MADADI Page 101 to 110

Halisa mirmushi tayi ta girgiza kanta kafin tace”Yarinyar nan fa lafiyarta lau wallahi uwarta ce ke d’ora mata lalurar ‘karya duk dan ta hanaka zaman lafiya sannan kuma bukatarta ta biya ta kuntatawa Najaatu.
Ya dinga kallonta yana nazarin maganarta yace.”Yanzu Halisa Zainab sai ta ‘kir’kiri ciwo ta d’orawa ‘yarta dan biyan bukatarta.” Halisa dariya tayi kafin ta ta’be bakinta tace”Gashinan kuwa ka gani ni da kunnena naji suna maganar ita da ‘yan uwanta a dazu dana shiga duba jikin yarinyar naji suna maganar to ban fahimta sosai ba sai da kayi min maganar wai ashe a gidan nan ma ka kwana.”
Cikin wani irin yanayi Yace.”Kika ce kinji da kunnanki suna maganar kan al’amarin..”
“Idan nayiwa Zainab da ‘yan uwanta sharri meye ribata wallahi kaji rantsuwar muslumi da kunnena naji suna maganar suna dariya sai da kayi min maganar a yanzu na sake fahimta amma ni ban fad’i maganar dan ka dauki zafi b…….. Hannu ya d’aga mata bai bari ta karasa ba ya miqe ya fita daga dakin, kai tsaye gurin Zainab ya nufa, Hayaniyarsu da shewarsu yaji a daya dakin can kunnuwansa suka jiyo masa kukan Ummi dake dakin Zainab da sauri ya nufi dakin yaga yarinyar saboda kuka da mutso mutso har ta fito daga cikin net dinta ga bargon dake jikinta ya toshe mata hanci! da mugun sauri ya ka’rasa inda take bargon yayi gaggawar daukewa yarinyar ta sauke wata zazzafar ajiyar zuciya! gumi hawaye majina duk sun ‘bata mata fuska! Abbah hannusa yasa ya dauki yarinyar jikinsa sai kyarma yake ya shiga jijjigata inaa! kamar sake tunzurata yake ta dinga kuka tana yakushin fuskarsa, cikin tsantsar tashin hankali gami da nadamar kar’bar auran Zainab ya fita da yarinyar a kafadarsa
Cin karo yayi dasu sun fito daga dakin dik su ukun a sakamakon jin kukan yarinyar daya cika falon……Zainab a tsorace! ta karasa kusa dashi ta miqa hannu zata kar’bi yarinyar ya wanke fuskarta da wani gigitaccan mari! Gefe guda ta matsa tare da dafe kumatun ta da hannunta jikinta in banda rawa babu abunda yake…..Ya kalli su Aunty Balaraba yace.”Wallahi kunji kunya kun zama annoba a guri yanzu da girmanku da komai kuke aikata abu irin na marasa imani! me yarinyar nan tayi muku kuke azabtar da ita! Kuna manya masu shekaru wanda suke sama da nata ba zaku d’orata a hanya mai kyau ba sai ku d’orata hanya mara kyau! hanyar da zata cutar da kanta da abinda ta haifa, hakika zamanku a gidan nan be amfaneni da komai ba sai sharri! ya kalli Zainab dake wani irin kuka na tsoro yace.”Zainab ban ta’ba tunanin kishi zai rufe miki ido ki nemi hanyar halakar da abinda kika haifa ba, ashe dama karya kike Ummi lafiyarta lau amma kika dora mata lalura duk dan ki hanani samun nutsuwa shin yanzu meye ribarki nayin hakan? Jiya Dr sai da ya fad’a miki matsalar yarinyar nan ashe kamar ‘kara tunzuraki yay kin barta ita kadai a daki tana ta kuka ke kina ta tare da wad’anda zasu kaiki su baro, wallahi in banda darajar mahaifinku da dukkaninku sai na baku mamaki ni ba shashashan namiji bane da zaku dinga wasa da hankalinsa, sabida haka ko wacce ta fita ta bar min gidana zaman ya isa haka, kuma ku sani sai na sanar da Ya sheik abunda ke faruwa.” Yana gama maganarsa ya shige ya barsu a gurin….Zainab na wani irin kuka na nadama tabi bayansa….Zubewa tayi k’asan kafafunsa tana kuka hade da bashi hakuri, Abbah ya dinga jin tamkar yayi ta boll da ita gurin, hakuri ya bawa zuciyarsa ya buga mata tsawa tare da fadin”Kar’beta ki bata nono muguwa kawai.” Zainab jiki na rawa ta kar’bi yarinyar a hannunsa ta fito da nono tasa mata a baki………Girgiza kafafaunsa yake yana tunanin irin hukuncin da zai dauka akanta, ba zai saketa ba amma sai ta gane kuranta harshi zata yiwa wasa da hankali lallai sai ya wulakantata dan baya iya had’a kowa da ‘ya’yansa…..Zainab kuka take tana masa magajiya gami da kokarin wanke kanta yaki sauraranta data isheshi ma cewa yay ta rufe masa baki ko ranta yay mummunan ‘baci! Gum tayi da bakinta ta cigaba da shayar da ‘yarta nono………….
*Littafin na kudi ne….!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar biyan kudin littafin ga yanda abin yake…..Vip group #600 normal group #300 account…. 0542382124…Binta umar gtbank…Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
85*******’Bangaransu aunty Balaraba kuwa hankali a mugun tashe suka had’a kayansu suka bar gidan cikin nadama gami da dana sanin abinda sukayi dan sunyi masifar tsorata da yanayin ‘bacin ran da suka ga maigidan a ciki tabbas daba dan darajar mahaifinsu ba to da babu shakka sun san sai ya dauki mataki a kansu kamar yanda ya fad’a musu fargabarsu daya kada ya sami mahaifinsu ya fada masa abunda ke faruwa babu shakka idan mahaifinsu yaji wannan al’amarin to sai sun fuskacin bacin rai mai tsanani.
Abbah da babbar murya ya gargadin Zainab gami da kafa mata dokoki akan ‘Yarsa duk da yasan rai da rayuwa na Allah ne haka kuma cuta da lafiya shima na Allah amma dan ya tsoratar da ita yasa yace mutukar wani abu ya samu ‘yarsa tofa ba zai kyaleta ba sai ya dauki mataki a kanta tunda ya gane inda ta dosa wato yarinyar bata itace a gabanta ba kishin jahilci ne yake damunta to kome za tayi taje tayi akan kishinta amma kada ta kuskura ta sake yi masa yawo da hankali ko kuma ta dauki ciwon karya ta d’orawa ‘yarsa wannan itace damarta ta karshe idan ta sake ta kuskura ta sake maimaita masa abu makamancin haka to zasuje gaban mahaifinta ya sheda masa abubuwan da faruwa………Sosai take kuka ta kuma raina kanta da wayonta bata ta’ba tsammani al’amarin zaiyi zafi hakaba hakuri take bashi ya’ki sauraranta sai da ya ‘kare mata tanadi tukkuna yayi ficewarsa daga dakin ya barta cikin nadama mara amfani.
Rai a bace ya isa gidan Najaatu a maimakon ya samu sassauci sai ya tarar da wani ‘bacin ran dan kicin -kicin ya sameta tunda ta gaishe shi ta tambayi jikin Ummi bata sake masa magana ba fitowa ma falo tayi ta kyaleshi a dakin shi kadai……Takaicin sa ya sake nunnkuwa a gaskiya al’amarin mata yana da wuyar sha’ani tabbas lusarin namiji ba zai iya had’a mata biyu ko uku ba.
Wanka yayi ya kintsa jikinsa ya fito falo ya sameta a zaune tana wasa da d’anta tana murmushi kamar yayi mata magana sai ya rabu da ita, gurin cin abinci ya nufa, a tunaninsa zata zo ta had’a masa abin kari, sai yaga ta kara gyara zamanta, girgiza kansa yay da kansa ya hada tea ya zuba soyayyar doya da kwai a plate a nutse ya gama karyawa ya miqe daga gurun, inda take ya nufa ya tsaya a kanta tare da tsira mata idonsa.
Kasa d’ago kanta tayi ta kalleshi tana dai ganin Inuwarsa tsaye a kanta, yatsun hannuwanta ta shiga wasa dasu kwallah na kokarin zubowa daga idonta tana kokarin mayar da ita.
Gyaran murya yay ya kira sunanta”Najaatu.” A hankali ta kalleshi tare da amsawa ciki ciki ta mayar da kanta kasa, Yace.”Gaisawa kawai mukayi da juna babu wata mu’amular arziki koda akwai wani dake damunki ne.”?
Girgiza kanta tayi tace”Babu abinda ke damuna.” Yace.”Karya kike ai ba haka fuskarki take ba tunda na shigo gidan nan na lura da canzawarki ko dan na kwana gidan Zainab ne kike fushi! kada ki manta fa na nemi alfarmarki kuma lalura ta wuce komai.