KYAWUNA JARAFTA TA Page 1 to 10

???? KYAWUNA JARABTA TA ????
✍️ M SHAKUR
Don yin magana directly da M Shakur click on this link wa.me/+2347012181461
M Shakur nada group din Matan Aure wanda idan kinason kishiga is just 1k.
hakama idan kinason advert shima M Shakur duk tanayi.
free page
EPISODE 3️⃣
Girgizamatakai tayi ahankali gwaninban tausayi alamun bada ita takeba, cikeda mugun tsana tace “haka zaki kare rayuwanki awanan dakin, agabanki yayyinki da kannenki duk zasuyi aure ke kina nan adakinnan har tsufa bazakiyi aureba saidai ko indaga dangin ubanki aljanune wasu zasuzo kuyi wup dake, mai bakin jini kawai mara kunya” tana maganan tawuce tafice daga dakin, sosai tafashe da kuka, har bakin suka tafi su Nana suka dawo dakin nan kuka take bata denaba, dayake sun saba bawai sabon abubane kukantaba saisaima babuma wanda yabita kanta saima shirin kwanciya dasuka shigayi suka gama Hawwa takashe wutan dakin, haka taci kukan nan har batasan sanda bacci yay awon gaba da itaba.
Yau Monday sabida taci kuka batai bacci dawuri ba sai wuraren 8 ta farka, koda ta tashi babu kowa adakin saidai sababbin novels datagani manya guda uku agefenta dasauri ta tashi zaune ta dauka tana dubawa, sunan Novel din farkon The Noisy Naigbour, na biyun sunanshi the killer tree, saina ukun Disastrous Love, wani kalan murmushi tayi sanan ahankali tace “thank you Ya Hamad” ajiyesu tayi tawuce bayi alwala tadauro sanan tafito tai sallan asuba tabude Al Qur’ani tana koya Haddan da Abba yabata, saida ta tabbatar ta haddace shafi daya darabi sanan ta tashi, dakinsu ta shiga gyara musu wanda yanzu zata iyacewa a rayuwa that’s the only thing data iya gyaran daki shima da karfi da yaji takoyama kanta, ta gyaramusu gado sanan tawuce bayi tayi brush tayo wanka tafito ta shafamai sanan tasaka wani riga da skirt na atampa daya mata kyau tai parking gashinta da kyar sanan tadauki novel kaman barauniya tabude kofan dakinsu ahankali sanan tasakai taleko kadan ganin babu kowa yasa tafito duka, sanan tashiga sadadawa tafara tafiya ahankali zatai stairs. “Ina zaki”? kaman daga sama taji muryan Mami dasauri tajuyo, hada ido sukai da Mami data fito daga dakinta tana kallonta, saukar da kanta kasa tayi tana kara kankame novel dinta ahankali tace “Mami good morning” batare data bata amsaba tace “wuce kikoma dakinku ga Uwani nan zansa takawomiki break” gyadama Mami kai tayi ahankali sanan tajuya zata koma dakinsu bintada kallo Mami tayi harta shige sanan tasauke ijiyan zuciya ahankali tawuce tasauka kasa, hada mata breakfast tayi kunun gyada da kosai, samin kanta tayi da daukan wani karamin plate tajuyemata ragowan naman da Abban su yarage sanan ta kwalama Uwani dake wanke wanke kira dasauri Uwanin tazo tray tabata tace “kaima Du’a abinci adakinsu” karba tayi tawuce sama bude kofa tayi tashiga tana kallon Du’a data bude novel tana karantawa, har gaban Du’a tazo sanan ta tsugunna ta ijiye tray din still kallon Du’a take, ahankali Du’a ta janye novel din datake karantawa daga kan fuskanta jin kaman ana kallonta hada ido sukayida Uwani, almost 2yrs Uwani na aiki a gidansu but she thinks yaune 3rd time datake ganin Uwanin hakan yasa cikin yar muryan nan nata tace “kece uhmm yama sunanki U….uuuuu….” takasa tuna sunan dasauri Uwani tawashe baki tace “Uwani sunana mai aikin gidan nan” gyadamata kai Du’a tayi sanan tasake maida fuskanta kan novel din tacigaba da karatun dan ko kadan batada surutu kusan cikin duka yaran tafi gado halin mahaifinta indai rashin surutu ne.
Sosai Uwani takasa motsi daga wajen sai wani irin kallon Du’a take dabamatasan tanayiba, bude kofa Mami tayi ahankali ganin yanda Uwani ke kallon Du’a dabamatasan tanayiba dan ita karatun novel dinta take bilhakki yasa ta dakamata tsawa. “Uwani” firgigit ta farka daga dogon tunanin datake haka itama Du’a tadan firgita jin muryan Mami hakan yasa duk suka kallo Mami, cikeda bacin rai Mami tace “kin manta kinbar aiki a kitchen ne zoki wuce kifita” dasauri ta tashi ta taho tace “yakuri Hajiya” fita tayi Mami kuma ta watsa watsama Du’a data zubama mahaifiyar nata manyan fararen idanunta harara sanan tajuya tafice, tai kasa danso take tadaura girki, kitchen ta shiga tana duba naman data saka a wuta itakuma Uwani tacigaba da wanke wanke tana tunani sai chan tajuyo ta kalli Mami da hankalin ta kekan juya naman datake dake wuta tace “Hajiya” “ya akayi Uwani”? Mami tamata tambayan batare data kalletaba, tsayarda komi Uwani tayi tace “Hajiya kunada y’a haka maisa kuke boyeta wanan yarinya taki haka aiko shugaban kasa tafi karfinshi, maisa kuke kulle ta adaki haka” tunda tafara maganan Mami takasa cigaba da juya naman datake ta tsaya chak harta gama maganan datake sanan tace “ki tsaya a huruminki Uwani inba kinaso mu sallameki mu nemo watabane” dasauri tace “yakuri Hajiya tuba nake, kawai daman abin ya tsayamin araine” juyawa Mami tayi tacigaba da aikinta bata karabi takanta ba.
*******************
Yau Friday
Sunada wata al’ada agidan ranan jumma’a kowama gidan nacin gayun Jumma’a. Su Nana tun 11 suka dawo yau sabida lectures daya kawai sukeda shi, tun safe batai wanka ba sabida Novel din Disastrous Love datake karantawa daya daukemata hankali gabaki daya, su Nana ko harsun sake wanka sunci gayu abinsu sunfice daga dakin zuwa dakin Mum dinsu. Bude kofa akayi Mami tashigo daga bakin kofan ta tsaya binta tayida kallo sanan tace “yau bazakiyi wankan bane”? Dasauri ta ijiye novel din ta kalli Mamin ta dataci gayu cikin wata hadaddiyar bubu na shadda, tashi tayi dasauri tasauka daga kan gadon daga ita sai rigan baccin data saka iya guiwa, ahankali tasaukar da kanta kasa tana wasada yatsunta tace “yanzu zanyi Mami” tana maganan dasauri tajuya zuwa bathroom dinsu tabude kofa tashiga Mami tabita da kallo harzata bude kofa tafice saikuma ta dawo cikin dakin, gaban wardrobe din dakinsu taje budewa tayi ta tsaya tana kallon side din kayan Du’a, bangaren bras dinta ta kalla danta lura kwanan nan bata saka bra at all, daukan bra din tayi ta kalla sai lokacin tagane duk su mata kadanne saisa bata sawa kuma bazata iya fadan mataba, kwasosu tayi gabaki daya tadauki wani leda tazubasu aciki sanan tawuce tafita daga dakin, dakinta tashiga ta ijiyesu agefe sanan ta kwaso mata wasu new manyan bra masu kyau guda uku sanan tafito tadawo dakin, wardrobe din taje ta ijiye bra din sanan tazakulo mata wani lace mai bala’in kyau pink and white flowers dan tasan Du’a da hauka babu abinda ta iya kowani kalan kaya tasamu saka wa take, taciro tahada mata da sabon bra da pant tadauko ta ijiye mata kan gado, sanan tamaida wardrobe din tarufe takoma dakinta, kwalli tadauko mata sabo dawani sabon turare tadawo ta ijiye mata kan gadonta daidai lokacin tafito daga wankan daureda towel a kirji, juyowa Mami tayi takalleta daga sama har kasa, sunnar da kanta tayi kasa cikeda kunyan Mami tana gyara towel din dan bai rufe mata cinya da kyau ba kuma batasan zata sami Mami adakinba data maida rigan baccin ta, juyawa Mami tayi tafice abinta, dasauri tazo kan gadonta ta zauna, kwallin da Mami ta ijiye tafara dauka tace “laaaaa yama sunanshi irin nasu Ya Nana dasuke sawa a ido” wani irin murmushi tayi ta ijiye tadau kwalin turaren tana budewa tace “laaaa nima inada turare yanzu sunanshi Zara” budewa tayi ta ijiye cikeda farin ciki, agurguje tashare jikinta sanan tashiga shafa mai sabon bra tadauka tasaka aiko yamata cip cip lace din tasaka yamugun mugun mata kyau turaren ta tadauka ta feffesa yafi feshe goma sai murmushi take sanan tadau dan kwalinta da kwallin ta tafi gaban madubi, zama tayi tadauki comb taje gashin tayi sanan tai parking gashin da kyar sanan tadau dan kwalin duk yanda taso tadaura takasa daga karshe daurin yan kauye kawai tayi dan bata iyaba amman dudda haka tai kyau sanan ta bude kwallin taciro zata saka takai idanunta looking so excited kafin tasaka tawani tsirama idanunta ihu tayi sosai tawani zarooo hakan yasa tama tundaga idanun har zuwa gefen idanun har kunnenta bakin zanen layi, sosai ta kankame idanunta tana ihu ga radadi sai kuka batasan lokacin data mikeba tana tangadi tana ihu. “wayyo idanuna wayyo idonta” Mami da haurowanta sama kenan taji ihun ta dasauri tai hanyar dakin bude kofa tayi daidai yana shirin kuma kanta da bango tana ihu dawani irin sauri Mami ta tarota tana kokarin tallabo fuskanta tace “maiya sami idon”? Rirrike Mamin tayi cikin kuka tace “Mami idona zafi kwallin nanne ya tsiremin kwayan idanun” Mami na rikeda ita ajikinta tai bathroom dinsu da ita bude tap tayi ta tare hannunta ta debo ruwa wanke mata fuskan tayi tass sanan takashe tap din tana rikeda fuskan nata tace “bude idanun naga” ahankali tabude idanun kadan, aiko idon yayi jajir, kallon Mami tayi tanadan kyafkyafta idon tace “yadena zafi Mami” Mami na rikeda ita tafito da ita daga bayin zuwa gaban madubi zaunarda ita tayi sanan tadauki wipes din Nana data gani awajen tabude taciro kwara daya sanan takama fuskanta tagoge kwallin dayamata layi har kunnenta tagoge tass, sanan ta gyara kwallin dabama tasa a ido ba saidai kasan idanun sanan tadauki kwallin, habanta takama tace “bude idanun nagani” budewa tayi sanan Mami ta zizara mata kwallin aduka idanun rirrike Mamin tayi tawani tura fuskanta kan cikin Mami tace “Mami idona wani iri daman haka yakeyi wayyooo” chak Mami ta tsaya tamanta the last time da hannunta yama taba jikin yarta saiyau, firgigit kaman wacce ta tuna wani abu sai kawai ta hankadeta daga jikinta batare data kalleta ba tace “dau dankwalinki ki daura” tawuce tafita daga dakin, bin Mamin tayi da kallo sanan tajuya ta kalli Madubi kwallin sunma idanunta wani irin hadadden kyau, murmushi tayi tadauki dankwalin tasake mai wanan local daurin yan kauyen nan sanan ta tashi hijabi tasaka tai sallan azahar ganin biyu tamayi sanan ta tashi tacire hijabi taje tagaban window dakinsu ta yaye kannenta tagani su Aneela da Amal a compound suna guje guje suna wasa duk sunci gayu suma, hakanan taji inama itace komawa tayi tazauna sanan tadauki novel dinta tabude zata fara karantawa saikuma kannenta datagani a compound suka kara fadomata arai jitayi she’s damn tempted to go out, maida novel din tayi tarufe sanan tamike tsaye tana rikeda novel din tabude kofa taleko ganin babu kowa yasa da sauri tafito ta maida kofan ahankali ta rufe sanan tai stairs dagudunta har tana neman faduwa tasauka kasa nanma babu kowa, motsi dataji daga sama anbude kofa taji muryan Mum tanama Nana magana “kinduba zobon dayasa kimai hope yay sanyi”? wani irin kwasa tayi dagudu tashiga kitchen dinsu gabanta nafaduwa, gani tayi anama girki a kitchen din ga hadaddun kula na baki dataga an jera asaman kan fridge tana mamaki baki zasuyi yaune kuma, jin muryan su sun sauko kasa yasa da sauri tabude kofan kitchen dazai sadata da backyard tafita dasauri tamaida kofan tarufo dasauri daidai sun shigo kitchen din sanan tawani irin kwasa da gudu taidan mini garden din da Abban su yamusu awajen yawanci weekend Abba nazuwa garden din yazauna yasha iska, is very small a portable ga flowers sosai na daidai kudi ba irin na masu kudiba, ko kadan bata lurada mutumba sabida tana gudu tana waigan bayane jitayi kawai tai tuntube da mutum taiwani irin tumble tasaman kanshi tatsallako gabanshi zatai baya ta fadi yawani irin rikota gam gam hakan yasa dankwalin kanta yawani irin zamiye yafadi kasa, novel din datake rikeda shi yawani fadi shima, yanda gabanta ke faduwa dan tariga tasarai fadi zatayi yasa ta kankame idanunta gamgam cikeda tsoro tana wani irin nishi da bakinta dake fitowa afili.