Our website is made possible by displaying online advertisements to our visitors. Please consider supporting us by whitelisting our website.
KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

KAMAR SU CE DAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ad

_____

[1/14, 4:57 PM] Sis Asma: 🏉KAMAR SU CE DAYA🏉
COPY BY ZAINAB BUTALAWA

      1-5

Official

By
AsmaBaffa

  BISMILLAHAlhmdllh Allah ya kawo mu sabon Novel dina fans KAMAR SU CE DAYA.
Allah yasa ku ji dadinsa kamar sauran Novels dina da suka gabata,ina fatan zaku bibiyeni readers ba sai an gama anyi Doc ba Nafi son wanda za ana bina page by page ana min sharhi muna nishadi da zumunci.kamar yanda muka fara lfy Allah Sa mu gama lfy mu amfana da juna da sakon da Novel din ke isarwa.  FCT Abuja unguwar sai wane da wane a Abuja ma sai ka Isa kake zama cikinta ba kowanne me karamin kudi ke iya zama ciki ba sai ka sharaha ka gawurta kuma ka tumbatsa ka fetsara a Naira zaka iya zama cikinta,ba wanda zai zaton cewar a kasar nan akwai unguwa me tsari da kyau irin nan ba ko a turai sai haka,shi yasa ma kafin kaga bakar fata a unguwar zaka dade kusan duka fararen fata ke zama a wannan unguwa irin su Ambasadors,consilor na embassy da Sauran masu zama a kasar Nigeria lokaci zuwa lokaci,wani tsantsararren gida da kusan ma yafi da yawa kyau a layin,wasu motoci ne sunfi biyar tafka tafka suka shararo zasu shiga wannan gida wawakeken gaske tsayawa fada muku tsaruwar wannan gidan kadai zai cinye mana Pages duka ma,remote Driver me jan motar gaban ya danna sai ga gate ya dage sama,suka shiga wannan gidan wanda ko ina motocine na alfarma,gidane na nunuwa a duniya,tunda motocin suka shiga ko ina ma'aikata da Securities sun dai daita sahunsu suna jira me gidan nasu ya fito,sai da aka dauki kusan 30mnt bai fito ba har an kosa da jira su kam da Alama sun saba da hakan.

 Kofa aka bude masa ko ina ka juya Sojoji ne a gidan ana tsaro,kafa daya ya zuro hakan ma ya dade bai fito ba sai daga bisani ya zuro kafar dayan ya fito a gadarance cikin Isa da takama yana shan kamshi yana basarwa,wow Tabbas wannan Bature ne ko balarabe babu abinda ya hadashi da suffar bahausa ko jinin Nigeria,domin ta ko ina ba kalar nan bane,cikin turawa da Larabawa ma sai an dage da gasken gaske za a samu me kyan wannan matashi,domin wasu ma da dama zasu ce Aljani ne,za a iya karade kasar nan kowa zai iya cewa Bai taba ganin me kyau irinsa ba,kamar Aljani haka yake,tun daga dirinsa da baiwar sura cikar zati da haiba baza ka gama rudewa ba sai ka kalli fuskarsa,dole kayi kabbara ga Allah,iya saninka wannan Matashin ya zarta saninka a baiwar kyau idan ya shugo waje ko waye sai ya raina kansa Bai isa ya matsa kusa dashi ba, hancinsa codede zarkadede,dan bakinsa cut dashi pink kamar yasa jambaki,idanunsa Dara Dara shanyayyu kamar bacci zai yi,sumarsa me uban yawa baka me santsi tasha gyara Naira tayi kuka a kanta,ga wani hadaddun Saje da gemu nasa, kafafunsa da yatsunsa abin kallo,girarsa kuwa har hadewa take sabo da baki da yawa,gashi fari kar kar dashi ba irin fari na jigari jigari ba farin bature ne dashi domin yafi Balarabe fari,amma kyansa da cikar hallitar kamar Balarabe,ba zai wuce 32years ba.

gaisuwa ake kwasa cikin harshen turanci amma ko saurarensu baiyi ba fuska ba rahma ya shiga cikin palon tare da danna code din kofar cike da takama da gadara, sai ka shiga palon zaka San ma a duniya kake ne wai ko a Aljanna domin kyansa da tsaruwarsa ya wuce hankali,kamshi ne da sanyi ke tashi kawai,
Wata budurwa ce kyakyawar gaske ke zaune a palon ta nitse cikin kujeru kafa daya kan daya tana cin Apple tana kuma danna kafcececiyar wayarta,tana ganinsa ta Mike tare da Fadawa jikinsa cikin harshen turanci take masa sannu da zuwa,dan murmushi yayi kadan,cikin hausar daya fara koya Bai iya ba yace yau…Shi..ni…kinka Jo?wai yaushe kika zo yake nufi,Budurwar tace since in the morning,ci..danna…mini… English,(ki daina min English). Kansa ya nuna da yatsa ni…sho nace na gane..hausa, dariya tayi ita dai hausar sabon saurayinta na bata dariya,ba haka ake cewa ba Honey,cewa zakayi ina so na iya hausa ki daina yi min turanci.Ok na gano shi(na gane) na gane zaka ce,

Wuyansa ta sakalo cikin salo ta fara aika masa da kiss ya fara biye mata kenan yaji kamar an rike masa harshe tam,da kyar ya finciketa daga jikinsa yana huci kamar zaki,bata gane ba Sam ta kara rungumeshi nan take taji anyi jifa da ita gefe can har sai da kanta ya bugu da bango,ihu ta saki tare da rike keyarta ta dago tana kare masa kallo,honey lfy kake kuwa?jiya fa muka hadu ka bani address kace nazo mu dan huta muna mu'amula daga nan ma sai ka koyi hausa duk cikin turanci take kora masa bayani,cike wulakanci da isa,izza da gadara cikin lalacacciyar Hausarsa wacce a dole sai ya koya yace ni...ni...ba Jan iska bane,ta tari numfashinsa to kai ba dan iska bane ni kuma itace?, cike da takaici yace ni bana cinye mata,nan take ta kwashe da dariya sabo da hausar abin dariya,shi kanshi sai da yayi murmushi,wai haka hausawa suke cewa,

Tace to ai ba haka zaka ce ba na gane baka sex amma zamu iya Romancing ko? Baki ya tabe tare da cewa nop…ni bana con ina tabo mashe ne,cin can me na Shana?tace a’a Bana con noanoa irin naki,tunani ya fara na Kalmar da zai ce yace ayi maka surgery noanoa naka naki yana kamar da tsayi har cikinka ni na fada ma fact that komi ma Bana con shi na taba masha,ina feeling Bana so temper na yana rising,what do u people called it?I wanna know?Harara Ruky baby ta watsa masa sabo da ta gano tsab ci mata mutunci yakeyi baya son ta dan dai ba Jin hausa sosai yake ba,wai ayi mata plastic surgery a breast yake nufi nata ya zube,kuma baya son komai ba dan iska bane shi,tsaki taja tare da mikewa ta fice fuuuuuuu tare da shiga motarta ta bar gidan,tana cewa ita dashi har Abada dama haduwarsu ta farko kenan a resturant,dan iska har ita zai ciwa mutunci amma tana mamakin karfinsa yanda ya jefar da ita kamar Aljani daga tabashi taji wata iska ta fisgeta ta makata a bango,kai gaskiya Aljanune da shi,taya kamar ta zai ce mata boobs nata har ciki,ita da bata da girman su ma har magani take Sha dan su kara girma sai dai idan idonsa ne ya nuna masa haka,Ruky sai masifa take tana driving dama kallonsa tayi kalar kyau da gani gwarzon namijine gashi me kyau,ga kudi idan suka saba gaskiya ta more yanda zai dinga biya mata bukatunta na masha’a kuma zai tafi da ita kasar su ma suci gaba da Jin dadinsu ga Naira wannan ya cuceta dakikin banza a haka kamar gwarzo Ashe lagwani ne.

  Shi kuwa wannan Matashi tana barin gidan wani farin ciki ya ratsashi kamar an masa bushara da Aljanna,bedroom ya wuce wanka ya fesa sama sama ya shirya kansa Ashe musulmi ne sai gashi yana sallah sosai karatun Quranin sa abin saurarone sabo da dadin muryarsa ba a cewa komai sai masha'allah,yana idarwa ya fara azkhar ya dade sannan ya gama ya fada saman bed tare da jawo wayarsa ya latsa number lovely M,hello Sweet heart cike da shagwaba kamar zai yi kuka ya fara magana kamar wata mace haka yake shagwaba har yafi matan ma,Sweet heart am tired of this country gaskiya,My Son na fada ma ka daina min turanci Hausa zaka yi min so nake ka iya min yaren hausa, ur mother's tongue shi yasa nace ka fara aiki acan sabo da so nake ka iya yarena kuma ina so ka saba da kasar sabo da soon zamu dawo kasar Nigeria gaba daya da zama tunda Abbanka ya rasu me zamu zauna muyi,idan kana son yan uwanka kazo ka kawo musu ziyara,amma bazan zauna a kasar nan ba Nigeria zan dawo gwara ma ka saba,ya aikin? Alhmdllh sweetheart da wa'ala aiki,not wa'ala wahala,tun kana karami NA'IM nake koya ma Hausa amma ka kasa koya amma bari zamu dawo Nigeria ne zaka iya dole.,My love pls ba dadi kasar nan me zamu dawo muyi?tunda ina da kudi kema kina da shi me zamuyi kuma pls Sweetheart idan kina so na zauna ki dawo kasar to I missed u, miss ur food badly Dear.
 Oh! My son ka jirani zan dawo duk abubuwanka zan taho dasu ba sai ka dawo ba, kai kam ka dawo Nigeria kenan,ka jirani nan da 3wks zaka ganni Insha'allah,Kukan shagwaba ya fara mata shi sai dai yazo ya taho da ita,kashe wayar tayi cike da farin ciki.

 Asalinsa Babansa musulmin Balarabe ne tsantsa kasar Lebanon Al'awwal Mahmud,aiki ya hadasu a airport da Mummy Hajiya Zuwaira kyakyawa fara tas itama,sonta ya kamashi haka ya dage da kyar iyayenta dake Kebbi suka yarda ya aureta,Hausa Fulani ce sosai, Allah yasa itama iyayenta masu kudi ne gaba da baya,
Al'awwal dan sarkin Lebanon suna da dukiya me tarin yawan gaske,Bayan rasuwar Babansa aka bawa Al'awwal Sarauta Bai dade kan kujera ba Allah ya masa rasuwa,lokacin Na'im za a bawa sai dai yayi kuruciya da yawa sai yace shi baya son Sarauta ya barwa kanin babansa,tun kafin Al'awwal ya rasu ma basa Zama a kasarsu wato Lebanon a Manchester city suke zaune dake Amurka,danginsu kaf suna Lebanon kuma alhmdllh suna zumunci sosai, bayan aurensu Na'im shine Babba sai kannensa Irfan,Hunaif sai auta Aisha,duk a uk suke zaune can suke makaranta,Irfan da Na'im sun gama har Masters,Hunaif yanzu ya fara University,Aisha tana secondary schl,Hunaif da Aisha baza a dawo dasu Nigeria ba sai sun gama karatu zasu dawo sai dai suzo Hutu.

Kasarsu daya ta rage tal a duniya wato ta bangaren uwa Dada Babar Hajiya Zuwaira Mummy, Zuwaira mutuniyar kirki ce ga son yan Uwa da dangi,kuma ga taimako tana son kasarta da hausawa shi yasa tunda mijinta ya rasu tace baza ta kara aure ba yaranta zata rike ta dawo gida Nigeria kusa da yan Uwanta,Arzikinsu yayi yawan da duk wani dan uwan Zuwaira dake kauye tuni sun maidasu cikin birni,Dada kakarsu Babar Mummy ma gidanta daban a cikin Abuja da yan aikinta, sauran kuwa duk suna Kebbi cikin city suna Jin dadi,maza da mata Zuwaira tana nema musu aiki tana biya musu kudin makaranta,ta ko ina Zuwaira halayenta sunyi bata da makusa,haka ma mijinta Al'awwal Abban su Na'im kafin ya rasu mutumin kirki ne na gaske.

 Na'im da yan uwansa suna da tarin ilmin addini dana zamani,kuma alhmdllh suna aiki dashi kasancewar sun samu tarbiyya sai dai yanayin Zamansu a kasar waje dole suna abubuwa da basu dace ba da Rayuwar tamu kasar ko nace rayuwar musulmi,baya ga haka dama dole a samu dan Adam da laifi dole ne sai dai wani yafi wani.
basu dauki mace Nada banbanci da maza ba Sam,yanda zasuyi kawance da namiji haka sukeyi da mace,gwara ma Na'im shi baya neman mata sai dai tarin frnds mata kamar me hadadde wayayyu masu kudi amma kuma yana son yayi Sex,yana so yayi rayuwa dasu yana da karfin sha'awa amma abin haushi ya rasa dalili da mace ta rabeshi da niyyar Jin dadi sai yaga ta fadi ko ta bugu da jikin bango,kuma nan take zaiji ya tsaneta sai yaga ta rikide ta koma mummuna me suffa marar kyau,duk abinda ke birgeshi a jikinta sai yaga sun koma abin kyama,abu daya ne ke rage masa Zafi Shan giya sama sama bada yawa ba,sabanin su Irfan basa Shan giya sai dai suna dan having sex da mata amma bada yawa ba sai lalura ta taso,
 Aisha kuwa zaman turai yasa mata ta saba da shaye shayen kwayoyi da syrup, sai Lesbian da ta fara jefa kanta ciki, amma dukkansu suna addini sosai kuma kowa yasan laifin da dan Uwansa ke aikatawa.

Na’im Babban likitan kwakwalwa ne a Abuja Mummy ta bude masa katafaran Hospital na gani na fada wanda babu kamarsa likitoci ko ina a ciki,sannan kuma consilor ne a cikin Embassy na kasar lebanon dake Abuja,sune masu yarda a baka visa kasarsu sune masu interview cikin lebanon Embassy, haka kuma yana kula da dukkan business da companies nasu dake kasar Nigeria,shi ke kula da komai na dukiyarsu dake Nigeria,Irfan kuma me Kula dana kasashen ketare,Hunaif ma yana taimakawa.
Na’im duk yafi yan uwansa kyau da komai ma,jinin Sarauta jinin kudi,gadon Arziki,ga kyau shine kadai ke nuna Sarauta a jininsa take,kana ganinsa kasan ya hada jini da Sarauta, matsalarsa Shan giya kadan,tarin kawaye mata amma fa masu class ba karamar wacce ta isa bace zata iya ganin Na’im har su hadu ba, ba a haduwa dasu wajen kananan yara masu karamin karfi,

Matsala ta biyu bashi da mutunci idan yaga dama yanzu zai wulakanta mutum,ga isa takama da gadara,baya saurarar rayuwar wasu bare har ka bata masa rai ko kuma ya wulakanta talaka yaushe ma ya shiga harkarka da har zaku samu matsala,kuma ko uban me zakayi bazai ce ka daina ba wai shi Bature ba ruwansa rayuwarka ce,yasha kama Aisha da mata suna Lesbian Bai taba ce mata ta daina ba kyau ba,haka kannensa ko me zakayi Good for u rayuwarka ce,
 Akwai barnar kudi wajensa yanzun nan sai yayi wasa da dollers ba abinda ya dameshi mahaukaciyar kyauta yakeyi baya karama,ko zakka idan zai fitar to sai wanda ya bawa ya washe,kyautar kudi a wajensa ba komai bane,ko ina a motarsa kudine,haka kayansa ma a aljihu ma har cikin takalmi idan yaga dama Dollers zaka gani ya fyalla ta a cikin takalmi ya baka kyauta,
Watarana mutunci watarana babu sai tsiya,haka ma'aikatan sa duk sun San halinsa da kallon Banza watarana watarana fara'a.
Hospital idan yaje tab ai duk patient din da sukayi dace ya dubasu da kansa ba sauran Doctors dake aiki karkashinsa ba to zai wahala patient ya biya kudi kyauta zai masa komai komai girman cuta.
Shi yasa yanzu sunansa ya koma Me Imani,Doctor me Imani,baya Jin hausa sosai sai dai akwai me karasa bayani yanda zai gane idan yana mu'amula da hausawa,shi yasa ma ya dan iya hausa da yawa,a hospital har so ake yazo aiki ranar Monday da Tuesday yake zuwa suna Shan dariyar hausar tasa,wanda basa Jin hausa ya musu turanci amma Mummy dukkan ma'aikata da tasa aka Eba a Hospital Hausawa sunfi yawa sabo da kishin kai, kusan Kullum sai yaje wajen Dada kakarsa sun gaisa tana kara koya masa hausa.wannan kenan nan gaba zaku ci gaba da Jin halayen Na'im wanda ban fada ba sai gaba zaku jisu yanda suke,amma wannan sune Manyan.


   Hanyar Abuja Can cikin daji akwai wata ruga ta yan Fulani usul ciki,amma duk da haka rugar a kusa da gefen titi take,tana da girma ba laifi,harda makaranta primary da secondary tare da islamiyya,Fulanin dake wannan dajin ko hausa kadan suke ji basu iya sosai ba amma suna Jin hausar,
 Wata Dattijuwa ce kyakyawa me cikar haiba ta fito domin zuwa asibiti dake Suleja Hanyar Abuja kusa dasu,Dattijo yana rike da hannunta da Alama mijinta ne sai sannu yake mata,haka suka shiga mota har suka karasa wannan asibiti,bayan an duba Lafiyarta an tabbatar rashin haihuwa ce ta kawota tunda likita yace baza ta taba haihuwa ba haka ma mijinta shima,cike da tawakali suka siyi magunguna suka fito wajen me gadin wannan asibiti suna hira dashi sama sama,me gadi ya kalleta tare da cewa Hajiya idan baza Ku damu ba ko zaki iya rike min yata guda daya danake da ita?tunda bakya haihuwa kuma na yaba da halayenku zan baku tarihina idan kun amince sai na bar muku yata kyauta Ku riketa Amana.
Sunana Ahmad wanda akewa lakani da Tall Man a cikin Garin Borno muke da dangina tare da dangin matata wacce Allah yayiwa rasuwa kwanan nan,Matata yar Asalin Nijar ce buzuwace gaba da baya amma danginta kaf suna Borno a unguwarmu,Yan uwanta da kuma kanin babanta sai sauran danginta amma iyayenta dama sun Dade da rasuwa,Bayan munyi aure da shekara biyu Allah ya bata ciki ta haifa min yata sunanta Salma watan Salma 7 a duniya Allah ya karbi rayuwar matata Khairat wacce Hawan jini ya kama da karfin gaske,
Bani da Uwa bare uba nima bani da yan Uwa mata sai maza a zamanin nan idan na bawa dan Uwana namiji rikonta matar zata iya gallaza mata tunda ba shine zai zauna da ita ba,haka idan nayi aure ban san wa zan aura ba,haka na hakura na bawa dangin matata Khairat yata Salma,amma yau Salma shekarta biyu a duniya wahalar rayuwa take Sha a hannunsu rayuwar yanzu ba imani ba tausayi,

idan kun yarda muje garinmu kuga gidanmu ayi yarjeniya da dangina da dangin matata kusan juna sai ku tafi da Salma wajenku Ku rike ta Amana,sai Ku dinga kaita wajen dangin ubanta dana uwarta suma zumunci kawai amma na baku ita halak malak Allah yayi jagora kune iyayenta daga yau,Murna wajen wannan dattijai ba a magana,kamar wasa ya dauki Hutu washe gari suka tafi har Borno state,Dukka sun gaisa da danginsa dana Khairat Babar Salma,hannu biyu suka karbesu amma da gani Salma a cikin wahala take ba a kula da ita Sam,haka yayi musu bayani ya dauki Salma da kayanta na sawa ya bawa wannan dattijai da sharadin zasu dinga kawo Salma ana gaisawa da danginta suna zumunci,cikin dangi babu wanda yace kar ayi haka su zasu rike kowa mukus yayi harda fatan alkhairi,cike da murna dattijai suka koma gida suka nuna Ahmad Tall Man baban Salma ga kowa dake da alaka dasu a rugar Fulani duk da cewar yan uwan nasu suma kusan duk sun kare sai kadan daga ciki sai makwafta da abokan arziki,

 Kamar wasa tsakani da Allah suke rike Salma ko yarsu baza taji dadi haka ba sabo da gatan da suke nuna mata,ubanta Tall Man idan yazo ganin yarsa dadi yake ji ba kadan ba yana shi musu albarka,haka mutanen gari ma,Salma sai abinda take so shi yasa ta taso cikin shagwaba da tabara ta gaske,amma suna bata tarbiya ta gasken gaske, tana da shekara biyar suka sata a schl tana ilmin addini dana zamani,kamar yanda alkawari yace suna kai Salma Hutu cikin danginta tayi Hutu acan,duk Hutu a Borno take yinsa Affa da kansa yake kaita can abin sha'awa.

tana da shekara takwas Ahmad Tall Man mahaifin Salma ya rasu sakamakon ciwon Koda daya kamashi ba tare da doguwar jinya ba,masu rikon Salma sunyi kuka sunyi zaman makoki,Salma tana primary 4 aka fara ganewa kamar tana da tabin kwakwalwa,sai aganta tana ta maganganu ita kadai,ko aga tana dariya ita daya,wani lokacin kuma tayi ta kuka tana shagwaba,sai ta dinga kallon waje daya,watarana kuma tayi ta wasa tana maganganu kamar da wani takeyin maganar,sai aga tana shafa iska ko ta rungumi iska,a schl ma haka takeyi,watarana kuma aji tana ta rawa tana cashewa kamar tana Jin kida har karkata kunne takeyi,bata da kokari a sauran Subject da dama banda English da French,amma fa Idan anzo exam,a class duk tambaya zata amsa amma kuma bata da kokari kan kowanne subject sai dai English kadai sai French idan ana musu,har kure malamai takeyi indai akan yare ne to baka isa ka kureta ba.

 Haukar Salma bata kara ta'azzara ba sai da ta shiga js1 nan aka fara kiranta da living things,sabo da bata iya ba,ance what is living things?Salma tayi sauri ta mike cikin iyayinta tace Living things cike da shagwaba,tace living things is a living things that live on earth with a life,akwai aka kwashe da dariya sabo da Salma kowa yasan a exam kadai take kokari ta cinye du ana mamakin hakan,
 Gata dakikiya a class amma da anzo sauran Subject sai ta koma jaka sentence daya baza ta iya kawowa ba bare ta bada definition na abu, sai languages, wani lokacin ma gani za ayi ta tsurawa waje daya Ido tana murmushi ko tana Surutu kasa kasa,kayi mata dariya taci ubanka tana da karfi idan tsokanarta kayi amma idan ita ta tsokaneka to sai ka mata duka baza ta iya komai ba,wasu har suna cewa Aljanune da Salma living things, Sunyi wani Sabon Malami komai sai yace collaborate,shine kullum Salma ta rike aikinta tace Collaboration,shike nan wannan sunan ma yabi Salma,Salma Collaborate ko Salma Living things.

 Salma tana da hakuri da Hankali,bata Harka da kowa daga iyayenta da suke riketa shike nan kowa nata ne ba ruwanta da duniya da abinda ke cikinta,Salma me tsananin kyau ce na gasken gaske,fara ce ba fara can ba normal farinta yake,hanci me kyau dan dai dai dashi,bakinta dan karami me dauke da kananan hakora masu kyau farare,tana da Dimple,skin dinta luwai luwai,doguwa da ita ba siririya ba ba ramammiya ba,gashinta ya wuce kafada baki me kyau da santsi,ga wani kwantacce yalala a gaban goshinta dankwali baya iya rufewa har wajensa, idan kaga Salma sai kace yar kasar Ethiopia ce skin dinta da ko irin nasu ta hadu karshe a Ethiopia ma sai kyakyawar gaske za a samu irin Salma komai yaji ga uban Hips.

Salma bata da makusa sai dai akwai babbar matsala Salma bata Sallah ko kadan,duk yanda ka damu da tayi Sallah to baza ta taba yi ba,haka duk wani abu da ya shafi addini bata yi,yin duniya baza tayi ba,ko na ganin Ido sai taga dama,tana da surutun tsiya idan ta samu waje fadi ba a tambayeka bace,komai ta fada idan taga dama bata da sirri,haka ga tambaya har tafi dan jarida amma ba a gane hakan sai Salma ta aminta da mutum sosai zatayi ta zuba har sai ya gaji. Halayen Salma kenan zaku iya tsintar wasu a cikin novel nan gaba.

AsmaBaffa
[1/14, 5:09 PM] Sis Asma: 🏉KAMARSU CE DAYA🏉

 6-10 11-15

Official

By
AsmaBaffa

Godiya nake fans Allah ya bar kauna.😍❤.  Salma kamar kullum ta dawo daga Islamiyya wajen magriba ta ajiye Jakarta ta fada kitchen dinsu wanda kamar yanda gaba daya gidan na kara da yayi ne irin bukkar fulani,haka shima kitchen din nasu,
Tuwon da Ummitu ke tukawa shi ta karba tare da cewa Ummitu kawo na tuka miki,a'a jeki ki huta kiyi sallah ga magriba ta gabato,badan taso ba haka ta fito ta dauki buta tayi alwala tana jin bakin ciki a ranta kamar ta kashe kanta Sabo da takaici haka dai taje tayi Sallah tana kunci.

Tuwonta ta karbo taci ta koshi,suna zaune a tsakar gida Affa ya shigo ya dawo daga kiwon shanunsa da baza su wuce guda biyar ba,domin Affa talaka ne sosai a rigar tasu,sannu da zuwa Salma ta masa tana washe baki,sai da ya huta shima yana cin tuwonsa Salma tace Affa ka dinka min Sababbin kayan sawa nawa duk sun mutu gashi muna komawa hutu zamu shiga Ss2 kaga na zama yan mata,kuma aure za ayi min,wai Affa yaushe za ayi min auren ne?nima na huta? Dariya Affa da Ummitu sukayi in da Sabo sun saba da shirmen Salma,Magana Affa yayi yana murmushi yace 'Yata kenan bakya rabo da shiririta ina Saurayin naki?ke da ba kya kula kowa a samari da wa za a daura auren?
Da Sauri Salma tace Affa ai ina dashi kullum wlh yana zuwa zance Sunansa Raheel fa,baka ganshi ba babu me kyansa a duniya,ya hadu,kuma me kudi da ilmi,tun ina primary yake zuwa zance wajena yanzu ma har kasashen waje yace zai kaini harda China,Paris etc ni wlh Bazan taba son wani sama dashi ba shi nake so idan ba shi mutuwa zanyi kawai.

 Ummitu ta saki baki tana jin rashin kunyar Salma,Affa kuwa dariya yayi yace To Salma Allah nuna mana,yanzu sabon dinki bani da kudin da zan miki Sabo ki jira Allah ya hore min,kinga shanuna sun kare saura kadan wanda dasu muke samun na abinci da muke ci da makarantarki.
To Affa Allah ya hore maka,ta tashi tare da cewa sai da Safe bacci nake ji,Tare da Ummitu suka shiga dakin tana tursasata dole wai sai tayi Sallar Isha ,gefe guda ta kalla sai suka hango trolley set guda kala Uku masu tsananin kyau,Ummitu da gudu ta bar dakin tana kiran Affa jiki na rawa.

 Da Sauri Affa ya shigo ya ga akwatina shima ya girgiza,yace kar a taba sai ya fadawa malaminsa,Amma Salma ta kalli jikin Bango gefe daya sai dariya take bangalawa,tana magana cikin yaren Larabci kamar balarabiya ta koma,
Suna tsaye tazo ta bude akwatin tana murmushi,kaya ne na alfarma kamar lefe kayan kalar na yaran shugaban kasa haka suke Sabo da karshe ne wajen tsada da haduwa,shaddoji,atamfofi ,laces,materials,kanan kaya, inner wears,ready made dogayen riguna dasu Pakistan,takalma na gaske da jakankuna,harda cosmetics masu tsadar gaske,sai Uniform sababbi kala biyu da schl bags kala biyu da sandals,harda hijabai na sawa komai wanda mace zata nema akwaisu a wannan kaya,ba abinda babu komai yaji,Ummitu da ta manne jikin Affa Sabo da tsoro tace kaga dariya ma take tana jin dadi.

Salma kuwa tace da wannan hadadden saurayin Aljani Raheel tnx alot ka gama birgeni dan Allah karka juya min baya Bazan iya rayuwa babu kai ba,matsowa yayi cikin takunsa na birgewa tare da rungume Salma tana shakar madarar kamshinsa,
Ki shirya Babyna zan baki ajiyar yarana idan time na haihuwa yayi zan dauke abina,Salma Hawaye ya tsiyayo mata tace ai za ace cikin shege nayi fa ta karasa cike da shagwaba,

Raheel ya saki murmushi yana lashe mata Hawaye da harshensa yace kwantar da hankalinki bafa saduwa zanyi dake ba kawai cikin Matata zan Sa miki months din haihuwa na cika sai na kwashe abina,murmushi Salma tayi tace tunda ina Sonka ai ba komai yanzu yaushe zan fara yin sallah kullum kullum ka hanani yi,
Nan take Raheel ya bata fuska yace ba yanzu ba sai nan gaba kafin mu rabu Sabo da naga Alama sai mun rabu watarana,Shagwaba su Affa suka ga Salma nayi hade da kuka da burbuwa tana Allah mutuwa zanyi idan ka rabu dani,ina zan samu me kyanka a duniya?

 Wani kallo me dauko da zallan so Raheel ya cillawa Salma wanda yasa nan take taji kunya tare da wani sabon shaukinsa,yace akwai mai kama dani sak a duniya watarana kuma zaki ganshi,suffar mu iri dayace ba banbanci,share zancen tayi tare da cewa ni tunda kama kuke ba kai bane Bazan taba sonsa ba,kwantar da ita saman cinyarsa yayi yana shafa kanta a hankali tace My love ya kamata ka aureni mun dade tare tun ina yar 3yrs na sanka nake ganinka muke tare muna soyayya gashi har na zama yan mata,
 Ina 17yrs fa yanzu,kallonta Raheel yayi cike da shaukin yana wani lumshe mata ido kirjinta ya tsurawa ido sannan yace lallai kin zama yan mata Salma ina matukar son wannan Balls din naki guda buyu,hannu yakai da niyyar shafawa Salma ta rike hannun tace ai kayi alkawari sai munyi aure fa karka taba.

 Dariya yayi hakoransa masu matukar kyau suka bayya dimple dinsa ya lotsa yace ashe baki manta ba,yanzu kunyi hutun schl My Heart ya kamata mu koma Paris wajen yan uwana ku gaisa sannan na kaiki yawo ki zaga duniya ki waye ki san me duniya ke ciki,
 Murna ta fara yi tana tsalle gaba daya su Affa suna kallon ta ita kadai basa ganin masoyinta,Kallon Raheel tayi tare da shafa gemunsa tace wannan kayan da ka siya min kasan Su Ummitu baza su yarda kuma zasuce magani zasu yi min wai bani da lfy.

 Kyalesu maganin su bazai ci mu ba,kuma batun kaya daga yau ko me zan baki baza su iya magana a kai ba shuru zasuyi kisa abinki so nake duk inda kika shiga kifi kowa a wajen,mota ma zan koya miki kwanan nan na siya miki ki dinga hawa,

Murmushi tayi tace to idan su Affa suka ki yarda fa?baza ma su iya magana ba na fada miki,just do as i said,kuma ko kudi kike nema kawai kice Raheel ina son Kaza zaki gani na baki karki ji tsoro kome zaki gani na baki,yanzu zamu fara love ma dama rainonki nayi kuma Babyna ta girma sai na canja miki rayuwa kin koma yar gayu me kudi duk inda me kudi ke jin kansa kema haka.

 Salma sabo da murna bata San Sanda ta fada jikinsa ba ta rungumeshi tace ka canja mana katon gida mu bar kauye,Raheel yace a'a ni bazan taimakawa kowa ba sai ke kadai ko zasu mutu da talauci sai dai idan na baki ki taimaka musu amma bata hannu na ba,ni haushinsu ma nake ji suna hanamu sakewa da addua,dan kawai iyayenki ne amma da tuni na batar dasu a duniya,

Salma tace ai kuwa kana musu wani abu wlh na daina kulaka,karya kike yarinya,ko ta dole sai kinyi abinda nake so,Salma tace wlh baka isa ba,cikin hasala yace kin San ko ni waye kuwa kike fada min haka karki sa na gwada miki rashin imani,
Allah indai baka son su Ummi da Affa ni ma Bana Sonka kuma bazan rike ma yaranka ba a cikin cikina ba,nan take idon Raheel ya koma jajir,Guguwa ta tashi tayi jifa da Salma,nan take sai ga Salma ta fara tsiyayo da hawayen jini sharrrrrr,Hannu tasa ta cire dankwalinta ta fara tsigo gashinta tana zubesu a kasa,Affa da Ummitu duk suna kallonta amma basu San me take cewa ba sabo da ta koma yaren Spain Spanish dashi take magana.

 Faduwa kasa tayi hannayenta da kafafunta suka shanye tana ta faman kakari da gurnani,
 Affa da gudu yayi kanta yana karanta mata ayatul kursiyyu,shima jifa dashi akayi gefe ya Sume,Ummitu ta fice da gudu tana kiran jama'a a taimaka mata,sun taho tare da maza da yawa Affa suka gani har ya farfado ya Dafe kansa yana Nishi,Salma kuwa ba ita ba labarinta,

 Tuni Raheel ya Lula da ita kasar Paris,cikin wani katafaren gida ya ajiyeta yana gefenta abin mamaki Salma tana farkawa sai gata garau kamar bata yi komai dazu ba,gashinta Bai ragu ba duk kuwa da yanda ta tsigeshi,Bata san ma tayi komai ba bata iya tunawa,Tana kusa da Raheel cikin hadaddun kujerun wanda babu kamar su a duniyarmu,
Ta saba da gidan yana kaita duk wani abu ta iya amfani dasu sabo da komai na manyan masu kudi Raheel ya gama koya mata ta waye,

 Amfani da waya da kuma computer Salma ta gama kwarewa sabo da yanda yake bata nasa yana koya mata,
 Cikin yan uwansa duk ya kaita amma a suffer biladama take ganinsu,sunsha yawo kasashe daban daban,ta kara wayewa,kimanin 3wks aka kwashe ba Salma ba labarinta,yau katsam Ummitu da Affa suna tsakar gida sai ga Salma ta fito rike da buta daga cikin bayi,ga jakarta a rataye na kayayyakin da ta siyo a paris.

 Ummitu sun rigada sun gano Aljanu ne masu karfi suka kama Salma,basu ce mata komai ba haka suka ci gaba da muamularsu

Cikin kauye kuwa magana ta watsu cewar Salma Karuwanci ta fara yi,ta koma sa kaya na masu kudi ta koma kamar yar shugaban kasa,komai nata me tsada,musamman irin wayar dake hannunta da computer ko a city babu me irinta a tsada da kyau,
 Kuma sai aga tana ta fito da kudi sababbi tana kyauta dasu sai abinda take so takeyi,watarana kuma a nemeta a rasa har tsawon kwanaki,basu San Salma har daji Raheel kaita yakeyi waje waje yake kaita,
 States na Nigeria kuwa ba inda bata sani ba,karatu ma tunda suka shiga ss2 sai taga dama take zuwa,kullum Raheel na tare da ita ya hanata addini,tana so tayi amma a ranta baza ta iya ba.

 Tun ranar da ta karanta Qurani sau daya sai da tayi sati guda tana kulle a daki Raheel yana gana mata azaba iri iri dole ta daina karantawa da kanta.

Soyayya kuwa Shanta suke basu fasa ba,yanzu anga kawai Salma ta iya tuka mota abinta,kuna tsaye za kaji tace Raheel I need money ko adadi nawa ta fada sai kaga ta zaro daga aljihu ko bag dinta,abin haushi kudin basa mafanar kowa ayi abu me muhimanci sai na shiririta,Affa garin gigin nemowa Salma magani gaba daya ya rasa shanunsa kaf da suke samun na abinci dasu,talauci yayi musu katutu da kyar suke iya daura tukunya watarana,abun yaci tura addua sukewa Salma ba dare ba rana amma kullum abin gaba yakeyi,domin yanzu sai ayi wata guda ba a ga Salma ba,ga gorin mutan kauyen cewar sun kasa bawa yarinya tarbiyya suna fakewa da Aljanu bayan Karuwanci takeyi,me Aljanu za a gani harda mota tana ja ta alfarma,kaya kamar yar Gomna,wa zai ce Salma a kauye suke har ta fi yan Birni komai da komai,kudi wasa takeyi dasu,marikanta suna cikin talauci sai taga dama zata basu yar Dari biyar ko Dubu daya,basu San Aljani Raheel shine Bai son yaga su Affa sunyi kudi ba,sabo da kar su samu kudin yiwa Salma magani,shi yasa ya jefa musu talauci,suna ta cikinsu ina neman wani magani.

Ad

_____

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button