JIDDAHTUL KHAIR 28

Jiddah ta langwabar da kanta tace “Ai ban sani ba, in dai mata na xuwa sai mu dinga tafiya tare” That wasn’t were Abuturrab wanted the conversation to end, but because of how cautious he was with time sbda sllhn juma’ah, ya kalleta kawai yace “Kafin in dawo masallaci ki tabbatar kin sake wanka kin shirya cikin atamfa, sannan ki karya…” Sae kuma ya hade rai, Ta sauke idonta kasa tace “Ni na karya da asuba ai” Daga sama har kasa ya kalleta sannan ya juya ya fita ta bi sa da kallo…. Ko da ya dawo juma’ah har ta shirya kamar yanda yace mata, Hijab ya sa ta daura kan atamfar, bayan ta sauko ta tsaya tana kallonsa, sau daya ya kalleta ya dauke kai yace “Fita ki jirani a waje” Ba musu ta nufi kofa ta fita daga parlon, sae a sannan ya tashi ya kashe appliances din gidan ya dau makullin motarsa da hulansa ya fita, the ride was silent har suka iso gidansu, gaba daya he was absentminded, yau da safe ma kiran Aunty ne ya tashe sa, har sannan kuma ya ki daukan kiranta, then is he even suppose to go home now? bai yi parking a kofar gidansu ba in case of necessity, ya juya yana kallon Jiddah yace “Ki jirani” Bai jira tace komai ba ya bude motar ya sauka…. Da murmushi Abuturrab ya amsa gaisuwan mai gadinsu ya shiga cikin gidan, sosai ya ji hankalinsa ya kwanta da kanninsa suka ce Aunty ta fita, Yana kallon Ramlah yace “Ina ta tafi?” Ramlah tace “She left for Abuja this morning” Shiru yyi yana kallonta, can ya nufi parlon Umminsa, ganin bata parlon ya fito, ganin ya nufi kofar fita Ramlah tace “Ummi na bedroom fa” Bai tanka ta ba har ya fita, tare ya dawo cikin gidan da Jiddah, murmushi kawai tayi ma su Ramlah da suka gaisheta, ta bi bayansa xuwa parlon Mahaifiyarsa, kafin yace mata komai ta xauna a kasa, ya karasa cikin bedroom din Ummi da sallama, gaisheta yayi da ladabi, ya shafa kansa yace “Ummi xa ku gaisa da ita a parlor” Ummi tace “Ohkk” Mikewa yayi ya fito parlon, ya xauna kan kujera, ba a dau lkci ba Ummi ta fito, jiddah ta sunkuyar da kanta ta gaisheta, Ummi ta amsa da murmushi fuskarta tace “Ya ku ke?” jiddahh tace “Lafiya lau” Ummi tace “To madallah, sannun ku da xuwa” Ummi dake kallonta kasa kasa ta ga ta canxa mata sosai, haskenta na ainahi ya fito ga wani glowing da take yi, Shi dai Abuturrab danna wayarsa kawai yake, jin Umminsa bata kuma cewa komai ba ya daga kai ya kalleta yace “Ummi wai Aunty ta tafi Abuja?” Ba tare da ta kallesa ba “Ai na xata xaka fi kowa sani tunda kun fi kusa” Ya sunkuyar da kansa yace “Aa bamu yi magana ba” Ummi tace “Ayyo” yace “Yaushe tace xata dawo?” Ummi tace “Baka da lambarta ne?” bai kuma cewa komai ba kuma bai dago ba, Jiddah dai sai kallon Ummi take, Bayan few seconds Abuturrab ya dago yace “An kawo lefen Ramlah ne?” Ummi tace “Bakwa magana da Ahmad din ne?” Yace “Shekaranjiya mun hadu a Abuja da na sauke jirgi a airport din can” Da sauri Jiddah ta kallesa, suka hada ido ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta, turo baki tayi, Ummi dai tv kawai take kallo, Ya dauke kai yace “Amma yace min xai shigo kadunan yau, kilan xanje daukosa a tashan jirgi anjima” Ummi tace “Allah ya kawosa lafiya” yace “Ameen” Ummi tace “Idan kaga xaka iya sai ka bar ta nan har bayan bikin, tunda ranan talata xa su fara shagalgulansu” Abuturrab ya d’an yi shiru, can ya daga kai ya kalli Ummi yaga kallonsa take, suna hada ido tace “Ranan bikin sae ka kawota” Da sauri yace “Aa Ummi gobe xan kawota tunda bata xo da kaya ba” Ummi tace “Aa a bari ranan bikin dai” Yace “Uhn xan kawota goben in sha Allah” Ummi tace “Baxa ka siya mata ankon bikin ba?” Ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Nawa ne?” Ummi tace “Kala uku ne, daya na family, sai general one da xa a saka ranan yini, sai kuma na dinner, although naji yan matan sun fidda wani da xa su saka ranan talata” Yace “Nawa ne duka” Ummi ta hada masa kudin gaba daya tace “Gaba daya 40k ne” Yace “A dinke xa a siyo kayan?” Ummi tace “Ehh, da yake kayan dama a kyauta aka samosu daga kasuwa, iyakar kudin dinkin ne dubu arba’in” Abuturrab ya bude ido ya fara dariya yace “Ummi tambaya fa kawai nayi” A takaice tace “Nima amsa na baka” Ya shafa kansa yana murmushi bai ce komai ba” Ummi na kallon Jiddah tace “Su Ramlah na can daki kije ki samesu tunda naga baki son magana” Tayi murmushin karfin hali ta mike ta nufi kofa, Abuturrab ya mike yace “Ai bata san dakin ba, i will back Ummi” Da ido kawai Ummi ta bisa da kallon mamaki har suka fita. Dakinsu Ramlah ya kai ta, Ramlah na xaune da Siyama sai wata kawarta da Aisha step sis dinta, tana ganin Jiddah ta mike tana welcoming dinta da fara’a, bai amsa gaisuwan yan dakin ba banda na kawar Ramlah da bai sani ba, sannan ya juya ya fita ya koma bangaren Umminsa….
Karfe hudu saura yace da Ummi xai je dauko Ahmad a train station, Ummi tace “Toh Allah ya tsare” Yace “Ameen” Daga haka ya fita daga parlon, dakin su Ramlah ya nufa, Jiddah na xaune tana ma Siyama tsifa, su Ramlah suna ta labari a dakin ganinsa duk suka yi shiru, yana kallon Siyama yace “Ke tsifan sai an maki??” Tayi dariya tace “Ita tace ta xata min Yaya” Yana kallon Jiddah yace “Kinci abincin ko baki ci ba?” Ramlah tace “Yanxu muka gama cin abincin fa yaya” Wani kallo ya jefa mata yace “Nayi da ke?” Bata kuma cewa komai ba, yana kallon Jiddah fuska daure yace “Tambayar ki nake” Tace “Mun ci” juyawa yayi ya fita, Sai da Ramlah ta tabbatar ya tafi don har sai da taje ta d’an bude kofar taga babu kowa wajen sannan ta dawo tana kallon jiddah da murmushi tace “Yaya yana ji dake kamar yanda yake ji da profession dinsa…” Jiddah dai bata ce komai ba ta ci gaba da tsifar da take…. Bayan kusan awa daya da tafiyar Abuturrab Aunty ta dawo gidan, alamar dai ita ma train din ta biyo daga Abuja ta dawo, tun da ta kyallara ido taga Jiddah taji kamar taga mugun abu a gidan, ko gaisuwar Jiddah bata amsa ba, bata sake shiga damuwa ba sai ganin wani haske da kyan da Jiddah tayi alamar kwanciyar hankali, ita Abuturrab xai raina ma wayo?? Ta kusa minti ashirin xaune gefen gado a dakinta, ta saka wannan ta kunce wnn, ita Abuturrab ke son kunyatawa gun aminiyarta? Takanas ta shirya yau ta tafi Abuja ba mahaifiyar Aneesah hakuri bayan sun sanar mata abinda Abuturrab din yyi ma Aneesah a airport kamar yanda Aneesan ta gaya ma uwarta… Wani murmushi Aunty tayi tana gyada kai. Jiddah na ta xaune parlorn Ummi ita kadai don su Ramlah da yan matan gidan sun fita xuwa gun tailor, Ummi kuma ta hanata bin su tace mijinta bai sani ba, Jiddah na ta juya furucin Ummi a kanta, wai mijinta, ai ba mijinta bane Aliyu, tunanin hakan kawai sai taji jikinta yayi sanyi sosai, Ummi ce ta fito daga dakintaz ganinta xaune ita kadai tace “Ki shiga kitchen kiga ko aunty na ciki ki tambayeta abinda xa ki kama mata Jiddah” Jiddah ta kalli Ummi a hankali tace “Toh” Mikewa tayi ta fita bangaren Ummi, tayi hanyar kitchen din, jikin kofa ta tsaya tana lekan kitchen din don ita har taji tana tsoron matar nan da ake ce ma Aunty, ganin Auntyn a ciki, cikin sanyin murya tace “Aunty me xan kama maki wai?” Juyawa Aunty dake yankan cabbage tayi tana mata wani irin kallo tace “Me xa ki kama min?” Jiddah ta gyada mata kai gabanta na faduwa, Aunty ta ajiye wukan hannunta ta kunduma mata xagi tace “Ke a wa xaki kama min aiki?? Yanda kika samu wajen xaman yin iskanci gidan Aliyu kin xata nan ma haka ne, toh bari kiji… Wllh ki saka a ranki cewar xamanki ya xo karshe a gidan Aliyu, sai dai ya dinga bin ki can kauyen naku yana iskancin da yake dake, yau xai san ni mahaukaciya ce wllh” Jiddah dai kallonta kawai take a ranta tana kara nanata kalmar da ta jefa mata wai iskanci, tana nufin iskanci suke yi da Aliyun kenan? Muryar Aunty ya sake dawowa da ita, ciki tsawa tace “Baxa ki fita ki bar min kitchen ba mayya….” Cikin sanyin murya Jiddah tace “Ni ba iskanci muke yi ba wllh….” Aunty ta fixgi roban cabbage din gaba daya ta watsa mata ranta bace ta kunduma mata xagi tace “Kina shige da karuwar xaki ce min ba iskanci ku ke ba, dama mace da namiji na xama gida daya tare babu