya.

Malam Muddasir ya haɗa rai yace, “Kai bamasan iskanci ka gaba faɗar dalilin shiga jikinta na babbakeka ko yaya?” Jariri ya yi jim kamar me nazari sannan yace,

“Ai ban faɗi uwa uban abin da yasa na maƙale a jikinta ba, ba nace muku tana fitowa ƙerere cikin dare babu ko ɗan mayafi ba? To bayan wannan ko addu’a ba ta yi yadda kasan rana haka take fitowa fakam-fakam ta faɗa banɗaki haka take yi, duk abin da take yi a banɗakin ina laɓe ina kallonta. Wai ka san da me nayi niyyar yi kuwa?” da sauri Malam Muddasir y girgiza kai.

Jariri ya ci gaba da cewa, “Wallahi da so nay nai wuuf da ita kawai dai mata ta na da tsananin kishine ina tsoron karta kasheta haƙƙin ya yi yawa akaina. To ka ji wannan dalili yasa na ɗafe na ɗauke ɗanta mukayi habzi da shi.”

Malam Muddasir na gama jin haka bai tankawa Jariri ba ya ciro wayarsa ya danna kira, daga cen ɓangaren aka ɗauka bayan sun gaisa yace, “Abokina wani aiki ne ya ɗan taso amma ina gidansu Halifa na sabon titi ka ƙaraso yanzun nan.” Jariri na jin Malam Muddasir ya gama faɗar haka ya sa hannu ya dafe ƙeyarsa yace, “Yau ina ganin rayuwa ko wacce uwar ya kira wani ƙaton yazo ya yi mini oho?” Malam Muddasir ya kalleshi yace, “Duk uwar da za’ayi maka dai ka sa ido ka gani.”

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    45&45



 Bayan wayar Halifa babu jimawa Nasiru ya ƙarasa gidan da sallama ɗauke a bakinsa, amsa masa suka yi su Inno sai nannan suke da shi duk da basu san dalilin zuwansu ba, shiga ya yi wajen Malam Muddasir da mamaki ya kalleshi yace, "Abokina lafiya baka ganin akan Jariri ka ke?" Jariri ya juya ya kafe Nasiru da idanu yana watsa masa harara dan tun daga zuwansa ya fahimci wanene shi, kafin Malam Muddasir ya bashi amsa Nasiru ya ƙurawa Jariri idanu, don ko ba'a faɗa ba ya fahimci wannan jaririn mutanensa ne.

Malam Muddasir ya katse masa tunani da cewar, “Nasiru wannan da kake gani taƙadari ne irin mutanenku ne, yanzu Baba yana gida?” Nasiru ya yi dariya yace, “Eh yanzu haka na baro shi a gida” Jariri ya ɗago kai yace, “Amma ai ina da haƙƙin da za’a barni na yi magana, ba a dinga yin maganganu ba a sakawa da ni ba.”

Nasiru ya kalli Jariri yace, “Lallai wannan da alama ya ci ya ƙoshi wai da haka yake zaro magana?” Jariri yace, “Da so kake ka ganni a bushe kamar wannan falalun?” ya faɗa yana nuna Malam Muddasir.

Malam Muddasir ya yi ƙwafa sannan yace, "Da so nake na ƙoneshi amma sai nake ganin me zai hana mu haɗashi da Baba saboda wannan yadda yake da idanu a tsaitsaye yana jin na fara karatu idan azaba ta isheshi yana iya guduwa bayan bana nan ya ci gaba da wahalar da su." Nasiru ya jinjina kai yace, "Ai hakan ma ya yi kuma ko munje gurin Baba sai mun babbake shi kafin mu ƙarasa cen inda ya fito."

Jariri harara ya wurgawa Malam Muddasir sannan yace, “Wallahi da zan samu dama ka ga waɗannan falfelar kunnuwan naka sai na rage maka girmansu.” Malam Muddasir yace yanzu ma zaka iya ai”

Malam Muddasir kira ya ƙwalawa Halifa yana zuwa ya sa shi ya tattaro mutanen gidan, Tarasulu ban da aukin shafa sulluɓeɓen kanta babu abin da take yi. Gabaɗaya zama suka yi suna sauraron abin da zai sanar da su.

Malam Muddasir ya kallesu ɗaya-ɗaya bayan ɗaya yace, “Assalamu alaikum, haƙiƙanin gaskiya bakusan dalilin da yasa na tattaraku waje ɗaya. Ina san na ƙara tunasar da ku game da muhimmanci riƙo da addu’a, bawai ima nufin bakwayi ba a’a ina nufin ku riƙe ta da addu’o’in kariya wala kuna cikin kwanciyar hankali ko akasin haka. Nusaiba kinji dai abin da ya faɗa wanda wannan ba baƙuwar magana bace a wurinmu, naji cases kala-kala na aljannu da dama da zaku ji sun ce sakacin addu’a ne ya taka muhimmimiyar rawa akai, ba wai iya me ciki ba kowa da kowa ya kamata ya rike addu’a ya zama idan dare ya yi zaka yi wani uzuri ka dinga A’uziya da karanta ayatulkursiyya, kuma idan dare ya yi ba kowacce shiga ya kamata mace tayi ta fita waje da ita mai bayyanar da surar jiki waje ba, yadda muke sabgarmu da iyalanmu da rana suma haka suke tasu da dare. Sannan duk wani hali da ɗan adam zai faɗa addu’a ita zata fitar da shi, ihu ko kuka babu abin da zai amfanar da shi, ina fatan zamu ɗau wannan ƴar tunatarwa kuma Allah ya tsaremu daga sharrin irin wannan taƙadarin Jaririn.” Jikinsu a sanyaye suka amsa da Ameen, Malam Muddasir ya jima yana yi musu nasiha mai ratsa zuciya sannan yace Halima da Daddy zasu iya binsu zuwa gurin Mahaifin Nasiru dan a gudanar da komai a kan idonsu.

Daddy bashi da sukunin zuwa saboda ciwon jikin da yake fama da shi, Halifa da Salim ne suka yi miƙe zasu bu Malam Muddsir. Malam Muddasir haɗa hannun Jariri ya yi da ƙafafuwansa wuri ɗaya a riƙe da hannunsa ya miƙe tsaye, ban da zillo babu abin da Jariri yake yi sai yana cewa, “Dan Allah karku rabani da su wallahi mun yi saboda, to idan ba za ka barni da su ba ka barni muyi sallam da su Goggo” Halifa da ke gefe yace, “Sai dai kayi sallama da su a gidan uwarka.” Malam Muddasir bai bi ta kansa ba ya fice da shi daga gidan.

Suna fita Nusaiba faɗa jikin Mummy ta rushe da wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi, Mummy rungume ta tayi tana jin tausayin Nusaiba a ranta tabbas kowacce uwa tana san ta haihu ta buɗi ido tana jaririnta cikin kwanciyar hankali, sai ga Nusaiba bayan ta ƙwallafa ranta akan ɗan da ta haifa har ya yi sati guda tare da ita amma lokaci ɗaya an raba ta da shi. Ɗagowa ta yi ta kalli Mummy ta ce, “Mummy shikenan bani komai dama ba ɗana bane?” sai ta kuma rushewa da kuka. Mummy cikin lallashi ta ce, “Allah ya nufa dama cen wannan baza a moreshi ba Allah yasa haka ne yafi alheri.”

Goggo dake gefe cikin jin haushi ta ce, “Yau naga salawaitun iya shege anya Nusaiba kanki ɗaya kuwa akan wancen taƙadarin kike hawaye a banza, da ba a fargaba haka zaki ci gaba da salawaitun ɗirka garjejen gardi a cinyarki yana tsotse ki, idan baki rufe mini baki ba inban zagi ubanki ba kice Mai salati be haifeni ba.”

Sorry Nusy da ban tausayi???? Amma rabaku da jariri ne mafita???? ayi haƙuri da errors ban tace shi ba.

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    47&48


  Lokacin da su Malam Muddasir suka ƙarasa gidansu Nasiru a soro suka tsaya Nasiru ya shiga ya yi ya sanarwa da Mahaifinsa halin da ake ciki, babu jimawa ya fito soro ya same su. Kallan Jariri ya yi ya cewa Malam Muddasir, "Sake shi babu inda zai je" Malam Muddasir ya saki Jariri ya tafi rijib ya faɗi a ƙasa, Baba ya kalli Jariri yace, "Kai wanene kai?"

Jariri ya sunne kai ƙasa yace, “Ni ne Gundur?” Baba ya zaro ido waje yace, “Gundur! Dama duk neman da iyalanka suke yi maka kana nan laɓe a wajen bayin Allah? Tsohon banza tsohon wofi Allah dama baka ji kashe din da nayi maka rannan ba ko?” Jariri haushi ne ya kamashi ganin ana neman tozarta shi a gaban su Halifa cikin jin haushi yace, “To cin fuskar na meye kuma da suke nema na cewa nai bazan koma wajen su bane, wai ma da za’a takurani ina da ƴan cin shiga ko ina a cikin duniyar nan fa tun da dai duniyar ba ta uban mutum bace” Baba ya riƙe baki yace, “Gunduru zagina kake?” Jariri a fisge yace, “Eh to kusan haka ne idan kaji na zage ka kuskuren baki ne kamar yadda kaima kayi”

Baba bai tanka masa ba saboda ya lura kansa hayaƙi yake, bismillah ya yi ya fara karatu Jariri tun yana dakewa har ya kasa jura ya ci gaba da ihu yana neman taimako babu wanda ya bi ta kanshi daga ƙarshe dai Malam Muddasir da Baba suka ƙoneshi ƙurmus, nan take suka ga Jariri ya ɓingire ya faɗi ko numfashi baya yi. Baba ya kalli Halifa yace, “Alhamdulillah ƙarshen wannan azzalumin da nayi niyyar na mayar da shi gurin iyalansa amma taurin kai irin nashi nasan ko na mayar da shi ba zai daina bibiyarku ba. Yanzu kuje haƙa rami ku binne gangar jikin nan”

Jiki a sanyaye su Halifa suka ɗauki Jariri suka fice daga gidan zuciyar Halifa fes yana jin kamar an sauke musu wani nauyi a kansu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button