MADADI Page 31 to 40

Halisa tace”To shikkenan zan bada kudi sai ayi duk yanda za’ayi tunda ni dai bansan inda zan samu wasu abubuwan ba.” Boka yace.”Kada ki samu damuwa yanzu yanzu zamu tura aljanu su samo mana abubuwan bukata.
Halisa ta fito da kudi dubu dari cif ta ajiye gabansa, tace”gashinan Ubana ina fata ka dade kana kar’ko a duniya.” Boka yasa mahaukaciyar dariya da fad’in godiya nake kuna iya tashi ku tafi.”.
Suka mike da sauri suka juya baya suna tafiya tare da sambatun kirari ga boka najadu mai aiki da kafuran aljanu……
*Ubangiji Allah kasa mufi karfin zukatan mu amin*
*Ina taya d’aukacin al’ummar musulmi masoya Annabi Muhammad (Saw) murnar zagayowar ranar haihuwarsa ina rokan Allah ya karawa Annabi daraja da wasila fil jannati????????*
*Ka/ki Daure ki bada sadaka a wannan rana domin Annabi! sadaka bata yawa bata kad’an! tufafi ko abinci ko wani abu makamcin haka*
*Uwar gida karkiyi miyar nama ko ki soya kaji ki ‘boye ki hana makotanki daure ki bayar dan Annabi! wanda kika bayar shine rabonki. Ina fatan dani daku mu kasance cikin walwala da farin ciki a cikin wannan rana mai albarka*
*ALLAH YA MAIMAITA MANA????????*
*33*
Mdd
A mutukar gajiye suka dawo gida, Halisa ta nemi guri ta kwanta kanta nayi mata wani irin ciwo gabadaya yanayin jikinta ya sauya zuciyarta in banda tashi babu abunda takeyi, Ramlatu ta sami Sakina kishiyarta tana tambayarta abinci wai idan ta dafa ta basu zasuci.
kai tsaye Sakina tace”Nayi girki amma bashi da yawa mun cinye nida yara.” Tsaki mai karfi Yaya Ramlatu taja ta bar gurun. Sakina kuwa cikin zuciyarta cewa tayi babu wani girki da zatayi musu tunda su din sun kasance masu sabon Allah tasan gantalinsu suka tafi na malamai shiyasa suka yi asubanci……….Yaya Ramlatu na kokarin hura wuta sai kawai taga Halisa ta fito a guje ta tsuguna bakin rariya tana ta kwara amai.
Da sauri tazo ta tsaya a kanta tana yi mata sannu.
Halisa ta dinga kakari tana rike kirjinta wani irin ba’kin amai take kai kanka ka ganshi sai ya tasar maka da zuciya saboda muninsa, duk ta hada zufa! sai rike kirji takeyi.
Da kyar Yaya Ramlatu ta riketa suka nufi daki. kafin su kai ga shiga dakin Halisa ta yanke jiki ta fadi a gurin.Wani irin abu ta shagayi kamar wacce farfadiya ta kama ta.
Iya firgita Ramlatu tayi ta kai ta kawo a gurin tana kiran sunan Halisan gami da tattaba jikinta.
Sakina ta fito daga dakinta tana ganin Halisa a kwance tana turjiya sai hankalinta ya tashi, cikin zuciyarta tace”Dama kowa ya sayi rariya yasan zata zubar da ruwa koda Halisa bata da iskokai to gurin yawon bokayenta zata iya haduwa dasu.
Ramlatu cikin tsoro ta matsa gefe guda tana zare ido tunda take da Halisa bata ta’ba sanin tana da iska ba sai yau…Sakina ta tsuguna gaban Halisa ta shiga tofa mata adduoi tana shafa mata a fuskarta, cikin ikon Allah Halisa ta daina buge-bugen da takeyi a gurun bacci ya dauketa
Sakina ta kalli Ramlatu a nutse tace”Wallahi Ramlatu kuyiwa kanku fada ku daina abinda kukeyi yanzu meye ribarku a duniya idan kun cutar da wani, ki duba fa ki gani Halisa aljanu takeyi kuma daka ganinsu masu cutarwa ne me zai sanya ku dinga kai kanku ga halaka! me kuke nema a duniyar nan da gabadayan mu zamu tafi mu barta.”
Ramlatu ta daga mata hannu da fadin”Kinga Sakina ba wa’azi nace kiyi min ba, ko wane mutum da kika ganshi da akwai kashi a gindinsa kuma kina maganar mu daina cutarwa to wai wa muka cuta! idan ni macuciya ce ai ba zaki kai labari a gidan nan ba, dan haka dan Allah idan ba zaki fadi alkairi ba to kiyi shuru da bakinki.” Sakina tace”Alheri na fada miki ba sharri ba kuma dama ita gaskiya ai daci gareta kun gama da Halimatu yanzu kun dawo kan Naja’atu to ku sani duk abinda Allah ya hukunta zai faru a kan mutum sai ya faru saboda haka wallahi ku guji haduwarku da Allah.
Yaya Ramlatu jikinta ne yayi sanyi da kalaman Sakina gabadaya bata ta’ba tsammanin cewar sakina tasan irin abunda sukeyi kan halimatu ba cikin borin kunya tace”Allah yasa dai aljanna ba a hannuki take ba ballanta na ki hanamu shiga.
Sakina ta girgiza kanta cike da takaici ta bar gurun
Yaya Ramlatu ta tsirawa Halisa ido tana kwance kasan simintin tsakar gidan lokaci guda ta fyad’e tayi wani iri da ita, gaskiya itama jikinta yayi sanyi da aikin wannan bokan daka gani bashi da imani tana jin tsoro kada ya cutar mata da dan uwa.
Jikinta a sanyaye ta nufi kicin taje ta dora abinci ta fito.
Dakinta ta shiga ta dauki wayar Halisa ta shiga neman numbar ‘dan uwan nata
Abbah Abbas na kasuwa yaga kiran wayar kamar kada ya daga wayar sai kuma ya daure ya daga cike da tsare gira yayi sallama.
Sai kawai yaji muryar Yayarsa, bai damu ba saboda yasan kusancin dake tsakanin Matar tasa da Yayar tasa
Yace.”Yaya barka da rana ina fatan kuna nan lafiya? Tace”Lafiyarmu kalau ya kasuwa.”? Yace.”Alhamdullhi dazu Salim yake sake tuna min da sa’kon ki insha Allahu zan bashi ya kawo miki yau.
Yaya Ramlatu tace”Ni ba wannan ne yasa na kira ka ba inaso na tambayeka me ya hada ka da Halisa.”?
Kai tsaye yace.”Me tazo ta fad’a miki.”? “Tace kana fifita yaranka a kanta kuma kana rashin adalci a gidanka.” Cikin takaici yace.”Yanzu tana ina.”? Tace”Gata nan muna tare da ita bama ta da lafiya.”
Yace.”Me yake damunta.”? Kai tsaye tace”Iskoki take dan Allah Abbas ka rike matarka domin itace matar rufin asirinka duk arzikin daka samu tare da ita ka samu bai kamata kana fifita ‘ya’yanka a kan matarka ba.
Yace”Dan Allah Yaya ki daina wannan maganar Halisa muguwar makarciya ce itace take zalintar yaran nan amma tazo ta juya miki magana har yanxu ta kasa gane muhimancin rike maraya.”
Ramlatu tace”To me yasa zaka ce lallai sai itace zata kula maka da yaran meye amfanin auran Madadi da kayi da Naja’atu.? Sai maganar ta bashi mamaki sosai wato saboda yayi auran Madadi sai akace Halisa ba ruwanta da ‘Yayansa sai wanda ta haifa, Ganin Ko ya fahintar da yayar tasa ba zata gane ba yasa yace.”Mu bar wannan maganar dan Allah sabida ba zaki ta’ba fahintata ba Halisa kuma bani nace ta fita daga gidanta ba, idan taga dama ta dawo shikkenan idan tana ganin zaman gidanki yafi mata sai taje tayi .
Yaya Tace”Ai shiyasa na kira ka domun na baka hakuri saboda nasan bata kyauta ba tunda ba kaine kace ta fitar maka daga gida ba, dalilin daya sa na yanke hukuncin dawo da ita bayan sallahr isha’i.” Yace.”To kin taimake ta dan nayi alkawarin babu inda zan taka naje domin dawo da ita, sannan kuma inaso ki gargade ta sosai koda ta dawo bana son tashin hankali a matsayinta na babba kullum itace mai tayar da fitina a cikin gidan.” Ya Ramlatu tace”Magana dai ta kare insha Allah zanyi mata fada.”
Sallama sukayi da juna, ta kashe wayar ta fito nan ta tarar da Halisa ta tashi zaune tana ta soshe soshe sai gumi takeyi ta kalli Yaya Ramlatu da fadin”Me ya faru ne na ganki kwance a kasa a cikin rana.” Ramlatu tace”Iskar ki ce ta kayar dake! Halisa shuru tayi tana kallon guri guda, Ramlatu tace”Yanzu mukayi waya da Abbas da sauri tace”Me yace dake.”? Yaya Ramlatu tace.”Kin san halinsa da tsari gabadaya ya d’ora laifi a kanki! dan haka kada ki damu ki koma domin ganin yanda zamantakewar gidan zata sauya na tabbatar da cewar kina komawa hankalinsa zai dawo kanki.