JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

ASSALAMU ALAIKUM

‘Yan uwana musulmai maza da mata wanda na sani da wanda ban sani ba. Sunana Fatima Aminu wadda aka fi sani daUmmu Saddik ga masu bibiyar littafaina. Taimako nake nema kan wata baiwar Allah da ta kuka min da damuwarta.Wata baiwar Allah ce ƙawata aminiyata kuma maƙwafciyata ta shiga wani hali na buƙatar taimako kun san komai ya zama na kuɗi mijinta aka zo har gida aka ɗauke yau kwana 45 ba amo ba labari mutumin Niger ne ba shi da kowa sai ƙanin mahaifinsu kuma basu kula da ita ba baiwar Allah. ‘Yaƴan ta uku tana daya daga cikin wadanda Allah ya jarabta da bandit maganar da nake a yanzu mutanen garinsu kaso saba’in da biyar cikin dari sun yi gudun hijira. Yanzu a halin da take ciki ƴarta ba lafiya ko asibiti ba a je ba saboda babu kudin tafiya. Hakazalika abincin da za su ci ma wuya yake mata. Don Allah duk mai niyar taimakawa ya tuntuɓe ni ta wannan number 08146711395.

Idan ma ba ka da halin taimakawa don Allah ko da addu’a ce ku yi mata. Allah ya yi mana maganin abin da ya fi karfinmu. Ya yi mana katangar karfe da sharrin wannan zamani.

????????????????????????

 Halifa ji ya yi jikinsa ya yi sanyi tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafin ƙafarsa, ji yake kamar ƙafarsa bazata iya ɗaukansa ba. Kiran wayar ya ƙara yi nan take ya ji ta a kashe, Nusaiba ta tambayeshi me yake faruwa. Sai da ya ɗan jingina da bango sannan yace. "Wai kinji Jaririnmu ya tafi da su a mota" zaro ido waje tayi tana daɗa kallan Jaririnta ta ce. "Banda wanda yake hannuna yanzu? To a ina na taɓa ji Jariri yayi tuƙi idan ba aljani ba" Halifa yace. "Gaskiya lamarin ya fara bani tsoro wallahi, anya kuwa babu shafar aljanu a jikin su Inno amma ta yaya su kaɗai a mota za'a neme su a rasa alhalin babu mukulli a hannunsu." Halifa ƙarasawa ya yi gaban wata kwantaina ya yi wa ma kwantainar sallamar sannan yace. "Dan Allah Malam ka lura da wata mota fara bakin glass a gurin da nayi parking, ko ka ga wanda ya buɗe ta?" Me kwantainar yace. "Gaskiya Abokina ban lura ba tunda ka ga nima a bakin neman kuɗina nake" jiki a sanyaye Halifa ya yi masa godiya ya koma gurin da ya bar Nusaiba a tsaye. Jigun-jigun sukayi aka rasa me magana Nusaiba tayi ƙarfin halin cewa. "Habibi me zai hana ka kira su Daddy ka sanar da su wannan fa ba ƙaramar magana bace." Fuska ɗauke da damuwa yace. "Wallahi ina fargar sanar da su saboda Abba da Daddy kinsan kowanne  na da hawan jini bansan ma ta ina zan fara sanar da su ba, kinsan dai kowa zan gayawa abin da Goggo ta faɗa bazai yarda ba  to ni me ma zan ce musu? Cewa zan Jariri ya ɗauke su a mota ko me?" Nusaiba ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Habibi tafasar tukunya fa ba ta gefe ɗaya bace wannan ba maganar da zamuyi shiru bace, ya zama dole su Daddy su sani.

Hannu ya zura a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar mahaifinsa, sai da ta kusa katsewa yaji anɗauka. Kamar me ciwon baki haka ya buɗe baki a hankali yace. "Daddy barka da safiya" daga cen ɓangaren Daddy ya amsa sannan Halifa yace. "Daddy dama nace dama... dai.." Daddy yace. "Halifa lafiya kuwa duk naji ka wanj iri" Halifa ƙarfin hali ya yi ya sanarwa da Daddy halin da ake cikin, cikin tashin hankali Daddy ya dinga maimaita, " Innalillahi'wa ilahirraji'un" Daddy ya ci gaba da cewa. "Yanzu kuna asibitin ne?" Haliha yace. "Eh muna cen Daddy" Daddy yace. "Ka nemi securities ka sanar da su abin da ya faru dan suyi gaggawar sanarwa da hukumar asibiti yanzu zan kira Yusuf na sanar da shi halin da ake ciki daga nan zanje Bompai nayi report, inyaso sai ku wuce gida" Daddy bai jira cewar Halifa ba ya katse wayar.

Kamar yadda Daddy ya gayawa Halifa haka ya samu securities ya sanar dasu nan take maganar ta zagaye cikin asibitin, Halifa da Nusaiba adaidaita sahu ya tarar musu suka wuce cen gidan Mahaifinsa, lokacin da suka je suka samu mutanen gidan duk sunyi jigun-jigun saboda tashin hankali.

Lokacin da Jaririn ya fisgi wayar hannun Goggo kusan mutuwar zaune tayi, gashi sai fafara uban gudu yake dasu kamar zai tashi sama. Goggo tun tana iya ihu har tayi laƙwas ga kanta da ƙeyarta duk ta gwabje da jikin motar, daga gefen goshinta har kumbura gurin ya yi.

Kai tsaye bai wuce ko'ina da su ba sai gidan Halifa yana yin parking da sauri ya sauka ya fita, Goggo bata iya komai sai ido da take binsa da shi tana kallan ikon Allah, yana zuwa bakin ƙofa ya kallin kwaɗon da aka rufe gate ɗin yasa baki ya fisgoshi memakon ya wurgar dashi sai kawai ya haɗiye, Cikin Gwaggo ne ya hautsine, nan take ta fara sakin fitsari jikinta na karkarwa.

Daga gurin da yake ya buga tsalle kamar ƙwallo sai gashi a cikin motar yana shiga ya fisgi motar ya wuce cikin gidan da gudu, wannan karan Goggo kan Inno ta faɗa saboda yadda ya fisgesu da ƙarfin gaske, yana shiga ya yi parking ya yi tsalle ya fito daga motar hanyar falon Nusaiba ya nufa yana dafe ƙeya haɗe da tura ciki gaba yana wata irin shakiyyar rawa, kamar wani ɗan ƙwaya haka ya dinga layi sai ya yi gaba sai ya dawo baya har ya shige gida. Goggo duk yadda taso buɗe motar abin yaci tura wayarta ta hango a cen gefe da sauri ta ɗauka ta kunna ta, sashen kira ta nufa tana danna labar tayi dace da lambar Halifa, bugu ɗaya taji an ɗauka.

Goggo ƙasa tayi da murya kamar me raɗa ta ce. "Dan Allah ko waye a layi ya gaggauta zuwa gidan Halifa ya ɗauke mu nida ƴar uwata" Halifa yasan dai Goggo magana take yi amma sam bayajin me take faɗa. Da sauri yace "Goggo ce? Yanxu kuna ina?" Goggo satar kallan ƙofar da Jariri yabi tayi cikin raɗa ta ce. "Halifa ba sanya zakuyi ba kuzo ku fitar dani dan ƴar uwata tuni nasan matambaya sun dafe ta" sai a lokacin Halifa yaji shima sai da yasa a speaker.

Da murnarsa yace. “To kuna ina yanzu zan zo” Goggo ta ce. “Gamu a gidanka idan kuka yi jinkiri nima sai dai ku ɗauki mushe dan Rakiya kam tuni tayi mushe” Halifa na jin haka ya katse wayar da murna ya fara sanarwa da mutanen gidan, Halifa da Adam ne suka taho gidansa.

Halifa na zuwa ya tarar da ƙofa a buɗe da sauri suka shiga gidan, Halifa na zuwa bakin motar ya sa key ya buɗe da sauri Adam ya zagaya ya buɗe murfin motar ya tallafo da ta jima a sume. Goggo na ganin an buɗe murfin motar ta fito da sauri ko bi ta kansu batayi ba ta nufi bakin gate da guje, Halifa ne ya biya yana kira ta waigo ta ce. "Har abada na bar salawaitun gidanka da motarka gwara na shiga duniya na yi mushe a hannun ɗan iskan salawaitun gidanka." Tana rufe baki ta bazama waje a guje Halifa ya rufa mata baya.

???????????????? KU TARO GOGGO KAR TA FAƊA SALAWAITUN RAYUWA A ƊEBE MATA ALBARKA

Ummou Aslam Bint Adam
[02/11, 19:22] Ameera Adam????: FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    19&20

Adam da ke riƙe da Inno gyara mata kwanciya ya yi a akan kujera shima ya rufa musu baya dan ganin an shawon kan Goggo, dan tun da tace bazata bisu a mota ba sun san ta zauna kenan. Halifa na ganin Adam na binsa ya wurga masa key yace. “Maza ka taho da motar, sai ka rufe gidan.”

Adam ɗaukan mukullin ya yi ya juya ya tayar da motar sannan ya fito ya koma ya janyo gate ɗin ya rufe ya zura sakata sannan ya shiga ta ciki ya buɗe ƙaramar ƙofar ya fito yana fitowa ya datse ta da ƙarfi.

Halifa bai taɓa sanin Goggo na da gudu haka ba sai da wannan tseren ya haɗasu, da ƙyar ya sha gabanta yana haki yace. “Goggo dan Allah ki tsaya kiji, yanzu idan muka koma gida babu ke me zamu cewa su Daddy?” Goggo itama mayar da numfashi take saboda tsabar gudu zaninta ya tattare ya koma kusan gwiwa, takalmanta duk sun shige wajen idanun sawunta kamar yadda yara suke zura ƙafafuwansu cikin igiyoyin takalmin. Sai da ta ja numfashi ta ce. “Halifa kasan Allah yau ko Ubanka Salisu ne yazo bazan shiga motarka ba, haka kawai hatsabibin yaro sai nuna mana salawaitun siddabaru yake yi. Kai bari ma kaji muddin muka koma gida ana yiwa Rakiya sutura zaka sakar mini jika” Goggo na zuwa nan ta fara ƙwallah tana cewa.

 "Allah sarki Rakiya ke kuma ta wannan hanyar tazo miki. Mutuwa kenan rigar kowa Halifa wallahi tsakanina da kai Allah ya isa da baka yiwa Nusaiba ciki ta haihu ba ai Ɗanka bazai kashe mini ƴar uwa ba. Kaico rayuwa zan idar da salawaitun tsautsayin da ya sameni ni ɗiyar me Salati." Haushi ne ya fara kama Halifa yace. 

 "To muje idan munje gidan duk abinda kika ga dama sai ki faɗa, amma wallahi idan sama da ƙasa zata haɗe ba wanda ya isa yasa na saki matata. Kuma karki ƙara yi mini Allah ya isa haka kawai tsofaffi kwata-kwata bakinku baya furta alheri." yana rufe baki Adam ya ƙaraso da motar ya kashe ta sannan ya fito ya zagayo gurinsu.

Goggo tana daga tsaye  ta faɗi daɓar irin zaman ƴan bori, hannu ta ɗora aka ta fara kuka kamar wata ƙaramar yarinya, Adam ne ya tambayi dalilin kukanta aikuwa kamar me jira ta kuma rushewa da kuka ta kalli Adam ta ce. "Adamu wai yau ni Halifa ya nunawa salawaitun iyakata. Ya nuna bani na haifi ubansa ba har yake yi mini salawaitun rashin kunya. Maza ka bashi mukullin motarsa ta tun bai rufeka da salawaitun duka ba ya ƙwaci abinsa" Adam yasan rikicin su sarai dafe kai ya yi ya ce. 

“Goggo dan Allah ki tashi mu tafi kinga mutane sun fara kallonmu…” A hassale ta katse shi da cewar.

"Adamu wacece ni a gurinka?" Adam a daƙile kamar zai yi kuka yace. "Wace ce kuwa ban Kakata" Goggo sakin baki tayi tana rafka salati sai da ta gama cikin ƙunci tace.

"Haka kake bawa Nadabo amsa dama, gatsal ba ladabi ni kake cewa haka kamar bani da wata salawaitun alaƙa da kai." Goggo ta rushe da kuka tana share majina da gefen zaninta tace.

"Allah na tuba dama wace salawaitun alaƙa garemu? Na san dai nina haifi Ubanka Nadabo bayan wannan sai me kuma? Dama nasan tsaf sai ka kwaso mugun halin uwarka dan wannan ba salawaitun halin Nadabo bane." 

Ana cikin haka ya hango Ɗan sahu da sauri ya tsayar da shi dukda Goggo ta ƙona masa rai yace. “To muje ga Adaidaita sahu nan na taro mana” alama ya yiwa Halifa yana miƙa masa mukulli.

Goggo ta yunƙura ta miƙe tana cewa. “Haka kawai da ka nacewa motar kamar gadon ubanka. Me ake da Halifa ni da Ɗansa ya kashe mini ƴar uwa wallahi har abada Halifa ka ƙara yi mini salawaitun magana sai na ɓalɓalce ka.”Halifa ƙwafa ya yi bai kulata ba ya shiga mota ya bata wuta ya barsu Goggo anata kiciniyar shiga Adaidaita sahu.

Halifa shi ya riga su Goggo zuwa gida lokacin da suka ƙarasa ana ta kiciniyar kwantar da Inno akan tabarma, Goggo na shiga taje gabanta ta fara matsar ƙwallah.

Ruwa Mommy ta ɗebo aka fara yayyafawa Inno a hankali ta fara buɗe idonta, cikin juyewar kai ta fara kallansu da suke tsaitsaye akanta. Ɗago hannuwa biyu tayi alamun roƙo tace.

 "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Annabi muhammadu bawansa ne kuma manzan sa ne. Saboda wannan ranar aka koyar da mun dan gudun ɗebe mana albarka. Salloli biyar basa wuce ni harda nafila da dai Hansai ce nasan bata cika ƙara farilla akai ba, Wa saumu ramadana har na alhamis da litin baya wuce ni."

KU DAGE DA COMMENTS NA CI GABA DA POSTING KULLIN KAMAR DA.

JAMA’A KUJE KU TAYA INNO AMSA TAMBAYOYI FA????????????????

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[06/11, 14:58] Ameera Adam????: FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    21&22


  Gabaɗaya ido suka zurawa Inno dake kwance tana ta sakin zance cikin gigita, Halifa na ganin haka ya ja guntun tsaki ya bar gurin saboda ya lura tsabar ruɗewa ce take damun Inno. Daddy ne ya russuna yace. "Sannu Inno ya jikin?" Inno wani marayan kallo ta bi Daddy da shi kamar bazata tanka masa ba zuwa wasu ƴan sakanni ta ce."Eh to, zakkar ce dai ban samu ikon fitarwa ba ƴan kadarorina basu kai a fitar da zakka ba, gonar bayan gidan Idi me saniya ce sai awaki biyu. A yanzu kam bakin alƙami na ya bushe amma da ana komawa da babu tantama Salisu zai bayar da zakkar a madadina" Goggo na jin haka ta ja da baya ta kife a gurin ta rushe da wani irin matsanancin kuka, gurin shiru ya ɗauka dan da alama kansu ya fara ɗaukan zafi.

 Goggo sharce hawayenta tayi ta ɗago ta ce. "Kai jama'a yau ina ganin salawaitin tashin hankali a gidan nan. Amma dai Allah ya tattaro salawaitun albarka ya kwashewa wannan hatsabibin jaririn, ku dubi yadda yasa akayi jinkirin kai Rakiya har matambaya sun dafeta tun daga gida. Wallahi bazan ɗauki wannan salawaitun rashin imanin ba wallahi sai dai hukuma ta rabamu, nikam ba zan yi salawaitun ja'inja da wancen hatsabibin ba amma wallahi yadda aka kashe mini ƴar uwa sai ankashe Halifa da Nusaiba har lahira" Juyowa sukayi suna kallon Goggo saboda yadda ta rikice musu ga Inno take ta zabgo surutai.

 Abba ne ya tsugunna gurin Goggo cikin lallashi yace. "Goggo dan Allah kiyi haƙuri kiyi shiru Inno fa ba mutuwa tayi ba rikicewa da tayi"

  Goggo wani kallon tsana take bin Abba da shi, saboda takaici rasa abin faɗa ta yi cikin takaici ta rufe Abba tayi da duka hannu bibbiyu ta ce. "Wallahi Na dabo da ba dan bakin Uwa kaifi gareshi ba da babu abin da zai hana in kwashe maka salawaitun albarka ba ka ɓalɓalce kowa ya huta." Abba tashi ya yi yana ƙara bata haƙuri amma Goggo ko ta kansa bata bi ba tana cewa.

 "Wallahi Na dabo ko kaine akan Rakiya sai hukuma ta rataye ka bare Nusaiba, yadda Ɗansu ya kashe mini ƴar uwa sai anhukunra su." ta ci gaba da kuka sannan ta ce. "Sai dai idan kuɗi zaka bayar a sake su amma ko cikin dare ne sai na bi na datse igiyoyin numfashinsa." 

   Babau wanda ya tankawa Goggo ana cikin haka Family Doctor ɗinsu ya shigo hannunsa ɗauke da kayan aiki, da sauri suka tare shi suna yi masa barka da zuwa. Yana zama ya buƙaci da su ɗan basu guri saboda yana buƙatar ya dubata cikin nutsuwa, Goggo ƙaddabe ƙasa tayi akan babu inda zata sannan ta baɗe shi da maganganu.

“Kai yaro dube ni da kyau karka nuna mini salawaitun cin mutumci ido biyu, wanne ha’incin ne basu iya ba iye? Gaya mini meye bakwa yi salan na fita ka cicciri sassan jikin ƴar uwa saboda salawaitun rashin imani. To wallahi kurwar ƴar uwata kur…” Abba ne ya katse ta ya cewa. “Haba Goggo wannan fa likita kuma shi ne fa yake kula da mutanen gidan nan babu wani abun cutarwa da zai…” a hassale Goggo ta ce. “Kai Na dabo ka saurara mini wallahi bar ganin ka tara abin duniya ka yi mini salawaitun duniyanci kar nake kallanku sakarkaru.” Dr Muhsin ne ya kalli Abba yace. “Barrister ka ƙyale ta babu damuwa.” Goggo ta bishi da harara tana yin ƙwafa.

  Abba da Daddy kan kujera suka koma suka zauna Dr Muhsin ya matsa gaban Inno da ke kallonsu da shanyayyun idanuwanta, a hankali ya fara gwaggwada ta yana dubata sannan ya saka mata tare da allurar bacci, ba'a ɗauki lokaci ba bacci ya yi awon gaba da Inno ta fara sauke wahalallen numfashi.

  Dr Muhsin ya fara tattara kayansa da niyyar haɗa su kafin ya yiwa su Daddy bayanin abin da yake damun Inno da halin da take ciki, Goggo na ganin haka da sauri ta shaƙo wuyansa katamau tana cewa.

 "Alƙur'an babu inda zaka je. Baza ka tafi ko'ina ba sai sai ƴar uwata ta tashi" Dr Muhsn cikin wata irin murya yace. "Baba lafiya me nayi miki ne?" Kafin Goggo ta yi magana Daddy da Abba sun taso kan su Goggo cikin tsananin jin kunyar Dr suka fara magana.

"Haba Goggo dan Allah meye haka kike yi yanzu abin da kikayi kin kyauta kenan?" Daddy ya ƙarasa faɗa yana ƙoƙarin ɓamɓare hannun Goggo daga wuyan Dr Muhsin. Goggo ban da nishi babu abin da take yi saboda yadda ta taƙarƙare ta sa ƙarfi ta maƙure Dr Muhsin, Shi kuma kawaici ya yi ganin Mahaifiyarsu da Daddy ce kuma ga girma dan bazai iya hankaɗe ta. Da ƙyar da siɗin goshi suka cire hannun Goggo daga wuyan Dr Muhsin. Ana cire hannunta Dr Muhsin ya yi caraf ya miƙe ya yi gefe yana maida numfashi.

 A gagguce ya fara musu bayani dan ba ƙaramin shaƙa ya sha a hannun Goggo ba.

"Barrister ba wani babban ciwo bane yake damunta ta ɗan shiga firgice ne na ɗan wani lokaci, amma da zarar ta tashi daga bacci zata koma normal. Akwai magungunan da zata dinga sha zan rubuta musu sai a siyo mata, kar a dinga yawan barinta ita kaɗai saboda kar ta dinga yawan tunani.

 Yana gama faɗa ya fice daga falon ko waiwaye baya yi, Goggo miƙewa tayi ta ƙarasa gaban Inno da take bacci tana ƙarasawa ta share hawayenta a hankali ta ce. "Allah ya baki salawaitun lafiya Rakiya" Daddy da Abba babu wanda ya tanka mata gabaɗaya suka fice daga falon.

Inna sai da ta shafe sama da awa huɗu tana bacci sannan ta farka, tana farkawa a cen gefe ta hango Goggo tana ta zabga gyangyaɗi a hankali ta ce. “Hansai” da sauri Goggo ta buɗe ido aikuwa tana ganin Inno ta tashi zaune ta fara yekuwa a cikin falon, nan da nan mutanen gidan suka ɗauko zuga suka shigo falon.

Tana hango Nusaiba da Halifa ta miƙa hannuwa biyu ta ce. "Ku matsa wallahi karku ƙaraso mini idan ba haka ba sai na ɗebe muku albarka duk kun ɓalɓace." Kallan kallo aka fara yi kowa yana kallan ɗan uwansa babu wanda ya fahimci ga da wanda take. A hassale Inno ta ce. "Halifa wallahi ko a lahira na ganku a kusa da ni saina ɗebe muku albarka." Halifa baya ya ja a hassale ya ruƙo hannun Nusaiba zasu fita. Nusaiba ta marairaice fuska ta ce. "Hubby karka biyeta kasan rikici irin na su Inno" Inno na jin haka ta ce. Uwarki ce me rikici sakarya maras ɗa'a kai Salisu wallahi idan baku dakatar da su Halifa ba zan bar muku gidanku na shiga duniya dan na Allah basa ƙarewa." Goggo tayi karaf ta ce. "Wallahi ƙafa ta ƙafarki dan ba zan zauna ganin salawaitun rashin ɗa'a da cin mutumcin da za'a yi wa ƴar uwa ta ba."

 Halifa da sauri ya fisgi hannun Nusaiba suka fice daga ɗakin yana huci ya wuce falon su Hajiyansa.

 Bayan kwana biyu jikin Inno ya dawo dai-dai kuma Halifa da Nusaiba sun dawo gida gabaɗaya da zama saboda Inno da Goggo sun ce Allah ya kashe su bazasu ƙara zuwa gidansa su zauna ba, Kuma tun daga ranar babu wani abun firgici da suka ƙara gani. Ana gobe suna gidan cike yake da baƙi daga ɓangare daban-daban, Kayan miya a sayo da kayan abinci kala-kala na ƴan suna. Kayan drinks da kayan gift ɗin da za'a bawa ƴan suna.

Da daddare bayan sallar isha"i Hajiyan Halifa ta shiga cikin store, tana shiga kamar almara ta hango ɗan dunƙulallen mutum ya juya bayansa. A gaban kabewa ta hangoshi ya zage iya ƙarfinsa sai gwaguyar kabewa yake, jikinta na tsuma ta ja gefe banda karkarwa babu abin da take ji, Jariri na jin motsinta ya juyo hannunsa ɗaya ɗauke da rabin ƙatuwar kabewa, da sauri ya fara takowa yana tafe yana tura ciki gaba yana wata rangwaɗa. Yana zuwa gabanta ya fisgota da ƙarfi har ta kai ƙasa, kabewar hannunsa ya miƙa mata cikin wata irin murya yace. "Ungo zauna ku sha tare" Jariri ɗuk abin da ya gani ya ɗauka ya ci idan ya rage sai ya wurgowa Hajiyan Halifa yace ta cinye. Fakar idonsa tayi ta miƙe saɗaf-saɗaf ta fice daga store ɗin, har ta  kusa shiga babban Falo ta Jariri ya ta ho da gudu ya cafko zaninta, Hajiyan Halifa iya ƙarfinta ta zage ta fara kwarara ihu. Jariri bai fasa ba har sai da ya ga ya fisge zanin jikin ta.

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[06/11, 16:06] Ameera Adam????: FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    23&24

Hajiyan Halifa na ganin ya fisgi zaninta daga ita sai ɗan fatarin ciki ta miƙe ta shiga cikin falon, da sauri tafi da gudu ya cafko siket ɗinta yana niyyar fisge shi shima gabaɗaya. Da ƙyar ta saau tayi ta maza ta hamɓare shi da ƙafa ta samu ta shige cikin Ɗaki, Daddy na zaune ya ga shigowarta da sauri ta banka ƙofar ta rufe. Daddy da mamaki yake kallonta yace. "Mommyn yara lafiya me yake damunki?"

Mommy dake sauke haki ta ce. "Wallahi aljani ne ba mutum ba jaririn Halifa aljani ne da idona naga yana cin Kabewa" zaro ido waje Daddy ya yi yace. "Jariri kuma? Wai me yake faruwa ne ke kince Jariri su Inno sun ce Jariri wai kaina fa ya kulle" Mommy ta ce. "Wallahi nima na gani da ido na, dubi fa har zani ya cire min Allah me kaɗai yasan abin da ya yi niyyar aikata mini, wallahi kamar wacce zai haikewa haka naga yana ƙoƙarin farmaka ta."

murmushin takaici Daddy ya yi yace. "Dan Allah ki daina faɗar haka karma wani yaji, kema ruɗa kanki zakiyi ne kamar yadda su Inno suke gigita kansu, wannan zancen banza ne dan Allah wuce ki ɗau zani ki ɗaura Allah yasa ƴaƴanki basu ganki a haka ba." Mommy ta ce. "Amma fa..." Ya katse ta. "Amma me?" ki wuce ina da abin yi banasan jin wani abu." Cikin ƙunan rai Mommy ta wuce tana ƙwafa dama tasan idan zata kwana tana faɗa bazai yarda ba.

 Cikin tsakiyar dare Daddy ne zaune a falo ya jona laptop yana wani aiki, gidan shiru babu motsin komai sai ƙarar keyboard ɗin laptop ɗin da yake dannawa. Yana nan zaune yaji an jefo wani abu da ƙarfi, yana waigawa yana ƙafafauwan ragon guntulallu da jini yaɓe-yaɓe a jikinsu, da sauri ya zaro ido cikin mamaki yana ture Laptot ɗin gefe.Yana ƙoƙarin tashi ya takun tafiya ƙwas ƙwas ƙwas yana kallon bakin ƙofar yana Jariri hannunsa saɓe da kan rago ya rungumo shi gigin-gigin kamar zasu faɗi tare, Jikin Daddy ne fara ɗaukan tsuma yana yunƙurin tashi ya ga Jaririn ya datse ƙofar falon sannan ya sunkuyo da kan ragon yana lasar jinin da ke ɗiga daga jikin kan ragon.

Daddy ja ya fara yi da baya yana karkarwa da sauri Jariri ya wurga masa kan ragon yace. "Ungo tayani ci tunda da kai muka haɗu." Daddy kallan kai ragon ya yi yaga anyi masa ɓuloli ta ko'ina, tsugunnawa Daddy ya yi yace. "Dan Allah ka yi haƙuri ka mun rai bazan iya cin ɗanyan nama ba." Jariri kallan tsaf ya yiwa Daddy yace. "To cire rigarka" ba musu Daddy ya tuɓe rigarsa daga shi sai gajeren wando kuma har lokacin jikinsa sai ɓari yake." Jariri yace. "Wallahi ko ka ɗauki kan rangon kaci ka na saɓa kamanninka" Daddy ya tsaya yana kallon Kan jaron sunan da aka siyo na jaririn da za'a yanka, a zuciyarsa ya ce. "Ina ɗayan ragon badai shima ya cinye shi ba, ashe dai maganar su Inno a hanya take?" Jariri kamar yasan abin da yake zuciyar Daddy yace.

"Na cinye ɗayan ragon da kuka siyo ba dan ni kuka siyo ba? To wannan kai zaka cinye shi." Daddy yayi tsumu yana zare idanu, Jariri na ganin haka ya nufi gurun da Daddy ya jona laptop ɗinsa ya fisgo chager, riƙewa ya buga tsalle ya ranƙwalawa Daddy kan cazar a kansa da ya sha ƙwaryar molo. Daddy durƙushewa ya yi a gurin yana lailaya kai cikin azaba, bai yi aune ba yaji Jariri ya kuma rankwala masa a kai.

Cikin tsananin azaba Daddy ya dafe kai yana cewa. "Wayyo Allah jama'a ku cece ni zai kashe ni" Jariri tsalle ya buga ya dira a kan tumbulelen tumbin Daddy ya fara sukuwa a kai, Daddy tun yana iya roƙo har ya fara kasa magana. Jaririj ɗaga shi ya yi, ya koma kan kujera ya zauan. Wani tsoronsa ne ya ɗarsu a zuciyar Daddy saboda wahala ko motsi ya kasa yi. Daga gurin da yake Jaririn yace.

 "Tashi tsaye" Daddy jiki na ɓari ya yunƙura da ƙyar ya tashi kansa har yayi ƙullutu biyu gurin da Jariri ya ranƙwala masa kan caza. Daddy na tsaye Jariri yace. "Maza kayi mini rawar Ɗan maliyo maliyo" Daddy hawayen wahala yake yi yace. "Ranka ya daɗe wallahi ban iya ba" yana rufe baki Jariri ya diro ƙasa ya dafe kai da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya dafe ƙugu da shi, turo ciki gaba ya fara yi idan ya yi taku ɗaya sai ya tura baya har wata rangwaɗa yake yi yana cewa. "Ɗan maliyo maliyo, maliyo. Ɗan maliyo nawa, Maliyo." idan yace maliyo sai ya dafe ƙeya ya girgiza ciki.

Yana gamawa yace. "Maza kayi irin rawar da nayi yanzun nan" Daddy hannunsa biyu yasa ya riƙe ƙugu yana yana cewa. "Ɗan maliyo maliyo, maliyo." 

(???????????? Mai karatu ka harsaso min muryan Daddy yana waƙar ɗan maliyo maliyo)

Jariri na jin haka ta ja guntun tsaki ya fisgi cazar laptop ɗin ya ƙara ranƙwala Daddy a ka yace. "Haka nace masa hannuwa biyi zaka riƙe ƙugu da su? Ba hannu ɗaya a ƙugu ɗaya a ƙeyar ka zaka riƙe ba." Daddy kuka yake shaɓe-shaɓe ya miƙe ya ci gaba da dafe ƙeya yana tura tumbi gaba yana waƙa.

Sai da ya jima yana abu ɗaya har ya galabaita banda gumi babu abin da yake yi, Jariri ya dakatar da shi sannan yace. "Yanzu kuma rawar salawaitun salo zamuyi" A wahalce Daddy yace. 

 "Dan Allah ka yi mini rai" Jariri yace. "Ai mun dinga rawa kenan dana yanzu har wayewar gari kuma wallahi duk wanda ka gayawa yadda na gwaguye kan ragon cen haka zan yi maka" Daddy ya hau muzurai yana raba ido wannan karan hawaye sharara yake yi.

Jariri ya miƙe tsaye ya tale ƙafarsa sannan ya sunkuya yace. "Ka ga yadda na yi?" Daddy ya gyaɗa kai. Jariri yace. "Maza kayi haka" ba musu Daddy ya sunkuya kamar me ruku'u sannan ya tala ƙafafauwa, Jariri ya dinga gyaɗa kai daga sunkuye yana ya dafe kwankwaso yana kaɗawa. Daddy na ganin haka ya basar aikuwa Jariri ya ɗago  ya buga masa ƙafa a baya, sai ga Daddy ya tafi  ta ka ya faɗi rigijib. Jariri yace. "Maza-maza ta shi mu ci gaba" Daddy ya tashi ya yi yanda Jaririn ya yi sannan suka fara waƙar salawaitun salo.

 Daddy yana kuka rera waƙar . "Salawaitun salo"  ana cikin haka sai ji kake kiriff Daddy ya kife a gurin.

KUYI HAKURI DA ERRORS BANYI EDITING BA

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[10/11, 09:39] Ameera Adam????: FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    25&26


   Jariri na ganin haka ya tuntsire da dariya harda riƙe ciki, zage Daddy ya ci gaba da yi yana ci gaba da waƙar Ɗan maliyo maliyo. Sai da ya gaji dan kansa sannan ya yi tsalle ya dira akan ruwan cikin Daddy yana cewa. "Kaji tumbuloƙoƙo tumbul-tumbul" baka jin ƙarar komai sai sukuwar Jariri akan ruwan cikin Daddy, yana sauka ya je ya ɗauko kan ragon ya ɗora a cikin Daddy ya janyo hannuwan Daddy ya ɗora akai sannan ya buɗe ƙofa ya yi tafiyarsa.

Da asuba Inno ce ta fara tashi har tayi alwala ta ce. "Kai anya Salisu ya tashi kuwa na ji shiru kamar masu baccin mutuwa banda rashin ɗa'a sallar asuba abar wasa ce, idan mutum bai so yake a ɗebe masa albarka ba a shiga jam'i yana kwance." Dada ɗaya daga cikin ƙawayen su Inno ne da suka zo suna dan ɗakin Inno cike yake da ƙawayensu tsofaffi wasu ma sun daɗe basu haɗu ba. Dada tayi caraf ta karɓe zancen.

“A’a Rakiya kika sani ko bai dawo daga masallaci bane?” Goggo da tashin ta kenan ta riski maganar ta ce. “Gaskiya Salisu bai tashi ba ai baya taɓa tafiya masallaci sai ya yi salawaitun bugo ƙofa.” Inno fuuuu ta nufi bakin ƙofa kamar wacce aka dakatar da ita ta dawo ta ce. “Bari dai nayi tawa sallar kar na rasa jam’i na ɓalɓace dan wannan ba halin ɗa’a bane” Sallah suka gabatar ko carbi basu ja ba suka ji daga falo Mummy na rafka salati cikin kukan.

Inno cikinta har karkarwa yake ta ce. “Shikenan ni dama nasan ruwa baya tsami banza. Wallahi Salisu bai taɓa yi mini rashin ɗa’ar nan ba” da sauri suka fice har suna gware da junansu, suna zuwa Falo kowa ya yi turus dafe ƙirji suka yi suna ja da baya ganin abin da yake faruwa. Inno da Goggo cikin haɗin baki suka, “Wallahi shi ne” Mummy da ke ta kuka tana jijjiga Daddy ta ce. “Inno shi wa?” Inno ta ce. “Jariri wallahi ba kowa zai yi wannan rashin ɗa’ar ba sai shi” kafin Mummy tayi magana Goggo ta sheƙawa Daddy ruwan da ta ciko a cikin kantamemen kofi. A zabure ya sauke ajiyar zuciya sannan ya miƙe ya sunkuya ya dafe ƙugu yana cewa. “Salawaitun salo, salawaitun salo…” gabaɗaya sakin baki suka yi suna kallon ikon Allah Goggo ta ce. “Yau ni nake ganin salawaitun rayuwa Salisu wani sabon salon salawaitun ka samo haka?” Sai a lokacin Daddy ya ɗago ya kallesu sannan ya koma daɓar ya zauna ya fashe da kuka yace. “Inno ku taimaka wallahi zai iya kasheni” Inno ta dafe ƙirji ta ce. “Wa?” Daga wajen bakin ƙofa suka ji ance. “Ni ne nan…” tun basu gama jin abin da Jariri yake faɗa ba gabaɗaya zabura a guje kowa ya yi ta kansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button