MADADI Page 101 to 110

Karbar yarinyar tayi kamar gaske tasa towel ta goya ta……mikewa yay yasa hannu cikin aljihun jallabiyar jikinsa ya dauko wayarsa, number Dr Mahir ya nema yana addua Allah yasa ya sameshi….Cikin ikon Allah kuwa tana fara ringing ya daga, gaisawa sukayi kafin ya sheda masa abinda keda akwai, Mahir yace kawai su sameshi a asibiti…….Dr Mahir ya jima yana duba yarinyar domin sanin abinda ke damunta, tabbas binkicensa bai nuna masa komai ba sai abinda ya nuna masa a baya sai kuma zazzabi da mura daya fahimci sun d’an kama yarinyar suma kuma ba suyi karfi ba amma maganar daukewar numfashi shi dai duk iya binkicen da yayi a kan yarinyar bai ga abinda zai janyo numfashinta ya dauke ba na farko yarinyar bata da sanyi a jiki…. mura mai zafi ko asma da sai sauran cututtukan dake sanya numfashin mutum ya sar’ke! yarinyar nada lafiya matsalar rashin samun ingantaccen nono ne kawai yake damunta
Wannan bayanin shi yayi Abbah Abbas yana sake jaddada masa cewar yarinyarsa lafiyayyace dan duk binkicensa bai ga abinda ya sar’ke mata numfashi har ta suma ba sai dai yanzu daya fahimci shigar zazzabi da mura a jikinta yace.” Amma kuma hakan na iya faruwa da yarinyar mussaman idan ta nemi nono a lokacin da take bukata bata samu akan lokaci ba hakan na iya janyowa tayi kuka mai tsanani wanda zai sanya har numfashinta ya dauke ”
Abbah ajiyar zuciya ya sauk’e! bayan ya gama jin jawabin Dr mahir din yace.” Dr idan na fahimci maganarka kana so ka tabbatar min da cewar Yarinyar nan babu wani ciwo mai zafi a tare da ita wanda zai janyo mata shiga matsalar da muka zo maka da ita kenan.” Dr mahir yace.”Kwarai kuwa yarinya lafiyarta lau in bayan abubuwan dana fad’a maka a baya suma kuma ina ganin idan an kiyaye to ba za’a sake samun wata matsala ba.” Abbah yay shuru yana nazarin maganar ikon Allah dai ya wuce komai amma kuma ya soma hango k’amshin gaskiya a kan maganar Najaatu ta dazu….Ajiyar zuciya ya sauke ya miqawa Dr din hannu tare da fadin Nagode kwarai dr insha Allah za’a kiyaye da dokokin daka fad’a.” Dr mahir ” Ya miqawa Zainab wata leda da magunguna a ciki yace.” Wad’annan magungunan zasu taimaka insha Allah yanzu ma idan kunje gida sai abata maganin mura da zazzabi ne.”
Zainab tace”To mungode Dr.” Abbah hannu ya sake miqa masa hannu sukayi sallama kafin su fita daga ofis din…..Tun mota yake nazari akan al’amarin tabbas yana ganin zai sanya ido sosai domin ya tabbatar da gaskiyar magana…..maimakon daya sauketa ya wuce gidan Najaatu sai kawai yasa maigadi ya rufe gate din, Zainab na gani haka taji tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha dan farin ciki…..Tare suka nufi dakinta ya zauna gefan bed yana kallonta tana ta wani lallaba yarinyar yace ta zauna ta bata nono tukkuna sai ta bata maganinta, ta zauna kusa dashi ta fito da nono tasawa yarinyar a baki, Allah sarki baby Ummi ta kama nono ta dinga tsotsa kamar ba zata bari ba hakika Zainab na zalintar ‘yarta…..Sai da ta koshi tukkuna ta cire nonon daga bakinta, ya fito da maganin ya na nuna mata yanda zata bata
Kar’ba tayi a nutse ta bata maganin ya kar’beta daga hannunta, addua yay mata ya tofa mata a jiki sannan ya sata a net dinta ya rufeta da bargo……Zainab kuwa kayan bacci tasa tazo ta kwanta kusa dashi tare da fad’in “Abbahn Mufida ba zaka tafi ba dare yayi fa.”
Yace”Zan kwana tare daku domin naga yanayin jikin Ummi.” Farin ciki kamar ya kasheta tace”To ka kwanta ka huta mana.” Yace.”Kada ki damu zan kwanta. Shuru tayi tare da rufe jikinta da bargo,
Wayarsa ya dauko ya duba lokaci d’aya da kwata na dare! Yanzu Najaatu watakila tayi bacci kuma bai zama lallai ta bar wayarta a kunne ba, gwada kiran wayar yay sai ta shiga………Najaatu sai da taci kukanta ta koshi tukkuna taje ta tsarkake jikinta ta dawo ta kwanta da sha’awarta dan gabadaya ta kasa samun nutsuwar da take bukata, so take tayi bacci takaici da bakin ciki ya hanata, sai ta dauki wayarta ta kunna tana dube dube nan taga har d’aya tayi bai dawo ba jikinta yay sanyi zuciyarta tace watakila acan zai kwana kawai kiyi kwanciyarki ki kyaleshi kuma kada ki kira wayarsa……da wannan shawarar take kokarin kashe wayar sai kiransa ya shigo, da kamar kada ta dauka sai dai ta d’aga ciki ciki tayi sallama da fadin”Ya jikin Ummi.”
Abbah ya sauke ajiyar zuciya a nutse yace.”Da sauki yanzu yanzu muka dawo daga asibiti dama na kira ki ne domin na fad’a miki cewar zan kwana tare dasu saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo ba dai fata nake wani abun ya ‘kara faruwa ba”.
Ta daure zuciyarta tace”Eh dama nima abunda nake tunanin kiran ka na fad’a maka kenan babu damuwa ka zauna kawai sai da safe.” Tayi gaggawar kashe wayarta dan ma kada yayi mata wata maganar da zata sanya ta fada masa mai zafi…………shuru yay da waya a hannunsa yana mamakin katse masa hanzari da tayi, wannan maganar data fad’a ba har cikin zuciyarta ta fad’a ba saboda shi ba yaro bane ya fahimci kamar gatse tayi masa to idan ma hakane baya tunanin zai koma gidanta har sai ya tabbatar da zarginsa…..Wayarsa ya kashe ya dan juya bayansa gurin Zainab inda ita kuma tayi saurin rufe idonta kamar me bacci nan kuwa a kunnanta komai ya faru, murna da farin cikinta sai ‘kara nunkuwa suke a cikin zuciyarta.
Kwanciyar rigingine yayi a kusa da ita ya cigaba da nazari da tunanin al’amuran da suke faruwa, da wannan tunanin bacci ya daukeshi………Kiran sallar farko a kunnanshi ya miqe da sauri ya nufi toilet wanka yayi ya fito daure da alwala, bashi da matsalar kayan sawa tunda ko’ina yana dasu, ya sanja jallabiya ya fita zuwa massalaci…….Zainab yana fita ta tashi da sauri ta bude kofa ta nufi dakin dasu aunty Balaraba suke kwana. Cikin murna da farin ciki take sheda musu abunda ya faru. Aunty balaraba murmushin samun nasara tayi tace”Ai na fad’a miki sharrina yafi kala dubu kinga dai lokaci kankani kin rikita musu lissafi jiya ya yini a kasuwa yau kuma ya kwana a gidanki haka zaki dinga kirkirar abubuwa iri iri duk ranar girkina dan ki raba masu hankali.” Zainab tace”Ai naji dadin shawarwarin ki wallahi dama ni babban burina na k’untatawa shegiya.” Aunty balaraba murmushi tayi ta miqe ta nufi toilet domin daura alwala Zainab zama tayi har suka idar da sallar suka cigaba da shirye shiryen makirci da sharrin da zasu shiryawa Najaatu……Abbah bai dawo gidan da wuri ba kasancewa ya tsaya gurin jana’izar wani bawan Allah daya rasu a bayan gidanshi a massalaci a kasanar da mutuwar sai ya tsaya akayi jana’iza dashi sannan ya dawo gidan koda ya shiga gidan kai tsaye gurin Halisa ya nufa, Baba Larai na ayyukanta yara kuma basu dade da tafiya makaranta, tsayawa yay suka gaisa da ita kafin ya nufi bedroom din Halisa……Tana zaune a kan kujerar mudubi tana gyara daurin dankwalinta ya shigo dakin sallamarsa ta amsa ya k’arasa bakin gado ya zauna…….Kallonsa tayi cikin nazari da tunani tace “Abbahn Mufida lafiya kuwa? na ganka a hargitse!
Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad’in ” Jikin Ummi ne ya hargitsani Halisa na rasa abinda ke damun yarinyar nan wallahi daga jiya zuwa yau duk na damu gashi likita yace lafiyarta lau amma kuma Zainab kullum sai ta kirani a waya da daddare tana kuka tana fad’amin cewar yarinyar babu yanda take jiya a rikice na shigo gidan nan sabida ta kira ni tana fad’a min yarinyar numfashinta ya dauke tun farkon dare har sha daya na dare be dawo ba haka nazo na tarar dasu suna shafa mata ruwa a jikinta a daran mukaje mukaga likita ya dubata yake tabbatar min da cewa yarinyar bata da ciwo mai zafi wanda zai sanya numfashinta daukewa na tsawon wannan lokacin.