MADADI Page 31 to 40

Naja’atu kuwa bayan fitar Dr daga dakin, zanin jikinta ta kwance ta bude cinyoyinta gabad’aya ta d’an zame pant d’inta ya sauka dai-dai cinyoyinta a hausarta wai gurin ta bude yasha iska a ganinta rufewar da tayi shine yake sanyawa yana k’ara yi mata zafi…..Aikuwa yana shigowa da abinda yayi tozali kenan, Tsigar jikinsa ce ta wani tashi sai yayi Saurin kauda kanshi jiki a mace ya ‘karasa bakin bed din…..ita kuwa sai jan zaninta take tana kokarin rufewa had’e da dauke kanta sam bata san kallon fuskarsa…..Ya jima a tsaye a kanta yana kallonta tana ta kici-kicin jan zani ta rufe sai ya sunkuya yayi mata rumfa numfashinsu ya dinga had’uwa! goshinta ya sumbata cikin taushin murya yace.”Sannu kinji ko zai daina yi miki zafi insha Allah! kuma naji dadi sosai Dr tayi min bayani cewar baki samu matsala ba yanzu zamuje tare da ita domun a kawo miki magani wanda zai taimaka miki gurin dauke zafin da gurin yake…..Ba tace masa uffan ba sai ma wasu hawaye da suke kokarin zubo mata, sam bata so tana sha’kar numfashinsa gashi ya wani sunkuya mata a jiki….Jin bakinsa tayi kan le’bunanta yana lasa da harshensa, tayi gaggawar juyar da kanta tana jin mugu-mugun mamakin abinda yake mata gaba’daya ma ta lura dashi ya manta matsayinsa a gurinta abinda ya ga dama shi yake yi.
Tsayuwarsa ya gyara yana kallonta da idanunsa da suka soma risinawa yace.”Me kike so na kawo miki kici nasan dole kina bukatar abinci.”
Uffan ba tace masa ba…Yace.”To tunda ba za kiyi min magana ba idan na dawo zan maimaita abunda nayi jiya .” Tayi saurin kallonsa bakinta na rawa! girarsa ya daga mata yana so ya tabbatar mata da maganarsa…..da kyar tace”Koma me ka siyo zanci dan Allah kada ka kuma wani abu dani zan iya mutuwa.” Yayi murmushi yana shafa gemunsa had’e yi mata kallon ‘kasa-‘kasa yace.”Bana jin zan iya yi miki alkawarin abinda kike so yana da kyau ki zama jaruma mai daukar ko wacce irin lalura wannan abun ba zai sanya ki mutu ba sai dai ma ya ‘kara miki lafiya.”
Wannan maganar da yayi tasa taji wani tsoronsa ya shigeta Murya na rawa tace Dan Allah kayi hakuri kada ka ‘kara yi wallahi ba zan iya ba.” Tausayi ta bashi ganin har ta soma hawaye kuma ya hango tsantsar tsoronsa a kwayar idonta, sai yace.”Daina kuka ba zan sake ba shikkenan ko.” Tace”To ka rantse da Allah.” Maganar sai ta bashi dariya yace.” Ba sai na rantse ba tunda nayi miki alkawari shikkenan ki kwantar da hankalinki ki daina kuka.”
Kanta ta shiga d’agawa tana kallonsa wai so take ta tabbatar da gaskiyar maganarsa, shi kuwa hularsa dake saman kansa ya gyara ya kama hanyar fita daga dakin tare da fad’in “Sai na dawo ko.” Kallo tabishi dashi tana jin tsana da tsoronsa na sake ‘karuwa a cikin zuciyata, hakika da tana da inda za taje ta fake to data gudu gabad’aya sun nemata sun rasa…
Halisa da Dr din ya samu a palon suna hira, yana fitowa Halisa ta kura masa ido zuciyarta na tafarfasa! Shi kuwa nan da nan ya daidaita nutsuwarsa cikin dakewa ya kalli Dr Sa’adatu da fadin “Muna iya tafiya yanzu.”
Dr ta kalli Halisa tana dan murmushi tace”To madam Allah ya bamu alkairi.” Ciki ciki tace”Okey.” ya kalleta tare da karantar yanayin da take ciki, yace.”Zan dan futa sai na dawo.” Iskar da yake ma bata kalla ba dan wani irin mugun haushinsa takeji ganin yanda yake ta wani rawar jiki ko maganar zuwa kasuwa ma bayayi.”
Suna fita ta mike ta nufi dakinta, ta dauki wayarta ta shiga sanarwa da Yaya Ramlatu halin da ake ciki.” Yaya Ramlatu tace”Halisa ki rabu dani naji da bakin cikin dake damuna! Halisa tace”Me ya faru dake Yaya.”?
Yaya Ramlatu tayi ‘kwafa! cikin tsabar bacin rai tace”Mutsiyaciyar yarinyar nan Naja’atu itace ta kai ‘karata gurin Alhaji da Hajiya yau da safe sai ganin d’an aike nayi, koda naje gidan Alhaji baiyi min da sauki ba rufeni yayi da fad’a sosai hajiya har da cewa duk sanda na sake zuwa gidanku bata yafe min ba.’
Halisa tace”Lallai al’amarin Malam Baba yayi tsanani! to nima nan a cikin matsala nake dan gabadaya na kasa gane kan maigidan tun jiya daya kwanta da yarinyar ya zama sakarai sai rawar jiki yake yi yama kasa zuwa kasuwa gabadaya ya lalace a gindin yarinyar……Yaya Ramlatu tace”To ke yanzu wane mataki zaki dauka dangane da faruwar hakan.”? Halisa tace”Kawai so nake na samu malamin da zaiyi min aiki akansa gabad’aya a zare masa sha’awarta a zuciyarsa ko kuma idan yaje zai sadu da ita gabansa ya mutu ya’ki aiki.”
Yaya Ramlatu tace”Wannan aikin ba mai wuya bane mutukar zaki futo da kudi ni kuma zan baki goyon baya dan nima abinda yarinyar tayi min yasa gabadaya na sake tsanarta.
Tace”Wallahi idan zan samu malamin da zaiyi min wannan aikin ko nawa ne zan biyashi.” Yaya Ramlatu tace”Shikkenan yanzu zan kira ‘Yar shagamu a waya zan fad’a mata duk abinda ke faruwa, nasan zata kaimu inda bukata zata biya.” Halisa ta sauke ajiyar zuciya tace “To sai naji daga gareki Yaya Ramlatu nagode.” Sallama sukayi da juna kowanne ya kashe wayarsa cike da mugun nufi
Bayan fitarsa daga dakin bacci mai nauyi ne ya dauketa, sai ji tayi ana shafa mata tafin kafafunta had’e shara’bar ‘kafafunta.
Bude ido tayi da sauri ganinsa zaune dab da ita yasa ta zabura! da sauri zata mike zaune! ya ri’ke hannunta cikin lafazi mai dadi yace”yi hankali kisa nutsuwa kada ki fama ciwon naki.” Maganar tasa yasa ta tuna abinda ke da akwai.
A hankali ta saukar da kafafunta kasa tana so ta mike tsaye ya kama hannunta suka mike tare….kamar me koyon tafiya suka nufi toilet brush tayi suka fito tare…….zama tayi gefan bed tana jin yanda cikinta ke murd’a mata yunwa takeji sosai….Idonta ne ya sauka kan ledar Osis daya shigo dashi. dauka yayi ya mika mata da fadin”kici abinci sai kisha magani ko.”
Kar’ba tayi tana kokarin sauka kasan kafet, shi kuma sai ya shiga duba maganin da Dr ta bashi……..abinci taci sosai ta had’a da lemo mai sanyi lokaci guda ta dawo cikin hayyacinta. ganin ta samu nutsuwa sai ya mika mata maganin da ruwan dake hannunsa, kamar zata fashe da kuka ta kar’ba tana jujjuya maganin a hannunta, a rayuwarta ta tsani had’iyar ‘kwaya. Yace.”Kisha mana kin tsaya kina kallonsa.” ‘Daya bayan d’aya tasha maganin tana wani ya mutsa fuska.
Ya dan sassauta murya wanda idan ba ita d’in ba babu me ji yace”Yanzu sai shiga ruwan zafi ko.” ?
Tsintar kanta tayi da kallonsa domin ita wallahi abinda yake mata mamaki yake bata tsakanin jiya da yau duk ya sanja magana ma idan zaiyi mata da wata irin murya ta mussaman yake mata babu abinda yake bata haushi dashi sai munafikin kallon da yake mata ta ‘kasan ido……kawai ta shiga bin bayansa da kallo a lokacin da yake kokarin shiga toilet din.
Minti goma ya fito yana kallonta yace”Zo muje ki shiga ko.” Ta mike a hankali dan itama tana so ta shiga ruwan zafin ko ta samu saukin wani abun.
Ya nufeta yana tattare hannun rigarsa yace”Ki cire kayan jikinki sai ki daura towel sai kinfi sakewa.” Kafin tace wani abu ya sata a jikinsa yana kokarin kwance mata zani!
Da sauri tace”Zan iya cire kayana dan Allah kyaleni.”
Girgixa mata kai yayi ya cigaba da kwance daurin da tayiwa zanin jikinta yanayi yana sumbatar wuyanta, ji tayi tsigar jikinta ta soma tashi sakamakon gemunsa da yake goga mata fatar jikinta.