JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ɗanka nake san kamun iyaka dashi karya ƙara shiga sabgata, ai inace jikata ce ta haihu ko?” Daddy da Abba suka gyaɗa kai Inno ta cigaba da cewa.
“To kuce ya haɗa ya nasa ya nasa ya bar gidan nan idan mun tafi ya dawo” Halifa ya watsawa Inno harara suna haɗa ido ta rushe da kuka.
Goggo ta kalli Halifa ta ce, "Li'ilafi ƙuraishi aniyarka ta faɗa kanki ƴar uwar tawa kake yiwa wannan mugun kallon to kurwarta kur, oh yau naga sabon salawaitun mugun hali ido biyu anya Nadabo wata rana Halifa bazai rufemu da duka ba a gidan nan kuwa?" Halifa tsaki yayi ya miƙe zai bar gurin da sauri Inno ta riƙo gefen rigarsa ta ce. "Dawo-dawo wallahi sai ka zane mu gwara ka dake mu a gaban iyayenka kar sai sun tafi ka kwashe mana albarka" Sai kuma Inno ta fashe da kuka ita Goggo kamar haɗin baki suke share kwallah. Abba ne ya kalli Halifa yace. "Dawo ka zauna."
Halifa ya cika fam kamar zai fashe ya zauna Abba ya sauko daga kan kujera ya dawo ƙasa yace. “Goggo dan Allah kuyi haƙuri kunsan yaran nan sai ana haƙuri da…” A hassale Inno ta katseshi ta ce. “Allah ya tsinewa haƙurin albarka mun dinga haƙurin kenan har sai ciwon zuciya ya kamamu nida ƴar uwata, wato baƙin cikin rayuwar kuke mana ko Nadabo kuzo ku kashe mu kawai ku huta” Abba dafe kai yayi yai shiru bai ƙara furta komai ba. Daddy kallan Abba da Halifa yayi ya ƙifta musu ido sannan ya fara cewa.
“Halifa yanzu abinda zaka dinga mun kenan kana tayarwa da mahaifiyata hankali, to maza ka fice daga gidan nan ka shiga duniya kowa ya huta gwara nayi rayuwar farinciki da mahaifiyata ya fi mun komai.” Halifa miƙewa yayi bai ce komai ba ya wuce ɗakinsa, wata jakar goyonsa ta zuwa gurin aiki wacce yake sa uniform ya ɗauko ya goya ya fito.
Tsugunnawa yayi a gaban Daddy yace. “Shikenan Daddy tunda haka ne ni bari na tafi zan fita daga rayuwarku tunda Inno da Goggo basasan gani na” yana gama faɗa ya mike zai bi hanyar ƙofar.
Inno ɓingirewa tayi a ƙasa ta zuba wani uban salati tana kuka, Goggo ce ta ɗagota zaune itama tana share nata hawayen. Inno kallan Daddy tayi ta ce. “Salisu wallahi idan Halifa ya shiga duniya sai na ɗebe maka albarka, yanzu dama baka ƙaunar Halifa ban sani ba a gabana zaka koreshi ya shiga duniya saboda rashin ɗa’a” Daddy yace. “Inno ke fa kika ce ya fita daga rayuwarki nikuma duk abinda bakya so nima bana sanshi…” da sauri Inno ta ce.
“Ittaƙillah ittaƙillah wallahi karka mun sharri oh na shige su ni jikar mutum huɗu, yanzu haɗani zakayi da yaron nan da uwarsa, jikan nawa na cikina zaka ce bana ƙauna?” Wallahi Salisu idan baka dawo da yaron nan ka fice daga gidan nan ba sai na kwashe maka albaka, ni bansan wacce uwar ma zakuyi mana ba muna zaman lafiya nida ƴan jikokina da farar safiya kuzo ku kawo mana tarzoma”
Goggo ta karɓe zancen da. “Wallahi Rakiya barni dasu Allah yaran nan hukuma ce zata rabamu da su” Abba ya kalli Halifa yace. “Ka wuce cikin gida ka ajiye jakar nan” Halifa murmushi yayi saboda yasan dama Daddy da biyu yayi haka sai yace. “Abba ku bari kawai na tafi gwara na shiga yawon duniya” ya faɗa yana murɗa kofar.
Inno ta kuma matso ƙwallah tana jan majina ta ce. “Allah ya tsinewa yawon duniyar ni ɗin banza da wofi wallahi kanasa ƙafarka ka fita daga gidan nan sai na kai ƙarar Ubanka gurin hukuma, ni zaka tozarta ka ɗebewa albarka ku tashi ku bar gabana kuma ko a mafarki karna ƙara ganinku a gabana, yo dama me kake mun Allah na tuba ba Halifa ne yake mun komai ba, badan shi ba da nashiga wani hali tunda shine uwata shine ubana.” Daddy na shirin magana suka ga Inno ta miƙe zata fita da sauri Halifa ya dawo yana sauke jakarsa.
Goggo tsuke fuska tayi ta kalli su Abba ta ce, “Ku fice daga gidan jikana tun kafin na ɓata muku rai da sabon salawaitun rashin mutumci, haka kawai zaku zo ku hargitsa mana gida muna zaune lami lafiya.”
Su Daddy miƙewa sukayi suka fita suna murmushi ƙasa-ƙasa Inno ta ɗaga murya ta ce. “Kuma ko a mafarki kar na ƙara ganinku idan ba haka ba na ɗebe muku albarka marasa ɗa’a kawai.” Suna fita Goggo ta rufe kofa ta wuce ta ɗauko ruwan wankan Jariri ta wuce ɗaki dan tayi masa wanka. Goggo ta fara yiwa Jariri wanka ta ga ya ƙura mata ido yana kallo hura masa idon tayi da bakinta, nan take yayi tsalle ya ɗafe bakinta tana shirin kurma ihu ya saketa ya dinga tsalle a cikin ruwan kamar ana wulla ƙwallo, daga cikin robar tsalle yayi ya fara ɗafe labulewa daga kan wannan ya faɗa kan wannan, yana faɗowa daga kan labule ya fara fisgar zanin gado yana bankaɗawa yana shigewa yana fitowa, fitowa yayi daga cikin zanin gadon ya hau kan ƙafafuwan Goggo yana tsalle, daga ƙarshe zaninta ya bankaɗa ya shige ciki, wani uban ihu Goggo ta zunduma ta ce. “Ku dubi Allah karka shige mun oh na shigesu yau ga sabuwar salawaitun rashin ɗa’a da iskanci jama’a kuzo zai illata ni.”
FANS BA ZAN DINGA POSTING KULLIN BA SABODA LITTAFIN KUƊI DA NAKE YI, ZAN DINGA SAKAR MUKU KO SAU HUƊU A SATI NE.
Ummou Aslam Bint Adam????
FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️
ANYA BAIWA CE?
Na
AMEERA ADAM
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI.
FREE PAGE 3
Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? "
Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa.
Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba "
Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani.
Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."
Yana rufe baki cikin azarɓaɓi Fulani Maryama ta ce, " To itama ta ukun nasu Aljanar ce? kuma meye alaƙar su da junan su? Kuma meye alaƙarta da gidan masarautarmu? "
" Maryama kenan azarɓaɓin me kike yi? Ai duk gaggauwar asara ta jira samu, kuma duk gaggawar unguwar zoma ta jira a haihu, mai kike ci ne na baka na zuba inkinyi haƙuri sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba'a je ba "
Murmushin tayi sannan ta bashi amsa da, " Hmmm Marduska ai Ranar biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba, na ƙagu na ji matsayin Yarinyar da ka ce da kuma ya alaƙarsu ta ke? "
Marduska ya cigaba da cewa, " Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su na nan ya wanzu a dora ƙasa, sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu, kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku, har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan, sai dai bincike ya nuna akwai wani ɓoyayyen al'amar dake bibiyar jinin zuri'ar sarki Aminullahi "
Damuwa ce ƙarara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya, " Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta? "
Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yauƙi, wata irin ƙara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata, cikin damuwa Bokan ya ce, " Gaskiya gaba ɗaya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali, haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni, na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta "
Abin duniya gaba ɗaya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana faɗin, " Ka taimaka mun kayimun wani abu, ni da kai kaɗai na dogara "
Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce, " Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai, babu uwar da zan iya taimaka miki, bincike na biyu da zan gaya miki shi ne, idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin ƙasa da makwanni goma zai faɗa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki daɗi ba, dabara ta ragewa mai shiga rijiya..."
Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa, " Marduska wai dole sai akaina wannan masifun yarinyar zasu sauka? Kaina ya kulle fa, dan Allah ka bani mafita..." katse ta yayi da ƙarfin gaske yana cewa, " Da alama kin manta dokar kogon dutsen, azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki " sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, " Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya, ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ƙara ja da zamanin ka "
Motsa bakinsa yayi alamar jindaɗi sannan ya ɗauko wani ruwa dake cikin tukunyar ƙasa ya ɗaga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi, ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya leƙa wani tiriri ne yake fitowa, sai da ya gama kallon ƙwaryar ya ce, " Akwai wasu ɓoyayun al'amura mai tafe da sarƙaƙiya, da alama shuɗaɗɗun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ƙila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa, amma bani da tabbas harsashe ne nayi, ƙarɓi wannan " Ya miƙa mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani.
" Ita wannan layar ki saƙaleta aɗakinki zata taimaka miki na bunnuwar wasu sirrika na ki, wannan kuma ki binneta akan ƙofar shiga gidan masarautarku, bance zata Hana faruwar komai ba sai dai wannan layar zata hana tonuwar muhimmin sirinki musamman akan wance yaran, kinfi kowa sanin dai ba jinin Aminullahi ba ne hasalima ba jinin masarautar Kano bane, to ki saƙale ta gun da kikasan bazata faɗo ba, ita wannan ta ƙofar gidan wasu aljanune zasu miki gadin bakin ƙofar don hana ta shigowa, amma banda tabbaci yaƙini nake watakila shigowar Rayzuta gidan ya sa ta faɗowa wata ƙila kuma bazata faɗo ba, kuma na lura da faɗuwar gaba a duk lokacin da zaku haɗu da ita wannan yarinyar, sai ki riƙe wannan duk lokacin da kikaji faɗuwar gaba ki dinga lura da waɗanda suke tare da ke, ni nayi iya yi na ku tashi ku bani guri "
Jakadiya dake gefe tsumu tayi najin kalaman boka cikin zuciyarta ta ke faɗin, " Au dama Salman ba jinin Takawa bane? Lallai duk inda makirci ya je Fulani Maryama ta kai cen, babu ko tantama ɗan wajen Fulani Zulaiha shi zai zama magajin Izza, muje zuwa mahaukaci ya hau kura na tabbata akwai ranar da Ya zata ɗakin Ƙanwa, Fulani Maryama kinyi shuka a idon makwarya, lokaci na nan zuwa da kwaɓarki zatai ruwa, tafiya sannu-sannu kwana nesa. "
Kamar Fulani Maryama tasan abinda yake ran Jakadiya aikuwa ta juyo cikin tsuke fuska ta fara mata magana, " Jakadiya duk abinda kika ji agurin nan ki tabbata da ya zama sirri banasan kowacce magana ta fito daga bakinki, bakinki ƙanin ƙafarki, kinsanni sarai kinsan wacce Fulani Maryama bani da kyau banida daɗi, idan na sake naji wata magana ta ɓilla waje to daga gareki ne, kuma insa a hallakaki ba abu ne mai wuya agurina ba "
Jakadiya sarai ta san Fulani Maryama zatayi abinda yafi haka ma ta rissinar da kai ƙasa ta ce, " Wane ni da wannan ɗanyen aikin ya Shugabata indai wanda ya mutu zai dawo to maganar nan zata tashi, ai duk wanda ya ƙona rumbunsa yasan inda toka take tsada, ina ni ina bayyana sirrin Uwar gijiya ta idan nai haka ai kamar na daɓawa kaina wuƙa ne "
Fulani Maryama ɗauke kanta gefe tayi tana faɗin, " Ki tabbatar da kin kiyaye abinda kika faɗa domin ni ginshiƙin dutse ce kowa yayi karo dani shi ka faɗi, idan kunne yaji gangar jiki ta tsira " Jakadiya haɗiye yawu tayi mai ɗaci saboda jin haushin maganar Fulani, cikin zuciyarta ƙwafa tayi ta ce, " Tunkafin ahaifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta, Fulani Maryama dani kike zance wallahi duk wannan wulaƙancin da kike mun akwai lokacin da zan farke miki laya. "
" Muna godiya Ubangidana maganin kuka na dukda yau ce rana ta farko da zan fita daga kogon dutsen bada biyan dukkan buƙata ba, amma ni mai bin umarnin ka ce akan duk abubuwan daka gindaya mun, tsafi ya dafa hatsabibancin ka ya cigaba da wanzuwar har ƙarshen zamani " Fulani Maryama ta faɗa tana karɓar layun da ya bata.
Cikin jindaɗin kirarinta ya ce, " Taɓewa ta tabbata ga mai yin shirka kije tukwicin aikinmu na ga cikin bayin Masarautar ku kamar yanda muka saba duk lokacin da kuka ziyarce mu, zan ƙara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi, ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu " yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita, suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta ɗalasiman tsafin, atake haske ya kuma mamaye su suka ɓace daga gurin.
Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabobbi, Fulani karɓar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata, " Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba " rissunawa Jakadiya tayi ta ce, " Ina ankare ya shugaba ta "
UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[13/10, 19:37] Ameera Adam????: ☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
???? JARIRI ????
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
7&8
Goggo waigawa tayi jin babu wanda ya tako hanyar ɗakin domin kawo mata a gaji ta buɗe baki ta kuma magana da ƙarfi ta ce. "Jama'a ku dubeni ku dubi tsufa ku taimaka mun zai hallakani da raina, ku zo ku fitarmun da shi yau na shigesu nikam ina ganin salawaitun rayuwa" Wani uban tsalle Jaririn ya buga har sai da zanin Goggo ya ɗaga sama sannan ya fito ya cigaba da dafe ƙeya yana wani irin rangaji sannan yayi tsalle ya faɗa cikin robar wankan, ga mamakin Goggo sai ji tayi ya fara magana cikin wata iri gwarjejiyar murya kamar ta ƙaton gardi yace. "Ko da wasa naji kin buɗi baki da niyyar magana sai shaƙe miki wuya kin mutu har lahira" Goggo buɗe baki tayi tana zaro idanu ana cikin haka su Inno suka shigo ɗakin da sauri Nusaiba ta ce. "Goggo lafiya naji kina ta kurma ihu" Inno ta hau tattaɓa kafaɗar Goggo ta ce. "Oh ni jikar mutum huɗu Hansai ince dai wannan ɗan ƙundalon Jaririn ba wani rashin ɗa'ar yayi miki ba, dan wannan ihun ɗiban albarkar ba banza ba" Goggo ido ta zurawa Inno tana jin bayaninta sai kuma ta tuno da kashedin da Jariri ya yi mata, nuna hannu ta fara yi irin na kurame tana gunguni da baki kamar yadda kurame suke yi idan zasuyi magana.
Goggo nuna Jariri tayi da hannu sannan ta ɗan bankaɗa zaninta tana nuna mata, Nusaiba ta ce. "Goggo kiyi magana mana kya dinga bankaɗa zani me zamuyi a ciki" Goggo ta kuma kallan Jaririn ta bankaɗa zani sannan ta nuna gado, sai kuma ta nuna dai-dai maƙogaronta. Inno ta rafka salati ta ce. "Yau naga abinda ya tsone idon Kakata Laure mun shigesu Hansai Kurumcewa kikayi?" Goggo kasa magana tayi ta kuma nuna Jaririn ta bankaɗa zaninta ta ce. "Ummmm ummmmm" Inno ta riƙe baki ta ce. "Hansai ban fahimci ɗiban albarka da kike nuna mun ba ta bankaɗa zani, wai ko haihuwa kike sha'awar yi" Goggo da sauri ta gyaɗa kai sai kuma ta nuna Jaririn ta ce. "Ummmm ummmmm" Inno ta ce. "Yoooooo Hansai ko sharafa kike yi ke da haihuwa ai har abada banƙi ba ko a lahira idan anayi, amma wallahi ina jiye miki tsoron ɗiban albarkar da yaron nan yayi mun yayi miki shi a cikin zanin nan da kike ta bankaɗawa." Goggo na jin haka ta fara gyaɗa kai tana cewa. "Ummmmm Ummmm"
KUYI HKR BAN ZAUNA BA DANMA NA MUKU ALƘAWARI NE.
UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[15/10, 19:49] Ameera Adam????: ☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
???? JARIRI ????
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
9&10
Inno ta rafka salati tana tafa hannuwa haɗe da karkata kai ta ce. "Wannan bankaɗar ɗiban albarkar da kike mana na meye haka Hansai?" Nusaiba da takaici ya rufeta ta ajiye kayan Jaririn a kan gado ta fice daga ɗakin dan yin wanka, Inno sunkuyowa tayi ta ce. "Hansai ki dubi Allah kimun magana karfa daga wasa abu ya zama gaske dan wannan ɗiban albarkar ya fara bani tsoro" Goggo ta sauke wata ajiyar zuciya murya na rawa ta ce. "Rakiya babu komai lokaci ɗaya ne kawai naji salawaitun bakina ya ɗauke" Inno ta taɓe baki ta ce. "Wallahi keda Allah ƙarya kuma haramun ce amma duk wanda ya ƙare miki kallo yasan kina cikin halin rashin ɗa'a, wallahi badan ina duba zumuncin Allah ba da tuni na kwashe miki albarka yadda kika faɗar mun da gaba, haka kawai ki ɗora mun ciwo ki cuci ƴaƴana ki barsu da jinya suna kashe kuɗaɗe banda ma Allah ya rufa musu asiri, Kai duniya ni jikar huɗu Hamsai ina zaki bar mugun hali? Kiyi ki wanke musu ɗa kin tsaya bankaɗe-bankaɗen ɗiban albarka." Inno ta ƙarasa faɗa tana wucewa cikin ɗakin, kamar wacce ta ga mugun abu da sauri Inno ta dafe ƙirjina tana zaro ido ta ce. "Hansai waya yiwa jika ta wannan rashin ɗa'ar da labulaye, Oh nikam yau naga abinda ya tsone idon kakata Laure anya wannan ɗanƙundalon yaron aljannu basu mulmuleshi ba" Goggo cikin suɓutar baki ta yarfe hannu gefe ta ce. "Yoo Allah na tuba ba dole kiga sabon salawaitun abubuwa ba, muna tare da Ƙunduss..."
(ME SAN JIN YADDA NA SAMO SUNAN ƘUNDUSS YA NEMI LITTAFINA NA ƊAN BA ƘARA???? WOLLAH DARIYA SAI TA KUSA SAKU FITSARI A ZAUNE)
Da sauri Goggo tasa hannu ta rufe bakinta tana zare idanu kamar wacce tayi saɓo sabida tuno kashedin da jariri yayi mata, Inno ta dafe ƙirji ta ce. "Allahu Akabar kabiran Alhamdulillahi kema ya nuna miki ɗiban albarkar ko" Goggo da tayi fiƙi-fiƙi da idanu ta ce. "Waye kuma?" Inna ta keɓe baki ta ce. "Ina ce da wannan ɗan ƙundalon kike?" Goggo da sauri ta ce. "Nina gaya miki wallahi karki zabga mun sabuwar salawaitin ƙarya ido biyu, abinda baki sani ba wannan Jaririn ya fi mun ke sau dubu" Inno ta zaro ido ta ce. "Jaririn da kika sani jiya-jiya shine ya fini a gurki saboda ɗiban albarka" Inno ta fara matsar ƙwallanta ce. "Yanzu saboda uban yaron nan na da abun duniya ko Hansai?" kafin Goggo tayi magana Halifa ya shigo cikin ƙananan kaya ba ƙaramin kyau yayi ba, Inno washe baki tayi tace. "Halifun har an fito" Halifa yace. "Goggo wai har yanzu ba'ayi masa wankan ba? So nake fa na kaisu asibitin nan da wuri inasan na shiga office da wuri"
Goggo ta ce. “Au dan ƙaddara yanzu Halifa sai munje asibitin nan bazaka haƙura ba?” Inno ta kalleshi a watse ta ce. “Yoooo ina zai haƙura yana fama da idanun rashin ɗa’a a tsaye-tsaye bishiyar kuka, Ni bansan sanda yahudu ya lalata mutane ba ace wai Jariri ma sai anyi masa BBC wannan ɗiban albarka har ina? da ruwan zafi zaiji ko da allurai sai kace sanda na haifi ubansa allurar akayi masa, kuma uban me ya same shi Allah ba tuba kowane kibibabbe ya yi ɗiban albarkarsa ya gama.” Nusaiba ce ta shigo ɗakin da tawul a jikinta ta fito daga wanka ta tsaya jin abinda su Inno suke faɗa.
Inno kallan Nusaiba tayi tana jan dogon salati tana tafa hannu ta ce. "Nusaiba yau sabon ɗiban albarkar da zaki mana kenan wai ke me miji kin fito gandandan kinyi tsaye kina rangaji a gefensa cikin kissa, bakisan kin haramta agaresa ba, anya Nusaiba zamu iya zaman kwana arba'in a gidan nan kuwa, ummm Allah na tuba nima banda abu na me zan zauna yi a gidan yara tsofai-tsofai da ni, bari ma nayi wanka na kira Salisu yazo ya ɗauke ni ya maidani gida bakina alaikum."
Halifa ya tsuke fuska yace. "Inno wai ya kuke neman haramta mun mata ta ne ina ji ina gani, gaskiya nifa sa idon ku yayi yawa wallahi kawai dan ta fito daga wanka ta tsaya kusa dani shikenan ba matata bace?" Halifa ya ƙarasa Faɗa yana rungumo Nusaiba har tawul ɗin jikinta na niyyar faɗuwa, da sauri Inno da Goggo suka saki wani uvan salato lokaci ɗaya Inno har tana runtse ido Goggo ta ce.
"Oh yau naga abinda zai ƙonemun idani ni Hafshe yau na shiga uku Allah na tuba Alla ka yafe mun" Inna daɓar ta zauna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki tana zubda hawaye ta ce. "Allah mun tuba nida ƴar uwata kana ganin bamu da laifi a ciki, kai jama'a Allah ka yafemu ni ƴasu yau naga takaina Halifa ashe ɗiban albarkar taka takai haka, wallahi nan dai ba gidan zama bane na rantse da Allah kuyi gaggawar tuba kar fushin Ubangiji ya tabbata akanku sakarkaru marasa ɗa'a" Inno na gama faɗa ta bankaɗa zaninta cikin kajarta ta zura hannu ta ɗauko waya ta miƙawa Halifa ta ce.
“Maza maza kiramun Ubanka tun fushin Allah bai sauka a kanmu ba” Halifa ya tsuke fuska yace. “Bazan kira ba ke ki kirashi mana, ke Nusaiba idan bazasu yi masa wankan ba ki karɓa ki masa ki shiryashi mu tafi asibiti, na lura waɗannan tsofaffun nan gaba kafurtamu zasu fara yi” yana gama faɗa ya fice.
Inno ta rushe da matsanancin kuka ta ce. “Wallahi duk waɗannan maganganun rashin ɗa’ar ka gayawa ubanka Salisu Hansai ki wanke musu ɗa mu wuce dan baza’a dinga aikin kafurci a gabana ba”
Goggo taba ɗau lokaci ba ta wanke Jaririn ta tsane shi a towel ta kwantar da shi akan gado Inno sai aukin danna wayya take, ita dai taga lamba amma batasan ko ta wa ta kira tana ji an ɗaga ta ce. "Salisu duniya da lahira waya halicce mu?" daga cen ɓangaren akace "Allah" Inno tace "To wallahi Idan baka maza kazo ka ɗauke mu daga gidan nan ba sai na ɗebe maka albarka, saboda gidan Halifa sam ba gidan zaman musulmi na gari bane, nikam wallahi har azumi sai nayi na tuba ga Ubangiji wannan saɓon Allah har ina, ace dan jaraba yarinya tana cikin biƙi jage-jage amma yaro na naniƙe da ita to Allah ya yafe musu wannan kam ya riga da faru amma tun kafin fushin Ubangiji ya sauka kazo ka ɗaukeni atoh, yoo Allah na tuba dama fa Jikoki ne banda ma ƙaddara me zai kawo ni gidansu" daga cen ɓangare taji an kashe wayar batare da an amsa mata ba. Inno rushewa tayi da kuka tace. "Amma wallahi Salisu ya iya ɗiban albarka ki duba kiga Hansai wai ni Salisu zai wulaƙanta." tana kuka ta miƙe ta nufi hanyar banɗaki dake cikin dakin ta ce. "Wallahi nan ko gidan Ubana me salati ne na barshi kenan bari nayi wanka na fito" Inno ta faɗa banɗaki tana kici-kicin cire kaya taga Hansai tsaye a gabanta. Zaro ido waje Inno tayi tana dafe ƙirji ta ce. "Yau wata sabuwar ɗibar albarkar kike ji da kika biyo ni har banɗaki ki ga tsiraicina?"
FATAN ALHERI FANS????????????????
UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[17/10, 16:18] Ameera Adam????: FIRST CLASS WRITERS ASSO☀️
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
???? JARIRI ????
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.