MADADI 1-END

MADADI Page 31 to 40

Saddiqa ta shiga binta da kallo ganin yanda take mata magana a hasale! sai abin ya bata mamaki! cikin sanyin jiki taje ta dauki maganin tasha ta kwanta kan bed dinta……

Sai da ya gama abinda yake a tsanake tukkuna ya rufe loptop din ya mike ya nufi gurin cin abinci…..Komai gashinan a shirye a kammale cikin tsabta ba kamar tsarin Halisa ba da wani abun ma idan tayi yake sashi tashin zuciya……Abinci yaci sosai irin wanda ya jima baici irinsa ba, ya goge bakinsa da tissue kafin ya mike ya nufi bedroom dinsa domin kintsawa.

Halisa bayan sun gama karya kummalo sai ta dauki wayarta tana dubawa gaskiya tayi mamaki sosai da ko text bata bai turo mata ba, jikinta yayi sanyi sosai hankalinta ya sake tashi, ta azalzali Yaya Ramlatu ta shirye suje har gidan ‘Yar shagamun su sameta.

Babu arziki Yaya Ramlatu tayi wanka ta shirya a gurguje suka fito sunayi wa Sakina sallama….Binsu tayi da kallo har suka fita daga gidan bakinta bai daina yi musu adduar shiriya ba.

*’Yar Shagamu* wacce taga jiya taga yau tsuhuwar kilaki ce ta gama yawan karuwancinta ta siyi gida tana tara maza da mata suna she’ke ayarsu a gidan, ita kuma tana gefe ta kasa sigari da goro da shisha duk maiso yazo ya siya….

Halisa da taga irin rayuwar da Yar shagamu takeyi a gidan sai data tsorata, tana zaune a tsakar gida daga ita sai breziyya da dogon siket ga maza ‘yan bana bakwai sun kewaye ta.”

Ramlatu da ‘Yar shagamu ciki a daidaita sahu suka had’u shikkenan sukayi musayar numbar, tunda Yar shagamu ta fahimci cewar Ramlatu yar son duniya ce sai ta makale mata suka kulla abota. sa’i da lokaci Yar shagamu na kawowa Ramlatu ziyara har gidanta itama Ramlatun tana zuwa gidan nata duk da kasancewarsa matattarar ‘yan iska……. Yar shagumu ta nufi dakinta cikin gaggawa ta sako wasu matsatstsun kaya da karamin mayafi ta fito tare da kallon wani dan daudu dake zaune gaban kayan sana’arta tace”Kai sarai zan je unguwa ka kula min da kayana sosai kuma kada ka bawa kowa bashi kaji ko.

Cikin muryar mata yace.”Kada ki damu uwar dakina.

Yar shagamu tace”Ku tashi mu tafi.” Da sauri suka mike kowacce ta zira takalminta suka fita daga gidan.

To kafin su nufi zauran malam din sai da Halisa ta tsaya a banki ta ciri kudi kimanin dubu dari tukkuna…………Wannan dai ba za’a kira shi da malami ba sai dai boka saboda yanayin kayan dake jikinsa da tarkacen kayan tsafin dake gabansa harda ‘kokon kan mutum, ga wasu fatoci na dabbobin daji iri-iri a manne a bangon dakin dake suke ciki…

Yana bud’e bakinsa da niyyar magana wari! ya d’umame! gurin Halisa da Yaya Ramlatu da sauri suka sa hannunsu suka toshe hancinsu….Yar shagamu tayi saurin cire musu hannu tana girgiza musu kai wai kada su rufe…..Boka ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya kawai sai tsotsutsi marasa kyawun gani suka shiga zubowa daga bakinsa….Halisa da Ramlatu suka tsorata mutuka! sai jikinsu ya kama ‘bari! ganin yana daukar tsotsutsin yana sawa a bakinsa yana taunewa!

Halisa tsigar jikinta ta shiga tashi ta dinga dauke kanta saboda masifaffan aman dake kokarin kufce mata…….Cikin tsawa gami da yanayin hausarsa yace”Wacece Halisa a cikinku.”? Ai a furgice Halisa ta juyo inda yake tana kallonsa, Sai ya sake kwashe da wata dariyar yayin da tsotsutsin suka cigaba da zazzagowa daga bakinsa.

Cikin bada bada! yace”Rarrafo kizo gabana ki dinga d’ibar wannan tsotsutsin kina sawa a bakin ki kina taunewa.

Halisa taji cikinta ya karta gudawa na nema ta kufce mata! yau ta kawo kanta mahallaka. Boka ya zabga mata razananniyar tsawa yace.” Nakadu yana kanki a tsaye idan baki bi umarinsa ba zaki tashi da shanyayyar ‘kafa yanzu.

Yar Shagamu tayi maxa tace”Ayi mata afuwa ubana bata saba zuwa irin wannan gurin ba shiyasa.

Boka yace”To anyi mata afuwa. tayi maza tabi umarin da aka bata!

Yar shagamu ta zunguri Halisa da take ta faman zare ido kamar kace kyat ta ruga da gudu……Ai kafin tayi aune taji mari tas! a kuncinta na hagu! kafin ta dawo hayyacinta boka ya soma wata iriyar jijjiga yana zabura hade da dukan tarkacen dake gabansa da jelar karan dake hannunsa….Yar shagamu ta fadi a gurin tana makyarkyata da fadin”Halisa zaki janyo mana masifa da tashin hankali kiyi maza kafin boka ya dawo hayyacinsa kije kiyi abinda aka saki idan ba hakaba to dukkaninmu zamu shiga cikin matsala.” Jin haka yasa Yaya Ramlatu tsurewa da sauri ta shiga tura Halisa gaban bokan bakinta sai rawa yake kana ganinta kasan tana cikin tashin hankali.

Halisa ta gurfana gaban boka ta shiga kwasar tsutsa mai abun kyankyami tana sawa a bakinta tana taunawa cakal-cakal!! Boka ya daina jijjigar da yake ya dawo dai-dai yana wani irin huci!!! wani daddaud’an ruwan gumi na diga daga jikinsa…..Hannusa ya dora saman kan Halisa yana wani sambatu kafin ya cire tare da daka mata tsawa wai ta matsa daga gurin

Cikin mawuyacin hali Halisa ta matsa daga gurin tana jin yanda kanta ke wani irin sarawa.

Boka ya kallesu daya bayan daya kafin yace.”Wannan matar mai kama da bulunboti tana nema ta janyo mana fushin babban aljini! yanzu kwana na ne kawai yake a gaba dan yanda ya ri’ke ni yana shan jinina da ban bashi hakuri ba to ba zai sake ni ba sai ya tabbatar da cewar na zaman mushe! kuma idan ya gama dani kanku zai dawo.”

Sukayi masifar tsorata mussaman Yaya Ramlatu da taji fitsari na diga a wandonta

Wani koko ya dauko ya rike a hannunsa yana duba cikinsa, dariya yasa ya hannu ya dagawa Halisa wai taje ya nuna mata abinda ke cikin kokon.

Da sauri taje tana lekawa ….Abbah Abbas ne da Naja’atu suke magana a yayin da suke daf da juna! Kafin Halisa ta gama nazari taga Abbahn ya rungume Naja’atun a jikinsa yana shafa bayanta.

Boka ya ajiye kokan yana kallonta yace”Abbas da Naja’atu ko.”? Da sauri tace”Kwarai kuwa haka sunan yake…..Kinzo akan a taimaka miki domin a kashe masa mazakuta kada ya samu karsashi da kuzari a yayin da yake tare da yarinyar hakane ko ba haka ba.” Tace”Hakane Boka! Yace.”Bukatar ki ta biya zamu tura Aljana yar Zabira!! ta dinga shafe masa mazakutar a duk lokacin da ya tunkari yarinyar da niyyar auratayya.

Halisa tace”Alhamdullhi Allah nagode maka.” Boka yace”Maza ki gyara maganarki nan gurin ba’a kiran Allah yanzu zaki b’ata aikinki kice Kina godiya ga uban kafuran Aljanu.” Da sauri ta fadi hakan tana zare idonta…

Boka yayi mirmushi mai muni ya kalleta da fadin”Sarkin Kafurai yace a fada miki labari mai dad’i nan da lokaci ‘kan’kani ma yarinyar za’a neme ta a rasa karshe ma Auran ne zai mutu.”

Wani irin sanyi ya sauka a zuciyarta da sauri tace”A mika min godiya gurin Sarkin sarakuna.” Boka yace.”Yana jinki gashinan a saman kanki.” Halisa tayi saurin waiwaya wa bayanta…..Boka ya dinga mahaukaciyar dariya yana dan dukanta da jelar karan dake hannunsa yace”Idan kina so a bude miki ido ki dinga ganinsu kiyi min magana yanzu.” A tsorace ta matsa kusa da Yaya Ramlatu tana girgiza kanta.

Yar shagamu tace”To godiya muke ubana yanzu meye abin sadaka.” Shuru boka yayi yana kallon kusurwa! yakai minti biyar a haka yana ta gyada kansa tare dayin wasu surutai ya juyo yana kallon Halisa yace.”Ana bukatar jaririyar kyanwa(mage) mai launin ‘baki da zaiba! Sannan ana bukatar kayan cikin kadangaru guda bakwai! sai gashin jikin Gurgun kare mai launin baki da jajayen ido, sannan kuma ana bukatar bakar akuya mai dauke da karamin ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button