MY LADY BOSS

MY LADY BOSS 8


Idan kin San kan ki baxai ɗau abun dake ciki ba,bazaki iya jura ba ,don Allah kar ki karanta ki dawo mun da zancen kutumelesi…ban san wani kitimurmura labarin Romantic ne????haka kema idan kin san zaki saya ne don ki fitar mun na yafe ki adana kuɗin ki, kar ki fitar mun adawo mun da zancen gntlw…..masoya na billions naji saƙon nin ku gareni ina gdy Allah yabar????

Free page na dab da ƙarewa,Zai ƙare a page 10 inshallah…ku hanxarta wajen biyan kuɗin littafin LADY BOSS domun jin daɗin ku na cigaba da karanta wannan labari , kin shirya biya?? Na shirya! To yanda tsarin biyan ya kasance… Regular payment ₦300 vip payment₦500 special payment ₦1000…zaku iya turo da kuɗin ku ta wannan asusun bankin 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank…ko kuma ki tura katin MTN naki ta wannan number 08081202932…Idan Vtu trnsfer ne ki tura ta wannan MTN number 09061466409 sai ki tura da shaidar biyan ku duka ta wannan WhatsApp number 08081202932 asha karatu lafiya…

SADAUKARWA GA MUTAN ZAZZAU gami da godiya ga masoyana billions ko trillions ne gdy duk????????


Miƙewa Diyana tayi tana fichewa daga Station tana mawa ƴan sandan godiya suma suna mata , tare da jajanta wannan hali nata ,macen zata kawo mijin ta Station a wannan marraba ai abun mamaki ne da kallo.. Diyaana kenan ita take koman ta a cikin gidan mijin ta yarinya ƴar shekara ashirin da huɗu ,ko wani nauyi ita ta ɗauke a wuyan ta…. Hattara mazan wannan zamani masu hali irin na Ɗan Asabe da kuma mijin Diyaana , ba ko wacce mace bane take haƙurarra , wata in tayi haƙuri wata bafa zatayi ba…mu dingi kyautatawa matan mu sai gidajen Auren mu ya dauwama cikin farin ciki da annashuwa .


Kwanan su biyu suna tafiya daga Lagos zuwa Zaria , wanda a hanyan su na isowa gab da garin Zaria ne suka ga abin da basu taɓa gani ba, shine Fashi da Rana tsaka …. Salati Sumayya tasa tana faɗin dama na faɗa maku wallahi mu gudu , kuɗin hannun mu zasu ƙwace dama sauran na mutane…Harbin tayan Driver n nasu akayi , wanda don dole suka tsaya moton na wani irin kugggi a kwalta…..Alamu sukayi da su fito , wanda cikin salati tare da kalmar shahada kowa na moton nan yayo waje…..Ciki harda Su Sumayya da suka gama tsarawa kansu abinyi a ƴan sekanni.

Fitowan su ke da wuya , wata mace da ta rufe fuskar ta da Shadow spce ta kalli mazan ƴan uwan ta biyu tana cewa ” Ku leƙa ko da saura…jin haka yasa su nufan moton don su leƙa , Safna ne dake bayan ta aƙwance ta miƙe cikin sanɗa tana maƙurar wuyan ta , wanda motsawa takasa yi alama take mawa sauran amma ina sam basu luraba. Sumayya ce ta saɓa Umma suna yankan daji da basu san inda zasu dosa ba…..Laurat tayo bayan su, ganin haka yasa mutane miƙewa kowa yana cin hanya ,wannan ya an ƙarar da sauran ƴan fashi , bugata Safna tayi da moton tana bin hanyar dasu Sumayya suka bi….wani irin harbi suke yi na kisa , don da dama sun sami mutane wasu kuma sun shaaa!


Wani irin dariya ne Addiya taji ya ɗauki ɗakin da take zaune ,wanda faɗin ƙawatuwan shi ba’a magana “. Cikin gusassar Muryar sa ta marasa imani da tsoron Allah taji ɗakin ya amsa da amon Muryar sa kaman haka” Hjy Adiyya har kin manta mune gomnati , don kina ɗan wannan matsayin taki ta ƴar majalisa shine zaki turo aga baya na? . Mu da mulki n mu muka baki! Cikin wani irin jan rai da rashin tsoro tare da dakewa tace ” Kaci nasara a wannan karon , kasha da rayuwar ka , amma bance maka gaba zaka kuɓɓuce daga hannu na ba…. Wallahi indai ina raye Ni Addiya sai naga bayan malamai matsubbata irin ka ,Ni Addiya ba’a cuta na!

Ke Addiya ya kamata ki shiga hankalin ki , kar ki manta da Gundumirƙi kike magana , wanda na kashe ki naka kashe banza , baza A tuhumi kowa ba , kuma baki da kowa da zai zauna maki koda zaman makoki ne ya ƙare yana wani sa Dariya na irin azzaluman matsafan nan….. Sai taji ɗiff ɗakunan nata sun bar juya mata .

Lumshe ido Addiya tayi tana buɗe su ,kana tace ” Kayi gaskiya gundumi Ni bani da kowa Ni marainiya ce, a cikin gidan marayu na taso ban san kowa nawa ba , wannan Matsayin da nake kai , da ƙarfi na na ƙwato shi har naxama , don haka Ni mutuwa bata bani tsoro a shirye nake da zuwan ta , indai akan son ganin bayan mugaye irin ku ne.


Basai na faɗa maku bana ji ba , ku sani a sahun masu ji! Suka ji Muryar wacce masu yi tsammani ba ya dirarar wa dodon kunnen su …A matuƙar razane , suka jiyo suna kallon Bilkisuuuu da take zaune a wata itaciya hannun ta babu makami sam ,kan ta kuma a ƙasa. Inalallahi wai’ina ilaihir rajiun , baiwar Allah me muka yi maki? Ki taimaka ki bar mu mu tafi mun haɗaki da Allah. Cewan Sumayya tana ƙara riƙo Umman ta da take bin kowa da kallo.

Ku bamu kuɗin hannun ku ku tafi cikin salama. Wallh baki isa ba , kin san yanda muka sane shi ne? . Cewan Laurat tana fiddo da idanun ta waje.

Me yasa kk zaɓi wannan sana’ar zalunci n a matsayin ki ta mace? Mata da tausayi aka sansu bada irin….ke yi mun shiru Nice nan Bilkisu mai gado , ba zaku tafi da kuɗin nan ba indai kun tafi dashi to na tashi daga sunana ne. Kina faɗin Ni macace , a lokacin da yunwa yake damuna da ƙanƙantan shekaru na ,ina kuka ina cewa ” Su bani abinci ko ruwan sha basu bani ba , da ƙarfi na na ƙwata daga hannun su , na zama sarauniya a fadata , na zama tantitiyar mara ji na fara fashi , yanxu sai ku kawo mun Allah ɗaya ne…ku bani kuɗin kona gwada maku damtse.

Shiru sukayi Idon su kaf ya kyakyashe babu mai iya kuka , Sumayya ne tace ” Da hakan kika yi da yafi mana ,idan kin cika Bilkisu ki amashe kuɗin nan daga gare mu , ba tare da makami ba , kawai ƙarfin naki , yanda ki ke taƙama kin wahala ,muma duk a wahalcen muke……wani irin zafi maganan Sumayya yayi mata wanda yasa ta miƙewa tana tun karo ta kai tsaye….zagaye ta sukayi suka rufa mata dambe suke na ƙwatan rai ,tabbas sun ji jiki a hannun Bilkisu , wanda Sumayya ce ta buga ta da bishiya nan take ganin ta da jin ta ya ɗauke , ɗaukar Umma tayi suna neman hanyan barin jejin….


Saukar jirgin yayi dai dai da fara saukowan Fahad cikin shigar ƙananan kaya da suka amshi fatan shi ƙwarai , ɗaga kai yayi yana hango Sir Khamal da yake sanye cikin shigar Trac suit arsh colour abin ka ga farar fata baƙaramin kyau sukayi mashi ba…Nufo inda yake Fahad yayi yana bashi hannu , suna gaisawa ba tare da kowa yace komai ba suka shige moton haɗi da barin airport ɗin take…..


Me napep ne ya kalli su Sumayya yana cewa ” Hjy ina za’a kai ku? .shiru su duka sukayi don Basu san ko ina anan ba! Sumayya ne tace ” Kai mu layin masu kuɗi a Zaria.

Me napep ɗin ne yace” Aƙwai G.R.A , aƙwai Tukur Tukur , aƙwai kuma ƙaura…wanne ciki za’a kai ku? . Laurat ne tace ” Yi mana bayanin ko wacce a ciki ya tsarin wurin yake?.

Me napep ɗin ne ya basu amsa da” G.R.A. Nan ne unguwan masu kuɗi alhazan Zaria mny ƴan siyasa da sarakuna.

Ƙaura a cikin City yake unguwan masu mulki da sarauta kenan da ƙafarta , kuɗin akwai amma ƙaryar su tasha ƙarya….

Tukur Tukur unguwan matasan masu kuɗi yara samari da masu shekaru dai dai….kuɗi boko ƙaryar komai ya haɗaa
A wannan layi . Aaa’aaa’aaaa kai mu Tukur Tukur cewan Safna da Sumayya suna haɗa baki a tare. Nan take me kafu babur ya kwana yana nufar tk road.


A tangaɗi ta Nufo Asibitin A.B.U tudun Wada…cikin tangaɗi take tafiya wanda kowa darewa yakeyi yana bata wuri , kai tsaye inda likitocin ke zaune Bilkisu ta nufa ,kanta na xubda jini kaman jinin jikin ta zai ƙare….da sauri wata nurse tayo kanta don taimakawa ,amma sai ta ɗaga mata hannu alaman a’a .

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button