JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

Inno ta ce, “Au Halifa haɗani zakayi da Ubangiji na? Wallahi ba dan Allah ba da adaren nan zan tafi kowa ma ya huta, tunda banida kowa babu mai ƙaunata.” Goggo ta fara matsar kwallah ta ce.” Rakiya karki mun haka saboda Allah idan kika shiga gari ina na kama ina zani wa nake da shi? Mu biyu kaɗai fa muka rage kema in kika tafi ya zanyi?” Inno ta taɓe baki tayi ta ce.

“Hansai dama wace alaƙa garemu? To nasan dai uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya bayan haka fa? Da kinsan da haka kina ji Halifa na kwashe mun albarka kikayi shiru saboda rashin ɗa’a. Wallahi kunci daraja ɗaya amma zuwa safiya zanga uban da zai hanani tafi” Ta ƙara matsar kwallah ta ce.

“Dama nasan Nusaiba ba ƙaunar zamana take ba waya sani ma ko ita ta turo ɗan ta ya tsorata dan na bar gidan jikana” Nusaiba zatayi magana Halifa ya ɗaga mata hannu yace.

“Inno yanzu koma dai meye kiyi haƙuri badai Daddy kike so a kira ba? To Allah ya kaimu safiyar duk abin da kike so za’ayi.” Inno ta ce “Shikenan Allah ya kaimu kuma wallahi tas a kunnensa duk ɗiban albarkar da kuka yi mun” tana gama faɗa ta koma ta kwanta.

Goggo ma ta koma ta kwanta Halifa ya ƙarasa bakin gadon Nusaiba yana shafa jaririnsu cikin so da ƙauna, Goggo ta ɗago ta tafa hannu ta ce.

“Halifa wata sabuwar salawaitun fitsarar zaka yi wa ƴar mutane a gabanmu, wallahi a hir ɗinka fita ka bamu guri ba nace maka yarinyar nan haramiyarka bace har sai tayi arba’in.” Halifa tsaki ya yi zai yi magana Inno ta ɗago ta ce.

"Halifa wannan jarabar har ina kai amma gaskiya albasa batayi halin ruwa ba, lokacin da uwarka Halima ta haifeka sai da ta yi wata biyu cir a gidansu, zaka fice daga ɗakin nan ko sai na ɗebe maka albarka kowa ya huta?" Halifa kamar ya yi kuka saboda takaici Nusaiba zatayi magana ya mata alama da ido, cikin takaici ta gyara kwanciyarta ta kwanta Halifa ya fice yana ƙunƙuni.

Washegari da sassafe Inno ta fito falo ta fara ƙwalawa Halifa kira, cikin bacci Halifa ya fara jiyo muryar Inno na kiransa. Guntun tsaki ya yi ya ƙara jan bargo ya rufa bai yi aune ba yaji ta fara buga ƙofarsa da ƙarfi tana cewa.

“Halifa ka kira mun Ubanka kace ina nemansa maza-maza yazo” Halifa ba yadda ya iya ya fito fuska a tsuke ya karɓi wayar Inno ya nemo mata lambar mahaifinsa ya kira.

Inno na jin an ɗauka babu ko sallama ta ce, "Salisu dan Allah maza kazo gidan nan ga ɗan ka sai tijara yake mun tun tsakar dare, kazo ka bi mun haƙƙina dan maganganun da ya gaya mun ƙiris ya rage ciwon zuciya ya kama ni, wallahi ko maƙiyina bana fatan a gaya masa kwatankwacin abin da Halifa ya gaya mini" daga cen ɓangaren Daddy ya ce.

“Gaskiya bai kyauta ba amma kiyi haƙuri Inno me ya faɗa miki inyi masa faɗa” Inno ta saki baki ta kalli Halifa cikin ƙufula ta ce.

"Allah ya tsinewa faɗan da zaka yi masa Salisu" nan take ta rushe da kuka ta ci gaba  da cewa. "Yanzu duk ɗiban albarkar Ɗanka ya mun a iya faɗa kawai zaka yi masa saboda rashin ɗa'a. Kayi zamanka na yafe dama na lura ba ƙaunata kake ba kafisan Ɗan akaina, wallahi daga yau Salisu ko a mafarki kar inƙara ganinka a gaba na. Ƴar uwata Hansai ta isheni rayuwar duniya dama tare kuka ganni da ita, Allah na tuba dama wacce tsiyar kuke bani. Ƴar uwata dama ita ce rufin asirina"

Daddy yace. “Ayi haƙuri gani nan zuwa yanzu…” Inno bata jira ƙarashen zancen ta ba ta kashe wayar. Halifa na tsaye ya cika fam banda harara babu abin da yake aika mata.

Inno kallan sa tayi sheƙeƙe sai kuma ta wuce kitchen ta ɗauko muciya, dai-dai ƙafafuwan Halifa ta zauna ta ajiye muciyar tace. "Idan baka mun duka ba ka raina ubanka Salisu kuma wallahi bari ya zo gidan nan a gaba na sai na sa ya kwashe maka albarka kowa ya huta" Halifa ya ja dogon tsaki yace.

“Wallahi bari Daddy yazo bazan iya ba dama kece dolensa, haba wannan wane irin abu ne tun farar safiya ki addabi mutane” ya ƙarasa faɗa yana wucewa ɗaki. Inna baki sake tabi bayan Halifa ta ce. “Wallahi zaka maimaita a gaban ubanka bari ya zo.” miƙewa tayi ta wuce kitchen zata ɗora ruwan shayi.

Bayan ta dafa shayi ƙatuwar tukunyar farfesun kaji ta ɗauko da niyyar dumamawa, amma sai jin tukunya tayi fayau. A razane ta buɗe tukunayar farfesu yace ɗauke ni inda kika ajiye, babu abinda ta gani sai taunannun ƙashi da romo ɗan kaɗan. Ture tukunyar gefe tayi ta fito ta rafka wani uban salati, gabaɗaya suka Fito hankali a tashe. Inno kallan Goggo tayi ta ce, "Oh ni jikar mutum huɗu yanzu Hansai ki rasa me zaki aikata sai wannan ɗiban albarka da nuna halin rashin ɗa'a" Halifa fuska ba walwala yace.

“Me ya faruwa kuma” ƙanƙance ido Inno tayi ta ce. “A hir ɗinka da shiga tsakanin zumunci, mara ɗa’a bada kai nake ba. Idan kuma na ƙara jin bakin ka wallahi sai na kwashe maka albarka, sai idan Ubanka yazo duk abinda zai yi ya mun” tana gama faɗar haka ta wuce kitchen ta ɗauko tukunyar kajin da ƙarfi ta direta a gurin ta ce. “Duba mun nan kajin da ka kawo jiya da yamma gasu nan Hansai ta cinye.” Gabaɗaya zaro ido waje sukayi Halifa cikin mamaki ya ce. “Kaji biyar ɗin dana kawo jiya sune aka cinye tashi ɗaya.” Goggo rushewa tayi da kuka ta fara ƙoƙarin ɗauko wayarta da ke cikin kajarta, tana ɗaukowa tace. “Halifa maza kara mun Uban yarinyar nan” Halifa jiki ba ƙwari ya karɓa ya nemo mata lambar mahaifin Nusaiba, yana ɗauka Goggo ta ce.

"Nadabo duk abinda kake yi maza ka bari kuma ka taho da hukuma wallahi me rabani da Rakiya sai kotu tunda ni zata laƙawa sharrin maita."

Yawan comments yawan typing ɗin ku. Har yanzu ƙofa a buɗe take ga masu san siyan littafin ANYA BAIWA CE? karku bari a barku a baya.

UMMOU ASLAM BINT ADAM

FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

ANYA BAIWA CE?

         Na

AMEERA ADAM

LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI.

FREE PAGE 2

      Da daddare Bayan sallar Isha'i Jakadiya ce tafe tana lalube har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama, da sallama ta shiga  ta russuna tana cewa, " Barka da hutawa Uwar ɗakina ance kina san ganina yanzun nan " 

 Fulani Maryama dake tsaye hannunta ɗauke da  Salman miƙawa Jakadiya shi tayi ta ce, " Jakadiya inasan muyi tafiyar sirri kamar yanda muka saba da ke a shekarun baya, ayau basai gobe ba zamu kai ziyara ga Boka Marduska, saboda bazan iya kwana da maganar da kika sanar da ni ba, batare na nemi mafita ba " 
  Riƙe Salman Jakadiya tayi tsam kamar wani zai ƙwace shi sannan ta ce, " Duk abinda kika ce haka za'ayi, bani da ikon bijirewa umarninki, da kai da kaya duk mallakar wuya ne " 

    Fulani Maryama na gama jin haka ta juya ta shiga cikin ɗakinta, cen ƙasan adakarta ta buɗe ta ɗauko wani kurtu tasa hannu ta ɗebo waɗansu irin wuri guda biyu da wani ɗan ƙaramin zobe, maida kurtun tayi sannan ta dawo gurin da tabar Jakadiya ke tsaye.

  Miƙawa Jakadiya Wuri ɗaya tayi sannan ta fara karanta waɗansu irin ɗalasiman tsafi, ba'a ɗauki lokaci ba sai wani haske ya mamaye gurun atake suka ɓace daga cikin ɗakin.

   Tsaye suke abakin wani kogon dutsen dake cikin wani surƙuƙin daji mai matuƙar duhun gaske, Fulani Maryama runtse idanunta tayi ta fara ƙwalawa bokan kira har sau uku, " Marduska! Marduska!! Marduska!!! " tana gama faɗa ta buɗe idanunta.

   Ji sukayi ankece da wata mahaukaciyar dariya sai da aka ɗan ɗauki lokaci anayi sannan aka tsagaita, sannu a hankali haske ya mamaye gurin, cikin wata irin murya aka fara basu umarni, " Ku sanya ƙafafunku cikin waccen ƴar ƙoramar sannan ku tako ku shigo ciki.

 Kamar yanda aka gaya musu haka suka bi umarnin mai magana sannan suka shiga cikin kogon dutsen, daga cen nesa suka hango shi zaune akan buzun damisa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da gashi tamkar ba bil Adam ba, Fulani Maryama na gaba Jakadiya na biye da ita a baya.

    Zama sukayi sannan Fulani ta kalli bokan zata fara magana ya ɗaga mata hannu sannan ya kuma kecewa da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana,

    " Ai duk wanda ya bamu iska dole kwaɓarsa tai ruwa, Maryama kin ɗauke mana ƙafa na wasu shekaru sai da buƙatarki ta tashi zaki waiwayo mu " 

  Fulani Maryama ta russunar da kai ta ce, " A gafarceni sarkin bokayen duniya, nayi kuskure awancen lokacin amma yanxu baza'a sake ba " 

   " Na amshi tubanki kuma nasan abinda yake tafe dake, kalli nan " ya janyo wata ƙwarya mai cike da jini yana nunawa fulani.

   Tana leƙawa Fulani Zaliha ta gani kwance akan gadon ta tana baccinta hankali kwance, jinjina kanta tayi ta cewa Murduska, " Ya babban boka sarkin bokayen duniya so nake a salwantar da cikin da ke jikinta inda hali ma akashe su gaba ɗaya, domin bayan Salman bana san kowacce matar sarki ta sake haihuwa acikin su saboda bansan gaba mai zasu haifo ba kuma bansan mai hakan zata haifar ba " 

Ƙwala-ƙwalan idanunsa ya kafe ta dasu yana ce, " Daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi, badan kinzo ayanxu ba da tuni sauran damar data rage miki ta ƙare gaba ɗaya " A zabure Fulani Maryama ta ce, " Ban fahimce ka ba Marduska "


 Wani mudubin tsafinsa ya ɗauko yasa wata jelar ɓauna dake hannun sa na hagu cikin ƙwaryar ya yarfawa mudubin, inuwar wani ɗan ƙanƙanin Yaro ce ta bayyana na ɗan wani lokaci sannan ta ɓace, maida mudubin yayi gefe sannan ya maida kallonsa ga Fulani Maryama ya ce, " Alƙalami ya riga da ya bushe, duk duniya babu wani ko wata da zai iya dakatar da cikin jikinta har sai ta haifeshi, Zata haifo Ɗa namiji Mai kama sak da Mahaifinsa kuma koda baki ci wannan Alwashin ba haihuwa ta dakatawa Sarki Aminullah, duk wacce kika ga ta kuma haihuwa sai dai in wani ne  mahaifinsa ba Aminullah ba " 

 Cikin damuwa Fulani Maryama ta ce, " Yanxu babu wata mafita da zaka bani ya Shugaba na?? " 

 Wani Allon jar ƙasa ya ɗauko ya jingine ya na faɗan waɗansu irin kalmomi, yana watsa wani tafasashen jini dake cikin wani ƙoƙon kan Ƙwarangwal, yana cikin haka baiyi aune ba sai gani sukayi Allon jar ƙasa ya ruguje wani irin hayaƙi mai wari na fita daga jikinsa.

  A tsorace gaba ɗaya suka ja baya Marduska ba ƙaramin tsorata yayi da ganin faruwar haka, cikin yanayin firgici ya fara magana, " Tabbas Ruhin wasu ababen hallita na katange da shi, idan na matsanta halaka shi ba mu ba hatta Aljanun da suke taya ni aiki sai sun halaka, maganin kar ayi kar afara inba haka ba wanda baiji bari ba yaji woho " 

   Fulani Maryama jikinta ne ya gama sanyi amma duk da haka zuciyarta bata karaya ba ta ce, " Marduska abar batun Halaka shi tunda ni kaina ganau ce ba jiyau ba, amma bayan haihuwar sa ba damar a aiwatar da wani aiki akansa ko a nakasa shi? " 

 Matsawa yayi bakin wutar dake ci ya ɗebo wani garin magani mai haɗe da garin naman mage da haƙoran jemage ya zuba aciki, take wutar ta kuma tashi sama sannan wata ƴar ƙaramar ƙorama ta bayyana aciki, daga cikin ƙoramar wasu litafan tsafinsa ya ɗebo guda biyu ja da baƙi, baƙin ya fara jefawa cikin wannan jinin dake cikin ƙwarya sannan ya zura kansa yana karewa Ƙwaryar kallo dake ta zaɓalɓala.

     Sai da ya gama kallo tsaf sannan ya ɗago da kansa da yayi gumi sharkaf ya fara mata bayani, " Tabbas cikin biyun za'a iya gudanar da ɗaya amma biyun bazasu iya wanzuwa akanshi ba, zamu iya nakashi ta kowacce siga haka nan zaki iya sawa a fitar dashi daga cikin masaurautar, amma shi ne kuskuren da zaki fara tafkawa a rayuwar ki, domin kuwa ta wannan silar dukkan asiran da kika binne za'a binciko domin kuwa allura ce zata tono garma"

  Fulani Maryama harta fara jin daɗi ƙarshen maganarsa ya sa ta shiga damuwa, kallansa tayi cikin rashin fahimta ta ce, " Bangane mai kake nufi ba? " mayar da ƙwaryar yayi cen gefe ya ce, " Abinda na gani kenan zaɓi ya ragewa mai shiga rijiya..., kowanne zaɓi kika ɗauka yana da nashi ƙalubalen da zaki fuskanta ki nutsu da kyau ki saurare ni inba  haka ba zakiyi gudun gara ki faɗa gidan zago " 

   Jakadiya dake gefe tayi tsuru sai raba idanu ta ke cikin zuciyar ta ta ke faɗin, " Lallai Fulani Maryama kema ba ƙaramar makira ba ce, amma ajuri zuwa rafi..., Ay bahaushe ya ce inzaka gina ramin mugunta gina shi gajere, amma lallai wannan Ɗa na Zaliha ya zama kainuwa dashen Allah, wata ƙila shi ne zai zama magajin mulki muga ta tsiya, dama ance kayun Ɗan ƙwarai ya gaji Ubansa " 

   " Ina sauraren kowacce kalma da zata fito daga bakinka kuma kowacce zan saka ta amazaunin da ta da ce " Fulani Maryama ta faɗa.

 Miƙe ƙafafunsa yayi da gaba ɗaya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani, " Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da za'a zuba masa a ruwan wanka ina nufin wankansa na farko a duniya kuma ko yaya ne asamu a bashi wannaa maganin ya sha, sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Naƙuda zaki turara mata, karki bari yaro ya faɗo ba tare da kin turara shi ba, to idan kika yi haka bazai iya gani da idanunsa ba, har tafiya da magana ke komai da kika sani sai dai ayi masa, saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda za'a furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa " 

  Murmushin jin daɗi Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata, " Sai dai akwai sharaɗin da zaki kiyaye,  akwai ruhin wata da na gani tana jingine da shi, zata  shigo cikin gidan masarautar ku tana ƙasƙantacciya muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar, abubuwa marasa daɗi zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi suka haɗa ido, a ranar aljanun dake riƙe da ƙafafunsa zasu tarwatse alƙadarinsu zai karye, idan kika yi sake ta ɗau wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke riƙe da bakinsa zasu gushe zai fara magana, sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba ƙyaƙyƙyautawa kamar zai amayar da ƴan hanjinsa, hakan zai ɗaga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi, amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru "

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[11/10, 17:23] Ameera Adam????: ☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️

{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    5&6


Daga cen ɓangaren Mahaifin Nusaiba yace. "Subhanallah Goggo lamarin har yayi tsamari haka? Me zai hana ku daidaita ina Halifan?" Goggo ta ce. "Na rantse da Allah Nadabo sai anbi min haƙƙina ni za'a kawowa sabon salawaitin cin mutumci daga nazo gidan jikata" Abba yace. "To kiyi haƙuri Goggo insha Allah anjima zan zo" a hassale Goggo ta ce. "Idan har sai anjima zaka zo ka bari Nadabo na yafe tunda kai baka damu da martabar mahaifiyarka ba, zan tafi gurin hukumar da kaina ai na Allah basa ƙarewa tunda baka ƙaunata..." da sauri Abba ya katse ta yace, "A'a kiyi haƙuri ina nan tafe yanzu" tana jin haka ta katse wayar gabaɗaya. 

Inno shewa tayi ta ce. “Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji to wa zai cinye naman idan ba ke ba, kinsan dai tun muna yara ke kura ce to kuma kya nuna mun ɗiban albarka ki kira Nadabo. Wallahi idan bai zo da majalisar ɗinkin duniya ba sai na kwashe masa albarka.”

Haushi ne ya kama Halifa cikin ƙunci yace. “Dan Allah kuyi mana shiru haba dan Allah? Tun ɗazu sai abu ɗaya akeyi nikam gaskiya na gaji wallahi, Allah idan su Daddy suka zo tasaku zasuyi a gaba ku tafi ni bazan iya ba kwana ɗaya kacal kunƙi ku barmu muyi bacci cikin nutsuwa.” Nusaiba ta ce. “To wai ku dan Allah banda abinku me akayi muku na kiran su Abba? Idan zaman nan ɗin ne bakwa so basai ku koma mazauninku ba?” Inno kallan tsaf ta yiwa Nusaiba sannan ta mata daƙuwa ta ce. “Gidan ku ja’ira mara ɗa’a korar mu kuke yi nida ƴar uwata? Wacce uwar muke ci a gidan naku da har kuke korarmu” Halifa yace. “Inno yanzu mu dawo maganar nama wannan fa ba abin wasa bane wallahi tsoro ya kamani ace kaji biyar babu daga yamma zuwa safiya” Inno ta ce. “Gane mun hanya jikana ni kaina na fara zargin anya babu wata a ƙasa kuwa?” Halifa na shirin magana suka ji ƙarar fashewar abu a ɗakin Nusaiba, da sauri suka nufi ɗakin zanin Inno har yana niyyar faɗuwa, suna zuwa suka samu kwalaben turarenta ne a ƙasa. Baki suka saki suna mamaki Goggo ta ce. “Halifa kuna da ɓeraye ne a gidan nan?” Nusaiba ta ce. “Gaskiya bamu da ɓeraye amma nayi mamaki ya akayi har kwalabe suka farfashe haka?” Inno ta waiga ta kai kallonta ga Jaririn Nusaiba dake kwance kan gado ta ce. “Halifa kasan Allah wannan ɗan ƙundalon na fara zarginsa saboda naga ɗiban albarkarsa ido biyu, anya jinnu basu shafeshi ba kuwa” Halifa ya tsuke fuska ya ce.

"Gaskiya banasan irin wannan Inno ya zaki dinga alaƙanta mun ɗa da aljanu ba naso kawai daga kwalaben turare sun zubo sai ki ce ɗana ne, wai me yaron nan ya tsare miki" Inno ta riƙe baki ta ce. "Ubanka ya tsare mun Halifa ka kiyayeni fa ina nuna maka Annabi kana runtse ido tam, wallahi duk ranar da ya nuna maka ɗiban albarkarsa zakayi bayani da bakinka"

 Goggo haushi ya isheta ta ce, "Rakiya wai wannan sabon salawatin ruɗewar meye ya sameki, anya aljanu basu buɗe miki idanu ba? Ke Nusaiba ɗauko mun shi ma inyi masa wanka kar wannan ruɗaɗɗiyar ta ƙara ruɗa mu" Goggo na faɗa ta fice haɗa ruwan wankan Jariri" Halifa ma ficewa yayi aka bar Nusaiba da Inno, Nusaiba cire masa kaya tayi ta wuce ɗakin da Halifa yake dan ta ɗebo kayan Jaririn. Inno na zaune ta ga Jaririn ya buga tsalle ya miƙe tsaye, dafe ƙeyarsa yayi ya fara wani irin zagaye yana yi yana gwalalo mata idanu. Sai yayi gaba kamar zai hau kanta sai kuma yayi baya ya buga tsalle. Ihu Inno ta farayi tana tafe a guje fitsari na bin ƙafafuwanta. Da gudu duk suka fito dan ganin abinda ya faru gabaɗaya suka fara jero mata tambayoyi kala-kala, Inno ji tayi bakinta yayi nauyi kallan ƙofar ɗakin Nusaiba take tana nunawa, da sauri Nusaiba ta shiga dan ɗauko Jaririnta.

Ana cikin haka suka ji bugun gida da sauri Halifa yaje ya buɗe ƙofar Motocin Daddy dana Abba ne kusan tare suka ƙaraso, suna shigowa falon suka gaishe da su Inno sannan suka zauna.

Daddy ya ce. “Halifa Inno ta gaya mun abinda kayi mata meyasa kake yiwa mahaifiya ta haka ne? Yanzu idan ɗanka ya girma zakaji daɗi ya wulaƙanta mahaifiyarka” Inno ta ce, “Gaya masa dai wallahi Halifa bashi da ɗa’a sam, Albasa dai batai halin ruwa ba wallahi da niyyata inkwashe masa albarka kafin kazo” Halifa yace.

“Insha Allah za’a kiyaye Daddy, kuma idan babu damuwa ku wuce da su kawai zuwa gida” Daddy yace. “Dama ai kiran da Inno ta mun kenan to ita Nusaiba wazai zauna da ita?” Inno ta tattakura ta rafka salati.

“La’ilaha’illahu Muhammadur Rasulillahi Sallallahu Alaihiwasallam yanzu Salisu iyaka zaka mun da gidan Ɗanka saboda nazo zaman daɓaro, idan ka tafi dani gidanka wacce uwar zaka bani, Meye bana ci a gidan nan? Wallahi Salisu duk cikin jikoki banyi sa’ar jika kamar Halifa ba, baƙin cikin cin kazar kake mun? Ahir ɗinka wallahi ko a mafarki na kuma jin wannan zancen sai na kwashe maka albarka sakarai maras ɗa’a kawai. Yo idan ban zaunawa jikata ba wa nake da shi da zan zaunawa, kai nifa nazo kenan zuwa sojan badaskare kuma ka ɗebomun kayana tas ka kawo mun gidan nan” Daddy dafe kansa yayi zaiyi magana Halifa ya ce.

“Maganar gaskiya nikam bazaki zauna mun a gida ba, tun da kuka zo gidan nan baccin kirki bama samun isasshe” Abba ya masa daƙuwa yace. “Gidanku Halifa su Inno kake gayawa hakan?” Daddy yayi gyaran murya ya ce.

“Inno ta kiran da kika mun me kike so ayi” Inno ta ɗaga kai sama kamar me nazari ta ce.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button