HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

_shafi Na Arba’en_

 

Ranar Ango safwan ,Kwana yayi Yana tufka d warwara ,da kyar y Samu yayi bacci …

 

*******
NAWAL anata Aiki cikin kwanciyar hankali ,duk wata tanajin Alert ,Bata d wata matsala ,yara ko tasan Dole su nemeta ,safwan ko tasan yanacan Yana fama d begenta tunda har takai ga har y kaima asibiti ziyara sanadin rabuwa d ita d yayi ,fada ne kawai bazeyi ba …..

 

Ayanzu ma ta kusa gama night duty ,tsakanin ta da mama kuwa yanzu ba yabo ba falasa ta zuba musu Ido ita d Abban …

Tun lokacin d ta koma asibiti bayan sati biyun d Likita y d’iban Mata ,y Bata shawarari akan ta kwantar d hankalin ta tayi kokarin cire ko wace irin damuwa aranta ,haka t d’auki shawarar shi ta cire damuwar NAWAL ko ta Abban ta ….

 

Shima Abba hankalin shi kwance Yar shi na gabanshi Tana gudanar da aikin ta ,sanan Yana yawan tmby intanada matsala ta fad’a Mai takance Bata d wata damuwa Amman in Akwai zata sanar Mai ….

 

********
Indo d Inna d su Noor ,sun wayi gari lpy ,sun Sha kunu da kosai Mai dad’i sunata Santi …..

Indo ta musu wanka ta shafa musu Mai ,gashi ba kayan d za’a samusu Dan haka ta bar musu vest d short niker su ta wanke musu kayan d ta cire musu ta shanya Dan Kar Azo d’aukan su ,adauke su d dati ….

 

Suko hankalin su kwance sunata wasa Inna tanata musu labarai masu Dadi naban dariya ….

Indo ko tanata gyara gida d Shirin Dora musu girkin Rana ,har ta manta d wani Aure d aka d’aura Mata ma ,Dan ganin su Noor d yadda suke damunta d Hira yasa take manta wani damuwa d take ciki …

Bayan t Kamala komai ta shiga dakin Inna ,tayi tozali d akwatunan Auren ta ,sai idonta ya Fara Shirin zubar d kwalla,ganin Inna na kalon ta sai ta fita tabar d’akin ma gaba daya ….

Inna ta Lura tasan me take son yima kuka,Dan haka ta yanke shawarar rufe kayan da zanuwa Dan ko zata Dena tozali dashi …..

Shiru har yamma Babu Wanda yazo d’aukan su Noor gashi Indo ta gama shiryasu ,ta mayar musu d kayansu d suka bushe …

Har kusan magriba shiru ….

Inna tace, Indo ?

Noor tace ma Inna ,Kai ! Ammy ta Hana ce mata Indo fa “sunan ta Aunty Aishatu Inna Dan ALLAH kema ki dinga ce mata Aunty Aishatu kinji ?

,Noor tana kalon Inna Tana mele Baki ..

Inna tace ,oh yaro man kaza to ai Ni ba aunty na bace kune take Auntyn ku….

 

Haneef ma yace , Dan ALLAH Inna mu ki dinga cemata Aunty Aishatu yafi Dady ko dadyn mu ma Aishatu yake ce mata ,momyn muce kawai me cemata indoooo ba ko aunty Indo ma …..

Abun yaba Inna dariya ,ita kanta Indo Tana tsakar gida har seda ta Dara ta manta bacinran ganin kayan Auren ta d tagani y dagula Mata Rai tana mamakin surutu irin nasu Noor ,Abin gwanin birgewa ,Nan t Lula duniyar tunani Kan cewa ai ko Dan su tayi hakurin zaman Auren dadyn su ,tasasu a gaba suyita hirar su ,suna Bata nishad’i meze dameta Abinta ,gaskia Tana son yaran ….

“Inna tace ma su Noor ,to naji masu Aunty ,zande cemata Aishatu daga yau “DamaNi nabata Mata sunan ta ,Aiko suka had’a baki sukace yeeeeee Inna!

Inna t tsaya mamaki kawai …

Suna wanan hirar tasu Basu Ankara ba sai Kiran sallar magriba kawai sukaji ,lokacin da yayi daidai da shigowar nawara gidan….

Indo n tsakar gida tanata girka musu Dan waken rogo d dawa d filawa Mai santsi d Danko ga yaji d man kuli agefe ga zobo d ta had’a musu ta karbo kankarar pure water a gidan aunty me dinki ta jefa musu danwaken kawai suke jira y karasa sai ci insunyi sallah.

Nawara ta ,lakaci kumatun Indo tace Amarya ,y kwanan amarci?

Indo t harareta ,tace Yana wajen ki ai …

Nawara tajiyo su Inna d su Haneef anata dariya ,taje ta gaishe d Inna ta ma su Noor wasa ta dawo wajen kawar ta …

Har zata tafi ,Indo tace dalla can mutumin nakeyi fa Zaki wani tsere ,ki zauna muyi sallah muci mu more …

Nawara tace haba ai ban sani ba kinsan d ba inda zani , kawo tumatir na yanka Mana d Albasa d kabejin ,dafatan dai Akwai yaji sosai ko kinsan mu fa Akwai cin yaji …

Indo tace kin shigesu d basir yarinya ,kindai kusa Aure arage cin yaji …

Nawara tace Amman dai ba’a d’aura ba ,keda aka d’aura kune zaku rage koma ku daina ..

Wayo Amarya d yanzu kina can kin kwana kin hantse ko a gidan sahibi bbn su Noor?

Indo tace banza ban sani ba kyaga kwana da hantsewa a gidan haidar dinki” romio nd Juliet ku dinga wani Abu kamar zaku hadiye junan ku …

Nawara tace ,eh din Kinga lefi na ,tab ba Sanya wani Abun ma sai anshiga daga ciki wlh ,iskancin mu sai aciki a dakin mu inda ALLAH d manzon sa suka yadda muyi ,Nan za’aga Abu wlh…

Indo Baki t sake ,Tana cewa nawara yaushe Kika zama ‘yar iss?

Nawara tace ban zama ba zandai zama Nan da wasu watanni wlh ,zamu tsula up in Gaya Miki ,bakiji lecture ba a wajen Aunty zainab tace kema ai zata Kora Miki jawabi ,Dan wallahi mazan zamani sai matan su sun zama karuwan Sunnah sanan zasu samu shawo kansu d salon karuwancin su na gidan Aure ba irin na tsinanun tanbadadun waje ba Wanda suka kwashe kayansu daga gaban ma’aiki ba masu bin maxan mutane…

Indo Tana kwashe danwake ,Tana cewa kin shiga uku kekam ,nawara Ashe kin wuce tunani na ,tab wlh bansan haka kike ba !

Nawara tace munafuk…kema wlh kinaso ,watakila Abin d zakuyi d uban yaran can sai yafi namu ma …

Indo tace, banza kowa irin kine ,wlh Ni Ina ruwana dashi? Tab yayi sabgar sa nayi tawa ..

Nawara tace ,haka kikace ko ,uwar yaran ta dawo tazo ta dinga shamai sweet a gabanki kina zaune ,keda mijin ki”

Jin kalmar nawara d ambatar uwar yara yasa Indo tafiya tunani na wasu sakanni”

Nawara ce ta dawo da ita, anaso Ana kaiwa kasuwa” wlh ki farka daga nanauyan baccin da kikeyi ,gobe zan Baki wani fitinanen littafi ki duba ba batsa akeyi ba Amman Akwai tsimi d tanadin zaman gidan miji aciki wlh …

Indo tace banza ni kyaleni ,iskancin ki y girmi kaina yau” banaso karki maidani irin ki ,na fuskanta Aure kawai kikeso …

Nawara tace ,kema kina so ” Aure ai Halak ne ,in bakya so Zo muje kicema safwan ko Abba bakyason Auren d aka d’aura jiya ..

Indo t zaro ido ,tace kinada hankali kuwa ? Wai me kikasha ne yau?

Nawara tace giyar soyayya mayenta nakeyi baxan dawo daidai ba sai naganki a gidan safwan Nima na ganni a gidan my choice” hydar luv …

Indo tace, munafuka ,Maya kin zama ‘yar iskaro wlh ,na gudu sallar Aljanun iskanci ne akanki yau inajin wlh ….

Indo t d’auki buta t tafi Alwala ..

Inna ma ta fito yin Alwalar …

Nawara sai dariyar mugunta take shekawa ,har Inna take cewa ,lpy nawara?

Nawara tace wlh Inna nida aminiyata ne Ina sata a hanya Taki yadda ta hau…

A tunanin Inna gaskia take gayama Indo akan Auren d aka d’aura Mata ..

Sai inna tace ki dage sosai kam sai kinta dagewa akan kawar Taki wlh , ALLAH dai y muku Albarka,

nawara tace Amin Inna ai sai na Kara dagewa akanta har seta Gane gaskia ..

Dakuwa, indo ta ma nawara batare d Inna t gani ba ta murguda Mata Baki Tana hararar ta …

Nawara t Mata gwalo tasa dariya …

Bayan sunyi sallah har su Noor aka zubo ,danwake aka zuba kayan Hadi suka baje a tabarma a tsakar gida ,sunaci suna korawa d zobo Mai sanyi ,su Haneef sai surutu d Santi ake zubawa…

Nawara ta tabo mutuniyar tata da cewa ,kindai ji abinda Inna tace ko? ko ki nuna Yar garice ke ko na sakoki gaba wlh har sai kingane manufata ..

Indo t d’ago ,Tana cemata wlh in Baki kyaleni ba wlh zan barmiki Abincin d wajen na tashi wlh ..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button