UBAYD MALEEK 1-END

UBAYD MALEEK Page 81 to 90

*****************Tun dasukai magana da neges tasakawa jekadi ido sosai akan motsinta takai har bibiyarta tafarayi Amma sbd jekadin ta iya takunta fiyeda tunani lailan Bata taba samun damar sanin komai dangane da wani baqin yanayi ko sirri atareda jekadin ba harta fara sarewa daga bin daddaqin na jekadi sbd Sam ba dabiarta bace Dan ita ta dauki kanta tanada abinyi hakama ba girmanta bane tsayawa irin wainnan labe laben ga abun duniya yafara sakota gaba sbd yanzu rayuwarta ta wayi gari kowa baya tareda ita tun daga kan mijinta har yayanta su danginta ba’a magana sbd ta Jima da watsar dasu dama mahaifiyarta ta Dade da rasuwa mahaifintane kawai shima tsufa yacisa sosai har baya gane kowa sai anfada Masa wannan waye shiyasa batada lokacin kowa saina Gina rayuwarta sbd gidansu kaf kowa yazamo wani hamshaqan kansu duk da ita kadaice mace sai tana alaqanta kanta da matsayinsu suda suke maza bazata taba yadda itama ta zauna tana amfani da alfarmar wani ko sunansa so take ta Gina kanta da kanta ta yanda za’a fadeta da matsayin datake dashi badai da matsayin wani datake a qarqashinsaba shiyasa ta rufe ido ta watsar da ‘yayanta da komai Amma yau ta wayi gari ko ‘yan aiki batadasu sai guda biyu kacal da ganinsuma baqin ciki yake sanyata sbd Kamar Saida aka zabo wainda suka fi Muni da rashin kakkamtuwa aka Aiko matasu batada ‘da,

 batada miji, batada gidan kanta bare matsayin kanta ko sunan Wanda zatace a qarqashin alfarmarsa take batada Dan Haka gabaki daya yanzu Jin take kamar ta rasa nustuwa da tunaninta Bata iya tunanin komai kanta ya toshe zuciyarta bayan kwashe kwashen tunane tunanen duniya dasuka kusa haukatata Babu abinda takeyi tarasa wazata zauna dashi ko masifa tayi ta rage abinda takeji bare.

Tunanin ‘yarta afia ne yafado Mata Rai take taji idanuwanta na neman cikowa da hawaye ta hadiye tana miqewa zuwa bakin window ko zataji sanyi sanyi Amma takasa Saida hawayen suka tsinke Mata ta zauna bakin windon tana fashewa da wani irin kuka Mara sauti tana buqatan mutum atareda ita Wanda zai dubeta ya saurari damuwarta.

Afia take tsananin buqata ayau din sbd ta Dan duk duniya yanzu ‘yartace kawai me iya rarrashinta ta rungumeta ta saurari duk haukar dazata iya fada da wadda zata iyayima kaf duniya yanzu ‘yartace kawai me iya Mata wannan bayan ita ko maleek tasan bazai taba kallonta da idon sauki Kona mutunciba

Dan Haka hankalinta yaqara tashi tana jinta cikin mummunan yanayi na baqin cikin rayuwarta da Kamar tayi hasara.

Ta Jima Yana boyayyan kukan daya Gama kumbura idanuwanta da fuskar datake masifar ji da ita sunyi jajir sunyi suntum duk da hakan bataji wani sauki ko sassaucin komaiba ta miqe ta nufi toilet jiki amace ba kwari ta wanko fuskarta tareda yowar alwala Dan ko wankan batada karfin Yi tafito ta goge fuskarta ta tayarda sallar ishai da akai tun dazu bayan tagama akaro na farko bayan tsawon lokaci yau ta daga hannu tana rokon Allah sassauci da mafita sbd ada ganin tagama samun komai na rayuwa yasa sallah data zama Dole kawai takeyi Amma adhkar da sauran adduoi gurin ubangiji basa gabanta sbd duk abinda takeso tagama samu.

Agurin take zaune tana tsiyayar hawaye ta gefen fuskarta batareda ta iya tashiba takai hannu ahankali ta dauki wayarta ta Nemo sunan afia akaro na farko bayan tsawon lokaci taji qaunar ‘yayanta na dawo Mata sbd haryanzu tasan kome zata zama arayuwa ‘yayantane kawai bazasu taba iya guduntaba musamman afia datake kaunarta fiyeda komai saidai takasa duba kaunar da yarinyar ke Mata sai yanzu take ganewa Dan kuwa a yanda takeji yanzu ko ‘yayanta abata ta zauna dasu zataji saukin duhu da kuncin da zuciyarta ke ciki.

Numbern afia takira tayita ringing No answer harso biyar take jikinta yasakeyin sanyi hannuwanta sukai sanyi ta juyar da kanta ahankali tana kallon qasa kafin ta daga wayar ahankali ta shiga gurin saqo ta rubuta mata” _Kiyi hakuri afia_

Tura Mata tayi tareda ajiye wayar tana rufe idanuwanta zuciyarta na wani irin nauyi da kunci.

Jekadi jin tsarin na barin padima tareda tattalata tasamu lafiya amaida gida yasata sauya nata tsarin itama nabin umarninsa tafara bawa padima magani tareda kulawa da goge Mata fatarta data Gama konewa tana shafa Mata magani akai akai Wanda take padiman tafara dawowa hayyacinta Dan hartana Dan iya bude Baki Kuma tana iya zaunawa sai hakan yasaka jekadi sake bada himma sosai cikin kwana biyu padima tafara dawowa mutum sosai a ranar da padiman tafara iya bude Baki sbd tsananin farin ciki jekadi ta fita ta kebe tasake Kiran Mr Omar ta sanar dashi komai alokacin suna hanyar tahowa gizah suna cikin jirgi Amma Basu riga sun tashiba Dan Haka baida damar ganin maleek sbd Yana first class Dan haka yabari harsu Isa tukuna.

Dayake da daddare ne sosai jekadi ta fito tayi wayar adaidai lokacin lailah Tana zaune taji motsi me girma ta window din dakinta Kuma Kamar harma da mutum tagan gilmawarsa saita tashi zaune dakyau tana kallon windon zuciyarta na Dan harbawa Amma takasa riqewa ta miqe tsaye ta nufi windon tana Dan daga manyan dogayen labulayen windon saitaga kaman sake gilmawar mutum Kuma idan idonta ya gani kamar da kyau jekadi tagani.

Kallon hanyar tayi tana dawowa cikin dakinta zuciyarta na gargadarta da bin jekadin saidai Kuma wata zuciyar tana ingizata ga zuwan ta rintse ido tana komawa ta zauna saidai Kuma takasa nutsuwa tanason bin jekadin 

Ta miqe da sauri tareda daukan wayarta ta fito sanyeda slippers tabi hanyar baya ta fice daga sassanta tabi inda jekadin tabi tana tafe tana waige waige har tayi Dan nisa saitakasa gane inda jekadin tabi tafara waigawa koina tana dubawa saikuma tsoro yashigeta ta juya da sauri zata juya saiga jekadi ta fito ta wata hanya tabi hanyar Nayan sassan maleek tana tafiya cikin nutsuwa sbd kada tabar qarar sawu.

Da fargaba da mamaki me tsanani take kallon jekadin tareda rintse idanu tabude mamakinta na neman komawa tsoro sbd kayan dake jikin jekadin bashine kayan data ganiba ajikin jekadin data wurga ta windontaba Kuma tabbas Bata Isa ace yanzu yanxu ta sauya kayanba.

Kodai idanuwanta ne ke Mata gizo kokuma wanine ya wurga ta windon ba jekadiba?

To idan wanine waye?

Meyasa yayi irin shigar jekadin?

Girgiza Kai tayi da sauri cikin tsananin tsoro dason tabbatarwa tabi bayan jekadin cikin sanda tana Nemo camerar wayarta tareda kashe hasken flashlight sbd idan ba tabbarwa tayi da wacece jekadin acikinsu hauka zata iya kamata Dan haka a sidade sidade tabi bayan jekadin tana waiwaye cikin tsananin tashin hankali sbd Jin kamar Kuma Ana binta itama san’da san’da abayanta.

Wata boyayyar kofar dataga jekadi ta fita yasata zare idanuwa cikin mamaki da tabbatarda zancen neges kenan dai da akwai wani Abu da maleek ke boyewa¿Aikuwa yau saitaga ko menene to Amma Kuma ta Yaya tunda jekadi rufe gurin zatayi..

Tunani tafara ta yanda zata samu Isa cikin dakin Kota halin qaqa taga abinda kila zai dawo da aurenta da maleek Dan Haka bazata Bari wannan damar ta wucetaba.

Waige waige tahau Yi cikin sauri Idonta ya fada kan wani qaton katako Wanda batama tsaya mamakin ganinsa a guri irin wannan ba ta dauka da sauri ta lallaba taqarasa bayan jekadi dake kokarin rufe kofar da mukullin ta waje bata tsaya wata wataba ta daga katakon ta buga Mata akai bada karfi ba sbd Jin bazata iya da qarfinba sbd kadata illatata sai kawai ta tureta gefe ta Fadi ta qarasa dakin da gudu ta tura kofar ta fada ciki tana dubawa.

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button