MADADI 1-END

MADADI Page 31 to 40

Naja’atu tace”Ke Saddiqa Ya akayi kika yanke haka.” Saddiqa na share hawaye tace”Naje ciro kaza a freezar ne.? Cike da mamaki tace”Kawai sabida zaki dauko kaza sai ki yanke.”

Saddiqa ta kalli Halisa tsoronta takeji shiyasa ta kasa fadawa Naja’atu abunda ya faru..

Gurin ta karaso rai a bac’e ta kar’bi hannun tana dubawa gani tayi naman tafin hannunta ya fito yayi jajur! ta kalli Halisa da fad’in “Saboda mugunta zakice tayi shuru kada ta fadawa babanta so kike kenan hannunta ya lalace! duba fa yanda naman gurin ya fito.

Halisa tace” Ke kada ki fada min maganar banza mana ai ba sabida wani abu nace kada ta fada masa saboda nasan kin san halin masifarsa mussaman a kan ‘ya’yansa gabadaya ranmu zai iya ‘baci ta dalilin haka.”

Tace”Ranki ne dai zai ‘baci amma ya zama dole a fada masa domin ya kaita asibiti.” Halisa taja tsaki mai karfi ta bar gurin tana fadin”Ai sai kiyi ta fad’a masa.” Kicin din ta koma ta cigaba da aiki tana tararrabi da tunanin abinda zai faru mutukar Saddiqa tafada masa dalilin yankewarta da wuka to tasan ranta sai ya ‘baci!

A hankali ta zauna kan kujera ta zaunar da Saddiqar kusa da ita tana duba hannun nata! sosai yarinyar ta samu rauni amma saboda tsabar son zuciya irin na matar uba wai take cewa yarinyar tayi shuru kada ta fadawa babanta yanzu idan da Mufida ‘yarta hakan ya faru da ita ai ba za tayi shuru ba.

‘Kwallah ta goge tunawa da tayi da Halimatu! ta kalli Mussadiq da Mufida dake tsaye jikinsu duk yayi sanyi dan Mussadiq ma kuka yake..Tace”Ke Mufida jeki dakin mamanki ki dauko min wayarta ki sako a cikin hijabi kada ki bari ta gani.

Mufida da sauri tace”To” ta nufi dakin Halinsan….Halisa na kicin Mufida ta shiga ta dauko wayarta ta kaiwa Naja’atun, ta kar’ba tana kokarin saka numbarsa sunansa ya fito Halisa tayi serving da Abban mufida.

Abbah Abbas na can kofar na’isa gidan hajiya kiran wayar ya sameshi, Jin muryar Naja’atu cikin wayar Halisa sai abin ya bashi mamaki! kafin ya tambayeta cikin rawar murya ta sheda masa abinda ke da akwai…Ya kashe wayar cikin damuwa ya fadawa Hajiya abinda yake faruwa! tace”Ikon Allah to kayi maza kaje a kaita asibiti a duba kuma ayi mata allurar nan dan gudun shigar ciwo.” Ya mike tare da fad’in “Insha Allah Hajiya sannan dan Allah kada ki manta da maganar mai aikin da mukayi ina bukatar mace dattijuwa mai hankali gami da tsabta.” Hajiya tace”Insha Allahu zan fad’awa Jummai ta duba maka a kurkusa ai masu aiki ba zasuyi wahala ba.”

Kafin ya isa gidan magariba tayi dan haka sai da ya tsaya a massalaci yayi sallah tukkuna ya shiga gidan nasa, lokacin zafin ciwon har ya zuba mata zazzafi! Naja’atu da yaran duk sun shiga damuwa ganin Saddiqar sai rawar d’ari takeyi….Koda yaga yanayin jikin ‘yar tasa sai hankalinsa ya tashi, ya shiga tambayar ba’asi! Halisa na tsaye a baki danning jikinta duk yayi sanyi.

Naja’atu tace” Dawowar su kenan daga makaranta naji Anty Halisa na kwala mata kira dan ko uniform bata cire ba gasu nan ma a jikinta, ina ciki a kwance Mussadiq yazo yake fada min wai ga Saddiqa can ta yanke jini na zuba shine dana fito naga Aunty Halisa na daure mata hannunta da yanki kuma tana cewa kada a fad’a maka!

Ya kalli Halisa yana so yaji karin bayani daga bakinta, sunkuyar da kanta tayi kasa dan bata da abin da zata ce! ganin alamun rashin gaskiya a tare da ita yasa Yace.”Ki fada min dalilin daya sa Saddiqatu ta yanke a hannunta.

Cikin inda inda gami da rashin gaskiya tace”Kasan ka fita ka barni ina aiki a kicin to ganin yamma tayi yasa na kirata nace ta dan taimaka min shine ban san ya akayi ba naji ta rike hannunta tana kuka wai ashe wuka ce ta yanke ta.”

Yace”Saddiqa ya akayi shin maganar da Halisa tayi gaskiya ne? Saddiqa tace”Eh mommy tace”Na dauko kaza a freezar to dana kasa daukowa sai ta bani wuka tace wai nayi dubara na dauko da ita.”

Ya dinga kallon Halisa zuciyarsa na wani irin turiri! yace.”Ashe dama saddiqatu nasa aiki bake ba.”? Tace.”Wallahi ba’a sa….Kafin ta rufe bakinta ya bata kyakykyawan mari a fuska! 

Palon yayi tsit!! Halisa kuwa kunyar duniya ta isheta sai ta sunkuyar da kanta kasa tana jinsa yana ta zazzaga mata fad’a hawayen takaici ne ke kokarin zubo mata a fusace! ta bar gurin…Yaja tsaki mai karfi ya kalli Naja’atu da fuskar ‘bacin rai! Yace.”Tashi maza ki dauko hijabi muje asibiti da ita.”

Hakanan ta daure ta tashi tana tafiya salo-salo itama ba wani kwari ne da ita ba, tsoron abinda zaije ya dawo yasa ta lallaba ta fito jikinta sanye da hijabi, ya sunkuya ya dauki Saddiqan dake kwance a kan kujera ya nufi hanyar fita, ta rufa masa baya.

 Saddiqa tasha wuya sosai dan har sai da akayi mata din’ki a bayan hannunta sannan aka wanke gurin Dr ya hada mata maganguna masu kyau! tana kuka Naja’atu na taya ta dan gabadaya kasa daurewa tayi sai take jin ciwon tamkar a jikinta.

Dr ya gama aikinsa ya nad’e gurin da plasta kana ya hada mata magunguna masu kyau.

Halisa kuwa tana shiga daki zama tayi gefan gado tayi tagumi! tarasa abinda ke damunta, wai yau ita aka mara a gaban yara! lallai dole ta dauki mataki dan gaskiya abin yayi mata ciwo sosai! ita tarasa wane irin so yake wa yaran wanda baya iya sarrafa kansa, ga Mufida nan kwatakwata baya nuna damuwarsa a kanta komai Saddiqa da mussadiq!

Mikewa tayi ta bude wardrobe dinta ta dauki hijab ta dauko kaya kala uku jakarta ta dauka ta sa kayan ta dauki pose dinta da key din sabuwar motar daya siya mata fitowa tayi tana wani irin huci! sai taga Mufida da Mussadiq a zaune sunyi tagumi!

Tsawa mai karfin gaske ta bugawa Mufida tace”Tashi dan ubanki kin zabga tagumi sai kace wacce akace uwarki ta mutu.! Yarinyar ta mike a firgice tana kallonta tace”Mommy ina zakije na ganki da jaka.” Tace”Gidan Ubanki zanje.”! Yarinyar tayi tsuru tana kallonta, tace”Yi maza ki shiga dakinku ki dauko kayanki zamu tafi gidan Baba dan ba zan tafi na barki a cikin mayu ba.”

Yarinyar ta shiga girgiza kanta tana fad’in “Mommy dan Allah ki barni a gida tare dasu Mussadiq.” Wani irin mari ta kifawa yarinyar tace”Dan ubanki kinyi abinda na saki ko kuwa kina nacewa mutsiyatan yara zasu koya miki mugun hali to mutukar ni na haifeki babu ke babu so.

Yarinyar ta turje taki tafiya dauko kayan, halisa cikin rashin imani ta dinga marinta kamar ba ita ta haifeta ba, babu arziki Mufida ta ruga dakinsu a guje taje ta rufe kofa tana kuka…Halisa ta dinga dukan kofar tana fadin”Shikkenan sun lashe min kurwar ‘yata! kai ubangiji Allah ya rabamu da mayen mutum..Mussadiq ya sunkuyar da kansa kasa yana goge hawaye! A fusace! ta kai masa rankwashi a kansa tana fadin”Na tafi na bar muku gidan shegu mutsiyata.” Fuuuu! ta wuceshi ta nufi kofar futa.

Mussadiq ya tashi yaje ya tsaya a bakin kofar dakin nasu yana kiran sunan Mufida da fadin”Ta bude kofar mommy din ta tafi…Mufida na kuka tace”Mussadiq bazan bude ba sai Abbanmu ya dawo tsoro nake kada mommy ta dakeni.” Mussadiq zama yayi bakin kofar dakin yana kuka hade da bin palon da kallo.

Driving yake tana satar kallonsa ta mirror ganin fuskarsa tayi a hade tamkar tunda aka hallice shi bai ta’ba dariya ba, ba tun yau ba tasan shi da masifar son ‘ya’ya tayi mamaki ma da hukunci mari ne kawai ya shiga tsakaninsa da Halisa tabbas kowa yaji abunda ta aikata yasan bata kyauta ba, kuma ta nunawa duniya cewar ba zata iya ri’ke yaran tsakani da Allah ba…..Ita kuwa sai take ganin to meye amfani kana son mutum amma baka son ‘yayansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button