MADADI 1-END

MADADI Page 111 to 120 (The End)

Najaatu watanta uku da haihuwa yaranta sunyi kwari ta nemi alfarmar akan ya barta taje jos su gurin su Mmm Sajida, hanata yayi yace ba zata je yanzu ba sai yaran sun sake ‘kwari hakura tayi ta kyaleshi ta cigaba da kula da ‘ya’yanta dama tuntuni Daddy ya zama d’an gidan hajia ya jima a can dan har ya manta da cewa itace uwarsa Yaya Ramlatu ya ri’ke a matsayin uwa tunda da ita ya saba.

Lokacin da sukayi wata shida ta sake masa maganar zuwa jos nan ma ya dinga yi mata wasa da hankali ya’ki yayi mata magana d’aya, takaici yasa tasa shi a gaba tana kuka tana fad’a masa cewar bai dace ace ta watsar da mutanan ba koda be barta ta kwana ba to ya bari taje ta dawo a rana daya, da kyar ya barta tare da kafa mata dokoki tace to ta amince, Tare da Yaya Ramlatu suka tafi saboda ta taimaka mata da raino, a waya ta kira Mmn Sajida ta fada mata cewar gata nan akan hanya amma ba kwana za tayi ba, Mmn Sajida da sauri ta shiga gidan Mmn Ladi ta sheda mata a take suke shiga hidimar abinda zasu sauketa dashi……………Najaatu tayi mamakin yanda Mmn Sajida da Mmn Ladi suka karramata sun jere gabanta da kayan abinci nau’i nau’i sai farin cikin ganinta suke suna ta nuna farin cikinsu akan kyautar da Allah yay mata Mmn Sajida ta dauki Hassan ta rike tana ta sa masa albarka itama Mmn Ladi ta dauki Hussain sai addua take masa Najaatu hawaye ta shiga sharewa tana mamakin irin kaunar da mutanan ke mata……….Wannan karon ma manya manyan atampopi ta kawo musu da mayafai masu kyau da tsada kana ta basu kudi masu yawa tace su cigaba da juyawa akan wanda suke, rasa bakin godiya sukayi dukkinsu sai da suka zubar da hawayen farin ciki……Sai da zata tafi Mmn Sajida ke fad’a mata cewar itama ta kusa aure dan har ta kar’bi sadakin wanda zata aura….Najaatu ta dinga farin ciki tana mata fatan alkairi da zaman lafiya da mijinta, Cikin alhini na rashin son rabuwa sukayi sallama da junansu kowanne zuciyarsa babu dadi.

Yaya Ramlatu ta jima tana mamakin mutunci da karamcin su Mmn Sajidan inda ita kuma Najaatun ke fa’da mata irin taimakon da sukayi mata a lokotan baya lokacin da take bukatar taimako. Yaya Ramlatu tace “Eh lallai kuwa mutanan nan ba mutanan da za’a yar bane yana da kyau ki cigaba da zumunci dasu duk nisan inda suke.”  

Ayuba Abbah Abbas ya samu a kasuwa da maganar son mayar da matarsa dakinta, Abbah yayi farin ciki da jin wannan maganar dama zaman ‘yar uwar tasu a haka yana damunsu dan haka ba tare da wata shawara ba yace kawai ya tsayar da ranar daurin aure kada ya damu zai samu mahaifinsa da maganar itama kuma Yar uwar tasa zai fada mata…..Ayuba ya tsayar da ranar daurin aure sati daya mai zuwa, Abbah yace to Allah ya nuna mana ya sanya alkairi…….To koda ya samu iyayensa da maganar sai suka nuna farin cikinsu akan al’amarin sannan sukayi fatan alkairi gami da adduar zaman lafiya……..Bangaran Yaya Ramlatu kuwa ai babu wanda ya kaita jin dadi da farin ciki hakika ta d’and’ana zaman gida taji yanda zawarawa keji duk da babu abinda ta nema ta rasa a gidan ubanta amma ta tabbata dakin mjinta yafi mata daraja da mutunci ba tare da bata lokaci ba ta amince aka daura aure ta tare a dakinta wanda Abbah Abbas ya sauya mata komai na ciki tamkar d’akin ‘yar gatan budurwa Yaya Ramlatu d’an uwanta ya fito da ita sosai yasa mata komai na kyale kyale a dakinta, satin ta biyu da tarewa tazo da kanta ta had’a kayan Daddy tsaf ta daukeshi ta tafi dashi can gidanta, tace ai mai rabata dashi sai mutuwa shima yaron sati biyu da yay babu ita har ciwo sai da ya kwanta.

****

Wannan karon ma Zainab mace ta haifa yarinyar taci sunan Yaya Halimatu marigayiya Najaatu tayi murna da farin ciki ganin yasa sunan yayarta sai ta dauki son duniya ta dorawa yarinyar kome ta gani na yara ta siya mata Zainab tayi ta jin dadi, shima Abbahn sunan da yarinyar taci yasa yake kaunarta kullum adduarsa Allah yasa ta gaji me sunanta Halimatussadiya.

Alhaji Aminu Dan jarida da Matarsa suka shirya tsaf domun zuwa suga abinda d’ansu ya tafi ya bari a duniya, Munira ce ta jagoranci tafiyar……

Tar’ba ta mussaman akayi musu Alhaji yasa aka shirya musu abinci mai kyau aka saukesu dashi sannan yasa Dan Azimi yaje gidan Ramlatu ya dauko musu yaron…..Abbah Abbas na kasuwa ya samu labarin zuwansu abinda yake ya bari yazo ya same su, Alhaji Aminu ya rungume yaron sai zubar da hawaye yake Baba Malam da Alhaji na bashi baki gami da nuna masa yanda yanayin rayuwa yake Ubangiji na iya zartar da hukuncisa akan ko wane bawan sa ba dan baya kaunarsa ba sabida haka ya daina kuka da damuwa insha Allah yaron ba zaiyi maraici ba tunda yana da uba wato mijin mahaifiyarsa wanda ya daukeshi tamkar shi ya haifeshi…….Abbah jin akan maganar da suke yasa shima ya shiga jajjada masa cewar shine a matsayin mahaifin yaron a yanzu dan haka baya so koda ya girma su tayar masa da wata magana wacce zata d’aga hankalinsa abinda ya wuce ya riga ya wuce har abada.

Jin wannan magana yasa Alhaji Aminu yaji ya sassauci a cikin zuciyarsa 

Kwanansu biyu a gidan Alhaji suka shirya tafiya Munira har gida ta samu Najaatu ta sheda mata cewar Muktar ya dawo gurinta sun sasanta junansu har sun tsayar da maganar aure a tsakaninsu…..Najaatu ta nuna farin cikinta a fili tayi kuma adduar fatan alkairi…Wannan karon ma sai da tayi wa Munira kyautar sutturu da kudi dubu ashirin tace kuma idan auran yazo ta fada mata koda a waya ne.” Munira sai da ta zubar da hawayen farin ciki.

*BAYAN SHEKARA GOMA*

A cikin wannan shekarun da suka gabata abubuwa daya sun faru masu dadi da marasa dadi dama haka rayuwa take a cikin shekaru goma da suka wuce Allah ya dauki rayuwar mutumin kwarai nagartaccan mutum wato Alhaji Sama’ila wanda yayi mutuwar shahada watan azimi kuma ranar jumaa ga shedar arziki daya samu daga gurin Jamaar gari………A dai cikin shekarun ne Allah ya daukaka darajar Alhaji Abbas inda ya shiga sahun matane masu kudi a jahar kano idan aka kira *Dangwate*

a farko aka kira *BUA* a na biyu to za’a kira sunansa a na uku Alhaji Abbas Allah ya bashi duniya sosai kuma yana neman lahirar sa a cikinta dan dukiyarsa ta talakawa ce gami da marayu da nakasassu da duk wani mabukaci, gidansa kullum baya rabo da jamaa kullum cikin raba kudi da abinci akeyi, massalatai da makarantu kam shi kansa bai san iya adadin wanda ya gina ba kullum cikin hidimtawa addinin Allah yake……….’Bangaran iyali sai godiyar Allah Uwar gida Halisa nada biyu duk mata Zainab nada shida mata hudu maza biyu….Najaatu nada Bakwai duk maza har yanzu bata haifi mace ba, Dr Sa’adu ce har yanzu bata haihuwa Allah sarki ashe rashin haihuwa ne yasa tsohon mijinta ya rabu da ita shi kuwa Abbah ya ri’keta tsakani da Allah rashin haihuwata besa yaji ya gaji da zama da ita ba saboda yasan Allah ne ke bada haihuwa ba wani mahalu’ki ba………

A yanzu zuriar sa su goma sha bakwai ne kuma yana rokon Allah ya ‘kara masa wasu kafin ya dauki rayuwarsa …….

*To nima ina rokon Allah ya k’ara masa ya kuma had’a masa kansu tare da fatan ya cigaba da zaman lafiya da iyalinsa*

*ALHAMDULILLAHI*

_To Jamaa nan na kawo ‘karshen wannan littafi mai suna MADADI BA HARAM BANE ina rokon Allah ya yafe min kusakuraina Ladan da yake ciki kuma Allah ya sadamu dashi bakid’aya…..Ina mik’a godiya gare ku dubbanin masoyana na nesa dana kusa wanda na sani da wanda ban sani ba, Nagode sosai da kaunar da kuke nuna min Especially masu fitar da kudinsu su siya book d’ina wallahi ina alfahari daku mutuka ina fatan Allah ya cigaba da bani ikon nishad’antar daku gami da faranta muku Nagode sosai ‘yan uwana ‘kawayena iyayena ‘kannena Yayyayena dukkaninku ina muku fatan alkairi Assalamu alaikum_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button