MUTUM DA DUNIYARSA 57 – 58

*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[57➖58]_*
………….Ciwon dake ƙafarta ba shine matsalarta ba, hankalinta naga kuɗin
hannun ƙaninta, gashi bataga alamun wayarta na tare da itabama……..
Umma ta katse mata tunani da faɗin, “Maman Hussain ki daure kici abincin nan, ciwo bayason zama da yuwafa”.
Hajia hindu ta ɗan sauke numfashi, ta ƙasan ido ta harari Umma kafin ta yatsine fuska, “Zanci Maman Nafisa, abincinne gaba ɗaya bayamin daɗima ni wlhy”.
Umma taɗan murmusa, saboda tasan baƙa hajia hindu ta faɗa mata. Abba ma na jinsu, sai dai babu bakin magana, a zuciyarsa kam babu abinda yake jinjinawa sai ƙyaƙyƙyawar zuciyar Umma, wai ita wace irin mutumce mai maida sharri da alkairi?. Bashida mai bashi wannan amsar, sai hawayen da suka gangaro masa ta gefen ido wanda su Umma basu gsniba. Shi kansa baisan dalilin zubarsuba, zafin ciwone? tausayin kansane? Kokuwa nadamace?, shidai yasan har yanzu baiji a ransa ya aikata badaidaiba gasu Umma, yanzu da ace ƴaƴansane maza sukazo a manya da ƙasar waje za’a kaisama jiyyarnan………
Shigowar Uncle yahya ce ta katse tunanin Abba, tare yake da mijin Aunty Nafisa, saisu Aunty Zulai dake a bayansa suduka harsu kalifa.
Da gudu su Hassan suka nufi uwarsu, Maneer ne kawai yaje wajen Abba yana faɗin “Abbanmu bakada lafiya? Miya sameka?”.
Ummace ta janye Muneer ganin zai fara kuka, Abba ya janye idonsa daga Muneer da Umma ya maida kansu Kalifa da ko sau ɗaya basu kalli inda yakeba, sun zagaye uwarsu suna faɗa mata ƙarya da gaskiya da akai musu a gidan Umma. Tuni ita kuwa launin fuskarta yagama canjawa…
Tsawa Uncle yahya ya dakamusu, kafin ya zubamusu daƙƙuwa da faɗin, ”Kunci gidanku, toku su wanene da idan kukai laifi baza’a hukuntakuba?, waɗannan ba yayyenku baneba?, ko Walida ce ta tsawatar muku ba dole kujiba balle Zulaiha da Nafisa, duk wanda na ƙarajin bakinsa saina zanesa a asibitinnan, gida kam ai dole kuzauna tunda bakuda kamarsa yanzu. Kekuma maman kalifa kin zauna saurarensu bazaki ko tsawatar musuba”.
Cikin Kumbura fusaka tace, “Yo yahya minene abin tsawatarwa anan?, daba a cuta musuba zasu faɗane”.
Tsit gurin yay duk suna kallonta, Abba ne kawai yaji daɗin abinda tayi a ransa, danshima yaji haushin an dokar masa ƴan lelensa, saidai babu bakin magana.
Daganan babu wanda yakuma tofa baki acikin lamarin su kalifa, anan suka yini a asibitin har yamma liƙis sanan Uncle yahya yace su koma gida.
Hajia hindu naji na gani Uncle yahya ya kora su kalifa daketa ƙunƙunai su bazasu komaba, wai tuwo da koko da shinkafa kawai akeci a gidan, sukuma basu iya ciba (hhhhh ƴaƴan turawa????).
Ko kallonsu Uncle yahya baiyiba, danshi dariyama suke bashi wlhy.
Su Aunty Saudah suka tuntuɓi Uncle yahya akan batun faɗama Jiddah, murmushi yayi, “Karku damu zata sani, amma sonike sai zuwa kamar jibi haka, duka yaushe taje gidan mijin da za’a sakata fitowa?, sonake sai zuwa jibi ta cika sati biyu insha ALLAH, suma zuwa sanan sun fara samun sauƙi, kunsan Jiddah da ruɗiya, kuma zuwanta bashine zai basu lafiyaba ai”.
Sun amsa da to, tareda gamsuwa da maganarsa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*_Bayan kwana biyu_*
Har zuwa yau Jiddah batasan mike faruwaba, kuma tana waya da Umma da Uncle yahya, hakama aunty Nafisa, babu kuma wanda ya faɗa mata.
Yauma dai haka ta yini ita kaɗai a sashenta, saboda zuwan da Amina da Hassana sukayi gidan, sanda sukazo tana sashen Maimuna suna kallon wani tafseer ɗin Sheikh Aliy, amma tundaga shigowarsu jikinta yay sanyi, dan wani kallon banza sukaita binta dashi, koda ta gaidasu babu wanda ya amsa saida Maimuna tace Auntys jiddah nafa gaisheku. Duk a yatsine sukace “oh ALLAH sarki, bamuji bane”.
Jiddah bata gazaba takuma maimaita musu gaisuwa, lokacin ita Maimunatu taje kicin kawo musu ruwa, tsaki sukayi mata basu amsaba, hakanne ya sakata miƙewa tabaro sashen ta dawo nata jikinta sanyi ƙalau da tunanin sukuma su wanene? Tagadai ɗaya na bala’in kama da Maimunatu (Hassana). Koda ta dawo sashenta sai abin yakuma ƙuntata zuciyarta, tana cikin tunani a falo saigasu sun shigo Maimuna ta rakosu wai zasuga ɗaki, dan ita maimuna batasan abinda suka kuma yima Jiddah ba.
Jiddah ta saki fuska takuma tarbarsu da mutuntawa a nan ma, babu inda basu shigaba, amma sai wani yatsine fuska suke, komai suka gani sai Amina tace, “Aunty Hassana nikam ba wanan abun bane ranar muka taya a wajen ƴan gwangwan ɗincan dubu uku?”.
“Shinefa ƴar uwa, kinma manta dubu biyu suka barmana daga baya”.
“Hakanefa wlhy, nama manta”.
Gadajen Jiddah ma da kujerunta haka sukaita musu iskanci, wai Hassana taje kasuwa akace za’ai mata a dubu arba’in, amma tace basuyi mataba tawuce nan.
Ran Maimunatu ya ɓaci sosai, dan haka taja hannun aunty hassana suka fice, amma saita fisge tana mata masifa.
Acan kuma Amina nata gaggasama Jiddah magana ta rashin mutunci, itadai jiddah batace mata komaiba, saima kanta data duƙar a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, har Amina tayi tagama ta fice sanan ta ɗago tana kallon ƙofa hawaye na ziraro mata, ta daɗe a falon tana kuka kafin ta koma bedroom ta kwanta, ganin zata ƙuntata kanta da yawa ta kunna karatun Al-Qur’ani tana saurara, a haka barci ya kwasheta.
Sai da Maimuna tazo kawo mata ɗanwake da tamusu na ranane ta tadata dan har anyi salla ma.
Sannu tamata da godiya, Maimuna tafita saboda su Amina basu tafiba, da zama ta kawo mata abincinan da hanawa sukayi sunata mata masifa, sai da tace wlhy zata kira Malam ta sanar masa kafin shima Aliyu ya dawo ta faɗa masa, sannan ne suka bata hanya suna zaginta wai baiwar kishiya. Itadai batabi takansuba ta fito kawoma Jiddah abincin.
Har yamma lis su Hassana suna gidan, sai bayan la’asar ne suka tafi, jiddah najin tafiyarsu saboda dariyar da sukeyi suna sakin magana a kanta, amma sai taƙi fita, dan duk zuciya nason mai ƙyautata mata.
Maimuna sashenta ta koma, duk zuciyarta babu daɗi itama, dolene tasaka a takama su Aunty Amina birki akan zuwa gidan, dan itadai baza’azo a haɗa mata fitina a gidan aurenta ba, suna zaune lafiya a ɓata musu zama, badan Jiddar tanada hankaliba da biyema su Aunty Hassana zatayi sosai, dan ba kowa zai yarda da wannan cin kashinba, jitai Jiddah takuma birgeta, sai dai yanzu tsoronta karta faɗama Aliyu abinda ya faru ne.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Alhmdllh jikin Abba yaɗanyi sauƙi, dan kuwa kumburin fuskarsa ya sauka, sai daifa yanashan azamar ƙafa da ƙugu, wanima tashin hankali shine ɗorin karayar ƙugunsa bata ɗoruba, likitoci sukace sai an sake, ankumayi yau da safe yaci azaba iya iyawa amma ba’a daceba, shine Uncle yahya ya yanke shawarar kiran wani na gargajiya, dan haka yaroƙi likitan akan su sallami Abba za’a canja masa asibiti, sunyi hakanne dan sunsan idan sukace na gargajiya za’a likitocin bazasu yardaba, shikuma tsoro yake kar goma ta lalace biyar bata gyaruba.
Sosai hajia hindu tayi murna da wanan sallama, dan itafa ba damuwarta Abba ba, hankalinta nakan kuɗin data saka ƙaninta yazo yay musu fashi. Kamar yanda Umma da Uncle yahya suka yanke shawara haka akayi, kai tsaye gidansu Umma aka wuce dasu Abba, ɗakin dake soro Uncle yahya yasaka aka hudo ƙofa ta cikin gida tun jiya, ita kuma hajia hindu aka kwashe kayansu Zarah daga ɗakinsu aka gyara mata.
Su aunty sauda duk basuso hakaba, dan yanzu dai ba gidan Abba baneba na Jiddah ne, saida Umma taita tausarsu sannan suka bar zancen.
Sosai hankalin hajia hindu ya tashi, wai ana nufin wanan gidan data bari tsawon shekara sha shida dawasu watannine za’ace ta dawo da zama?, wanan ai ci bayane, dolene ta nemo ƙaninta a yau yakawo kuɗin nan tanemi ƙaramin gida tasai musu itada ƴaƴanta, shiko Abba yazauna nan yayi jiyya, idan ya warke ya nemesu.
Abba kam yana cikin azabar ciwo, bayama tantance a ina yake balle asan sirrin ransa
Gidan dai yamusu kaɗan sosai, amma haka sukai maleji, da daddare wasu sukaje gidan Uncle yahya suka kwana.
Su kalifa kam abufa ya damesu, sai kuka sukema hajia hindu basa son wanan gidan, sudai akoma gidansu. Hajia hindu saita sake rikicewa, dan ita kaɗai yaran suke addaba, basayi gaban su Uncle yahya.
Washe gari da safe mai gyara yazo, sabon ɗori ya sakema Abba a ƙugu, suma kam Abba yayita babu adadi, su Zarah kuka kawai sukeyi, hakama Umma takasa daurewa, sosai takejin tausayin Uban ƴaƴan nata dukda tsiyatakun daya shuka mata.
An gama gyaran Abba ya samu barci na wahala, a lokacinne hindu tasamu zarafin tambayar Uncle yahya wayarta wai zata sanarma danginta.
“Wayoyinku suna cikin wata jakarki na zuba, tana nan inaga an taho da ita, amma ina Zulaiha itace kamar nabama jakar dazamu taho?”.
aunty Zulai dake sharo ɗakin Umma tace, “Eh Uncle tana nan ɗakinta a jar jaka”.
“yauwa to kinji tana nan, sauran kayanku suna gidan malam Alfah na roƙi alfarma aka kai can, saboda mu gidajen namu babu inda za’a iya lode waɗan nan kayan, kayan gado dai dasu kujeru duk an saidasu harma katufun, guda ukunan dakika gani kaɗai muka bari, acikin kuɗinne ma akabama mai gyaranan kuɗinsa, dan wlhy nidai kuɗin dake wajena sun ƙare, a jiyama saida na taɓa kuɗin sadakin jiddah dubu ashirin aka ɗako sauran kayanku, amma an maida mata yanzu haka, wanan daliline yasa muka matsa aka sallamoku daga asibiti, tunda bamuda kuɗin cigaba da biyan kuɗin gado da sauransu, yarannan kuma su Hannatu iya ƙoƙari sunyi dagasu har mazajensu, koma nace suna cikinyi”.
A ɗage hajia hindu ta amsa da “Uhhum”. Dan taji haushin saida musu kayan gado kuwa, amma babu komai aiga kuɗinan.
Babu wanda yasakebi ta kanta, saboda amsar da tabama Uncle yahya ta Uhum kowa tabashi takaici.
Shidai Uncle yahya yay musu sallama yatafi gida danya ɗan huta kafin Abba ya farka.
***********
Da rana akayi faten doya da wake da alayahu, ƙiri-ƙiri su Hussain sukace bazasu ciba, babu wanda ya tanka musu sai Umma daketa musu nasiha da lallashinsu, amma ƙiri da muzu sukaƙi saurarenta, saima rashin kunya da suka nemi yimata, aiko Aunty Hannatu dukda haƙurinta tai azamar taka musu birki.
Hakan saiya harzuƙa hajia hindu tafara sakin magana, gashi tana ƙyaɓe waje ɗaya tana fama da kanta.
Aunty Zulai zatai magana Umma ta hana, takumace kar wanda ya sake tankawa, daga yanzuma komi su Halifa zasuyi a gidan babu ruwansu, abinci dai idan andafa a basu, suci ko karsuci wanan yarage nasu ai.
Hajia hindu dai tanata neman ƙananun magana babu wanda ya kulata, ga takaicin neman kaninta da take a waya amma taƙi shiga, tamasa kira yafi hamsin sai dai ace mata Busy, tun tana ɗaukar abin wasa har nutsuwa ta fara gagararta.
Hummm hajia Hindatu yaya dai⛹♀?????.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah na zaune a falo bayan tayi sallar la’asar tana duba littafin *Ahdhari* Aliyu ya shigo da sallama, ɗago idonta da sukai alamun tayi kuka tayi ta kallesa tana amsawa, ya tsaya a ƙofa tareda buɗe mata hannayensa alamar tazo gareshi.
Murmushi tayi tamiƙe jiki a sanyaye, dan yariga ya shaida mata hakan dokane acikin tsarinsa, kuma koba komai tana buƙatar jin ɗuminsa a halin yanzun da zuciyarta ta wuni a ƙuntacennan.
Shigewa tayi ajikinsa tana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
shima numfashi ya sauke, yace, “Nayi kewarki Jiddah na”.
Ahankali ta furta “Nayi kewarka sosai nima”.
Babu shiri yay azamar ɗago kanta, dan maganarta tabashi matuƙar mamaki, baiyi zaton hakan agareta ba nan kusa. Lumshe idanunta tayi tana murmushi, dan batason su haɗa ido.
“Jiddatulkhair da gaske koda wasa?”.
Fuska taɗan shagwaɓe tana tura masa baki, “Da gaske mana”. Ta kare maganar da maida kanta a kirjinsa.
“Masha ALLAH, Alhmdllh Adaratul ainy (Turaren zuciyata) ya kuma rungumeta yanajin sonta nakuma tasiri a ransa”.
Bayan sun zauna taje ta kawo masa ruwa. Yana sha idonsa a kanta, dan ya kula tana tare da damuwa kamar yanda maimuna ta sanar masa, saboda sashenta yafara zuwa, itama ya isketa cikin damuwa, ya tsareta da tambaya shine ta sanar masa abinda su Hassana sukazo sukayi, ransa ya ɓaci sosai. Amma sanin halin Maimuna bazata taɓa sakasu suma Jiddah hakanba sai itama ya lallasheta akan karta damu, shi yasan bazata sakasu suyiba hakanba ga jiddah, sunyine kawai dan raɗin kansu, amma zai taka musu birki insha ALLAH.
hakan sai ya saka zuciyar Maimuna ɗan samun nutsuwa, amma damuwarta kuma halin da jiddah take a ciki.
Aliyu ya ɗauki aniyar gwada Jiddah yagani kozata masa maganar abinda su Aminar sukazo sukayi.
“Ƴammatana mike faruwa? Na ganki wani sukuku, ga idonkifa kamar kinyi kuka”……
Murmushi jiddah tayi tana danne abinda ya tokare ranta, “Babu komai, kumani ba kuka nayiba, kawai kewar Ummana nakeyi”.
Idanu ya tsura mata zuciyarsa na tunanin ita takeson sanarma kenan? To amma dataso hakan ai da tayi tunda ga waya a hannunta, saurin kauda wanan tunanin yayima daga ransa, ya ajiye kofin da yasha ruwan yakamo hannunta cikin nasa idonsa akan fuskarta, “Haba tawan, anya kuwa kewar su Ummace kawai? Kodai Auntynki ce?”.
“lah A’a wlhy, ni aunty tsakanina da ita sai sambarka, kawai dai kewar su Ummance”.
“Shikenan, insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zan kaiki, yanzuma tashi ki shirya danayi wanka zamuje mu gaida su malam, kinga baki taɓa zuwa gidanba tunda kikazo.
Daɗine sosai ya kama jiddah, harga ALLAH tana ƙaunar dattakon tsohon, tuni taji nauyin da zuciyarta yayi kaso mafi yawa ya ragu.
tace, “To abincifa?”
“Naci abinci a office din mustafa, shiyyasa na kira auntynki nace karkuyi dani”.
Murmushi tayi, dukda batasan anyi hakanba, kuma girkin Maimuna ne har rana, sai yanzu da yammarnan ita zata karbesa, batareda tace komaiba ta mike, harta nufi ƙofar fita Aliyu ya kirata, juyowa tayi ta kallesa, yace,
”Ina zakije kuma?”.
“Zan haɗa maka ruwan wankane”.
“Karki damu zoki haɗamin a bayinki kawai”.
Kanta ta jinjina masa ta dawo da baya zuwa bedroom nata. Binta yayi da kallo harta shige, ya ɗan sauke numfashi yana jingina kansa da kujera, a zuciyarsa yana tunanin miyasa taƙi faɗa masa abinda akai matan? Zai sake gwadata dai ya gani, harga ALLAH yana mamakin yanda wasu lokutan halayyar Jiddah da Maimuna suke kamanceceniya da juna, kodan dukansu sunada ilimin addinine da tarbiyya, kuma Alhmdllh suna aiki da sanin da ALLAH yay musu, sarai yasan salon kishin kowacce amma hakan bai hanasu ƙyautata zamantakewar dake tsakaninsuba……….
Jiddah ta katse masa tinani, idanunsa ya buɗe, ya kama hannunta yana faɗin “Zomuje ki tayani wankan to”.
Sosai ta zaro idanu da faɗin “Wankafa?”.
Tabashi dariya data zaro idon, ya ranƙwafo kanta yana jan hancinta, “Malama baƙyason koyi da sunnar MANZON ALLAH ne? ANNABI yana wanka da Matansa har hannayensu na gogayya a cikin ruwa, baƙyason samun wanan ƙatotuwar ladar tawajena”.
Hannu ta saka ta rufe fuskarta tana ƙaramar dariya, shima yay dariyar yana jan hannunta sukai ciki….
✨✨✨✨✨✨✨
Gabda magriba suka fito da nufin barin gidan, dan Aliyu soyake yay sallah a masallacin ƙofar gidansu, Kasancewar Jiddah ce da girki maimuna tace ya shiga gaba, amma sai taƙi tace, “A’a wlhy Aunty ke zaki shiga, ba girki zaki dubaba, kimarki ta matsayin babba a gareni”.
Daga Maimunatu har Aliyu binta sukai da kallo harta shige baya, sanan suka kalli juna sukai murmushi, kowannensu yanajin ƙaunarta da kimarta a ransa, yayinda itama hakanne daga gareta.
Sun isa anata hada-hadar shiga sallar magriba, Jiddah da Maimuna suka shige cikin gidan, shikuma Aliyu yashiga masallaci……….✍????
_ZAFAFA BIYAR MASU ZUWA A 2020 INSHA ALLAH._
*ƊAURIN ƁOYE!* (Safiyya Huguma
*SAUYIN ƘADDARA!* (Hafsat rano)
*KAI MIN HALACCI!* (miss xoxo)
*BURI ƊAYA!* (Mamu gee)
*WUTSIYAR RAƘUMI..!* (Bilyn Abdull)
????????karku bari ayi babuku
*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*
*za’a tura kudin ta wannan accnt number din*
Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank
Saika tura shaidar biya ga wannan number
08030811300
Ga masu turo da katin waya kuma zaku tura katin MTN ta wannan number din
07067124863
Da zarar kin biya kai tsaye zaki tsinci kanki cikin gidan da zaki samu littafin da kika biya.
*Karki bari ayi babu ke*????????????????????????
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*????????????