JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

"Wayyo Allah ku agaza mini yau zai mini sabon salon salawaitu a haɓar baki na, dan Allah ku buɗe mun zan fita kar ya sauke mini haɓa na rasa bakin tauna" A hargitse suka jiyo dan ganin abin da yake faruwa, Halifa dafe kai ya yi ya tada motarsa da gudin tsiya a fili yana furta. "Innalillahi wa'inna'ilahirraji'un." da ƙarfi ya daki sitiyarin motarsa sannan ya ce. "Wallahi Goggo idan kuna alaƙanta Ɗana da wata manufa zaku ga ɓacin raina. Kuma ba haɓa ba idan fuska zai sauke miki sai dai ya sauke amma tunda na rufe motata bazan ƙara buɗewa ba. 

Jaririn na jin haka ya washe baki yana zaro idanu ya kuma ɗaga hannu da niyyar shafo haɓar Goggo Inno dake gefe tana matsalar ƙwalla ta hango dan gudil ɗin hannu, Inno gefe ta ja tana dafe ƙirji tana shirin kurma ihu ta hango hannunsa yana miƙowa caraf taji ya sa hannunsa cikin rigarta.

Inno kallan Goggo tayi ta rushe da kuka ta ce. "Dan Allah ku taimaka mini zai nuna mini rashin ɗa'a wallahi wannan ɗiban Albarka ya yi yawa nikam yau naga ta kaina zai ɗaye mini ƴan matana biyu" Kamar alamara taji Jaririn yace. "Inno zan sha Mama"

Inno ciki kuka ta ce. “Banda shakiyanci da ɗiban albarka me zaka yi da ƴan mata na abu duk fata, yooo Allah na tuba yaushe rabona da shayarwa sama da shekara talatin idan ba fatar zaka ɗaɗɗayemun ba…? Inno bata ƙarasa magana ba taji Halifa ya kashe Motarsa ya buɗe yana yiwa Nusaiba magana akan ta fito su nifa ward ɗin da ake alluran yaran. Nusaiba rungume da Jaririnta ta fice tana fita ya sawa ƙofar mukulli.

Goggo waro ido waje tayi ta na gani Jaririn dake hannun Nusaiba da wanda ya maƙale a hannun Inno, tana shirin yin magana Jaririn yace. “Inno ki bani Mama ko na fisga ta karfi na sha”

FATAN ALHERI FANS????????????

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[27/10, 12:34] Ameera Adam????: FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    15&16

SHIN KUNA DA MASANIYAR YAWAITA SADAKA YANA MAGANIN MUSIBU?SANNAN TAIMAKO BAYA KADAN, A DUK LOKACIN DA KA BAYAR SAI ALLAH SWA YA KARA YASSARE MAKA AL’AMURRANKA, BAYA GA DIMBIN LADAR DA AKA AJIYE MAKA A RANAR DA BABU SHAMAKI GA ZUWANTA.

ASSALAMU ALAIKUM

‘Yan uwana musulmai maza da mata wanda na sani da wanda ban sani ba. Sunana Fatima Aminu wadda aka fi sani daUmmu Saddik ga masu bibiyar littafaina. Taimako nake nema kan wata baiwar Allah da ta kuka min da damuwarta.Wata baiwar Allah ce ƙawata aminiyata kuma maƙwafciyata ta shiga wani hali na buƙatar taimako kun san komai ya zama na kuɗi mijinta aka zo har gida aka ɗauke yau kwana 45 ba amo ba labari mutumin Niger ne ba shi da kowa sai ƙanin mahaifinsu kuma basu kula da ita ba baiwar Allah. ‘Yaƴan ta uku tana daya daga cikin wadanda Allah ya jarabta da bandit maganar da nake a yanzu mutanen garinsu kaso saba’in da biyar cikin dari sun yi gudun hijira. Yanzu a halin da take ciki ƴarta ba lafiya ko asibiti ba a je ba saboda babu kudin tafiya. Hakazalika abincin da za su ci ma wuya yake mata. Don Allah duk mai niyar taimakawa ya tuntuɓe ni ta wannan number 08146711395.

Idan ma ba ka da halin taimakawa don Allah ko da addu’a ce ku yi mata. Allah ya yi mana maganin abin da ya fi karfinmu. Ya yi mana katangar karfe da sharrin wannan zamani.

????????????????????????

Inno cikinta ne ya karta take hankalinta ya tashi hannuwa bibbiyu ta naɗe a ƙirjinta tana tura ƴan yatsunta ƙasan hammatarta, da ƙarfin gaske Jaririn ya buga tsalle suka fara kiciniya shi da Inno, Inno sai maƙale hannuwa take Jaririn yana ƙoƙarin fisge hannuwa yana faɗin, "Ai dama nace sai nasha ko da tsiya ne" Goggo da ke gefe jikinta banda tsuma babu abinda yake yi ganin halin da ƴar uwarta take ciki yasa ta fara ihu. "Jama'a ku kawo mini salawaitun taimako kar ƴar uwata ta ɓalɓalce a hannun wannan salawaitun hatsabibin, wai babu me ji na ne ku kawo mana salawaitin taimako Jariri zai hallaka mini ƴar uwa." Goggo tana yi tana waigen gurin da Jaririn yake dan kar itama ya kawo mata farmaki.

Inno banda kokawa babu abin da suke yi gabaɗaya ta haɗa uban gumi, tun da ƙwarinta har ta fara gajiya gabaɗaya ta saddaƙar da Jariri zai turmushe ta, yaye Hijabinta tayi tana banƙaro masa ƙirji ta ce. "Kai kaci ƙwal ubanka wai ba ɗiban albarka ce zaka gwada mini ba, Indai fata ce gata kayi ta sha idan ma cinyewa zaka yi ma kayi gabaɗaya, yooo dama me yayi saura Allah na tuba banda fata abu kamar ledar nafkin, ka ƙarasa ni kawai ka huta ƴaƴana kuma suyi ta ɗebe maka albarka har ƙarshen rayuwarka ja'iri maras ɗa'a..." Inno tun bata rufe baki ba Jariri ya buga tsalle kansa har yana buga saman motar, dafe ƙeya yayi ya fara wata irin rawa yana tura ciki gaba yana cewa. "Ta bani dama ehh! In tsinke abubuwan ehh! Ƴan matan Inno in zuge su ehh! Intatse su ehh! In haɗiye su ehh" yana rufe baki ya warto Maman Inno yana shirin kaiwa baki Inno tayi ta maza ta hankaɗe shi ta fisge rufe idonta tayi ta dinga kai duka ta ko'in. 

Yadda Inno take kai duka hannunta sai wurgi take da Jaririn yana sama yana ƙasa kamar wani tamola, Goggo mutuwar tsaye tayi tana kallon Ikon Allah ace wai Jariri sabuwar haihuwa ne ake wannan ɗauki ba daɗin da shi. Goggo tana san taimakawa Inno tana tsoron karya dawo kanta, haka dai tayi ta maza itama ta runtse ido ta dinga kai masa duka har da ɗan ihunta. Jaririn na ganin haka ya ja da baya ya ɗare kan sitiyarin motar, ya wara ƙafafuwansa akai yana wani irin rangaji haɗe da zaro musu idanu yana kaɗa harshe, yana nan daga tsaye sai ga fitsari tsiiiii tun dana inda yake tsaye har zuwa kujerar baya gurin da su Inno suke, haka fitsarin nan ya tarar da su.

Cikin haɗin baki suka rafka salati Goggo harda tafa hannu Inno tace. “Yau naga abin da ya tsone idon kakata Laure mu kam mun gamu hatsabibin aljani maras ɗa’a, banda ɗiban albarka ya za’ayi ka fitsaremu kamar waɗanda aka ɗebewa albarka.” Goggo ta rushe da kuka tana fyace majina sannan ta ce. “Tun da ubana Me salati ya haifo ni ban taɓa ganin salawaitin siddabaru irin wannan ba, anya wannan Jaririn bazai kashemu ba kafin mu koma gida ba, ji yadda yake salawatun fitsari ido biyu kamar ɗan Kafirai. Kai amma wallahi ancuci jikata Nusaiba wallahi da biyu wannan Ɗanƙundalon da ta haifar mana badai tayin Nusaiba ba sai dai a tayin Halifa cen, daga ni har ƴaƴa da jikoki babu mai irin wannan salawaitin sheɗancin…”

Tun Goggo bata rufe baki ba Inno ta ce. "Aniya bi aniya. Aniyarki ta koma kanki badai jikana ba wallahi cen sai dai daga jikin Nusaiba aka kwaso wannan ƙamayamayar, ai wallahi anyi ɗaya ba ƙari baza'a ƙara wannan ɗiban albarkar dani ba, haka kawai jikana ya dinga haifar ƴaƴa marasa ɗa'a irin wancen. Babu ko tantama idan muka koma dole nasa Salisu ya raba auren nan ko na ɗebe masa albarka kowa ma ya huta."

Goggo tana tafa hannuwa ta ce. “Ahayye tafi nono fari wallahi ko baki faɗa ba sai Halifa ya miƙo salawaitin takardar Nusaiba, kuma babu inda zata je da wancen Ƙunduss ɗin dan bazamu iya da salawaitun iskancinsa ba, dama kuma ba da shi muka aura masa ba sai ku riƙe tsiyarku cen ku ƙarata da salawaitun hatsabibancinsa.” Goggo ta ƙarasa faɗa tana nuna Inno da ɗan yatsanta.

Inno ta rushe da kuka ta ce. “Hansai yau ni kike yiwa ɗiban albarka da rana tsaka saboda rashin ɗa’a, to wallahi indai nina haifi Uban Halifa auren Nusaiba da Halifa kamar ankashe shi ya mutu, zan nuna miki rashin ɗa’a da ɗiban albarka. Ke wallahi ba dan ina duba zumuncin Allah ba da tuni na ɗebe miki albarka kowa ma ya huta, to ina duba wasiyyar Me salati shiyasa kai Allah ya dai ya gafarta musu amma kedai Hansai albasa batayi halin ruwa ba.”

Goggo ta ƙara shewa ta ce. “Sai dai mu ɗebewa juna dai, dan nafi ƙarfin ki mun salawaitu ina kallonki, sannan kuma ai…” Wata uwar ƙara Jaririn ya ƙwala wacce tayi sanadiyar katsewar maganar Goggo ba dan tayi niyya ba.

Gabaɗaya nutsuwarsu suka shiga nan take jikinsu ya hau tsuma. Jaririn yana kan sitiyarin motar suka ga ya zura hannunsa cikin ƙwayar idonsa ya ƙwaƙwulota sai ga ƙwayar idonsa a tafin hannunsa. Sama ya dinga jefata yana caɓewa. Inno da Goggo nan take cikinsu ya fara ƙugi saboda tashin hankali har ana iya jin sautin ƙugin cikin nasu.

Buɗe bakinsa yayi ya jefa shi ciki ya fara taunawa, Inno wani irin ihu tayi ta janyo Goggo suka rungume juna kowacce jiki sai karkarwa yake. Wata uwar tsawa ya buga musu yace. "Maza-maza ku saki juna ko na ƙwaƙwale idanuwanku na haɗiyesu yanzun na" tun bai rufe baki ba suka saki juna Goggo ta ce. "Kayi mana rai Ɗan nan karka yi mana salawaitun abin da ka faɗa..." da ƙarfi ya katse ta da cewar. "Ta kanki zan fara bani salawaitin na cinye kafin nazo kanki" 

Goggo ta zaro ido waje ta ce. "Ita salawaitun zan baka?" Jaririn yace. "Ita zaki ban ko na fara karyar gaɓa-gaɓar jikinki ina cinyewa." Goggo ta fara matsar ƙwallah ta ce . "Yaro wannan salawaitun tun da ƙuruwaciya na wayi gari da ita bansan ya zan fasalta maka salawaitun bayanin ba"

Inno ta kalli Goggo da tayi jage-jage da hawaye da majina ta ce. “Banda abin ki ba sai kiyi masa bayani dalla-dalla ba kya yi masa rashin ɗa’a ai sai ki ja ya ɗebe miki albarka” Jariri ya kalli Inno yace. “Kema ina tafe gurinki ki bani ɗiban albarkar da rashin ɗa’ar” gabaɗaya shiru sukayi kamar wanda ruwan ya shanye.

Tsalle ya ƙara bugawa yace. “Naji kunce iyayena sai kun raba aurensu to naga wanda zai fita daga motar.” Yana gama faɗa ya murza sitiyarin motar da ƙarfi nan take mota ta tashi ya fara tuka ta da gudun gaske, Inno da Goggo banda gware da kawuna babu abinda suke yi da ya fisgi motar zaka ji kansu ya bada ƙwal sai kaji sun rafka salati, tun baiyi tafiya me nisa ba Inno ta sume a cikin motar.

Halifa na fitowa harabar gurin ya nemi motarsu ya rasa gabansa ne ya faɗi, suka kalli Juna shi da Nusaiba da take jijjiga jaririnta saboda kukan allurar da yake yi, Halifa da sauri ya ɗauko wayarsa ya fara kiran Inno amma ba’a ɗauka ba, ya kira yafi a irga sannan ya kira ta Goggo sai da ta kusa katsewa ta ɗauka, cikin fargaba Halifa yace. “Goggo lafiya naga babu motar kuna ina” Goggo muryar ta da ƙyar take fita saboda wahala ta ce. “Halifa ku kira ƴaƴa da jikoki ka sanar da su mutuwarmu ataru ayi mana addu’o’ domin tamu tazo ƙarshe” Halifa yace. “Waye ya ɗauke ku ne wai?” Goggo murya a shaƙe ta ce. “Jaririnka ne ya ɗauke mu yanzu haka sai fafara salawaitun uban gudu yake, ni da kake gani nayi salawaitun suma yafi a irga babu me tayar dani wahala ce kawai take farfaɗo da ni. Ga Inno dai yanzu kam nasan matambaya har sun dira kanta…” Tun bata gama maganar ba Jaririn ya fisge wayar ya kasheta gabaɗaya.

LITTAFIN ANYA BAIWA CE ANA CI GABA DA KASUWANCINSA GAME NEMAN CI GABANSA ZAI BIYA 200 TA WANNAN ACC ƊIN AISHA ADAM 3090957579 FIRST BANK KO KATIN MTN 0706 206 2624

UMMOU ASLAM BINT ADAM????
[31/10, 19:52] Ameera Adam????: FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

         ???? JARIRI  ????

Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM

SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP

       GARGAƊI 

BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.

    17&18

SHIN KUNA DA MASANIYAR YAWAITA SADAKA YANA MAGANIN MUSIBU?SANNAN TAIMAKO BAYA KADAN, A DUK LOKACIN DA KA BAYAR SAI ALLAH SWA YA KARA YASSARE MAKA AL’AMURRANKA, BAYA GA DIMBIN LADAR DA AKA AJIYE MAKA A RANAR DA BABU SHAMAKI GA ZUWANTA.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Leave a Reply

Back to top button