JUHUD 24

Har Mom ta gama mgnrta Meenah kallonta kawai takeyi daidai lkcn wayar Mom din ta dauki ruri ta duba taga number Rasheed ce gabanta ya fadi tayi kamar bazata dagaba ya sake Kira tadai sanyawa kanta nutsuwa ta daga suka gaisa yace “meye yake faruwa da Meenah ne na Kira wayarta yakai sau goma bata dagaba” cikin daburcewa tace “eh wlh batajin dadine tunda muka iso kasan yanayi na me qaramin ciki dan gwajab² din hanyar nan yasa mata zazzabi Amma dai Alhmdllh yanzu ta samu bacci, ya aikin?” 

Aje numfashi yayi yace “alhmdllh hankalina yaqi kwanciya ne da zaman Meenah a gidannan Mom inajin tsoron kada a Dora mata damuwa ba iya ramawa zatayi ba sanyinta yayi yawa ni kadai ne Meenah bata bari Amma Urwat ma idan yayi mata qyaleshi zatayi” “nasan da hakan Rasheed babu abinda zai faru insha Allahu ka kwantar da hankalinka ai bama dadewa zakayi ba ko?” Gyara kwanciyarsa yayi yace “wata uku zanyi saidai fah banjin zan iyashi ni kadai tun jiya nasa a gyaramin gda a barreck idan naga yanayin garin Daltan Babu matsala zanzo ko na turo a tafi da ita”  

Fatan Alkhairi Mom tayi masa sukayi sallama ta dubi Meenah tace “ko ya Kira kada ki daga kinsan halinsa idan yasan abinda ya faru bazatai kyau ba ki taimaka wajen boye koma mene daqyar nasamu na dsidaitashi da Mai Martaba mijinki akwai kafiya kamar kafirin farko don Allah Meenah kiyi hqr ga yar’uwarki nan ko kowa yaqiki naji a jikina jinina bazasu gujeki ba su kansu yayyenku sun gamu da kaidin matane musamman Arman saidai addu’a”

Juyawa Mom tayi ta fice Ya’isha ta zauna tana qara bata baki harsaida ta Dan saki jikinta suka qara gyara abinda baiyi musu ba tayi hamma Ya’isha tace “yadai da miqa ko a Kira Big Cele ne?” Murmushi tayi tana shafa cikinta tace “nazama jaka wlh bana jure yunwa Kuma da naci zanji an yasheni kamar wacce mukeci da wani kiga fah jikina har rawa yakeyi” dariya Ya’isha tayi tace “tab kice Big Cele ya qara daure dammara da saqale bindiga” duka takai mata sukayi dariya tace “hankali ne baa kwance ba bari na Kira Mom ta turo a kawo Mana abinci” sallama tayi tace “unborn din danki ne yakejin yunwa Yana neman wahalarmin da yar’uwa” dadi sosai Mom taji dajin ta saki jikinta tace “ok Bari na turo kausar ta kawo muku abinci tun dazu na hada wani abune ya daukemin hankali” 

Suna nan sunata hirarsu gabadaya hirar akan bikinsu Ya’isha ne Kausar ta shigo ta aje musu abincin ta fice Ya’isha ta dauko abincin ta zubansu abincin sunaci suna hirarsu ya sake Kiran wayarta ta dauka ta manna a kunnenta tace “girman kujerarka duniyata” ajiyar zuciya yayi yace “har naji dadi nakasa aikata komai banji lfyr rayuwata da babyna ba hope dai qalau kuke?”

Murmushi tayi tace “ni qalau nake saidai ko kai naji yanayinka a kasalce” qasa yayi da murya yace “meye yake faruwa a gdannan ne jikina na bani ba lfy ba kamar akwai abinda ya faru” shiru tayi tanajin bugun zuciyarta na qaruwa Ya’isha ta zungureta tayi firgigit kamar wacce ta tashi a bacci yace “akwai abinda yake faruwa din kenan ko?” Saurin girgiza kai tayi tace “babu komai kawai dai naji Babu dadine dazun Amma yanzun na warke” bawai yarda yayi ba domin a muryarta kadai ya fahimci akwai damuwa so baison takurawa da tambayar hakan yasa yace “shikenan lkcn la’asar yayi ki huta My Meenah Baffa’am dinki Yana kewa dama shekaran jiya baki baniba Kinga sai kumburamin wando qawanki takeyi” dariya tayi shikam baijin kunyar kalaminsa tace “idan ka zaneta zata nutsu fah…..” “Wht?” Ya furta da qarfi tasa dariya shima yayi dariya suka aje wayar tare ta juya zatayima Ya’isha mgn batanan ta miqe ta kulle barayinta tayi sallah ta qara gyaggyarawa shiru tana jiran Ya’isha har dare tama hqr tayi kwanciyarta a falon tana kallon wani Korian series tana latsa wayarta lkc zuwa lkc tana duba agogo sai goma ta miqe ta bude sashin da dakunan baccinsu suke  ta shiga ta watsa ruwa ta haye gado ta qudundune yanayinta yasa batada wuyar bacci nandanan bacci ya dauketa sai asuba ta farka shima tashinta yayi a waya tayi sallah ta shiga harkokin gyaran gdanta duk da akwai masu gyarawa tafiji a ranta tayi abinta domin ta fahimci mijinta ba Maison a rinqa dafdala a sashinsa bane.

Goma ta gama tayi karinta ta sako hijjab dinta har qas ta fito tare da kulle sashin ta nufi cikin gdan domin gaishe da surukanta abin mamaki yau dinma duk inda tabi sai taga jama’ar gurin sun miqe zunbur sun watse wani sanyin jiki ya kamata itan da a baya idan ta fito kowa yakeson yaga tayi masa mgn yanzu itace wai bayin gidan ma suke gudarwa hawaye ya ciko idanunta tayi qarfin halin shanyewa taci gaba da tafiyarta harta Isa qofar shiga bangaren matan gidan ta murda qofar ta shiga falon tare da sallama Mom Addah Amrah sai Urwat sune kadai a falon sai Mai Martaba dake duba jarida a gefe.

Ta nemi guri a qasa nesa da Mom cikin ladabinta da alkunya ta fara gaishe da Mai Martaba ya amsa da sakin fuska yace “Aminatuh baiwar Allah an fito to ya nauyin jikin?” Kunyace ta kamata yayi murmushi yace “kunyar nanan dai to madallah Allah yayi albarka” amsawa Mom tayi da Amin suka gaisa da Mom itama cikin kulawa take amsawa  ta juya ga Addah Abulle ta gaisheta ta amsa mata Babu yabo Babu fallasa bata damu ba domin tayi alqawarin jure komai domin mijinta ta dubi Amrah dake kwance tana latsa waya tace “sister ba mgn….” Da sauri tayi jifa da wayar tace “wace sister taki ta ina muka hadu Allah ya kiyaye irin gidannan Babu yanlasan wlh saidai a kwasosu a kwashe² kamar yanda aka kwaso Mana ke ak……” 

Wata qara ta saki tare da dagowa ga mamakinta sai taga Kareem ne ya sake kai mata duka Addah ta janyeta yace “na dade Ina fada miki ki rinqa saita kalamanki banason ku rinqa shigar da kanku abinda babu ruwanku kunqi ko to waima Ina ruwanku da lamarin Aminah ne kuke neman hana masa mata sakat a gidannan nine dai zakuce kuna tayawa jin haushi Kuma bada ita kuke ba da ubangiji kuke domin shine yayi alqawarin bazai taba bayar da rabon wani ga wani ba Aminatuh bata yaudareni ba tasoni tabani kulawa ta shirya rayuwarta dani qaddarar baa kaina take ba akan Ya Rasheed take matarsa ce rabonsa ce da iya wuya saita isa gareshi ni na yarda waman qaddarallahu haqqan qadarihi Babu wani ruwa dazai kwaranye zanen qaddararmu ta son Abu daya nida dan uwana Kuma dama duk inda mutum biyu sukayi tarayya akan son Abu day to dolene daya yayi nasara daya ya fadi”

Yana fadin haka ya juya ya fara takawa cikin tafiyarsa ta isa har yakai bakin qofar fita ya tsaya ya juyo idanunsa taf da hawaye yace “Meenah!” Yanda ya Kira sunanta hatta Mai Martaba Saida ya dago idanunsa suna tsiyayar da hawaye yace “kada komai ya dameki bakiyimin komai ba qaddarar so ce a haka har gaban abada ke nakeso Amma bazan taba goyon bayan ki bijirewa mijinki ba domin nasan kema kinasona Meenah (Fa Inna maal usri yusra) ba zance na bane zancen Allah ne kiji haka a ranki” 

Da sauri ya fice fit daga falon yabarsu zaune da sanyin jiki itakam Meenah gabadaya kalamansa tsinka mata jijiyoyin jikinta sukayi ta kasa koda miqa wuyanta miqewa Amrah tayi tana taunar dabino tace “aikin banza Harbin daurarre dama tunda an cinye maka zuciya Ina zakaga laifinta baqar munafuka wlh bantaba tsanarta irin wannan lkcn ba” daquwa Mai Martaba ya watsa mata yace “dake da tsanar na hada na dakaku a turmi naci kan uwarku ja’ira me qirar yar tsana” sumsum tabar gurin tana haarar Meenah Mom ce tace da ita Aminatuh tashi ki shiga ciki ki kwanta naga kamar sanyi kikeji ko?” Miqewa tayi ta nufi sashin Mom ta bude ta shiga ta ishe Ya’isha na guga ta karba tana tayata suna hirarsu itadai qarfin hali kawai takeyi da taji ma bazata iyaba sake mata gugarta tayi ta koma ta kwanta nandanan zazzabi ya rufeta wasa kamar wasa Abu ya rinqa qarfi hardai a qarshe Saida aka Kira likita ya daura mata ruwa da magunguna.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button