MADADI Page 101 to 110

Bayan ta idar da sallar asubahi ta jima kan dadduma hannu a sama tana rokon Allah ya dawwamar mata da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zamantakewar auranta ta roki Allah sosai akan ya bata zaman lafiya da mijinta da abokanan zamanta, iyayenta da sukayi silar samuwar farin cikinta suma tayi musu addau kan Allah yasa su cika da kyau da imani, Hajia da Alhaji suma bata manta dasu ba ta jima tana musu addua sannan ta rufe da fatiha ta shafa a fuskarta
Gefan katifa ta zauna tare da cire hijabin jikinta ta duba Daddy bacci yake bai tashi ba, kwanciya tay ta dauki wayarta ta kunna….Numbersa ta nema ta rubuta masa sakon gaisuwa kamar haka.
_Annur???? Barka da safiya ina fatan ka tashi lafiya ya kwanan iyali.”?_
Tura text din tayi tasan mutukar ya kunna wayarsa zai gani, Annur (Haske) shine sunan da take ganin ya dace ta dinga kiransa, domin yanzu shi kad’ai ne kesa zuciyarta tayi a haske, bayan soyayyar manzon Allah to babu wanda take so kamarsa bayansa iyayenta da suka biyo baya.(Soyayya ruwan zuma☺️) Abbah na bude wayarsa da text din yaci karo yana karantawa yana murmushi had’e da shafa gemunsa, iyeee! ashe shi dan gata ne an sa masar masa da suna mai dadi da ma’ana! (Haske) sunan ya kyatar dashi sosai, kawai ya dingi karanta text din yana murmushi sai kace wani shashasha! Halisa dake kwance a bayansa ta motsa, da sauri ya kashe wayar ya juya yana kallonta tamkar wani mara gaskiya, Halisa kuwa gyara kwanciyarta tayi ta cigaba da baccinta dan bayan ta idar da sallar asubah komawa tayi ta kwanta abunta.
To shima rufe wayar yay ya kwanta rigingine tare da tsirawa rufin dakin ido lumshe idonsa yayi da kyakyawan murmushi kwance a fuskarsa ya shiga tunanin yanda zata kasance a tsakaninsa da yarinyar idan sun had’u a daki daya.
*Naburago*
Ya fantsama harkar cah-cah! inda ‘yan kudin da suka rage a accont dinsa ya dinga zuwa yana sasu a caca wani lokacin yayi sa’a wani lokacin kuma a ‘kwamushe shi, mahaifiyarsa ta sake zama dashi tana masa fada akan ya daina wannan harkar domin kuwa bata da riba tunda dai yace ba zai mayarwa da mai kudi kudinsa ba to abinda yay saura a hannunsa yaje ya kama shagon haya ko chajin waya ya dinga yi, Naburago ya shafawa idonsa toka yace shifa yana kallon sana’a mai romo irin wacce take kawo kudi da wuri ba zai je ya wahalar da kansa gurin tada gen da zura chaza a jikin waya ba, dan haka idan ma zata daina wahalar da kanta ta daina ba zai bar sanar caca ba.
A ranar Salimat ta fusata ta farfada masa magana tare dayi masa gori akan kudin ita tayi silar samuwar kudin amma ko kwabo ya hanata sai biyan bukatarsa yake dasu….Naburago ya fusata sosai ya zare blet ya dinga laftar ta sai da yayi mata jini da majina ya farfasa mata jikinta sannan ya kyaleta, ko ajikinsa ya fita ya bar gidan.
Bank yaje ya ciro gabadaya kudin da sukayi saura a ciki…..Yau zasu buga da wani guy yana adduar Allah ya bashi nasara a kansa ya k’wamushe shi, parking din babur dinsa yay ya shiga gurin, kai tsaye yaje ya samu gurin zamansa, guy shima yazo ya zauna al’kalai suka kewaye su…..Basu ja dogon lokaci ba suka fara bugawa……Da farko guy nan sakarwa Naburago yayi yana ta kwamushe shi, sai da akazo karshe tukkuna yay masa kwaf daya duk uban kudin da Naburago ya zuba guy ya k’wamushe Naburago ya fusata kawai sai ya zaro key din babur dinsa yasa aka cigaba da bugawa, ai ba’a wani ja dogon lokaci ba guy nan yayi winning d’insa……Naburago yayi tsuru tsuru zufa sai yanko masa take, ya akayi yau rana ta ‘baci dashi an K’wamushe dik abinda yake dashi, shikkenan ya tashi a tutar babu, yana kallon guy nan na dariya da farin ciki yana had’a kan kudinsa abokansa na taya shi.
Hannu ya kai zai wafci kudin d’aya daga cikin abokanan guy ya zaro bindiga kai kace ta gaske ce amma copy ce suna yawo da itane saboda barazana! Naburago a gigice ya miqe tsaye yana daga hannunsa.
Daya daga cikin al’kalan gurin ya buga masa tsawa tare da nuna masa hanyar fita. Naburago simi simi ya kama hanyar fita gumi duk ya jika masa rigarsa.
‘Bangaran Salim kuwa sai dai munce alhmdullhi dan a tsakanin kwanaki bakwai da yay a kwance a asibiti jikinsa yayi kyau sosai Sakina matar Babansa ce take jinyarsa ita kuma Yaya Ramlatu na zuwa kullum tana dubashi yanzu tsakaninta da Sakina mutunci ne da ganin girman juna saboda ta gane cewar ko wane mutum yana da rana gashi dai duk irin cin zarafin da takewa Sakina bai sa ta guji Jininta ba, babu abinda zata ce akan wannan abinda tayi mata sai dai kawai ta roki Allah ya saka mata da alkairi.
Najaatu tayi mamakin yanda ya kashe kudi guri k’awata mata gidanta kayan kyale kyale iri iri kamar ma abin yaso yay yawa, duk wanda ya shiga gidan Najaatu ba zai so ya fito ba gidane madaidaici amma yanayin tsarin ginin da akayi wa gidan tun daga waje zaka gane cewar an kashe kudi gurin ginashi……..Babban abinda ya kara bata mamaki shine ganin jerin akwatina mai shida a bedroom dinta, wai kayan lefenta ne…kawai sai jin saukar hawaye tayi a fuskarta ita kuwa ina zata kai wannan farin cikin…..Aunty Maryam ta rarrasheta ta kuma sheda mata cewar mijinta ne ya basu kudi ita da Halisa sukaje sukaje sukayi mata siyayyar kayan lefenta…Tace”Aunty Maryam dole nayi kuka wallahi na rasa wane irin kauna Abbah keyi min kiga yanda ya ‘kawata min gida ni kadai sannan sai kace wata budurwa yayi min lefe har akwati shida abin yana bani mamaki.”
Aunty maryam tayi murmushi tace”Sai ma kin bude kinga abubuwan dake ciki dan gaskiya duk babu na banza kudi masu yawa ya bayar aka shirya miki kayanki….ni banga komai ba dan yay miki ai aure duka aure ne da bazawara da budurwa mutukar mutum nada iko babu laifi dan ya auri bazawara yayi mata lefe irin na budurwa karshe dai shi za tayi kwalliya da kayan.
Tace”Hakane maganar ki aunty maryam kema sannunki da kokari nagode sosai da abubuwan da kikeyi min.”
Aunty Maryam tace.”Haba ai babu komai an riga an zama zama d’aya.
Najaatu bayan tafiyar aunty Maryam ta jima zaune a gefan gado tana sa’kawa da kwancewa tunanin yanda zata tar’bi angon nata take, tana mutukar sha’awar kasancewa dashi sai dai kuma tana jin tsoron abinda zaije ya dawo……Wanka tayi ta shafe jikinta da humra mai k’amshin gaske, kayan bacci tasa farare masu taushi da hularsu sai ta d’auki katon hijabi tasa ta nemi gefan gado ta zauna. da wayarta a hannunta tana duba lokaci goma da rabi har ta gota bai shigo ba.
Abbah Abbas lafiya lau yay sallama da Halisa tayi masa fatan alkairi ita kuwa Zainab ai taqi sauraransa sai zum’bure zumbu’re take tana share hawaye, shi kuma ganin yanda ta shiga damuwa yasa ya zauna yana tausarta wallahi shi bai ga abin damuwa da daga hankali ba, shi suke aure kuma ko wacce yana kokarin sauke hakkinta dake kansa to me zai sanya ta damu kanta, abinci ma da kyar take ci yanzu yarinyar ta ba sosai take samun ruwan nono ba.
Yace.”To naji duk abinda kikace na kuma amince da maganarki duk domin a samu daidaito da zaman lafiya idan na gama kwana ukuna da amarya za’a cigaba da yanda aka saba, ma’ana ke kwana biyu Halisa ma haka Najaatu ma haka ina fatan dai shikkenan.”?