JARIRI COMPLETE HAUSA NOVEL

Abba takawa ya yi ya wuce ciki yana rafka sallama daga cen ɗaki yaji muryar Halifa yana cewa. “Abba ka wurgar da Jaririn nan wallahi ba mutum bane” Da mamaki Abba ya kai kallonsa kan Jariri yaga ya ƙura masa ido ko ƙiftawa baya yi, nan take yasha jinin jikinsa saboda ba yadda za’ayi ace mutanen gida gabaɗaya sun juyawa Jariri baya ba tare da wani dalili ba. Abba ya ce “Idan ma ba mutum bane ni zanyi maganinsa.” Jariri na jin haka ya wage baki ya fara tsanyara kuka.
FATAN ALHERI????
JARIRI ZAI SHIGA SIRAƊALLAZI????
UMMOU ASLAM BINT ADAM????
FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
???? JARIRI ????
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
33&34
Goggo na jin abin da Abba ya faɗa ta leƙo ta windowa tana nuna Jariri da hannu ta ce, “Nadabo Allah dai ya yi maka salawaitun albarka, wannan Jaririn da kake gani ba ƙaramin taƙadari bane. Wallahi da zan iya sai ha tsinke hanjinsa gida uku.” Nusaiba da ke gefe ta kalli Goggo ta ce. “Ummmm ummmm Goggo” Goggo ta yi mata kallon gefen ido ta ja guntun tsaki ta ce. “Ke rufe mini baki da Salawaitun ummmm ummmm ɗin ki. Haka kawai a nemi a hana bawa da bakin sa ya yi magana.” Inno ta karɓe zancen da cewa.
“Amma dai Nadabo Allah ya tattaro albarkar duniya ya afka maka, shi kuma wannan yaro maras ɗa’a Allah ya ɗebe masa albarka wuta-wuta, inda ka ga ɗiban albarka da Jaririn nan ya yi mana kare ma bazai ci ba, shiyasa ko haufi bana yi Ubangijin Sammai da ƙassai ya ɗebe masa jinginannun albarka, ya afka masa ɗiban albarka wafulan-wafulan a tsakar kansa.” Daddy ya kalli Inno ya yi gyaran murya ya yi ƙasa da murya yace, “Inno don Allah ku daina aibanta Jaririn nan bakwa tsoron ya kuma aikata mana wani abun”
Inno ta keɓe baki ta ce, “Kai raba kanka ɗiban albarka ta, bakaji me Nadabo ya faɗa ba tun shigowarsa, akan kunnenka yace zai ɗebewa yaron cen albarka.” Tarasulu ta yi caraf ta ce, “Ni kam yau na ga sababi wallahi tun da me cin ƙwal ubansa yazo mr muke jira da ba za mu yi ta kanmu ba? Ai nikam wallahi da ni zan samu sukunin da wannan Yaro Nadabo ya samu da idan na samu mazaunansa na dinga kafa masa cizo, har sai ya gane Annabi ya faku.” Halifa ya kallesu fuskarsa ɗauke da busassun hawaye yace. “Inno Ummmm ummmm fa” Uwani ta matso jikin window har tana bankaɗe Inno ta ce, “Nadabo don Allah kayi abin da yake gabanka, kar su cika ka da hayaniya maza ka sa shi a turmi ka kirɓe kowa ya huta.”
Abba mamaki ne ya kama shi dan ganin suna ta faɗar abunuwa marasa daɗi akan Jaririn, Jariri ɗaya bayan ɗaya yake sauraronsu da mugun alkaba’in da suke ja masa. Abba ya gyara tsayuwa har lokacin Jariri na rungume a hannunsa yace. “Wai dan Allah me ya yi muku haka ne” Jariri da yake mutsuniya a fakaice ya juya ya ƙwalalo musu ido, tsit suka yi aka rasa wanda zai yi magana. A hankali Abba ya taka ya ƙarasa cikin falom da babu kowa a ciki ban da ɗangwale da zannuwa, daga cen gefe harda ɗan gajeren wandon Inna Uwani. Zama ya yi ya kwantar da Jariri akan kujera yana rufeshi da wani zani da baisan ko na waye ba.
Ɗayan bayan ɗaya suka fara leƙowa daga baya suka fara fitowa, Daddy shine ƙarshen fitowa yana tafe yana muzurai.
Abba cikin girmamawa ya gaishe da Iyayen nasa da ƙawayensu, sannan ya ɗora da cewar, "Goggo kinsan yau ne fa tafiyar tawa yanzu haka na kusa makara a gaggauce nace bari na leƙo nayi muku sallama."
Goggo ta hangame baki lokaci ɗaya ɗebi salati tana tafa hannuwa sannan ta ce, “Nadabo yanzu tafiya zakayi ka barmu da salawatun hatsabibin yaron nan…” tun bata rufe baki ba wayar Abba ta fara ringing yana ɗauka daga cen ɓangaren aka ce.
“Saura minti arba’in jirginku ya tashi fa ba buƙatar ɓata lokaci.” da yake ya warware speaker wayar Inno na jin haka ta ce, “Aikuwa ƙafata ƙafarka Nadabo. Wallahi bazaka barni da wulaƙantaccen nan ba ya ƙara ɗebe mana albarka haka kawai ba.” Abba ya kira lambar Adam bayan ya ɗauka yace, “Son maza kaxo gidan Daddynku it’s urgent ni zan wuce dan Khalid na Nurain tuni sun wuce mini da kaya na.” daga cen ɓangaren khalid yace. “Ok gani nan zuwa Abba”
Abba yace, “Banda ɓata lokaci case ɗin Jaririn nan ya isheni ” Adam yayi guntun tsaki ba tare da ya bari Abba yaji ba, a zuciyarsa yake mitar wannan case na Jariri ya ishe shi.” amma a fili yace, “Yanzu zan fito Abba” Abba yana gama faɗa ya zaro dunƙulen kuɗi kashi uku ɗaya ya fara miƙawa Inno sannan ya miƙawa Goggo, ɗayan kashin kuma ya miƙawa Tarasulu yace. “Baba ga wannan ayi mana Addu’ar nasara” ya ƙarasa faɗa yana miƙawa tsaye, sannan yace, “Adam yana tafe zan sa ya taho da Ya sayyadi na ƙasan layinmu insha Allah koma menene za’a shawo kan matsalar, Yaya ni zan wuce ka wallahi naso zuwa da wuri wani uzuri ne ya hanani, sai na je dai mayi magan insha Allah.” Daddy gyaɗa masa kai kawai ya yi saboda gabaɗaya yawun bakinsa ya ƙafe saboda fargaba.
Su Inno murnar kuɗi sai ta sa suka manta da Jariri dake kwance a kan kujera, Abba a hanzarce ya tashi ya fice saboda gudun kar ya samu matsala a Airport.
Su Goggo na cikin irga kuɗi suka ji Jariri ya bankaɗe zanin da aka rufeshi, ya yi wata irin tsayuwa ta gwamim jaki da alama wannan karan kamar yafi jin ƙwarin gwiwa akan wancen karan, Ido ya gwalala musu cikin tsawa yace,
“Waye yace zai kafawa mazaunai na cizo da haƙoransa?” Jikin Daddy na rawa ya fara ɗaga hannu sama yana cewa, “Wallahi bani bane Inna Uwani ce…” a zabure Inna Uwani ta katseshi da cewar, “Bani bace sam kada ka sa a zalinceni bi gairi haƙƙina Tarasulu ce ta faɗa” Tarasulu tai tsilli-tsilli da idanu tana matsar ƙwalla.
UMMOU ASLAM BINT ADAM????
FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}
https://www.facebook.com/groups/856755331683130/?ref=share
???? JARIRI ????
Labari da Rubutawa: AMEERA ADAM
SADAUKARWA GA ƳAN GROUP ƊINA NA AMEERA ADAM FANS GROUP
GARGAƊI
BAN YARDA A SAUYA MUN LITTAFIN NAN TA KOWACCE SIGA BA BATARE DA IZININA BA.
35&36
Jariri ya juya yana kallon Tarasulu cikin tsawa yace, "Ke ce kika faɗa ko?" Tarasulu ta ɗan ja da baya ta ce, "Ranka ya daɗe bani bace aljanuna ne suka faɗa." Jariri ya yi tsalle caraf ya ɗafe kafaɗar Halifa, nan take cikin Halifa ya kaɗa. Jariri ya fara mulmula kan Halifa yana lasar baki, yawunsa har yana ɗiga a tsakiyar kan Halifa. Leƙo kansa ya yi ta wajen fuskarsa yace, "Daddy wallahi yawuna ya tsik..." Tun Jariri be gama maganar ba Halifa ya katseshi hankali a tashe yace, "Da me yawun naka ya tsinke?" Jariri ya kuma shafo ƙetar Halifa yana sunkuyar da kansa da niyyar lasar ƙeyar, a zabure Halifa ya yi tsalle cikin muryar ban tausayi yace, "Dan Allah kayi haƙuri wallahi kaina ɗaci gareshi" Jariri ya gungura ya sauka yace, "Wasa nake yi maka Daddy ba kanka zan gwaguya ba, kan waɗancen zan gwaguya" Jariri ya ƙarasa faɗa yana nuna su Inno.
Lokaci ɗaya gumi ya fara wanke musu jiki, jikinsu ban da karkarwa babu abin da yake yi. Jariri ya nuna Tarasalu yace, "Matso da ke zan fara na cire miki aljanun kanki" Tarasulu ta tsugunna gwiwa bibbiyu ta fara roƙonsa idanu cike da hawaye.
Jariri ya ɗare kujera yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yace, “Idan baki zo ba kika bari na ƙaraso idan na turmusheki sai na ɗaɗe mazaunanki dan babu abin da zai hanani yagarsu na cinye su tas” Tarasulu wage baki ta fara yi tana bin su ɗaya bayan ɗaya da jemammun idanuwanta, kallo take musu me ɗauke da ma’anar nikam tawa ta ƙare ku gafarceni, tana zuwa kan Inno ta ce, “Rakiya duk duniya ke kaɗai kike bina bashi kuɗi bayan na mutu ki kira su Ɗalha kicr su biya mini kar akaini da kuɗinki na faɗa hannun mala’iku, kinsan dai me Malam me haɗiyar alƙami ya taɓa sanar damu tun yarinta akan haƙƙin wani.” Inno ta sharce tata ƙwallar tana fyace majina ta ce, “Yanzu haka zamu yi mutuwar wulaƙanci muna ji muna gani, to Allah shi yafe mana amma nikam tsinke banzan amsa ba dan duniya da lahira na yafe miki, yanzu idan na karɓe na yi wa amintaka ɗa’a kenan?” Jariri ne ya buga musu tsawa yace, “Ke me karɓar wasiyyar basai kin fita da rai ba” aikuwa ko rufe baki bai yi ba gabaɗaya tsofaffun nan suka yage baki suna kuka me nuni cewar ta su ta zo ƙarshe, gurin banda rawar murya da makyarkyatar tsofaffi babu abin da yake tashi.
Daddy ma da yaga basu da wata mafita da sanin makomarsu, janyo gefen rigarsa ya yi ya fara goge ƙwallah. Halifa da su Mummy ban da ido babu abin da suke bin su da su na jikin a sanyaye kamar marasa jini a jika, Jariri tsalle yanyi ya ƙarasa gurinsu Inno ya yi ƙerere yana kallonsu sannan yace, “Maza ku shanye kukanku idan ba haka ba wallahi jikin ku ya gaya miki dan babu abin da zai haɗa na yi lugu-lugu da namanku.” Kamar anyi ruwa an ɗauke haka gurin ya yi tsit su Inno suka ja bakinsu suka yi shiru suna sauraron hukuncin da zai yanke akansu.