MADADI 1-END

MADADI Page 101 to 110

Tace”Haba dai saboda ka kwana a gidanka gurin iyalinka sai naji haushi nifa na baka damar haka wallahi babu komai yau ma kaje can kayi kwanciyarka sai yafi maka akan a kira ka da tsakar dare ace kazo..

Ya dinga kallonta yana nazarin maganarta dik maganganun da take fad’a tana fad’arsu ne iyakacin bakinta amma ba har zuciyarta ba……….”Wannan maganar da kike fada kina fadarta ne iyakacin baki ba har zuciyarki ba na kuma fahimci cewar al’amarin beyi miki dadi ba kiyi hakuri kinji ko Ummi ta samu lafiya insha Allah yau tare dake zan kwana.

Shuru tayi tana dauke kanta, Ya kalli agogo hannunsa ya mayar da hankalinsa kanta da fadin”Zanje kasuwa tunda na fahimci kamar bakya bukatata a gidan….Ba tare da damuwa ba tace”To Allah ya kiyaye hanya.” Ya amsa tare da kama hanyar fita, bayansa tabi da kallo tana jin tausayinsa da haushinsa duk wani abun da Zainab takeyi a ganinta duk shine yake bata dama ita kuwa duk tausayinsa da take ba zata yarda ya dinga daukar kwananta yana kaiwa wata ba, da dai da gaske ne yarinyar bata da lafiya sai ta iya hakura amma ko shakka ba tayi Zainab ta shirya mata ma’karkashiya ne……

Abbah cikin rashin walwala ya isa kasuwa gabad’aya rashin walwalar Najaatu ta sanyayyar masa da jiki ya dinga jin shigar zazzabi zazzabi a jikinsa, sai da ya kira wayarta sau biyar kafin a tashi daga kasuwar……..Abbah Abbas gudun tsegumi da surutai irin na Yaya Ramlatu yasa bai shedawa mahaifiyarsa abinda zainab da yan uwanta sukayi ba, lokacin dai da ya isa gidan Hajian ke sheda masa cewar basu dade da dawowa daga gidan nasa ba sunje sun duba yarinyar sun sameta taji sauki sosai…………..Godiya yayi dan jin cewa sunje duba yarinyar sannan yayi mata sallama ya nufi can babban gidan nasa.

Gurin Zainab ya fara shiga domin ya tabbar da cewa ta dauki maganarsa da muhimanci ko kuwa, a zaune ya sameta a falo da yarinyar a hannunta, yaci kunu sosai kamar bai ta’ba dariya ba, koda ta gaisheshi kin amsawa yayi ya kar’bi yarinyar ya dubata sosai kafin yace.”Ina fata dai kin bata magani.” Da sauri tace”Eh na bata. anjima zan kara bata na dare.” Shuru yay na minti biyu kafin ya miqa mata yarinyar ya kama hanyar fita ba tare da ya sake yi mata magana ba.

A sanayaye ta kira sunansa ya juyo tare da fadin”Menene kuma.”? Dan darajar Allah kayi hakuri ka yafe min wallahi bazan ‘kara ba nima na gane nayi wauta da ganganci kishi ya rufe min ido ina nema na kashe ‘yata.” Tsaki yaja mai kar’fin gaske yasa kai ya fice daga falon…..ta rushe da kuka tare da rungume ‘yarta hakika wannan fuskar gizagon da yake mata na masifar bata tsoro gashi kullum sonsa da kaunarsa kara karuwa yake a zuciyarta..

Ya jima a gurin Halisa suna hira da ita da yaransa sosai ya samu nutsuwa ganin yaransa na cikin walwala da farin ciki yasa shima yaji duk k’uncin da yake ciki ya dauke ya zauna yana ta saurarar shirmen su yana tambayarsu yanayin karatunsu, gefe guda kuma yana fargabar tunkarar Najaatu dan tsoron shiga gidanta yake saboda ya fahimci acikin fushi take……Halisa ta fito daga daki ta sameshi beda niyyar tafiya tace”Abbahn mufida baka duba lokaci ne tara saura fa.” Yay saurin kallon agogon hannusa yace”Kinga wa’inda suka tsayar dani nan kin san fa ni sune sanyin idanuna na gane a gurinsu kawai zan iya samun nutsuwa da farin ciki.

Wannan maganar yasa ta gane cewar akwai abinda ke faruwa tsakaninsa da Najaatu lallai babu shakka Zainab ta samu galaba a kansu, shuru tayi masa domin itakam bata da abin cewa a cikin al’amarin, guri ta samu ta zauna tana kallonsa, sai da ya gaji da kansa ya miqe tare da daukan wayoyinsa dake kan center teble ya kalleta da fadin” Zan tafi.” Tace”A gaishe da Najaatu.” Mussadiq ya rike hannunsa da fadin”Abbah muje tare.” Yace.” Akwai skull ka bari sai ranar da babu makaranta zan daukeka na kaika.” Su saddiqa suka ce Abbah harda mu ko.” Murmushi yay yace”To Allah ya kaimu asabar din.” Sai suka shiga Murna dan jin cewar zasu je suga Najaatun su, ya kama hanya da niyyar tafiya suka dinga bashi sakon gaisuwarsu zuwa gareta…………

Najaatu tsaf ta gyara gidanta tayi abinci har kala uku sannan ta shirya jikinta cikin atampa ‘yar ingila mai ruwan ganye atampar tayi mata kyau kuma d’inkin ya dace da jikinta fetted gwon ne da zif a gaba taji dadin zif din domin dama tana tunanin yanda zata shayar da danta nono, tattare jelolin kitson kanta tayi ta daure da ribbon ta daura dan kwalin atamfar akanta (ture kaga tsiya) tayi d’aurin dankwalin yay mata masifar kyau sosai ta fito falo ta zauna, zuciyarta sai sa’ke-sa’ke! takeyi ganin tara har ta gota yasa ta zauna taci abincinta ta k’oshi sannan koma falon ta kunna tashar tv Sky movies ta kama suna wani film mai suna Aganipath tsohon film ne na amita ta zauna tana kallonta tana lura da yaronta dake gefanta a kwance yana wasa.

 Lokacin daya shigo gidan kallon da take ya dauke mata hankali motsin sa taji amma ba taji sanda ya shigo ba, a nutse ta dago kanta ta kalli bakin kofar falon, lokacin ya juya domin rufe kofar koda ya juyo hada ido sukayi yaji gabadaya kuzarinsa ya k’are bata ta’ba kwalliyar data burgeshi irin ta yau ba daurin dankwalinta da yanayin fuskarta daya gani shi ya fahimta dashi cewar akwai tsiya kenan dan fuskarta har yanzu babu sasauci. Barka da zuwa tayi masa ya amsa yana kallonta tare da kallon tv dan ganin wane film take kallo daya dauke mata hankali. 

Kusan minti biyu yana tsaye a gurun kafin ya nufi bedroom jikinsa duk a mace ya tsani ya ganta cikin rashin walwala, ya zauna yay tunani da nazari ya gane akan duk abinda takewa fushi! wannan dalilin yasa ya d’aura d’amarar faranta mata rai , tabbas a tsakanin jiya da shekaran jiya Zainab ta shiga hakkinsu dan sai suna daf da biyan bukatarsu take katse musu hanzari yau kuwa duk zai fanshe bashin da ya tara……..Har ya kimtsa jikinsa ya fito falon tana zaune a inda take dan ko tunanin binsa dakin ba tayi ba, itama yau akwai abinda ta k’udurta a zuciyarta.

Zama yay kusa da ita yana nani’karta! ta dan gyara zamanta gabanta na fad’uwa, hannunsa yasa ya zagaye ‘kugunta ya d’ora kansa a kafadarta a hankali yace.”Amarya me zan samu ne.”? Cikin basarwa ta zame kafadarta tace”Akwai abinci nayi maka har kala uku sai wanda kake so…..Ya juyo da fuskarta suna fuskantar juna, yanayin kallon da yake mata yasa tsigar jikinta mikewa, kauda kanta tayi tana dan gyara zamanta, hannunsa yasa ya tuge daurin dankwalinta ya ajiye gefe da fad’in “Tunda na shigo naga wannan daurin dankwalin nasan akwai sauran rigima ashe baki huce ba nifa dana kwana da Zainab ba wani abune ya shiga tsakanina da ita ba.”

Cike da mamaki take kallonsa tace” Nima ai bance kayi wani abu da ita ba dama ai nasan zaka kula da baby Ummi ne yau ma kuma nace kaje ka kwana dasu wallahi ban damu ba.”

yana hargitsa mata jiki yace.” Baby Ummi ta samu sauki yau babu inda zanje insha Allah muna tare har gari ya waye.” Humm! kawai tace ta dauki dankwalinta zata daura, kar’bewa yay yace kiyi zamanki a haka inason wannan kitson yayi kyau.” Murmushi tayi ta dauke kanta,

Gefan kumatunta ya sumbata yace.”Muje ki bani abincinki mai sadi da gamsarwa! Ba tayi musu ba ta miqe shima ya miqe da sauri ya rike hannunta suka nufi gurin cin abincin……….Tsaf ta hada masa abincin ta tura a gabansa yana lumshe mata ido yace tare zamu ci ko” Girgiza kanta tayi tace”Ni Tuntuni naci abinci.” Girgiza kansa yayi ya gyara plate din abincin tare da bisimillah ya fara ci a nutse, tana kallonsa ta gefan ido sai kallonta yake kamar me? koda wasa taki kallonsa ballantana ta sakar masa fuska, sai da ya kammala tukkuna suka nufi falo, nan ma ya dinga janta da hira wai dole sai ta bashi labarin film din da take kallo, ba ta’ki ba tiryan tiryan ta shiga bashi labarin film din yana kallonta sha’awarta na kara tsananta a tare dashi…..Da kyar ya bari goma da rabi tayi musu a falo yace ta tashi suje su kwanta, ta dauki d’anta ta bi bayansa, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button