JUHUD 24

Wata qara ta saki tare da dagowa ga mamakinta sai taga Kareem ne ya sake kai mata duka Addah ta janyeta yace “na dade Ina fada miki ki rinqa saita kalamanki banason ku rinqa shigar da kanku abinda babu ruwanku kunqi ko to waima Ina ruwanku da lamarin Aminah ne kuke neman hana masa mata sakat a gidannan nine dai zakuce kuna tayawa jin haushi Kuma bada ita kuke ba da ubangiji kuke domin shine yayi alqawarin bazai taba bayar da rabon wani ga wani ba Aminatuh bata yaudareni ba tasoni tabani kulawa ta shirya rayuwarta dani qaddarar baa kaina take ba akan Ya Rasheed take matarsa ce rabonsa ce da iya wuya saita isa gareshi ni na yarda waman qaddarallahu haqqan qadarihi Babu wani ruwa dazai kwaranye zanen qaddararmu ta son Abu daya nida dan uwana Kuma dama duk inda mutum biyu sukayi tarayya akan son Abu day to dolene daya yayi nasara daya ya fadi”
Yana fadin haka ya juya ya fara takawa cikin tafiyarsa ta isa har yakai bakin qofar fita ya tsaya ya juyo idanunsa taf da hawaye yace “Meenah!” Yanda ya Kira sunanta hatta Mai Martaba Saida ya dago idanunsa suna tsiyayar da hawaye yace “kada komai ya dameki bakiyimin komai ba qaddarar so ce a haka har gaban abada ke nakeso Amma bazan taba goyon bayan ki bijirewa mijinki ba domin nasan kema kinasona Meenah (Fa Inna maal usri yusra) ba zance na bane zancen Allah ne kiji haka a ranki”
Da sauri ya fice fit daga falon yabarsu zaune da sanyin jiki itakam Meenah gabadaya kalamansa tsinka mata jijiyoyin jikinta sukayi ta kasa koda miqa wuyanta miqewa Amrah tayi tana taunar dabino tace “aikin banza Harbin daurarre dama tunda an cinye maka zuciya Ina zakaga laifinta baqar munafuka wlh bantaba tsanarta irin wannan lkcn ba” daquwa Mai Martaba ya watsa mata yace “dake da tsanar na hada na dakaku a turmi naci kan uwarku ja’ira me qirar yar tsana” sumsum tabar gurin tana haarar Meenah Mom ce tace da ita Aminatuh tashi ki shiga ciki ki kwanta naga kamar sanyi kikeji ko?” Miqewa tayi ta nufi sashin Mom ta bude ta shiga ta ishe Ya’isha na guga ta karba tana tayata suna hirarsu itadai qarfin hali kawai takeyi da taji ma bazata iyaba sake mata gugarta tayi ta koma ta kwanta nandanan zazzabi ya rufeta wasa kamar wasa Abu ya rinqa qarfi hardai a qarshe Saida aka Kira likita ya daura mata ruwa da magunguna.
Kwananta biyu tanajin jiki sannan taji dama sabon laulayi yasata a gaba batada aiki sai cin gurji shi dayane abincinta aikuwa nandanan ta zuqe kowa yazo ya dubata a gidan Amma Banda Aliya da Nana matan yayyen mijinta itakam Addah cewa tayi haqqin dantane da tun ranar daya zabgawa Amrah Mari yake kwance ciwon zuciyarsa ya tashi yanata Aman jini duk ya fice daga hayyaci sunan matar yayan nasa kawai yake kira a qarshe dai dole Mai Martaba ya daukeshi yabar qasar dashi.
Itakam tama manta da babinsa ta kanta takeyi da lfyrta gabadaya ta zuqe ta rame saboda tsangwamar da take fuskanta a gidan batada wani sauqi a gidan saina bangaren surukarta da kullum take rarrashinta da bata baki shikam Rasheed baisan meye akeyi ba kasancewar daga Dalta Enugu aka turasa wayarsa ma ba samuwa takeyi sosai ba a haka dai har bikinsu Ya’isha ya qaraso aka shiga hidimar biki ka’in da na’in dake bikin yazo mata a wani yanayi batama fiye shiga mutane ba warin jikinsu amai yake sanyata.
Ana jibi daurin auren yan uwan Mom sukazo daga Mali ranar Juhud yini tayi a daka Babu lau tana kwance taji an shigo part din batada qarfin miqewa ma shiyasa ta sake bin katifa ta lafe ya bude dakin ya shigo cikin dokin ganinta da shauqi ya tsaya jikin qofar dakin yace “Uhmmm qaddarar so! Kenake so!! So habo ya zabaran yayi naso!!! Yadda nakeyin nazarin so habone!! Ni inajinsa arai tuntubene!!! Dan Adam shikuwa Mai kuskurene!!! Afuwa ki agaran nayi zaune!!! Ban iyawa da rabon qaddarar so!!!!!
Wani tsalle tayi ta saki ihun murna ta rungumeshi tana kissing dinsa ta ko Ina shima kissing dinta yakeyi suka zube a gurin ta hade bakinsu cike da shauqin qaunarsa sun jima a haka ta janye ta shafa kansa zuwa qirjinsa tace “miss ur My life….” Miqewa tayi da sauri hawaye suka zubo mata ya miqe ya riqota yasa harshensa ya lashe hawayen yace “ina tsananin buqatar matata wlh nasha wahala a wata ukun bantaba gwadawa ba……” Hannun takai ta shafo mararsa zuwa qasa ta dago tayi masa murmushi tace “burina kenan Abba Aanam ya kasance me kiyaye kansa hakan shine farin cikina” harararta yayi ya riqe kunnenta yace “bakijin tausayin babynki?” Tasan meye yake nufi ta riqe hannunsa tace “asalin tausayi ma kuwa duk da ajiyarta ya hanani sakat Amma zan bata kulawa bakin gwargwado da haka ta samu ya tashi ta hadamai ruwan wanka yaqi Wai saidai tayi masa batason qamshin sabulum hakanan ta daure ta tayashi suna gamawa ya kulle dakin ya janyota jikinsa ya fara lalubeta ta sakensa jiki sosai sukayi qara’in watanni sun gurji juna kuwa son ransu ita kanta ta yarda sunyi missing junansu bayan komai ya nutsa ne ya dubeta itama shi take kallo ya lumshe ido yace “da kewarki da qaunarki zan mutu Meenah kowanne motsina kene na yarda so Yana canza mutum wlh tunda na tafi naji bana sha’awar kowacce mace bayan ke ko nayi qoqarin nema idan na tuna dake sai naji na qoshi nake nakeson ci………
*JH013 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*
*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*
*Oum Hairan*
*JH0024* Tabe baki suka rinqayi suna miqewa suna sulalewa da daidai ya rage saura iyakar yan dakinsu Rasheed Aunty Hamida Ya’isha Muntaz da Mom iyakar shaqiyancin Muntaz wannan cin mutumcin da akayiwa matar yayansa Saida yasashi hawaye shima. A wahalce ya miqe ya iso garesu sunata aikin rarrashinta kamar suna qara mata qaimin kuka yace “ni dama Mom saboda tsoron irin wannan abubuwan da ka iya tasowa naso kibarma Big Cele matarsa a inda ya barta Amma kika dage Saida kika dawo da ita yanzun ga irinta nan.Hamida ce ta quta tace “wlh nima Raina baiso dawowar Aminah cikin gdannan ba so abune dai da bakada yanda zakayi dashi Mom gsky a dauki mataki akan lamarin nan wlh idan aka barsu a gdannan zasu dorawa baiwar Allah hawan jini a banza ita gata mijinta ba mazauni ba balle yake rarrashinta” miqar da ita Mom tayi ta kama hannunta suka fito wani abun mamaki duk inda sukabi sai suga bayin gidanma suna darewa suna barmusu gurin lamarin daya qara tashin hankalin su.
Zama tayi a parlour tanaci gaba da kukanta da iyakar rarrrashin mutum bataji a ranta zai iya fada mata kalmar da zata iya kwantar mata da hankali ba, sai yanzu mom ta magantu da cewa “duk wani abu da zai faru ko Kuma yake faruwa Aminatuh kiyi watsi dashi ki durfafi rayuwarki ta gaba kisa mijinki da yayan da zaki Haifa masa a gaba shine komai zaizamo miki me sauqi Amma indai kika sake mutane suka jefa miki qulli a ranki to zaki samu matsala kinsani babu wani abu daya gagari Allah wlh Meenah banida ikon hana wannan mgnr fita da tun farko ban Bari ta fita ba balle tazo ta damemu hqrn dai shine zakici gaba dayi domin shine ya kamaki tsarin gdannan mijinki ya taka shiyasa komai ya dada lalacewa Kuma nasan komai akanki zai kware”