MADADI Page 111 to 120 (The End)

Halisa ta shiga girgiza kanta tare da fad’in “Al’amarin Zainab sai gyaran Allah ni tun zamanta a gurin na fuskancin sanjawarta tunda lafiya lau muka zo to amma ganin gold din dake wuyanki da wuyana yasa ta sanja fuska nasan abinda ya tayar mata da hankali kenan.”Murmushi Najaatu tayi tace” To ai sai taje tayi ta damuwa ita ciwo zai kama ba wani ba gold kuwa ni dake nake so muyi anko ita tayi nata ita kadai tunda bata da mutunci da kawaici wallahi ba kiji yanda raina ya ‘baci ba data fito fili ta nuna ba zata bani ‘yarta ba.”
Halisa tace”Ai sai kiyi hakuri ki kyale mata ‘yarta kema Allah zai baki.
A harabar gidan suka sameshi zaune akan wata farar kujera, Halisa ta gyara parking Najaatu ta bude mata kofar motar ta fito tana yatsine fuskarta dan zaman draving din nan da tayi ya janyo mata ciwon mara dama dai tanayi sama sama tun a gidan bikin daurewa kawai take…….mikewa yay ya nufi gurun Zainab duk suka rufa masa baya,zama yay kan kujera Zainab tayi wanka ta sanja kwalliya ta zauna kusa dashi tare da d’ora kafa d’aya kan daya a haka suka shiga suka same su…..dukkaninsu sai da wani abu ya ta’ba zuciyarsu amma suka dake suka zazzauna, falon ne ya dauki shuru na minti biyu kafin yayi gyaran mirya ya kallesu d’aya bayan d’aya yace”Halisa kece babba a cikinku inaso ki fad’a min abunda ya faru a gidan bikin Salim.” Halisa tace”Bangane na fada maka abinda ya faru ba okey tazo ta fad’a maka wata magana ne.”? Tsawa ya buga mata yace.”Kada ki mayar dani sakarai mana kin san komai kina nuna baki sani ba kome akayiwa Zainab ai kune kuka bada goyon baya saboda kunga kuna da fada a gidan jamaa sunfi sanin ku shine zaku ware ta ku had’u kuci mutuncinta akan wane dalili.”? Yakare maganar cikin tsawa.
Najaatu a dake! tace”Wallahi Zainab kiji tsoron Allah yanzu me akayi miki da har zaki zo ki fad’a masa duk dan ki had’ashi da ‘yar uwarsa.”! A fusace! Tace”Ke dallah malama kiyi mana shuru duk bake ce kika janyo komai ba da har zakice naji tsoron Allah kune dai zakuji tsoron Allah bani ba.” Halisa tace”Kawai saboda ta nuna kaunarta akan ‘yarki sai ki mayar da abin sharri a gaskiya Zainab ki sanja hali wallahi.”
“Ba zan canza Hali ba sai dai ku su sanja hali ni ba munafuka bace shiyasa ai kuka ware ni saboda ban iya gulma da munafurci ba yanzu meye na ware ni kuka saka gold irin d’aya bayan ni kunsan bani dashi Ai wallahi Najaatu kece babbar munufaka.” Najaatu ta bud’e baki tana kallonta cike da mamaki tace”Ni kike kira munafuka.”
“To idan ba munafuka ba mecece da har zaki siyo muku gold iri daya banda ni.”
Dariya tayi tace”Okey sai yanzu na gane abinda ke damunki ba’kin ciki da hassada kikeyi mana gold kuma na siyo bakya cikin tsarina shiyasa bana so nayi irin d’aya dake banza mara hankali kaw……kafin ta karasa ya buga mata tsawa wai tayi shuru! Ta kalleshi cike da mamaki me yasa lokacin da zainab take magana bece komai sai ita zai katsewa hanzari aikuwa sai ta fusata! ta cigaba da watsawa Zainab ba’ka’ken maganganu wanda yasa itama ta fusata! ta miqe tsaye ta fara mayar da martani! kafin kice kwabo gurin ya hargitse Najaatu da Zainab sai hayaniya suke Halisa dashi uban gayyar na hanasu amma kamar sake tunzura su suke….Halisa ta kalleshi rai a b’ace tace”Yanzu meye amfanin abunda kayi ashe dama taramu kayi domin muyi hayaniya kawai saboda Zainab tazo ta fad’a maka magana sai ka hau kai ka zauna babu binkice wallahi ka gyara zamantak……..Katseta yayi cikin d’aukar chaji yace.”Fita ki bani guri ki koma gurin ki.” Halisa tsaki taja ta dauki jakarta tinkis tinkis ta kama hanyar fita ba zata iya da jarabar nan ba……Shi kuwa tsakaninsu ya shiga yana musu magana su bari dan gabadaya hankalinsa ya tashi da yasan hayaniya zasuyi da bai tarasu a guri d’aya ba.
Najaatu jakarta ta dauko ido jawur ta kama hanyar fita sai dai kafin ta karasa bakin kofar ta yanke jiki ta fad’i! A take ta shiga yin wani irin hakki! tana rike kirjinta, bashi kadai ba har Zainab din sai da hankalinta ya tashi, a gigice ya rirriketa yana kokarin mikar da ita tsaye tana kokarin kwanciya, Zainab tazo ta tsaya gabanta na faduwa! Abbah fita yay da sauri ya fito da mota ya umarci maigadi ya bude gate, Najaatun ya hango ta fito daga gurin Zainab tana kokarin fita….Bayanta yabi da sauri yana kiran sunanta ta bude karamar kofa da sauri ta fita daga gidan, hanya ta fara bi hawaye na zubo mata wannan masifa ina zata iya da ita ace mutum ya kasa fin karfin gidansa…………..Halisa ce ta fito daga gurinta tana kiransa, ya tsaya yana kallonta dik ya zama kamar zautacce mata suna so su haukatar dashi, tana cizar lips dinta tace”Haihuwa zanyi fa ka fito da mota muje asibiti.” Sai ya rasa ina zai nufa gurin Najaatu ko gurin Halisa (Allah sarki ya bani tausayi????) Gurin Halisan ya nufa ya taimaka mata suka fito tare mota ya sata ya kira Zainab a gurguje ta fito ta shiga motar suka nufi asibiti.
Najaatu kuwa na fita ta samu adaidaita sahu gidan Alhaji ta nufa ranta a mutukar ‘bace! amma koda taje bata shedawa kowa abinda ya faru ba kawai ta bar abun a cikin ranta.
Karfe tara da rabi na dare Halisa ta haihu an samu ‘ya mace katuwa tubarkallah babyn na kama da babanta sosai dama duk yawanci ‘ya’yansa kama suke dashI Ummi ce kawai ke kama da mamanta……Dr Sa’adatu itace ta tsaya tsai a kan Halisa har sai da tabbatar komai yay daidai tukkuna hankalinta ya kwanta baby da mamanta sunyi tsaf gwanin sha’awa, karamcin Dr Sa’adatu ya tsaya masa a rai matar na mutukar kaunarsa da iyalinsa yasan duk abinda takeyi yafi karfin irin kudin da yake bata, lokacin guda yaji yana tausayinta a cikin ransa yana son mace mai hankali wacce tasan abinda take tabbas Dr Sa’adatu ta cancanta a sota.
Sha d’aya shaura na dare ya shiga gidan Alhaji shuru gidan lokacin duk sun kwanta, gurin hajia Rabi ya shiga Allah yasa ba tayi bacci ba jin sallama yasa ta fito da sauri, ganinsa a tsaye yasa gabanta ya fad’i Tace.”Allah yasa dai lafiya.” Yace.”Lafiya lau Halisa ce ta sauka ta hafi ‘ya mace yanzu haka tana gida lafiya lau ita da yarinyar.
Hajia Rabi ta fad’ad’a fuskarta da faraa tace”Ikon Allah d’azu fa muna tare da ita babu wata alamar haihuwa a tare da ita koda yake ai ikon Allah ya wuce wasa.’ Yace.”Wallahi kuwa Allah ya kawo mata da sauki.” Tace”Haka ake so ai Allah ya raya.” Ameen ya Allah bari na shiga gurin hajia.” bayansa tabi tana fad’in “Allah yasa ba tayi bacci ba dan tun dazu naji tana kukan kafafunta na ciwo…………..jin muryoyinsu yasa Yaya Ramlatu da Najaatu suka fito daga daki da sauri, Hajia Rabi ta kalli Ramlatu da fad’in ” Kunji halisa ta haihu yanzu yanzu an samu ‘ya mace.” Dukkaninsu farin ciki ya nuna a fuskarsu Yaya Ramlatu ta kalli Dan uwan nata cike da farin ciki tace”Yanzu tana asibiti ko tana gida.”? Hankalinsa nakan Najaatu yace tana gida yanzu haka.” Ramlatu tace”To ai sai mu tafi tare da kai na zauna a gurinta.” Tausayi ta bashi jin abinda tace Ramlatu na tsaye a kansa da iyalinsa mussaman Najaatu da Halisa amma ya rasa me yasa take nuna kiyayyarta akan Zainab, Hajia Rabi na kokarin fita tace”Hajia dai yanzu tayi bacci kada a tasheta da safe sai na sanar dasu haihuwar ita da Alhaji.” Yace.”To Allah ya kaimu.” Najaatu bayan Yaya Ramlatu tabi ba tare data kulashi ba, dan har yanzu haushinsa takeji….Yaya Ramlatu tace”Kema ai sai kizo mu tafi tare ko.”