JARUMA YAZILA COMPLETE HAUSA NOVEL

JARUMA YAZILA COMPLETE HAUSA NOVEL


Al’amarin hadiman gidan zaihar kuwa, dasu da
masu gadin gidan Bayan yazila ta sami nasarar
kashe maigidansu Sai suka ruga da gudu izuwa
gidan sarki daksur suka isar da labarin abinda ya
faru ga man yan hadiman gidan. Ai kuwa acikin
wannan dare labari ya riski sarki Daksur. Cikin
tsananin firgici da dimauta sarki daksur yamike
zumbur yayi shigar yaki ya jagoranci dakaru dubu
a shirin da kansa acikin dare suka bazama
neman jaruma yazila acikin birnin kisra amma sai
da suka duba ko ina basu gantaba.
Shikuwa hakimi barzuk yajin labarin abin da
yafaru sai ya ruga izuwa dakin yazila a fusace
rike da takobi. Da shigarsa cikin dakin sai ya iske
matarsa nuzaira atsaye rike da wasika tana karan
tawa tana zubar da hawaye cikin fushi barzuk ya
fisge ta kardar ya karanta jawabin dake cikinta
kamar haka.
YAke ummata ki gafarceni bisa abinda zan
aikata. Kiyi sani cewa bani da wani zabi face na
aikata hakan kuma ki gayawa mijinki da sarki
daksur abinda ya faru da sarkin yaki zaihar suma
yananan tafe garesu nan da wani lokaci a ko
yaushe kuma ina gargadinsu akan idan suka taba
lafiyarki nima saina taba lafiyar dukkanin
danginsu, sai na tabbatar da cewa na share
dukkanin zuri’arsu daga doron kasa. Idan har sun
matsu. Da son ganina su nemeni acan birnin
misra………..”
Koda barzuk yazo nan akara tun wasikar sai
zuciyarsa ta kama ta farfasa kamar zata kone.
Saboda tsananin fushi da bakin ciki ka wai sai
yasa hannu ya fyade nuzaira ta fadi kasa
sumammiya. Nan take ya kwalawa wasu hadi
mansa kira yace su dauki nuzaira su kaita can
babban kurkuku na kasar suce asamata sarka
atsareta har sai ranar daya nemeta. Nan take
kuwa wadannan hadiman suka cika wannan
umarni. Bayan hadiman sun tafi da nuzaira sai
yafita da sauri ya hau dokinsa yatafi gidan sarki
da zuwansa kuwa ya iske sarki daksur ya dawo
daga neman gimbiya yazila bai gantaba. Yana
zaune a fada shi kadai cikin tsananin fushi
tamkar zai kona gidan sarauta gaba daya barzuk
ya zube kasa gaban sarki daksur ya sunkui da
kansa kas cikin tsananin ladabi alokacin da gaba
daya jikinsa ke karkarwa don tsoro kada fushin
sarki ya kare a kansa
Bazato ba tsammani sai barzuk ya bushe da ma
haukaci yar dariya. Al’amarin daya matukar bashi
mamaki ke nan ya dago kai a tsorace yana
kallonsa.
Sarki daksur ya turbune fuska sannan yace ,
“hakika matarka taso ta watsa mana dukkan
shirimmu ta tona mana asiri bisa sakacinka na
kula da sa ido akanta. Hakika in ba don kayi
mata hukunci ba da kanka kasa ankaita kurkuku
da tuni kai da ita duk nayi muku hukuncin kisa.
Bisa bincike da nayi a halin yanzu na gano cewa
tuni jaruma yazila tayi nisa da barin wannan
birnin wannan kasa tamu saura tafiyar kwana
daya da yini daya jal ! Ta isa kofar birnin misra.
Jaruma yazila tana da matukar karfin sihirin tsafi
don haka bani da wa dansu hadiman aljanu da
zan turasu su hallakata kafin ta isa cikin birnin
misra. A cikin binciken da na yi na gano cewa
idan ta shiga cikin birnin misra bazata sami
nasarar samun abinda taje nemaba. Kuma zata
sha tsananin wahala wacce zata iya zama
sanadin ajalinta. A kwai wani lokaci da zaizo
muyi yakin karshe da sarki raihan na birnin misra
a wannan yaki ne zamu sami nasara akansa
mukama birnin nasa gaba daya a sannanne zamu
shiga har cikin birnin mukama yazila da
mahaifiyarta humaira sannan mu binciko duk inda
‘yar uwarta take dabira itama mu hallakata. “
Sa’adda sarki daksur yazo nan azancenta sai
farin ciki ya lullube barzuk bai san sa’adda ya
bushe da dariyar murnaba. Nan fa duk su biyun
suka ci gaba da kyakyata dariyar kamar bazasu
dainaba.
A dai-dai lokacinne matar zaihar ta shigo cikin
fadar ita kadai rungume da danta tana zubar da
hawaye. Batare da fargabar komaiba ta iso har
gaban sarki Daksur ta risina ta kwashi gaisuwa
sannan ta zaiyana musu sakon da jaruma yazila
tabata.
Koda matar zaihar ta gama jawabi sai jikin sarki
daksur ya kama tsuma. Nan da nan zufa ta karyo
masa. Zuciyarsa ta kama bugawa da karfi kamar
zata fado kasa cikin tsananin zafin nama ya zare
ta kobinsa ya fille kan matar zaihar ta saki dan
dake hannunta ya cafeshi da hannu daya.
Gangar. Jikin matar zaihar ya sulale kasa
alokacin da dan nata ya fashe da kuka. Sarki
daksur ya yunkura zai sare kan dan sai barzuk
yace, “kayi masa rai ya shugabana ai kankanin
yarone”Sarki daksur ya sauke takobinsa kasa sannan ya
bushe da dariyar mugunta ya killata barzuk
wannan yaro ya cafe yace dashi katafida shi
izuwa gidanka ka raineshi ya taso a cikina
bayinka masu yi maka hidima hakika
mahaifiyarsa ta cuceshi data sayi ajlinta a lokacin
da yafi bukatarta a rayuwa tayi kuskure babba da
tazo gabanmu da mugun lafazi domin itace mace
ta farko datata ba zuwa gabana ta fadi mugun
sako. “ Koda gama wannan ne abin daya faru
sarki barzuk ya nufi hanyar fita daga fadar rike da
wannan yaro yana ta tsala kuka bai fasaba. “
Wannan shi ne abin daya faru a birnin kisra
tsakanin jaruma yazila dasu sarki daksur bayan
ta sami labarin asalinta. Acan birnin misra kuwa
tun kimanin shekaru sha takwas da suka gabata
wato a lokacin da sarkin yaki zaihar ya kashe
hukairu a gaban matarsa humaira saita ruga da
gudu izuwa kan gawar mijinta a lokacin da masu
gadin kofar birnin suka rugo izuwa wajen suka.
Kewayeta suna kallonta kawai cikin alamun
tausayawa domin sun fahimchi cewa mijinta aka
kashe. Kuma ga jaririya a goye a bayanta. Bayan
humaira ta dade tana kuka har ta gaji sai
wadannan dakaru suka haka kabari suka binne
gawar hukairu a gabanta sannan suka shigar da
ita mata jagora har izuwa cikin birnin misra daya
daga cikin yayi masa bayanin duk abin daya faru
ga humaira a gaban idanunsa bayan wannan
badakare ya gama jawabi sai sarki raihan ya dubi
humaira cikin alamun tausayawa yace wannan
bakuwa ina mai yi miki marhaba izuwa wannan
birnin. Namu mai albarka wato birnin misra kiyi
sani ma abota addinin musulunci ne kuma bisa
tafarkin addininmu bamu yarda da zalunci ba
saboda haka muna son kibamu labarinki iyakar
gaskiya bisa abin dake tsakanin da wancan
mutumin wanda ya biyoku har izuwa kofar
wannan birnin namu ya kashe mijinki kuma igudu
idan har kina da gaskiya akansa da iznin ubangiji
duak inda ya gudu zamu tura a kamoshi domin
ayi masa hukunci dai dai da laifin da ya aikata
kafin sannan muna son muji sunanki da kuma
sunan garin da kika fito. “
Lokacin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai
humaira ta sunkai da kanta kas kamar bazatace
komai ba kuma taji tsoroya shigeta bisa sanin irin
tsananin gabar dake tsakanin birnin kisra dabirnin
misra amma data tuna cewa sarki raihan yace shi
mai adalci ne sai taji dukkanin tsoro ya kau daga
zuciyarta nan take ta baiyana masa sunanta da
kuma kasardata fito. Koda jin haka sai gaba
dayan jikin sarki Raihan yakama tsuma,
idanuwansa suka kada, zuciyar sa takama
tafarfasa kamar zata kone bisa jin sunan kasar
mutanen dasuka zamo sana diyar mutuwar ‘yar
uwarsa guda daya jal a duniya wadda yake
matukar kauna fiye da komai a rayuwarsa.
Cikin tsananin fushi sarki raihan ya kai hannunsa
izuwa kan kuben takobinsa da nufin ya zare
takobin ya sare kan humaira amma sai ya kasa
kawai sai hawaye ya zubo masa ya kasa yin
komai ya kura mata ido kawai. Daga can sai yayi
ajiyar numfashi sannan yace, “yake Humaira
hakika kinci albarkacin adalci irinna ma’abota
addinin musulunci amma da tuni yanzu nasare
kanki da takobina. Kiyi sani cewa na tsani
kasarku, natsani mutanen kasarku domin sarkin
kasarku ne ya kashemin ‘yar uwata wadda na
fiso fiye da komai aduniya a ranar da mukafara
yaki. Haka kuma sarkinku ya tsani mutanena ya
tsani addininmu. A duk sa’adda wani daga cikin
jama’armu yaje kasar ku koda da zummar fatauci
ne sai yasa a kamashi ayimasa. Kisan gilla. Ki
sani cewa mu bazamu kashekiba bisa tarbiyyar
addininmu, amma akwai sharadi mai girma a
tsakaninmu daku. Ba zamu yarda kuzauna a
kasarmuba face kun karbi addininmu idan kina
ganin bazaki iya karbar addininmu to kijuya ki
tafi izuwa wata kasar daban inda zasu iya
karbarki”.
Ya yin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai
Humaira ta fa she da kuka sannan tace, “ya kai
wannan sarki mai adalci, kayi sani cewa babu
wata kasa dazan iya zuwa na tsira daga sharrin
sarkinmu da mijin “yar uwata face wannan kasa
taka. A iya abin da na fa himta yanzu a zuwana
kasarka nagane cewa wannan addinin naku
addinine na a dalci gami da tausayi da jin kai,
domin da farko dakarun da suke gadin kofar
birnin sun kamani da karfin tsiya zasu kawoni
gabanka amma dasu fahimci halin dana ke ciki
suka an kashe min mijina kuma suka ganni da
goyon Jaririyata sai suka tausaya min suka tsaya
suka binne gawar mijina sannan suka taho dani
izuwa nan fadar ka cikin salama ba tare da cin
zarafinaba ko su taba lafiyata ba. Kaima da aka
kawoka gabana da kaji cewar na fito ne daga
birnin kisra sai zuciyarka tayi baki ka harzuka
kamar zaka ka sheni amma saboda tausayi da
adalci irin naka sai kakasa kasheni. Tabbas iya
wannan karamci dana gani daga gareku ya isa na
gamsu cewa wannan addinin naku shi ne addinin
da yafi cancanta ga bil’adama a doron kasa.
Saboda haka ni yanzu a shirye nake dana karbi
wannan addini naku mai daraja. “
Koda Humaira tazo nan azancenta sai taji gaba
daya jama’ar fadar sun rude da kabbara kuma
kowa ya kamu da tsananin farin ciki.
Shikuwa sarki rai han baisan sa’adda fuskarsa ta
fadada da murmushi ba. Nan take sarki raihan ya
biyawa kumaira kalmar shahada ta maimaita
sannan ya umarci wani hadimi nasa yace da shi
a kai Humaira cikin gidansa na sarauta abude
mata dakin matarsa marigayiya kuma a bata
sutura da duk abinda take bukata. Nan take kuwa
wannan hadimin ya tafi da Humaira izuwa cikin
gidan sarki ya cika wannan umarni.
Daga wannan rana Humaira ta tsinci kanta a cikin
sabuwar rayuwa mai cike da dumbin farinciki da
kwanciyar hankali, domin babu abinda tanema
tarasa. Haka kuma sarki yasa wata baiwa
masanar addinin musulunci ta dinga koya mata
yadda ake ibada kuma ta dinga karan tar da ita
addinin musulunci.
Humaira taci gaba da renun jaririya dabira tataso
a cikin son addini kawaici, fasa ha da jarumta.
Tsananin kyawun dabira ya dimauta gaba dayan
mutanen birnin misra, don haka tun tana da
shekara bakwai ‘ya’yan sarakai da ‘ya’yan
attajirai suka rinka zuwa wajen sarki raihan
kamun kafa. Shikuwa sai yarika gaya musu dabira
‘yace ta amana awurinsa don haka ba shi da ikon
bayar da ita face ta girma ta zabawa kanta miji.
Lokacin da sarki raihan yaga dabira ta taso
da.matukar basirar daukan karatu da kuma
jarumtaka taban al’ajabi saiya ji ya kauna ceta
ainun tamkar hi ya haifeta. Bisa wannan daliline
yasa yazana cewa kullum sai ya tura a daukota
ta yini a wajensa yana koya mata karatu da
kansa kuma yana koyamata yaki. Hakane yasa
dabira ta shaku ainun da sarki sarki raihan ta
dauka azuciyarta cewa shine mahaifinta, don
haka tana kiransane da “abbanta”. Ita kanta
Humaira bata gayawa dabira gaskiyar al’amari ba
domin kada hankalin dabiran ya dugunzuma ta
shiga wani hali. Kai a birnin ma gaba daya in
banda wadanda suka san taihi zuwan Humaira
garin da yawan matasa sun dauka cewa dabira
yar sarki raihan ce ta Cikinsa.
Wani abin mamaki shine, a tsawon wadanan
shekaru har dabira ta cika shekara goma sha
takwas sarki raihan da Humaira basu taba zama
tare ba tsawon dakika dari da sittin. A koda
yaushe duk su biyun suna gudun faruwar hakan
domin gudun kada soyayya ta shiga tsakaninsu.
A binda basu saniba shine sun makara, domin tun
a ranar da sarki raihan ya musuluntadda ita duk
su biyun suka ji suna kaunar juna.
Shidai sarki raihan tun da matarsa ta mutu a
lokacin da tazo haihuwa ya zamana cewa dan
cikin nata ma yarasu sai yaji gaba daya baya sha
awar yin aure a rayuwarsa domin a ganinsa ba
zai taba samun wacce zata maye gurbinta ba.
Tun a sannan ne yayi al’kawari a zuciyarsa cewa
bazai sake soyayya ba.
Ita kuwa humaira a duk sa’adda ta tuno da
tsohon mijinta Hukairu sai taga kamar butulci za
tayi idan ta sake yin wani auran. Abu na biyu
idan ta tuno cewa itafa ba jinin sarauta bace sai
taga babu yadda za ayima sarki raihan ya sota
har ya aureta. Bisa wannan daliline ta dunga
baya-baya da shi ta na tsoron duk wani abu da
zai jawo wata hulda a tsakaninsu duk da cewa
sautari ta kanji begensa yana darsuwa azuciyarta
domin gaba dayan halayensa suna burgeta.
Al’amarin gimbiya dabira kuwa lokacin da ta
shekara goma sha takwas, kyawunta ya kara
bayyana karara a fili fiye da ko yaushe kuma ta
zama gawur tacciyar mayakiya kuma jaruma
wacce babu kamarta akasar gaba daya. Sai sarki
yasa aka bata sarautar sarkin yaki. Tun daga
wannan rana ne dabira ta samu damar rufe
fuskarta da hular karfe, bata cire wannan hula
face tana cikin turakarta amma ko acikin gidan
sarauta idan zata je wajen ma haifiyarta ko wajen
sarki sai tasa hular sai ta shiga wajen nasu
sannan take cire hular saboda yawan kallon da
mutane suka yi mata yayi yawa bama maza ba,
hatta ‘yar uwata mata da zarar sun ganta sai
kaga sun kura mata idanu baza su daina kallonta
ba face ta kule.
Allah yayi dabira da tsananin kyawu na dirin
jiki,sannan gashin kanta baki ne sidik ga kyalli da
sheki tamkar madubi ya zubo har kasan
kwankwasonta. Saboda tsananin kyallin ga shin
idan mutum ya tsaya a bayanta sai ya dinga
ganin fuskarsa a cikin gashin.
Dabira nada dara-daran idanu farare soll masu
dauke da digon baki tamkar yankan wuka. Tana
da dogon wuya tamkar na barewa. Kalar fatar
jikinta kuwa bata kasance fara ba ko ja ba, wani
irin launine na musamman wanda ido bazai iya
tantance waba saboda tsananin kyau. Kai a ta
kaice dai babu wani da namiji da zaiyi arba da
jaruma dabira ba tare da ya kamu da tsananin
sonta da begen taba.
Lokacin da samari masu isa suka yi caa ! A kan
neman auren gimbiya Dabira sai ta taka musu
birki tace baza tayi aureba har sai ta sami na
sarar yaki a kan mutanen birnin kisra, kuma duk
saurayin daza ta aura sai ta tabbatar da cewa
yafita ilimin addinin muslunci.
Al’amarin daya matukar firgita samarin kenan
guiwowinsu sukayi sanyi domin sun san cewa
Dabira tasa sharadin abin da ba zai taba yiyuwa
ba domin a kasar gaba daya ana ganin cewa
babu mai irin iliminta. Hatta manyan malaman
kasar ma shakkar ta suke domin tun sa’adda
tana yarinya ‘yar karama ta rinka kure su yayin
da a ke musabaka ta karatun Al’qur’ani da
fassararsa.
A bangaren ilimin taushidi da fighu kuwa’ dabira
ta na zarci littattafai da dama. Wasu ma jama’a
da yawa basu taba nazarin suba saboda tsananin
yawon neman iliminta da bincikenta da kuma
baiwarta ta saurin daukar karatu. Duk abin da
aka biyawa dabira ko aka gaya mata ta haddace
shi kenan har abada tamkar a littafi aka rubuta
shi, komai tsaurin karatu da yawansa kuwa. Kai
da yawan mutanen kasar misra sun daina kiran
ta da dabira sai dai suce da ita “YAR BAIWA”
saboda al’amarinta ya wuce yadda kowa ke
tsammani.Lokacin da jaruma yazila ta hango kofar birnin kisra
daga can nesa, dabara ta fadomata na yadda zata
shiga cikin birnin bisa batar da kamanninta koda
wannan dabara tazo mata sai ta tsayar da dokinta ta
sauka, sannan ta daure dokin agindin wata bishiya.
Dama awannan lokaci rana ta kwalle gashi ta gaji
ainun kuma guzirinta ya kare har ta fara jin yunwa da
kishirwa. Ka wai sai yazila ta shimfida darduma a
karkashin wannan bishiya ta kishingida akai tana
tunanin yadda zata shiga cikin birnin misra. Tana
cikin wannan hali ne kawai sai ta hango an bude
kofar birnin, sai ga tawagar wadansu dakaru kimanin
su arba’in sun fito bisa dawakai a cikin shigar yaki
kuma sun durfafo inda take zaune.
Cikin hanzari jaruma yazila tayi girgiza, nan take ta
rikide ta zama tsohuwar mafarauci sanye da walki da
rigar fata, kuma. A rataye da kwari da baka. A kafarsa
yana sanye da ta kalmin fata. A kan dokinsa kuwa
tsuntsayene kala-kala kimanin guda bakwai duk
matattu alamar cewa harbosu yayi.
Nan take dardumar dake shimfide a kasa itama ta
rikide ta zama buzu. tsuhun yana ki shingida akan
buzun yana hutawa
A dai-dai wannan lokaci ne wannan lokaci ne wannan
tawaga tazo za ta gifta ta gaban mafarauci. Koda
ganin wannan mafarauci sai shugaban tawagar yaja
linzamin dokinsa ya tsaya a gabansa. Bawani bane
shugaban tawagar face jaruma dabira. Tana sanye da
kayan yaki, kuma tarufe fuskarta da hular karfe,
kofofin idanunta da hancinta da bakinta kadai ake
gani.
Jaruma dabirA ta dubi wannan tsohon mafarauci
sama da kasa tare da karemasa kallo cikin nutsuwa
sannan ta daka masa tsawa tace, “yakai wannan
tsohon mafarauci wanene kai, kuma daga ina ka fito
sannan menene ya kawoka nan kusa da kofar
birninmu?”.
Da jin wannan tambaya sai tsoho yakama
makyarkyata cikin alamun tsoro yace, ‘ki gafarceni
yake shugabata sunana kasim kuma ni bakon
mafaraucine na fitone daga kasar rum. Na shigo cikin
dazuzzukan dake kusa da iyakar kasarku ne da tamu
ina farauta sai guzurina da ruwan shana suka kare
shina na zonan na zauna ina hutawa idan rana tayi
sanyi na shiga kasarku na sayar da ‘yan tsuntsayen
dana harbo na sami abin da zan sake yin guzurin na
koma kasata”.
Koda jin wannan batu sai jaruma dabira tayi
murmushi saboda jin cewa tsohon daga kasar rum
yake domin birnin rum ma’abota addinin
musuluncine a wannan lokaci, kuma akwai alaka
tsakanin mutanen birnin Rum da mutanen birnin
Misra.
Dabira ta dubi tsuntsayen da tsohon ya harbo
wadanda ke kan dokinsa taji sha’awarsu domin babu
irinsu a cikin yankin dazuzzukan kasar misra don
haka sai ta dubi tsohon ta ce “yakai kasim nayi
sha’awar wadannan tsuntsaye naka saboda haka ni
zan siyesu nawa ne? Kuma inaso karamu izuwa dajin
daka harbo irin wadannan tsuntsaye domin nima na
farauto irinsu domin a halin yanzu farautar muka fito.
Zan biyaka da lada na musamman idan kayi mana
wannan rakiya “
Koda jin haka sai farin ciki ya lullube tsoho kasim yayi
godiya. Nan take jaruma Dabira tasa aka bawa tsoho
kasim abinci da ruwa sha ya cika cikinsa ya koshi,
sannan ya hau dokinsa ya wuce gaba yayi musu
jagora izuwa cikin daji.
A wannan lokaci zuciyar tsoho kasim daka take kamar
zata tsaga kirjinsa ta fado kasa domin bai san dajin
da zai kai su dabira ba su sami irin wadannan
tsuntsaye na sihiri da ya samar dasu.
MEZAI FARU TSAKANIN YAZILA DA DABIRA A CIKIN
WANNAN TAFIYA TA SHIGA DAJI DOMIN FARAUTA?
@SHIN JARUMA YAZILA ZATA CIKA BURINTA BISA
ABIN DA YA KAWOTA BIRNIN MISRA?
@YAUSHENE DABIRA ZATA GANE CEWA YAZILA ‘YAR
UWARTACE TA JINI, KUMA IDAN TA GANE HAKAN
MAIZAI FARU ?
@SHIN IDAN HUMAIRA TA HADU DA YAZILA ZATA
SHAIDATA A MATSAYIN ‘YAR CIKINTA KUWA ?
@YAUSHENE ZATA KOMA BIRNIN KISRA KUMA IDAN
TA KOMA MAI ZAI FARU?
Muhadu a JARUMA YAZILA littafi na uku don jin
cigaban wannan kaya taccen labari.
Daga ni BASHIR ISHAQ TOKARAWA
08105808371
.
JARUMA YAZILA
Littafi na biyu 2
Na Abdul’aziz sani madakin gini
Created and design by:- Shuraih Usman
Publishing shuraih Usman
From http://shuraih.waphall.com
.An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Previous page 1 2 3Next page

Leave a Reply

Back to top button