MADADI 1-END

MADADI Page 21 to 30

Kanta a ‘kasa ta shiga dakin da sallama a bakinta, Shi kadai taji ya amsa sallamar dan ko Halisa ta amsa ita dai ba taji ba.Kusa da Halisan ta zauna tare da sunkuyar da kanta ‘kasa, dakin ne yayi shiru na tsayin minti uku kafin yayi gyaran murya kamar yanda ya saba idan zaiyi magana yace.” Gabad’ayan ku nasan kunsan abinda yasa na tara ku anan ko.”? shuru sukayi babu wacce tayi magana.

Ya kalli Halisa a nutse yace.”Tun kafin na kawo miki Naja’atu gidan nan mun gama magana dake ina fatan zaki kar’bi yarinyar nan hannu biyu ki dauke ta a matsayin *’ya* ba kishiya ba, wannan kad’ai za kiyi min ki nuna min ke mai kaunata ce.” Halisa ta d’ago kanta da sauri ta kalleshi, lallai sai ta ri’ke yarinyar a matsayin *’Ya* ba kishiya ba sannan zai gane ita mai kaunarsa ce maganar ma mamaki ta bata sosai kuma ta ‘kara tabbatar da cewar namiji bashi da kunya, komai ‘kan’kantar kishiyarta yaushe zata dauke ta a matsayin *’Ya* wannan magana ma bai mai yiwu bace. To shima dai da ya fad’i maganar yasan abune da ba zai ta’ba yiwu ba dan ya riga yasan yanda Halisa take da masifar kishi ai da wuya ta ri’ke yarinyar a matsayin *’Ya* ko *’Yar uwa*……

Hankalinsa ya mayar kan Naja’atu ya dan tsira mata ido na minti biyu kafin ya kira sunanta.

Da sauri ta d’aga kanta tana kallonsa da idanunta da suka soma kawo ruwa.

Ganin ita yake kallo yasa tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad’uwa!

Yace.”Ke ma d’azu kafin na kawo ki cikin gidan nan mun gama magana dake kuma ina fatan dukkanin abinda na fad’a miki sun shiga kunnan ki kiji ki kuma shiga hankalin ki, zaman aure kika shigo kiyi a gidana ba shirme da shashanci ba, wannan da take zaune tafi kar’fin raini a gurinki.” Yafada yana nuna mata Halisa, bata kalleta ba sai sake sunkuyar da kanta ‘kasa da tayi

Ya cigaba da cewa”Duk ina sane da rashin kunyar da kike mata a lokotan baya! bakya ganin girmanta duk irin maganar da tazo bakin ki fad’a mata kike bakya gaisheta a duk inda zaku had’u! tsaki! harara duk babu wanda bakyayi mata, to duk nasan da hakan nake kyale’ki koda ita Halisan zata kawo ‘karar ki ina bata hakuri saboda a samu zaman lafiya ina kuma nuna mata ke yarinya ce idan kika kara hankali zaki daina…….

Halisa tayi hakuri da halayen ki a baya, dan haka a yanzu kada naji kada na gani kin zageta ko kin fad’a mata bakar magana ko kuma kinyi mata tsaki! tsakaninku mutunci da mutunta juna inaso ki dauki Halisa a matsayin Uwa abokiyar shawararki wannan kad’ai zakiyi min nasan cewar ke d’in tarbiyar Halimatu ce.”……………Tsit dakin yayi bayan gama maganarsa Halisa tamkar ta zuba ruwa a ‘kasa tasha dan farin ciki taji dadi sosai yau da ya nunawa yarinyar matsayinta a gurinsa, ashe duk yana sane da iskancin da yarinyar ke mata a baya amma bai ta’ba magana ba, ji tayi duk wani haushinsa da take ji ta daina, sai wani murmushi take tana jijjiga ‘kafa…….Ita kuwa Naja’atu kanta a kasa ta kasa dagowa dan tasan idan ta dago ‘kwallar dake kokarin zubowa daga idananunta zata tona asirin zuciyarta………..’Dan kashingid’a yayi kan bed din yana kallon Halisa babu alamun wasa a fuskarsa yace.”Yarinyar nan zata cigaba da zama anan dakin! tunda ya kasance d’akuna uku ne to bai kamata ta kwana cikin yara ba idan yaso ni nabi da’ki-d’aki! kafin komai ya daidaita.” Halisa ba haka taso ba amma sai tayi kokarin danne kishinta tace”To shikkenan hakan ma yayi dai-dai ai.” Yace.”To tunda kece uwargida sai ki shirya yanda al’amarin zai kasance.”

Cikin ya’ke! da danne wani mugun kishi tace”Kwana biyu zaka dinga yi kamar dai yanda kake yi lokacin Halimatu.” Gemunsa ya shafa yana d’an murmushi yace.”Ai na dauka ko zaki sanja tsari ne shiyasa na tambaye ki.”? ‘Yar dariya tayi tana ta’be baki tace”Kwana bibbiyu shine tsari mai ma’ana idan kuma kafi son kwana d’ai-d’ai to.” Ya kalli Naja’atu had’e da kiran Sunanta! A firgice! ta kalleshi dan ita bata san wainar da suke toya ba tana can tunanin ya za’ayi ta fece daga gidan.

Yace.”Ke a ganinki kwana nawa-nawa zan dinga yi a tsakaninku.”? Murya na rawa tace”Ban gane maganar ba.” Mikewa zaune yayi yana kallonta yace.”Muna maganar raba kwanan girki ne a tsakaninku shine nake tambayar ra’ayin ki.” Shuru tayi wasu lafiyayyun hawaye suka wanke mata fuska wai yau itace Abbah Abbas ke tambayarta maganar kwanan girki.

Ganin tayi shuru yasa ya kalli Halisa yace.”Kwana bibbiyu din shi zamu dauka kamar yanda kika ce.”Mikewa tayi tana fad’in “Hakan yayi! to ni dai sai dai nace Allah ya bamu alkairi.” Hanyar fita ta nufa zuciyarta kamar ta babbake! Kallo ya bita dashi kafin yace.”To Allah ya tashe mu lafiya idan kin fita kisa yara su tashi daga kallon da suke suje su kwanta haka.” Ai fad’ar wannan magana da yayi sai ya ‘kara tunzura ta a fusace! ta bud’e kofar dakin ta fita tare da doko kofar da karfin gaske……..Tana fita palon ta raraka yaran d’akinsu sai masifa take tana zaginsu kamar sune sukayi mata laifi……Mussadiq da Saddiqa a tsorace suka bar gurin.

Innalilihi wa’ina ilaiji raji’un! kawai take ta ambata bayan fitar Halisa daga dakin gabadaya Jinin jikinta ya daskare hatta da kafafunta jinsu take sunyi mata nauyi da sanyi tana ji kamar ba a jikinta suke ba………Gyaran muryarsa taji kafin taji ya kira sunanta, amsawa tayi tana kallonsa ya iya kiran sunanta tamkar a bakinsa a ka rad’ashi.

”Kinci abinci ko.”? Yafada yana mata wani kallo na ‘kasan ido! ‘Daga kanta tayi tana mai dauke idonta daga kansa, Yace.” To shiga toilet ki dauro alwala kizo muyi nafila ta godiya ga Allah.” Mi’kewa tayi salo-salo ta nufi toilet d’in………Minti biyar ta fito daure da alwala ya mike ya shiga toilet din shima ya dauro alwala ya fito.

Nafila sukayi raka’a biyu kamar yanda Annabi ya koyar da sababbin ma’aurata! Abba Abbas ya jima hannunsa a saman kanta yana addua kafin ya cire ya d’aga hannunsa sama nan ya jima yanayi wa Allah kirari, daga bisani ya rufe adduarsa da fatihatulkitabi suka shafa ita dashi, mikewa yayi daga kan abun sallahr ya dauki key motarsa dake kan drowar taga ya bude dakin ya fita.

 Zukud’un!! tayi bayan fitarsa daga d’akin, ita yanzu abun ma mamaki yake bata gami da tsoro! da gaske dai sai tayi zaman aure dashi, tunda gashin nan har ya zaunar dasu tare da matarsa yana kawo mata tsare-tsarensa harda kashedi da gargadi kada ta zagi matarsa, lallai Abbah Abbas yayi masifar bata mamaki! to ita yanzu ba wannan ne ma yake sake furgitata ba sai kawo ta dakinsa da yayi, to me zaiyi mata? bata da mai bata amsa! mikewa tayi da saurin gaske ta nufi kofar fita, cikin ikon Allah kuwa tana jan kofar ta bude! palon ta fita tana zazzare ido! tv a kashe yaran duk sunje sun kwanta.

Kujerar data zauna a dazu nan ta nufa ta duba wayarta zama tayi kan kujerar ta shiga lalubar numbar Salim…….Lokacin shi yana ma can gidan kallo hayaniya ta hanashi ya daga wayar sai ihu suke shida abokansa sunci ‘kwallo.

Text ta tura masa tana hawaye tace.

_Salim anya kuwa kana sona kuwa? tun jiya nake kiran wayarka baka dauka ba ashe dama duk soyayyar da kake min karya kake……Kada fa ka manta kai kad’ai nayi wa alkwarin mallakawa kaina da komai nawa dan Allah kada ka bari Abba Abbas ya samu nasara a kanmu dan gani nan a gidansa a cikin dakinsa ya kulleni kasan hakan da yayi yana nufin abubuwa da yawa, dan haka dan Allah ka daure kayi wani abu akan wannan al’amarin.”_

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button