MADADI Page 31 to 40

Gani tayi yay parking a gurin da suka ta’ba tsayawa yayi musu take away. Yauma gurin taga ya nufa ta bisa da kallo har ya shige cikin gurin, sannan ta mayar da hankalinta kan Saddiqa dake bacci a bayan mota, hannu ta mika ta dan shafi wuyanta taji har yanzu da zafi amma ba kamar dazu ba, cikin zuciyarta tace”Allah ya kareku daga sharrin matar nan.” Hango shi tayi ya tawo hannunsa da ledoji kamar yanda ya saba, tausayinsa taji ya ratsa mata zuciya, Abba Abbas mutum ne shi mai zuciya da kula da iyalinsa komai suke bukata sai yayi musu da jikinsa da aljihunsa a tarihin rayuwarta a gidansa bata ta’ba d’aura zani dan ‘kasa da dubu biyar ba manyan atampopi da lesuna yake dinka musu shadda kuwa komai tsadarta zai d’inka yasa a jikinsa suma ya d’inka musu, komai nasu mai kyau ne! Idan sallah tazo kuwa haka zai kwashe su a mota suyi ta siye-siye wanda har sallah ta wuce basu gama amfani dasu ba.
Gaskiya ta wannan bangaran ya ciri tuta tana jin da tana sonsa to babu abinda zai hanata ta kyautata masa, sai dai kash ta rasa a wane matsayi zata ajiye shi a zuciyarta duk da cewar ya kar’bi abu mai muhimanci a gurinta hakan bai sanya ta ta karaya daga kudirin dake cikin zuciyarta ba, tayi alkawarin ba zata kare rayuwarta da auran tsoho ba dole ne ma ya sauwake mata tunda ya kawar da kulafucinsa a kanta
Ganin yana kokarin bude motar ne yasa tayi saurin dauke kanta daga kansa…Ya zauna mazauninsa tare da kunna motar suka bar gurin.
BHRBN
*32*
Mussadiq najin motsin shigowarsu sai ya mike da sauri yana me kallon kallon kofar shigowa, Naja’atu ganin yaron kamar a furgice yasa tayi saurin ‘karasawa kusa dashi tana tambayarsa, sai kawai yasa kuka yana nuna mata dakinsu da hannunsa.
Tace”Menene kake kuka ina Mufida.”? Yace.”Tana daki ta kulle kofa wai tsoro take kada mommy ta daketa alhalin kuma mommy din ta tafi unguwa yanzu.
Da sauri tasa hannunta jikin kofar tana bugawa had’e da kiran sunan yarinyar.
Mufida najin muryar Naja’atu sai tayi saurin bude kofar ta rungumeta tana kuka.
Taja hannunta suka zauna kan kujera tana tambayarta.
Yarinyar na fada mata abunda ya faru………ya shigo palon ya tsince karshen maganar inda take cewa Mommynta ta tafi gidan Baba da jakar kayanta saboda tace ba zata bita ba shine ta doketa…….Ba tare daya nuna damuwarsa ba ya kalli Naja’atun yace.”Kije dasu daki suci abinci su kwanta amma ki tabbatar da cewar Saddiqatu tasha maganinta kan ‘ka’ida.”
A sanyaye ta amsa masa kana ta mike cikin dauriya ta nufi dakin yaran suka bi bayanta….Zama yayi kan kujera yana mamakin halin halisa wato saboda ya nuna mata kuskuranta shine tayi yaji, to kuwa babu shakka wannan karon zai nuna mata fushinsa da babu inda zai taka yaje idan ta gaji da zaman gidan ta dawo da kafafunta.
Halisa sai bayan ta fita daga gidan kuma sai ta shiga tunanin abunda zata fadawa iyayenta idan taje! duk ranar da tayi yaji taje gidansu mahaifinta ba yayi mata da sauk’i! fada sosai yake mata kuma ya daina kawo cefane mai kyau a gidan a yini a kwana ana cin tuwo washe gari kuma a dama kunu asha ko kosai babu sai dai ta fito da kudinta tayi siyi abinda take so, bayan haka kuma shimfidar arziki bata da ita a gidan sai da ta had’a summokara ta kwana a kai.
Yanke shawarar zuwa gidan Yaya Ramlatu tayi dan saboda tasan mijinta ba mazauni bane kuma Yaya Ramlatu tana da spire na daki sai ta shiga ta zauna ta rantse ba zata koma gidan ba sai yazo da kafafunsa ya bata hakuri wannan shine abinda ta kudurta a cikin ranta.
Yaya Ramlatu na shirye-shiryen kwanciya kawai taji sallamar Halisa a gidan, tayi saurin daga labule ta fito tana amsawa.
Halisa kece da daddaran ina fata dai lafiya.”? Halisa ta girgiza kanta cikin kunar zuciya tace”Mu shiga ciki Yaya.”
Yaya Ramlatu ta rike hannunta suka shiga dakin suka zazzauna….Halisa kafin ta fadawa Ramlatu abunda ya faru sai da taci kukanta ta koshi!.
Yaya Ramlatu tace”Ki daina kuka! kada ki jazawa kanki lalura idan baki manta ba dama na fada miki idan yarinyar nan ta shigo gidan to ki tabbatar da cewar auranki na tangal-tangal dan saboda ni narasa wane irin mutane ne su masu masifar d’afar tsiya idan suka rikewa mutum kurwa sai sun rabashi da kowa, amma babu komai ai mune maganinsu, dama dazu bayan mun gama waya dake na kira *’Yar Shagamu* a waya duk na sheda mata abinda ke faruwa tace”Babu matsala zata shigo gobe mu tattauna dan akwai wani malami da take saran kaimu gurinsa insha Allahu kukanki ya kare mutukar mun dangane ga wannan malamin, sabida haka zaki zauna tare dani muga abinda hali zaiyi nasan idan aikin malam ya fara tasiri a kansa zai nemi duk inda kike.
Halisa tace”Nima dama shawarar dana yanke kenan da nayi niyyar tafiya gidanmu sai na tuna idan naje can din wahala ce shiyasa na nufo nan domin muyi shawarar abinda ya dace..
Yaya Ramlatu tace”In dai kin futo da kudi ai komai mai sauki ne.” Tace”Cikin jakata a yanzu bai fi dubu bakwai ba amma na fito da Atm dina gobe zan fita na ciro kudin insha Allah.
Yaya Ramlatu tace”To Alhamdullhi bari na tashi na gyara miki shimfida ki kwanta.” Mikewa tayi ta shiga kici kicin sauko da katifa……(Kai jama’ai wai shin ita Ramlatu wace irin mata ce)
Sai da ta tabbatar da cewar yaran sunyi bacci tukkuna sannan ta mike a nutse ta shiga toilet kafin tayi wanka sai da ta sake shiga ruwan dumi tukkuna sannan tayi wanka ta fito daure da zanin atamfar jikinta….Tana kokarin bude jakar kayanta domin dauko kayan bacci ya shigo dakin, gabanta ya fadi sai ta shiga addua kan kada Allah yasa yace tazo dakinsa ta kwanta…..Yace.”Duk sunyi bacci kenan.”? Kanta a kasa ba tare da ta kalleshi ba tace”Umm.” Sai ya nufi gadon Saddiqa tare da tsayawa a kanta yana dubata.
Ganin haka yasa da sauri ta dauki hijabinta tasa ta fito da riga da wando irin na bacci ta ajiye a kusa da ita ta rufe jakar gabanta sai dukan uku uku yake.
Ya jima yana kallonta yana mamakin abinda tayi to meye kuma na rufe jiki dan shirme! wane dare ne jemage bai gani ba!
Gyaran murya yayi, ta zabura! da sauri ta takure jikinta.
Yace.”Zaki kwanta anan ko kuma zaki zo muje dakina.”?
Da sauri tace”Zan kwana tare dasu dan saboda Hannun Saddiqa.” Yace”Okey to zaki iya kwanciya kasan kafet kenan.?
Murya na rawa tace”Eh babu damuwa.”! Yayi shuru yana kallonta da murmushi a fuskarsa tsaf ya gane gudunsa take kuma ta tsorata dashi sosai dama haka yake so yana so ta gane bambamcin aya da tsakuwa yasan yanzu zata gane tsufa ko yawancin shekaru ba zai hanashi kuzari ba, d’an shekara sittin ma sai ya fishi fitina
Ganin ya kama hanyar fita daga dakin yasa taji wani irin sanyi a cikin ranta, yana fita ta mike da sauri tasa kayanta ta dauki bargo da pillow ta shimfida kasan kafet ta kwanta.
Ta dauka ba zai dawo dakin ba shiyasa ta cire hijab din jikinta, kawai sai taji ya turo kofar dakin ya shigo hannunsa rike da lallausan bargonsa ……Mikewa zaune tayi ta had’e gwiwoyinta guri guda taki kallonsa
Shima ganinta cikin kayan baccin yasa ya shagala da kallonta, yarinyar na masifar tafiya da imaninsa.
Tsayuwar da yayi a kanta yasa ta dinga jin tamkar ta saki fitsari a wando tuni hawaye ya soma d’iga daga idonta…..A nutse ya tsuguna gabanta yasa hannunsa ya dago fuskarta, sai kawai yaga hawaye na zirara!