MADADI 1-END

MADADI Page 101 to 110

Kasa tayi da kanta kunyar matar takeji sosai sam bata gajiyawa dayi mata hidima ga wahalar d’anta da take kullum daddy na goye a bayanta a mafarki ba ta ta’ba tsammanin Yaya Ramltu zata bautata mata ba.

Baba Talatu ta fito daga daki tare da fad’in ” Ke abinda kikayi a ganinki shine daidai? me yasa tunda bakiji kunyar su ba sai yau bana son munafurci ki gama bashi nono ki tashi ki tafi.

Kuka tasa tace”Allah ba zan iya komawa gidan ba Baba ki kyaleni kawai na zauna anan tunda nace miki kunya nakeji da gaske nake wallahi.” Baba talatu shuru tayi tana kallonta, tace”Ai shikkenan tunda a ganin ki haka shine ya dace.” Redion ta ta kunna ta shiga sauraran shirin ko wane gauta a tashar freedoom redio….. Allah sarki Ya Ramlatu duk wani abu data san Najaatu da danta zasu bukata sai da ta kawo mata Baba Talatu ta dinga yi mata godiya Najaatu kam nauyi da kunya yasa ta kasa cewa komai ita kanta mamaki takeyi wai yau itace ke jin nauyin hada ido da Ramlatu da Hajia babu shakka abun babbane

Karfe goma da rabi tayi shirin kwanciya ta shirya yaronta tare da kwantar dashi gefan katifa, kwanciya tayi tana duba wayarta…..A lokacin ne taga kiran Mmn Sajida har guda bakwai da yake saboda hayaniya tasa wayar a silent “Allah sarki Mmn Sajidata.” Miqewa tayi zaune tana duba gogo, gaskiya dare yayi data kirata ta bata hakuri tasan sun kira wayar ne suyi mata Allah ya sanya alkairi tunda suna da labarin duk abinda ke faruwa ta fada musu komai babu abunda ta rufe musu, tabbas data san zasu kira da bata rufe wayar ba, amma insha Allah gobe itace zata tashe su a bacci da wuri zata kirasu ta basu hakuri……….WhatsApp ta shiga ta danyi dube dube kafin ta fita number angon nata ta nema tana so ta kirasa tayi masa bangajiya……Tana fara ringing aka d’auka…Muryar Zainab ce ta daki dodon kunanta   

Gabanta ya fadi ta miqe zaune tana kara rike wayar a hannunta……Zainab cikin dusasheshiyar murya tace”To me kika bugo kice masa ai kya bari a kai masa ke tukkuna yanzu dai lokacin mu ne dan haka sai anjima.” Sai kawai ta kashe wayar, ta barta da tata a maqale a kunne.

Mutuwar zaune tayi ta kasa motsi sai tunanin hukuncin da zata dauka kan Zainab take, tabbas fa idan tayi sake yarinyar nan zata samu galaba a kanta idan da ta daga mata waya to a lokacin babu aure a tsakaninta da mijinta a yanzu bata isa ta daga mata waya ta fada mata maganar banza ta kyaleta ba……….

“Wai Zainab me Najaatu tayi miki ne kika damu kanki a kanta? Saboda na dawo da ita shine kike ta kuka kina da jego amma ki yini babu abinci a cikin ki shin kashe kanki kike so kiyi kome.”? 

Tana kuka tace.” Wallahi dole na damu sabida tun ba yau ba nasan irin son da kake mata, gabad’aya labarin abunda ya faru tsakaninka da ita babu wanda ban sani ba, amma tunda nake da kai baka ta’ba cewa yau ga laifinta ba duk da ta kasance mai laifi a gurinka amma kullum cikin kyautata mata kakeyi ko makaho ne ya shafa yaji zai san irin kaunar da kake mata, ni kam wallahi daka dawo da ita gwanda ka sake sabon aure sabida nasan da kyar idan zata bar mu zauna a gida……..Katse ta yayi a fusace! yace.”Ke bana son hauka da rashin hankali shin Najaatu ce ke aurana ko kuma nine ke auranta da har zaki dinga tunanin shigowarta rayuwata zai sa na rabu dake? wai me yasa bakya aiki da Iliminki ne! nasan gabadayan’ku keda “yan uwanki kuna da sani akan abu amma kuke takewa ba, kinyi saukar al’kur’ani har sau biyu kin san hadisan annabi da sauran littafan musulunci to me yasa kike adawa da abinda Allah ya hallata ? mahaifinki mata hud’u gareshi kuma idan ban manta ba kwanaki na fad’a miki cewar ba zan zauna daku ku biyu ba, shin me Najaatu ta isa tayi miki da har kike tunanin idan ta shigo k’arshen ki yazo. wannan rashin hankali ne, Najaatu a karkashina take kamar yanda kuke a karkashina duk so da kaunar da nake mata bata isa ta ta’ba martabarku na kyaleta ba saboda haka kada ki sakeyin wannan maganar.” Zainab ta dinga share hawaye tana jin wani katon abu ya tokare mata a kirji, itafa Najaatun ce kawai bata so amma da zai auri mata biyu a rana ba zai dameta ba……..Kira ne ya shigo wayarsa dake kusa da ita, Yasa hannu ya dauka yana dubawa… Sunan my dota ya gani yana yawo kan screen din wayar,

Ya sasaauta muryarsa sosai ya d’aga tare dasa wayar a kunnasa, a kasalance ta amsa masa, tace”Abbah barka da dare! dama na kira wayarka ne nayi maka ban gajiya.” Murmushi yayi yana jin yanda tsigar jikinsa take tashi, hanyar fita ya kama da wayar a maqale a kunnansa yace.”Nagode my wife Amma ni yanzu ba Abbah bane Darling ne sannan kuma naji dad’in wannan bangajiyar da kikayi min ina fatan kinyi min tanadi mai kyau dan ni na riga na gama kimtsawa ke kawai nake jira” Yana kokarin fita daga dakin yake magana…………..Zainab ta bishi da wani irin kallo bakinta a sake hawaye na sharara a kumatun ta

*Allah sarki har ta bani tausayi????*

*Malam Bahaushe dai yace Amarya ko tabuzuzu ce dole ayi Zumud’in ta???? To ballantana wannan dalleliyar amaryar daya san zai gwangwanje ai sai abinda hali yayi……Zainab sai a tanadi maganin hawan jini????*

*Littafin na kudi ne…..!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake…..Vip group #600…Normal group #300 account… 0542382124…Binta umar gtbabk…Idan katin waya zaki tura sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

81********Najaatu cikin jin kunya da jin nauyin maganar da yayi tace.”Humm! Abbah kenan wallahi har kasa naji kunya.” Murmushi yayi ya samu kan kujera ya zauna yace” Ai gaskiya na fada miki nasan da cewar amare na shirya jikinsu domin tar’ba ango shine dalilin daya sa nayi wannan maganar. amma nasan ke koda ba kiyi wani kintsi ba zaki gamsar dani irin yanda nake bukata ko ba haka bane.”

Najaatu ta dinga jin kunyar maganarsa tana ‘yar dariya da fad’in “Abbah kenan.” Yace.”Na fada miki ni ba Abbah bane a yanzu inaso ki tanadi suna na mussaman da zaki dinga kirana dashi amma bana son wannan Abbahn.”

Shuru tayi tana sauke wane irin numfashi, tsabar feelings ne yay mata yawa yasa ta janyo fillo ta rungume wannan d’an kalaman da yake mata yasa gabadaya sha’awarta ta tashi ta wani takure jikinta guri guda.

Jin shuru yasa yace.”Najaatu kina jina kuwa kodai kinyi bacci ne.”! A sarqe tace”Ina jinka Abbah baccin ne dai ya soma daukana.” Yace.”Okey to ki kwanta kiyi bacci amma kafin nan ki tabbatar kinyi addua kin shafe jikinki.”

Tace”To insha Allah Ab….kasa karasawa tayi saboda maganarsu ta d’azu, mirmushi yayi yace.”Zan kashe waya yanzu amma inaso kafin gobe kiyi tunanin suna na mussaman daya dace dani.” Yana gama maganar sai ya kashe wayarshi….Najaatu ta jima da wayar a hannunta sai sakin murmushi take tana juyi a kan katifa shin wane suna ya dace ta dinga kiransa dashi, gaskiya itama za taji nauyin kiransa da Abbah tunda a yanzu tasan babu wannan alaqar a tsakaninsu bayan haka kuma tana so ta siye zuciyarsa da kalolin soyayyarta dole ne ma tayi tunanin suna na mussaman da zata dinga kiransa dashi.

A hankali ta miqe ta fita tsakar gida, ruwa ta zuba a buta ta shiga bandaki, ikon Allah wai wannan ‘yar wayar da sukayi tasa zubar da ruwa, koda yake ai ta banki zuma da tsumi dole sha’awarta ta tashi to koda ma babu zuma da tsumi Najaatu nada karfin sha’awa, wanke jikinta tayi ta mayar da pant dinta ta fito a hankali ta ajiye butar ta shiga daki da sauri ta turo kofa bata so Baba talatu taji motsinta 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button