MADADI Page 31 to 40

“Humm! kawai tace ta fara kokarin mikewa jikinta duk yayi kura sabida birgimar da tayi a gurin Ya Ramlatu ta nufi kicin da fadin” Bari na juye miki ruwan sanwar abinci dana dora a wuta sai kiyi wanka dashi ko kyaji dadin jikinki…Halisa ba tare da tace komai ba ta daga labulan dakin Ramlatun ta shiga taje ta zauna tare da zabga tagumi! duk ranar da iskarta ta tashi takan kasance cikin kunci da takurewar zuciya kuma gabadaya takan rasa kuzarin jikinta, shiyasa bata son abinda zai tayar mata da hankali yanzu ma ta tabbatar da cewar zuwanta gurin boka ne yasa suka tashi, to amma babu damuwa mutukar bukatarta zata biya magana ta kare.
Ita kuwa Naja’atu a kwance ta wuni damuwa da bakin ciki sun cika mata zuciya, wai Salim ne ke kiranta da antinsa wannan al’amari ya bata mamaki.
Sai kusan biyar da rabi na yamma ta shiga kicin domin shirya musu abincin dare, farar shinkafa da miyar kifi kawai tayi musu ta shirya daining din kana taje tayi wanka ta shirya jikinta zamanta tayi a dakin, su kuma yaran suna falo a zaune dan tunda suka dawo daga makaranta suka ga yanayinta sai duk jikinsu yayi sanyi a duniya sun tsani suga tana bacin rai duk sai suma su shiga damuwa mussaman mussadiq.
Tana zaune kan dadduma bayan ta idar da sallahr isha’i taji muryar maigidan tare da yaran, motsawa ba tayi ba ya shigo dakin da sallama a bakinsa….Kamar mai ciwon baki tace”Sannu da zuwa.” Yace”Sannu ina fatan kun wuni lafiya.”?
A takaice tace”Lafiya kalau.” Yanayin yanda take amsa masa magana yasa ya fahimci cewar tana da damuwa, ba tare da ya sake cewa komai ba ya fita daga dakin, zumbura bakinta tare da barin kan daddumar taje ta kwanta kan bed cike da damuwa a zuciyarta.
Yaya Ramlatu da Halisa ne sukayi sallama suka shigo palon a tare, gabadaya yaran suka yi tsamo-tsamo jiki a sanyaye suka amsa sallamar…..Halisa ta dinga bin palon da kallo tana ta’be bakinta, ita kuwa Yaya ramlatu zama tayi kan kujera tana amsa gaisuwar yaran…Halisa ta bude bakinta kenan za tayi magana ya fito daga dakinsa.
Kauda kansa yayi daga inda take dan har yanzu bai daina jin haushinta ba.
Ita kuwa Ramlatu na ganinsa sai yasa ta janyo Saddiqa tana duba hannunta tare da yi mata sannu da jiki! Yarinyar ta dinga amsawa a tsorace, itama Halisan a sanyaye taje tana duba hannun yarinyar sai wani marairaicewa take kamar mutuniyar arziki
…..Shi kuwa ko kallonta baiyi ba yaje ya zauna suna sake gaisawa da yar uwarsa.
Halisa ta wani risinar da kai kamar mutuniyar kirki ta gaishe shi, amsawa yayi hankalinsa nakan mussadiq inda ya umarce shi da yaje ya kira Naja’atu tazo su gaisa da Yaya Ramlatun
Halisa kuwa ganin yana dauke mata kai duk sai jikinta yayi sanyi tana ganin anya kuwa aikin bokanta zaiyi tasiri a kansa ta lura yana da taurin kai da kuma dafa’i a jikinsa tayi yaji a maimakon ya tarairayeta ko kallo bata isheshi ba.
Koda Mussadiq ya gaya mata sa’kon Abban nasu cewa yaron yaje yace tayi bacci, yaron yayi jim yana tunanin maganar ta buga masa tsawa da fad’in ‘Ka wuce daga kaina kaje kace nayi bacci.” Yace.”Yaya Naja’atu karya fa babu kyau dan Allah kizo ku gaisa kamar yanda Abbah yace.
Mikewa zaune tayi tana hararsa tace”Naji jeka gani nan zuwa.” Da sauri yaron ya fita daga dakin…..Sai da tagama zamanta sannan ta mike ta fita.
lokacin ma yaya ramlatun ta mike da niyar tafiya. Ta dan risina murya a kasa tace” Yaya sannu Ina wuni.” Ta’be bakinta tayi tace”Na wuni kalau ai da kin sani kinyi zamanki ma ba sai kinzo mun gaisa ba.” Shuru palon yayi dan yanda ta fadi maganar kowa ya fahimci a hasale take da abinda Naja’atun tayi…Hanyar futa ta kama Abban da Halisa suka bi bayanta. ita kuwa juyawa tayi ta koma daki babu wata damuwa a cikin ranta dan tun ranar da matar ta zagi iyayenta ta daina jin tsoronta ba za tayi mata rashin kunya ba amma kuma ba zata lamunci a dinga tozarta mata iyayenta ba Daki ta koma ta kwanta tana cigaba da tunanin mafita a gareta…..’Kawarta Munira dake can jos itace ta fad’o mata, tabbas da tana da waya to data kira Munira tunda tana da numbar ta tasan zata bata shawarwarin da zasu taimake ta amma ta daina zuwa ta kaiwa anty Maryam shawara sabida ta lura itama tana goyon bayan zamanta a gidan Abbah Abbas din…shuru tayi tana sake nazarin yanda za’ayi ta sadu da Munira, tana ganin za tayi dubarar daukar wayar Abba Abbas din ta kira ta tunda tana da numbar ta. wannan tunanin da tayi sai yasa ta samu sassauci a cikin zuciyarta.
Halisa kam bayan sun raka Yaya Ramlatu sai tabi bayansa dakinsa ta shiga tana wani salo-salo ta rike hannunsa kawai sai ta fashe da kukan kissa tana bashi hakuri wai wallahi ranta ne ya ‘baci shiyasa ta yanke hukuncin bar masa gida amma insha Allahu ba zata sake kwatantawa ba.” Yace.”Idan kina ganin yin hakan shine mafita a gareki to sai ki cigaba da daukar mayafi kina tafiya ni dai ko yau na rabu dake idan nayi ra’ayi zan maye gurbinki da wata sabida haka wallahi duk sanda na nuna miki kuskuranki akan wani abu kika dauki mayafi kika fita to ki tabbatar da cewar kin fita daga gidana har abada.” Murya na rawa tace”Dan Allah ka daina wannan maganar insha Allah ba zan sake ba raina ne kawai ya baci shiyasa na tafi amma ka daina cewa zaka rabu dani har abada. Yace.”Ai na lura hakan kike so shiyasa nake sake jadadda miki.” Tace” Kayi hakuri na daina magana ta wuce insha Allahu.
Halisa sai da tasan yanda tayi ta wanke kanta a gurinsa sannan hankalinta ya kwanta.
Abbah Abbas shi kadai yayi kwanciyarsa dan da Halisan da ita Naja’atun babu wacce ya tunkara ya rabu dasu su samu nutsuwa tukkuna…Bangaran Naja’atu ma tayi mamaki sosai da ba taji yayi mata wata magana ba koda asubah da ya shigo tashinsu lafiyar Allah suka gaisa babu wani abu a tare dashi ya fita daga dakin, sosai hakan yayi mata dad’i dama bata so ya dinga ta’ba ta yana tayar mata da sha’awa tafi so suyi nesa da juna har Allah yasa su rabu ….Yini tayi cikin walwala dan har palo ta fito ta zauna tana kallo ita kuma halisa taci kwalliya kamar itace amaryar sai shige da fice take tsakanin kicin da dainng an shiryawa maigida girki iri-iri kuma sai jan Naja’atu take da hira, to itama ganin Halisan ta dawo da sigar son a zauna lafiya sai ta saki jikinta tana amsa mata jefi-jefi! Koda maigidan ya dawo ya gansu suna hira ga yaran suna zaune a kusa dasu, sai ya shiga mamaki sosai ikon Allah yau Halisa da Naja’atu ne a zaune a guri guda suna hira harda dariya! kyataccen murmushi ne a fuskarsa ya shiga kallonsu yana jin dadi…Halisa da sauri ta iske inda yake ta kar’bi abubuwan dake hannunsa tana masa barka da zuwa, ita kam naja’atu sunkuyar da kanta tayi ba tare da wata cikakkiyar kulawa ba tayi masa barka da zuwa. Ya amsa babu yabo babu fallasa ya kama hanyar dakinsa…Yau kwalliyar da Halisa tayi ta tafi da imaninsa sosai Halisa ‘yar gayu ce gashi ta iya ado da d’inkunan banza atamfa ce a jikinta riga da sket amma anyi mata dinki banza dan gabadaya saman rigar net ne brest dinta duk a waje ga wani masifaffan kamshin turare da takeyi…Halisa duk da ta san da cewar ba a cikin kwanakinta take ba hakan bai hanata bashi kulawa ba saboda tana so ta sake wanke kanta a gurinsa ta gane ba da asiri kad’ai zata tsaya ba dole sai ta had’a kissa da siyasa sannan bukatarta zata biya. A