MADADI Page 101 to 110

Dr yace”Akwai madara mai kyau da zan sa yanzu a kawo bayan nan kuma akwai magani guda biyu da za’a siya mata insha Allahu jikinta zai ginu koda bata samun nono a kai akai madarar zata gamsar da ita.
Abbah yace.”Okey to ina sauraranka ka sai ka had’a mata komai wanda ya dace nagode.” Dr waya ya dauka domin kira……………..
Zainab sai da ta kusa fashewa da kuka a sakamakon irin fad’an da yake zazzaga mata a mota murya na rawa take bashi hakuri da kawo masa misalai…..Yace.”Kiyi min shuru kawai ba zan dauki kowane misalin da zaki kawo min ba, kishi ya rufe miki ido kina nema ki cutar da kanki kuma ki kashe min yarinya babu yunwa balle ishirwa a gidana ki ‘ki cin abinci sabida mugunta yarinya ta nemi abincinta ki hanata to bazan lamunci wannan ba, Mutukar kina so mu zauna lafiya dake to ki dinga ci kina koshi Ummina na samun ruwan nono idan kika sake ciwon yunwa ya kamata to sai nayi sharia dake tunda ban gaza yin komai a gidana ba.”
Zainab hawaye take cikin kissa take bashi hakuri da fadin “Insha Allahu ta daina zama da yunwa zata dinga ci tana koshi.” Shareta yay ya cigaba da dravig ransa a bace .
Suna isa gidan kira ya shigo wayarsa koda ya duba sai yaga Abdulhamid ne ya daga wayar da sauri Abdulhamid ya gaisheshi ya amsa tare da fad’in “Ina fatan lafiya ko.”? Abdulhamid yace.” Lafiya lau Yallabai wasu mutane ne ke jiranka tun misalin takwas da rabi sun kira wayarka sau uku baka amsa ba..” Yace.”Okey ban gani ba wallahi yau banajin zan zauna a kasuwa komeye kayi magana dasu idan na shigo gobe sai ka sanar dani.” Abdulhamid ya tausa murya yace.”Nima nace musu hakan yallabai sai suka nuna cewar su lallai kai suke bukatar gani…..Agogon hannunsa ya duba tara da rabi yace.”Okey ganinan shigowa yanzu.” Kashe wayar yayi ya kalli Zainab dake rungume da ‘yarta yace.”Ki shiga ciki saura kuma mugunta tasa ki hanata magani a lokacin na dai fad’a miki idan ciwon yunwa ya kama yarinyar nan sai na baki mamaki wallahi tunda duk abinda kike kina sane.” Zainab a sanyaye ta bude kofar motar ta fita hannunta rike da ledojin magani da madara…Juya kan motar yayi da sauri ya bar gurin….Zainab ta’be bakinta tayi ta tura ‘karamar kofar gidan ta shiga bukatar ta biya ta ruguza ranar amarcin Najaatu sai dai kuma idan ta tuno kalmar d’auri sai gabanta ya fad’i tsoro take kada tsautsayi yasa ciwon yunwa ya kama yarinyar ya d’aure ta dan ta lura babu abinda ba zai iya ba akan ‘Ya’yansa…….
*Littafin na kudi ne……!*
Koda zaki ganshi a gruops na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake Vip…..#600 normal…#300 account… 0542382124…Binta umar gtbank…Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*****83 Najaatu kuwa bayan tayi wanka ta shirya jikinta sai tayi tunanin shiga kicin domun ta shirya musu breakfast ta gama komai a nutse ta shirya daining din tayi dan gyare gyaren ta a daki da falo tasa turaran wuta mai kamshi sai ta fito falo ta zauna tana duba wayar ta, gabadaya a dame take dan abin yayi mutukar ba’kanta mata rai wanda harda shi din ma ta ‘kullaceshi a zuciyarta sai daga baya data zauna tayi tunani ta gane baida laifi a yanda Zainab ta kirashi tana kuka da salati kowaye dole hankalinsa ya tashi yaji cewar ‘yarsa babu lafiya harda suma to dole mutum ya shiga yanayi na tashin hankali mussaman shi da yake da jarabar son ‘ya’yan tsiya.
Tana zaune ta falo tana tunane tunane da duba agogo a qallah da fitarsa yanzu zai kai awa hudu ko fiye da haka, tana ganin idan ba wata gagarimar matsala bace yaci ace sun gama da asibiti ya dawo gida, zuciyarta ta shiga sa’ke-sa’ke “Watakila ma tuntuni sun dawo daga asibitin Zainab din ta hanashi dawowa, taji gabanta ya fadi jin irin abinda zuciyarta ke sa’ka mata.
Number shi ta nema ta fara kira….Wayar ta gaji da ringing ta katse ba’a daga ba, a take idanunta suka ciko da ruwa, babu Shakka Zainab ta zame mata kadangaran bakin tulu zuciya ta ciyo ta ta dinga ji kamar ta dauki mayafi taje gidan Zainab din suyi wacce zasuyi wannan ai rashin adalaci ne.
Hanci ta sha’ka cikin tsantsar bakin ciki da takaici ta goge hawayen da ya zubo a fuskarta ta sake kiran wayar a karo na biyu……..Abbah na tare da ‘bakin sa dalili kenan da yasa bai samu damar daga wayar ta ba koda ya duba yaga itace sai kawai ya katse wayar ya mayar da ita aljihu ya cigaba da abinda yake……..Hakan yayi masifar d’aga mata hankali miqewa tayi tsaye ta shiga zurga zurga a falon zuciyarta sai sak’a mata mugun abu take tana cewa kawai taje taci uwar Zainab din shi kuma idan ya dawo ta nuna masa rashin adalacinsa a fili…..Zama tayi kan kujera ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana kiran sunan Allah, hakika kishi bala’i ne masifa ne dan yanda take jin wani irin zafi a zuciyarta tana ganin zata iya aikata komai ganin yanda zuciyarta keta tunzurata yasa ta mayar da hankali gurin kiran sunan Allah tare da adduar Allah ya sassauta mata abinda takeji a cikin zuciyarta..
Haka ta gaji da zaman jiransa ta zauna a dainig tayi break dinta cikin kunci da bacin rai ta shiga daki ta kwanta kusa da d’anta tana hawaye, a haka bacci mai nauyi ya dauketa.
Najaatu sai kusan la’asar ta tashi dan sallar azuhur ma ba tayi ba, sai da tayi wanka tukkuna ta tsaya kan dadduma ta gabatar da sallolinta, tana miqewa idanunta ta d’ora kan agogon dake kafe a dakin, hud’u da Rabi har ta gota.
Zama tayi gaban dressing mirror tayi kwalliya daidai misali turaruka tasa a jikinta masu kamshi da sanyi ta dauko wata bodywork white tasa a jikinta sai tayi amfani da wando roba jins blue wandon ya matseta ya fito mata da sharf dinta, after dressing ta d’ora akai ta ta d’aura dankwalin after din a kanta, falo ta fita ta zauna zuru tana kallon kofa tare da duba wayarta allai Abbah babu kiran waya bare text hummm! Kallo ta kunna ta kama tashar Arewa 24 lokacin suna maimaicin dadin kowa, sai film din ya dauki hankalinta sosai ta dinga dariyar (Adama da Kamaye)???? film din ya d’ebe mata kewa sosai wanda har yasa ta d’an samu sassauci a cikin zuciyarta, wannan karon ba ta sake tunanin kiran wayarsa ba text ta tura masa kamar haka…..
_”Assalam Annuri barka da yamma na kira wayarka domin na tambayi jikin Ummi baka dauka ba to ina fatan Allah yasa lafiya, ka dawo lafiya.”_
Tana tura masa ta miqe ta nufi kicin domin shirya abincin dare, tuwon semo tayi ta shirya miyar agushi da busheshshen kifi sannan tayi miyar nama daidai misali ta gyara kicin din tsaf ta shirya gurin cin abincin ta nufi bedroom domin duba d’anta dake bacci! Daukarsa tayi ta goya a bayanta ina dalili tayi ado da kwalliya shi wanda tayi dominsa yaki ya dawo ya gani, yamma tayi ba zata bar d’anta a kwance ba, dalili kenan daya sa ta goya shi a bayanta ta fito falo ta zauna, sai dai tana zama yaron ya fara motsi yana kuka da alama baya son goyon sauko dashi tayi tana dubashi, hannu yake sawa a baki yana kama rigarta nono yake so…..Haka ta cire after dressing din ta fito da nono tasa masa a baki….Fuskarsa ta tsirawa ido tana kallo yaron kammaninsa da ubansa sai sake fitowa yake, taji zuciyarta na karyewa, idanunta ya cicciko da kwalla kawai sai ta shiga kiran innalilihi wa’ina ilahi raji’iun! Hakika tana fargabar zuwan ranar da Daddy zai san waye ubansa me yayi a kashe shi.