UBAYD MALEEK 26

 26_*Washe gari sakayau taji ta Dan rage tashin hankalinta sbd ta rabu da dukiyar Dan hakanan taji Kamar jakadi Bata yarda da itaba ita yanxu data tabbatarda mutuwa ba abin Wasa bace data ji tafara Jin kamshinta zuwanta gizah sbd jiya harzuwama yanxu cikin matsanancin tashin hankali takejin kanta

gabaki daya kusan Rabin zumudin tafiyar yabarta tsoro da shakkun abinda zai iya faruwa gaba shine yafi komai cikata yanxu gefe daya gasu abal tana Isa sukaji wani abun yafaru ayanda tasan abal dinsu dakansa zai iya bada shedar kome yafaru itace…Gyaran muryan jekadi ya dawo da ita zurfin tunanin data shiga ta dago ta kalleta jiki duk amace  ta Dan rusuna ta gaidata 

Jekadi ta amsa cikin sakewa tace”

Bismillah zamu wuce Inshallah.

Janyo Jakarta tayi suka fito daganan har sassan Anneti aka fara kaita ta gaidata cikin tsananin girmamawa da tsarguwa kafin suka fito bayan sun Isa gate na biyu Dana uku Saida aka bincike kayanta tsaf kafin suka fito main gate inda dakarun tsaro suke sunfi guda ashirin suka fice daga delah gizah zuwa airport manyan motocin tsaro biyu na bayansu har airport.

********

Yau tunda safe suka fice duk su dukansu sbd exams dasuka fara ayau din ga uwa uba ita NURU tana gama da ciwon Mara sama sama dam idan zatayi period kusan kowane wata saitayi ciwon Mara ga uwa uba Imran da kwanakin Nan tunaninsa yakasa barinta Jin cewar bayada lafiya sosai 

Tausayinsa takeji har cikin zuciyarta saidai tasan matuqar ba afiace zataje ganinsaba tabita itadashi iyakaci addua.

Suna fitowa yau sbd sammako dasukayi cikin itace agaba tana gyara daurin kanta na scarf fari shikuma Yana fitowa daga geamin dinsa wasu qananun zufa dasuka fiffito Masa suna gangara daga fatarsa da tsantsinta ya hanasu zama ta dago ta kallesa wata irin mummunan kunya ta kamata tayi sauri dauke Kai kasa batasan lokacinda tace”

Gud morning ba.

Kallo daya tayi Mata daga sama zuwa qasa ta dauke kansa ya wuce Kamar bai lura dasuba afia dayake tasan halin dad dinta saitayi gaba sbd sanin jinin mulkin ya motsa akansu su ‘yayansa.

NURU ma hakanan tabi bayan afia tana kashe wayarta suka fada mota suka wuce.

Sai yamma lis suka dawo Kai tsaye daki suka nufa kowa yayi wanka ko abincin kirki NURU bataciba sallah kawai tayi ta janyo laptop tareda wasu takardun tahau karatu afia ma libry ta wuce Dan ita tafi ganewa karatu acan.

Daqyar kowaccensu tayi sallar ishai sbd bacci da gajiya suka Dan sake tattaba karatun bacci yayi gaba da kowaccensu a inda take.

Sai cikin tsakiyar dare su padima suka iso Dan haka ko cikin main gidan ba’a Bari sunshigo ba sbd MALEEK na Nan Dan haka part din masu aiki suka sauka akan seda safe zasu Shiga cikin gidan.

Tunda safe sukuma su NURU suka wuce school sbd jiya bacci be barsu sunyi karatunba sosai shiyasa Koda safe dasu padima suka samu shigowa su NURU sun wuce aka sauketa dakin dake kusadana mum Sarah na jekadi ma Yana gefen nata saiya zama sun sanya dakinta tsakiya.

Kallon aljannar duniya takeyi hawaye na silalo Mata a fili tace”

Wannan wane irin masiface take bibiyata,

Amed Kaine ka cutatarda rayuwata wannan rabon ya subuce min.

Kallon dakin da aka sauketa tayi Wanda aka Kira Dana saukan baqi Wanda tasan har abada kila ko a mafarki bazata samu irinsa ba matuqar ba aikin da aka Bata tayiba dasukai Mata alqawarin cikar buri.

Shafa kanta tayi taji maganin na ciki ta sauke ajiyar zuciya tana bawa kanta qwarin gwiwan aikatawa.

Da wannan tunanin tayini tana kallon kanta a madubi sbd ko tsaron dake Nan gidan ba qarami bane tsaf zatayi ta bakin ranta ba duniyar ba lahirar Dan haka Dole Saida taka tsantsan.

Da yamma suna dawowa farhat tafara tarbonsu da gudunta tayi musu oyoyo tana sanardasu isowansu padima Wanda yasa NURU sakin wani qayataccen murmushi tana ‘dan wartsakewa daga gajiyarta taqarasa ciki cikin farin ciki.

Jekadi ce tafara fitowa ta russuna cikin girmamawa tace”

Barka da dawowa ikon MALEEK na gizah.

Da murmushi ta matso tareda girmamawa itama tace”

Allah yaqarawa jekadi matsayi 

Kun iso lafiya?

Ya kuka baro Anneti.

Murmushin ganinta cikin sabon sauyi jekadi tayi sbd lurada Kamar taqara Dan sakewa fiyeda da tace”

Anneti na miqo gaisuwarta gareki da sauran iyalan MALEEK gabaki daya.

Muna amsawa tace tana kallon kofar da padima ta fito fes hartayi wanka ta Sanya doguwar riga me Fadi sosai ta qarasa da Dan sauri suka rungume juna suna yare tana tambayarta su abal da ammi da meryam.

Duk suna lafiya ta amsa tana yiwa afia barka da dawowa cikin ‘yar girmamawa.

Tareda padiman suka qarasa dakinsu sunata yare Wanda yasa afia keta Binsu da murmushin burgeta dasukai musamman NURU daketa nuna kulawa ga ‘yar uwarta saitaji NURUn na sake Shiga ranta tace”

Baby am jealous fa.

Murmushi NURU tayi tana cewa”

Karki damu itafa tafiya zatayi tabar Miki NURU.

Padima da batasan me sukace ba farko sai Binsu take da ido kishinsu na sake ciketa musamman NURU da idan ta tuni asalinta.

Wanka sukai kowa ya shirya cikin qananun Kayan Shan iska suka baje karatu suna fira da padiman at the same time.

Har dare tana dakin suna first gida Dana ciwonta Wanda take ce musu ba laifi tanajin kaman tafara Jin sauki sbd wani magani da abal yabata.

Sai dare sosai NURU ta rakata har cikin dakinta suka zauna suna dasa sabuwar zancen gida Wanda duk yasake tadowa NURU kewar gida da iyayenta ita kuwa padima satar kallon tsadaddun kayan baccin dake jikinta takeyi Wanda itama anhadota da daya na sawar yau Amma saitakega kaman na NURUn sunfi kyau da tsada Wanda batasan cewa daga jikin NURUn ne.

Sai after 12 tafito daga dakin Takoma nasu ta kwanta tanajin farin cikin saduwa da ‘yar uwarta.

Washe gari ma sammako sukayi sai yamma Amma ba sosaiba suka dawo zuwa lokacin farhat tadan fara sabawa da padima dake kokarin zama kamar yarinya itama tana Taya farhat din Wasa itadai jekadi idanuwanta na bude qyam akan komai dake wakana a gidan.

Kwata kwata su NURU basa zama sbd exams shiyasa Basu ma dauko maganar ciwon padima ba Bari sukai saisun Gama exams sunsamu lokacin kansu isashe tukuna itama padima Bata damuba Dan so take kadama su Gama exams din da wuri Dan kada a tado maganar tasamu ta aikata aikinta ta tattara Takoma Dan ita anan ko gurin zama Bata ganiba dan haryau datake batun cike sati biyu da zuwa Bata taba saka maleek a idontaba Dan haka gwara tayi wannan aikin Takoma can Giza kila nata rabon acan yake tunda anmata alqawari.

Kamar koyaushe yau gidan bakowa sai masu aiki sai ita saisu jekadi da mum Sarah datakewa laqabi da tsofin najadu.

Duk wata damar aikata aikinta Bata samuba tsanani da tsaron da ake bawa abincinsu yayi yawa shiyasa komai yafara cakude Mata musamman dataji jekadi tafara qyanqyasa zance komawarsu tunda sunyi sati biyu cikin na uku gashi ita Tama rasa uban hasarar metake idan Takoma ba wani sakamakon.

Yau da wuri NURU ta dawo sbd sauranta exam daya tagama hakama yau daya tayi Dan haka cikin walwala da gajiya take gashi tanason bawa padima lokaci su futa yawo takaita taga gari da ‘yan siye siye duk da kusan so biyu suna futa da afia data samu interval na Wana biyu.

Wanka tayo ta fito sanyeda doguwar riga sukaci abincin cikin nishadi da walwala har akai magriba suka shige ciki Acan sukai sallah dakinsu suna sake fira daganan NURU ta dauko maganar ciwon padiman kafin tabata amsa ta dauko wani zancen ita padiman da haka suka kamo wani zancen har lokacin bacci yayi suka kwanta.

1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button