Uncategorized

WAYAFI SOTA 7


P7

 “””Anty mariya tayi sallama! Fuska asake.yyinda zainab tayi Ido hud’u da wani k’atan photo ilage , Wanda ke pasing bakin k’ofa duk Wanda zai shiga parlourn dole yaga photon…wani mutum ne sanye cikin kakinsa na y’ansanda! Fuskarsa adaure akayi photon,hakan be Hana photon yin kyau ba…dg k’asan photon anrubuta asistan commissioner DSP ALIYU(haidar) mahamoud  Garba….da alama sadda aka k’aram  mashi girma akayi photon…..wani mugun faduwa gaban zainab yyi..harda bak’uwa kk ne mamana?” Da sauri zainab ta janye idonta dg kallon photon ” ta k’akaro murmushi ta zauna” ta kalli dattijuwar matar dabaza ta wuce 57 years ba,

tana zaune kan kushin ta kishingid’a “anty mariya tace eh wlh hjy ,gummu zata zauna na wani lokaci! ALLAH sarki ,ya gajiya mamana?” (Tana kiranta haka sbd sunan mahaifiyar ta kenan) murmushi anty mariya tayi tace alhmdllh Ina elham?” Tana week end gidansu mamanta” Masha ALLAH” hjy ta dubi zainab dake gaida ita da hannu cike da girmamawa” da mamaki ta dubi anty mariya tace banganeba,bata mgn ne kome??” Anty mariya tace eh,Amma ada tanayi ,dg baya ne abin yasameta befi yanzun shekara 3 da wasu watanni ba! subahanallahi ! Hjy ta fad’a cike da tausayin zainab d’in ganinta yarinya d’anya sharaf”meye sanadin ciwon kokuwa haka ta wayi gari Bata mgn??” Ah ah hjy abin Mai tsawone” zainab asanar da ita ?”hjy nata kallonsu “zainab ta d’ago Kai” fuska bbu walwala tad’aga Mata Kai alamar eh” hjy tace ok dama tanaji mgn kebatayi?” Anty mariya tace eh !

Hjy tace ah ah kuyi hakuri in sirrine basai najiba , ALLAH ya bata lfy , tafad’a sbd ganin yanayin zainab d’in yacanza…. girgiza Kai zainab tayi had’e da yiwa anty mariya nuni da ta sanar Mata komai ai bawani abun b’oyewa bane…anty mariya tafara bawa hjy labarin zainab in breaf….. yyinda zainab ta juya kanta gefe tasake kin Karo da wani photon na wani nmj shima kyakykyawa ne”da yarinya akafadarsa Yana murmushi…

 

   Inna lillahi wa inna ilaihir Raju un” wayyo ALLAH gsky natausaya Miki zainab, wannan ita ake Kira k’addara”Amma zainab natambayeki?”

d’aga Kai tayi alamar eh! Hjy tace husna tazo gun gaisuwar Umar?”

Zainab ta girgiza Kai” hjy tace kinsake had’uwa d ita kojin labarinta??” nanma zainab tace ah ah! hjy tace ok to shikenan” kallon hjy zainab keyi tana mamakin meyasa ta tambayeta ?

Bayan shiru yad’an ratsa parlourn,anty mariya tace zainab muje ciki ko?” Hjy tace ah ah abarta nan guna”ko wani aiki zata Miki mamana?” anty mariya tace ah ah hjy,bbu damuwa ta zauna! murmushi hjy tayi tace kinsanni da k’ulafucin y’a mace,tunda naga zainab naji ta kwantamun arai ,balle danaji labarinta abun tausayi”anty mariya tace eh hjy balle ga elham bata nan zaman bbu dad’i ke d’aya” wlh kuwa ga Alh da HAIDAR basa gari, shikuma faruq Yana office Usman Kuma yana skul…gashikema Baki nan yau kukadawo…wani mugun bugawa kirjin zainab yyi jin an ambaci Mai sunan Yaya Umar,Amma saita dake…anty mariya tafice bayan sun Yi sallama da hjy…

    Yyinda zainab har cin zuciyar ta taji tana k’aunar matar” sbd ganin kyawawan halayenta,sab’anin wasu masu kud’in” dabbu tausayi aransu da rab’ar talaka,sai izza da d’aukar Kai da wulakanci…Amma ita wannan bbu ruwanta… xainab kinyi shiru bara na kamiki lemu! Cewar hjy tana tashi tsaye, zainab tayi murmushi had’e da yiwa hjy alamar ah ah bazata shaba…hjy tace banyaddaba zainab,batajira amsartaba taje ta kamata ,kafin ta tashi ta kunna kallo! Tace ko kallo kiyi kinrage kewa…suna nan zaune suna fira sama sama tahanyar nunal har zainab taji ta sake da hjy,jin hjy nacewa bara ta hadawa faruq abinci har 6 pm tayi Yana hanya”hakan yasa zainab yimata sallama ta bar part d’in sbd saitaji batasan kowa nagidan yasanta inbacin hjy gara ta tsaya matsayinta…Moping tasami anty mariya nayi”da sauri zata k’arba” tace ah ah zee ki barshi nama Gama ai! dama y’an goge goge da share share nayi kwana2 bama gd ,sai abinci Dana aza…aikin bbu yawa! Kindawo ne dg gun hajiyar ne?”

Zainab tad’aga Kai ,kafin tazauna “anty mariya tace nasan kinyi mamakin kirkin hjy tamafi hakan wlh,tanason mutum Mai gsky  da Amana,shiyasa kikaga zamammu da ita yayi daidai” zainab ta tambayi anty mariya Ina biro?” Ok tace had’e da ficewa d bucket din datake moping din” bbu jumawa tadawo da biro had’e da memo tabawa zainab had’e da Zama kusada ita… zainab ta rubuta gsky anty nayi mamakin tambayar da hjy tamun game da husnah wlh…anty mariya tace eh wlh konima k’ila tana zargintane ko?” Zainab tad’aga Kai” had’e da rubuta dan ALLAH kisanar Dani tarihin family nan pls?”anty mariya tace ok muje muyi Sallah tukum sbd lokaci yyi..

 

 

   ********

Zaune suke amadaidaicin parlourn anty mariya suna kallon tashar arewa” anty mariya dadubi zainab tace zansanar dake atak’aice abinda nasani….baffanki ,akaduna kafin ya aureni ,wata rana yatsintsi walad da kud’i dasu ID card da wasu takardu,acikin walad din,atake yaduba jikin ID card d’in yadau number yakira…Ashe Alh mohamoud ne ya yarda ita,nan yamasa kwatance yazo yakamasa ,yyi farin ciki sosai sbd meeting yazoyi agarin ya yarda walad D’insa,shibata kud’in yakeyiba ,ah ah takardunsa masu mahimmanci dake ciki.. nan yyiwa baffanki godiya yabashi kud’i , had’e da tambayar sa aikin me yakeyi?” Yace bashi aikin komai ,nan yabashi card nasa yasamesa a Abuja yazama sakatarensa….harzuwa ya aureni sg baya yace mudawo gdn nan da Zama..

 

Ga yadda baffanki yasanarmun ,hjy Fatima da Alh mahamoud Garba aiki yakawosu Abuja ,sunsha wahalar rayuwa kafin suyi arziki…d’ansu na 1 ALIYU (haidar)Wanda ke mataimakin commissioner….. d’an sandane Wanda yasan kanshi ,Yana aiki tsakani da ALLAH middin kk kaimasa k’ara insha ALLAH zaibi Miki hakk’inki,talakawan garin nan na k’aunarsa , yyinda marasa gsky ke k’insa…jarimine namijin gske baya tsoro ko shakka ,Yana k’aunar iyayensa da musu biyayya tamkar zai mutu,gefe guda Kuma suna k’aunar juna shida y’an unwansa… har yanxun bashida aure sbd shi aganinsa beda lokacin mace ma ,kullum zirga zirga akirasa anan akamasa k’ara sai week end yakeda lokacin kansa wani sa’inma har week end din ana nemansa office… akalla zaiyi shekara 38 ko 40,tun ana Masa maganar har andena ,kwanaki b’arayi ko ince anmasa ture ,suka shigo gdn nan da dare, kasancewar week end Yana gd, ALLAH ya azasa akansu yagama dasu dukda sunmasa rauni sun harbesa… wannan dalilin yasa kikaga gdn zagaye da jami’an tsaro….hjy ke kiransa da HAIDAR sbd bata fadar sunan sa sbd shine na farko!baya shiga sabgar  dabatasa ba. gsky Kinga shekarar mu .5 agdn nan inbacin gaisuwa bbu abinda ke hadani dashi,danshi ko fara’a bayayi…inkinga Yana murmushi to da hjy ne ko elham y’ar faruq…sbd Yana k’aunar yarinyar da tausayinta…. Umar

Faruq shine d’a na2 agdn…wani dummm had’e bugawa kirjin zainab yyi and jin sunan Wanda aka kira…d’an jaridane Mai farin jini ,yanada y’a Fatima (elham) mmn elham tarasu gun haihuwa itada babyn..sbd shi faruq yyi aure shekarar su 5 da matar ta rasu….elham y’ar 4 years  ruk’wanta d kula da ita,yadawo gun hjy….tsakanin haidar da faruq shekara 4 ne….faruq shima kusan duk halinsu guda da HAIDAR dandai shi Yana sakin fuska da mgn da jamaa, sannan beda k’yankyami irin na haidar din…Kuma yanada saurin fushi da tausayi…usman dake lavel2 shine auta dg gareshi hjy Bata koma haihuwa ba ,bansan Kuma daliliba gsky..

hjy nason ganin y’a mace agabanta ,kafin muzo gidan nan ta rik’i Mata 2 duk sun ha’inceta saita Dena ruk’on kowa,dakuma masu aiki,sbd Kinga yaranta 2 faruq da HAIDAR kowa yanada mak’iya sanadin aikin shi,akwai wata me aiki da hjy tayi aka had’a Kai da ita ,akace taje gdn redio ta nuna faruq yamata fyade…tana aiki agdnsu…sai reshe yajuye da mujiya ,haidar yakamata ,yyi binkice har yagano Wanda suka sakata,batawa babban d’an jarida suna….hakan yasa hjy k’in yarda da kowa tadena daukar masu aiki…

Kullum baffanki inyatafi office tun 10 nasafe sai 6 na yamma yake dawowa ,hakan yasa tunda banida yara nashiga ciki innagama abinda Nike nataya hjy aiki…dama Mai gadi kebawa flowers ruwa yashare haraban gdn..taso ruk’a biyana wani Abu Amma nace aha ah wlh mungode d ahalarcinsu,sbd Kinga ada gdn haya muke ,muka dawo nan ,to gashi yanzun har baffanki yasiyi fili yafara gini zamu koma insha ALLAH….girgiza Kai zainab tayi. azuciyarta tana cewa ikon ALLAH kowa da irin abinda yadameshi…kafin  tayiwa anty mariya sallama ta nufi d’akin dake matsayin nata Wanda katifa ce kawai kan tayis adakin sai toilet gefe guda trolley dinta ne… toilet ta wuce tayi wanka had’e da alwallah tazo tayi shafa’i da wutiri da karatun alk’ur’ani me girma,kafin tayi addua ta kwanta, had’e da lulawa tunanin rayuwa…har bacci yyi awon gaba da ita…Washe gari duk bayan sunyi breakfast zainab ta Taya anty mariya aikace aikace suka Gama da wuri,kafin suyi wanka…sbd baffama har yawuce  gun aikinsa’!

Bayan sun shirya suna kitchen saiga wata kyakykyawar baby “sanye take da doguwar riga y’ar kanti iya gwiwa,kanta yasha gyara adaure bbu kitso,hannunta rik’e d big borm tana tsotsa ta shigo har cikin kitchen d’in”anty mariya tace oyoyo elham Ashe kin dawo”?dariya elham tayi tace yo eh Mana nagaji gidan bbu dad’i naita musu ihu suka maidoni nafison gun granny! Murmushi anty mariya tayi tace ,kodai kinfisan kiyita shagwaba ko?”kallon zainab elham tayi had’e da cewa anty wacece wannan?” Zainab tayi Mata murmushi hakanan taji yarinyar ta burgeta ,dama gata gwanar son yara”sunan ta anty zainab ! Cewar anty mariya.. elham tace yeeeeee! dama granny tace nazo nace Miki anty zainab tazo Ashe wannan ce” tafad’a cike da gwarancinta na yarinta had’e da Kama hannun zainab tace “anty kin iya goyo ki goyani?” d”aga Mata Kai tayi”anty mariya tace oh elham sarkin surutu to ita dai bakinta ciwo yakeyi bata mgn” elham tadubi zainab tace hakane anty?” Zainab tad’aga Mata Kai”kafin ta dauketa ta Goya,suka fice…anty mariya tayi murmushi kafin ta cigaba da aikinta… knocking zainab tayi,kafin ta murda’k’ofar su shiga..tasami hjy na waya kamar haka…eh dan ALLAH masu kyau kyauta zanyi dasu ko kala biyarne…kafin ta yanke war tana murmushi ganin elham bayan zainab ga zainab da uwar hijab iya gwiwa…har k’asa taduk’a ta gaida hjy ” fuska asake hjy ta amsa tana cewa sauketa zainab wannan Bata iyacin dawon garinba ,Koda safen nan inajinta sukayi baran baran da dadinta akan be goyataba ,shine zata Dora Miki d’awainiya…. murmushi kawai zainab tayi, elham tace yeeeeee granny Kinga anty zainab ta goyani ?tafi dadina kirki ko?”

Zainab muje ciki Dan ALLAH aiki Zaki tayani wlh Alh ne da haidar zasu dawo yau da marece shine Basu fad’a ba tun jiya sai yauda safe…ajiye elham ,inkika biye Mata akan goyo to bayanki yyi ciwo ,kowa agdn nan tace yagoyata,mayyar goyo ce yarinyar nan”sannan kicire hijab din inbbu takura Mana…Murmushi kawai zainab tayi tasaka d’ankwalin rigarta ta goya elham dashi…byn ta janye hijab d’inta!  kafin ta dubi hjy ta Mata nuni da mezata farayi Mata?

Hjy tace muje ciki na gyara nan ai… parlourn hjy d bed room nata zainab ta gyare ras very need ta turaresa d boner” tawanke toilet ! Duk abin nan elham na bayan zainab tana bacci…kicin ta koma tasami hjy da anty mariya suna aiki” hjy tayi murmushi tace sannu kinji nagode sosai”Amma muje ki kwantar da elham tunda tayi bacci”

bayan takwantar da ita tabiyo hjy kicin duk hjy tace Mata bbu aiki taje ta huta… Amma tace ah ah ai wannan ba aiki bane , alokacin Kuma har anty mariya ta gama wanke wanke Takoma part nasu sbd har 1pm tayi..hjy tace Dan ALLAH zainab kin iya alkubus?” Murmushi zainab tayi had’e da d’aga Kai….nan tayiwa hjy kwab’i ,kafin tayi sallar azahar awani had’add’an daki na bak’i,nan tasami hjy a kicin ta Mata nuni da taje tayi Sallah ta Ida Mata aikin…sai saka Mata albarka hjy keyi ta fice..itakuma tacigaba da Fara jifar alkubus din da had’a miyar…

 

    Hjy kuwa tana shiga bed room nata tasame shi fas yyi gwanin kyau…taji motsi a toilet ashe elham ta tashi dg bacci tana toilet tana wasan ruwa…hjy ta duba taga zainab ta dauke Mata kudinta da zoban gwal dinta ta azamata kan mirro,dama ta ajene dan ta gwada zainab d’in dukda harga ALLAH ta yarda da ita to Amma ance baa gane mutum afuska..

Bayan hjy tayi Sallah tama elham wanka…itama tayi ,kafin sufito….suka Sami zainab dake kicin harta Gama komai saura alkubus din dake kan wuta na karshe data jefa”tana goge kicin d’in….cike da jin dad’i hjy tadubi kicin din afili tace Masha ALLAH zainab gsky kinada tsabta mijinki yadace ,inason mutum me tsabta”yanzun kije bed room din d’azun kiyi wanka da sallar la’asar Dan lokaci yyi sai kuci abinci,Ni na Ida tsame alkubus din tunda kingama komai ,dama gulmar su HAIDAR ne sukace namusu ni innayi gaddama yakemun….

Bayan zainab tayi Wanka da Sallah sukaci abinci itada elham,kafin ,elham tace Dan ALLAH anty zainab kisake goyani kinji…goyatan zainab tayi tana Mata surutu ,itadai zainab saidai tayi murmushi…suna haka hjy ta shigo ta dubi zainab tace Wai zainab ke Baki gajiya ,kigoye wannan k’atuwar haka da ita?” murmushi kawai zainab tayi…tanama hjy nuni ko akwai aikin dazata matane?”hjy ta girgiza Kai “tace kije ki huta zanje nagyarawa HAIDAR d’akinsa ne…. zainab ta girgiza Kai ah ah tabari ta gyara….ganin zasuyi jayayya yasa hjy tace to muje sbd har cikin ranta taji ta yarda da zainab…nan suka fito ,sund’anyi y’ar tafiya tukum suka iso part d’in haidar d’in,hjy ta bud’e d’akin tabar key ajiki ta fice tana cewa asakko elham….

 

Masha ALLAH tamkar ba d’akin nmj ba ,bbu darti sai k’ura ko wani kalle kalle zainab batayi ba tacigaba da sharewa taje ta dakko mopa a kicin tayi mopping…ta wuce bed room nanma ta gyara kallo d’aya tama d’akin tacigaba da abinda take Dan talura akwai CTV camera adakin,ga wardrobe din masu key ne duk arufe suke taso canza bed sheet,Koda taga arufe suke sia wanke bayi ta fito ta feshe d’akin da air fresheners….ta fito dg d’akin ta rufe…ta zare kwy d’in ta nufi parlourn hjy…

Hjy tace sannu kinji y’arnan ngd kinji ,ta karb’i key d’in tanawa hjy sai anjima,hjy tace taje waiting parlour ta kwantar da elham dake bayanta tana bacci , sannan taje dining area ta Debi  abinda takeso…..fitowa kawai zainab tayi Amma aranta bazataje ta D’ebi komai ba,Wanda taci d’azun tagode ma…..horn da jiniyar mota taji…hakan yasa tagane k’ila masu tafiyarne suka dawo….tana kokarin kwance goyan taji k’amshin turaren namiji da ringing na waya…ahankali ta Kwantar da elham,tana rirrigarta ganin zata tashi…faruq dake saukowa dg down starss….yayita kallon zainab data bada baya tana rirrigar elham “beganin fuskarta Amma yasan elham ce ake rirriga…. tab’e Baki yyi Yana cewa k’ila wata Mai aikice hjy ta jajibo…itadai zainab batama San dashiba ,ta juya da sauri ta nufi k’ofar fita…. alokacin Kuma elham tafasa ihu tana Kiran zainab ganin ta tafi ,faruq na kiranta tamasa banza tabiyo zainab….. zainab na murda k’ofar Yana kawowa….acikin rashin sa’a hannunta yabige Masa  files2 dake hannunsa….suka zube k’asa…..wani bugawa kirjin zainab yyi had’e da jin mugun tsoro da Kirman jiki,bata kallesaba ,taduk’a ta kwashe files d’in da sauri ta mik’a Masa….mamaki yahanasa k’arba”wannan wane irin  rashin tarbiyya ne tayi laifi bazata bada hakuriba wacece ita??”yafad’a azuciyarsa” duk’awa tayi ta aza Masa bisa k’afarsa Mai takalmi sawu ciki ta da’go da niyar tafiya…..by surprise taji ya wanketa da wani gigitancen Mari….adenan elham daketa kiranta ta tsaya tana kallonsa….

 

Share

 

BY

MMN FAREESA

[9/20, 2:24 PM] Mmn fareesa: ????????????????????????????????????????

 

 

 

????WAYAFI SONTA ?????

 

 

????????????????????????????????????????

 

 

 

Written by mmn fareesa

 

 

It’s true life story????????

 

 

WANNAN LABARIN NA KUDINE…gamai bukata zata biya naira 300  kachal ta karanta ” tahanya mafi sauk’i Zaki siya Zaki tura kudin ta account number 0089110527  suwaiba Hussaini zakirai  access bank…    saikiyi screen shot kituro shaidar kin biya ko kuwa kituro MTN ta wannan number na 300″ 08100084251

 

 Domin karanta books namu..

 

Y’AR SADAKA book2 na mmn sultan dakuka dad’e Kuna nema danjin yazata kasance…naira…200 ne gamai bukata yatura kudin ta wannan  account 0089110527

 

WAYAFI SONTA ( mmn fareesa) naira 300

 

Induka kakeso naira 400 ne kachal…masu bada kati suyi mgn a wannan number 08100084251….bamasan Kira ,sak’o kawai…

 

Inkinsan Zaki fitarmana da books karki siya….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button