MADADI Page 31 to 40

Ya jima yana kallonta da mamaki a fuskarsa, yace.”Kukan me kikeyi.”? Girgiza kanta tayi tace”Babu komai.”? Yace.”Akwai dalili ki fada min ko tsorona kikeji.” Ta d’aga kanta tana me rike hannunsa dake tallafe da fuskarta tace”Abbah dan Allah kada ka ‘kara wallahi ni kadai nasan abinda nake ji.”
Yaji tausayinta ya kamashi, yace”Ba zan sakeyi ba sai gurun ya warke sosai amma kiyi min alkawari idan nazo zaki bani goyon bayan da nake bukata…..Cikin rashin dubara da wayo tace”Allah nayi maka alkawari zan baka.” Yace”To nagode ina rokan Allah yayi miki albarka ya kuma barni tare dake sannan ya albarkace mu da zuria mai albarka.”
Shuru tayi ba tace amin ba babban burinta ya tashi ya bata guri.
Fuskarta ya tsirawa ido yana kallon karamin bakinta, ji yayi ba zai iya hakura ba dan haka sai ya shiga kusantar fuskarta da tasa, ta wani irintse idonta tana takure jikinta.
Hawayen dake ziraro mata ya shiga lashewa yana dan tsotsar kumatunta cikin wani irin salo na mussaman! Tayi kasa’ke! sa’kon na ratsa mata jiki.
kafin yasa bakinsa anata sai da ya tsotsi le’bunanta sosai sannan yayi dubarar kama harshenta ya shiga tsotsa tamkar alawa
Wani irin yanayi ta dinga ji a jikinta, jikinta ya mutu kasala duk ta dabaibayeta, sosai da sosai takejin dadin kiss d’in! ta dinga mutsu mutsu tana so ta tsotsi harshensa ta rasa yanda za tayi dan da tayi yunkuri kamawa sai ya janye nata ya rike yake ta tsosa kamar zai tsinke shi…….. hannunsa da ya riko fuskarta ta kama ta ri’ke tamau! tana wani lumshe ido hade da d’an gyara zaman da tayi……..Shi kuwa ganin ta saki jikinta bata turje-turje yasa ya cigaba da abinda yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
A ‘kalla! sun dauki kimanin mintina goma cikin wannan yanayi kafin su rabu da juna! idanunta dake lumshe ta bud’e tana kallonsa, sai yayi gaggawar mikewa dan saboda yanayin kallon da tayi masa yayi masifar tayar masa da hankali
Hanyar fita ya nufa, kamar shashasha ta bishi da kallo tana ji kamar ta dawo dashi su cigaba da abinda sukeyi(Ikon Allah ) zamewa tayi ta kwanta hade da daukar bargon daya ajiye mata ta rufe jikinta har fuskarta tana matse cinyoyinta sakamakon jin wani irin abu da gabanta ke mata tasa hannu a hankali a hankali tana shafa lebunanta tana wani lumshe ido…Wani irin yanayi take ji a jikinta wanda ta kasa tantance na menene? (Naja’atu ta fara fahimtar abunda ke da akwai) Da kyar bacci ya dauketa cikin wani yanayi mara dadi kafin gari ya waye kuwa ta farka ya kai sau uku dan data rintse idonta zata ganta tare da Abbas din rungume da juna suna abubuwa masu dadi da wuyar mantawa.
Dalilin da yasa kenan da asubah ta riga kowa tashi a gidan, cikin kasala da mutuwar jiki ta nufi toilet ta tu’be gabadaya kayan jikinta har pant bata bari ba dan tana jin danshi danshi a jikinsa shiyasa ta kasa yarda da tayi sallah haka ba tare da tayi wankar tsarki ba.
Wanka tayi kafin tayi bursh ta daura alwala ta fito wanda yayi dai-dai da shigowarsa dakin domin tashinsu kamar yanda ya saba.
Ganin ta fito daga toilet din ne ya sanya ya sauke ajiyar zuciya ba tare da yace komai ba ya juya ya fita.
Bayan ta kintsa jikinta sai ta shiga tashi yaran kamar koda yaushe, sai da ta tabbatar sun tashi sannan ta hau dadduma domin gabatar da sallah………….Yaran bayan sun idar da sallah cikin nutsuwa suka shiga gaisheta ta dinga amsawa cikin sakin fuska, ta kalli Saddiqa da fadin”Ya jikin naki?”? Saddiqa tace”Da sauki yanzu bana jin zafi sosai.” Tace “Dama ai Dr yace” zafin ciwon jiya da yau ne kawai insha Allahu idan kina shan magani zai warke.” Saddiqa ta mike ta nufi wardrobe dinsu da hannu daya take kokarin dauko musu inform tace”Ke maye haka? da ciwo a hannuki zakije skull.”? Saddiqa tace”Yaya Naja’atu kin san halin Uncle Aminu ko.” Tace”Komai halinsa dana sani dole ya daga kafa ki kwana biyu a gida hannuki ya warke tukkuna…..Suna wannan ta’kaddamar ya shigo dakin
Sai suka shiga rige-rigen gaisheshi kamar dai koda yaushe.
Ya amsa a nutse yana tambayarsu, a nutse tace masa wai skull za taje a haka.”
Ya kalli Saddiqan tare da fadin”Kiyi hakuri ki zauna a gida kwana biyu ki samu sauki sosai ni da kaina zanje na na fadawa ancle din baki da lafiya.
A sanyaye tace”To shikkenan Abbah….Naja’atu ya dan kalla yana so yayi magana sai kuma yayi shuru da bakinsa yana sk yaga iya gudun ruwanta kama hanya yayi ya fita daga dakin…….. kamar kuwa tasan abinda yake cikin zuciyarsa, ta mike da sauri ta fito da niyyar shiga kicin nan ta sameshi a kan kujera yana duba loptop. ganin ta nufi kicin din sai ya sauke ajiyar zuciya me sanyi yana rokon Allah ya tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu.
Tsaf ta kammala musu break fast ta shirya daning din gwanin sha’awa duk yana zaune yana kallonta yanajin wani farin ciki a cikin zuciyarsa ganin ta tashi da kuzari kuma yanayin tafiyarta ya daidaita yaji dadin hakan sosai da sosai.
Tare da yaran ta zauna suna break fast shi kuma yana zaune a inda yake da alama yana duba mihimun abu cikin loptop din dake gabansa.
Salim ne yayi sallama ya shigo palon, yana sanye da kananun kaya wanda sukayi masifar yi masa kyau! Salim dan gayu kwana biyu ya sakeyin fresh saboda yana samun kudi sosai gurin Kawun nasa, Salim yanzu har bleecing yake yayi wani uban haske ga sumar kansa tasha gyara sai kyalli take…..Naja’atu kasa dauke idonta tayi daga kansa sai murmushi takeyi wanda kana ganinsa kasan na farin cikin ganinsa ne..
Shi kuwa Salim ganin tana nema ta tona musu asiri yasa yayi gaggawar kauda kansa daga inda take, kai tsaye gurin Abbah Abbas ya nufa ya ritsina tare da mika masa hannu da fadin”Barka da asubah Kawu.”
Cike da kulawa ya bashi hannu sukayi musabaha yana amsawa tare da tambayarsa mahaifiyarsa…Yace.”Tana nan lafiya Kawu tace Ma na sake tuna maka da sa’konta.”
Yace.”Kada ta damu insha Allah zan baka ka kai mata.” Yace.”To godiya take Kawu….Cikin basarwa Salim ya kalleta yana dan ya’ke yace.”Antyna barka da asuba ina fata kin tashi lafiya.”
Naja’atu wani iri taji jin sunan daya kira dashi…Dauke kanta tayi tana ‘bata fuska tace”Barka dai.” Hakan da tayi sai ya faranta ran Abbah Abbas din yaji dadi data nuna rashin kulawarta a kan Salim din.
Salim ya kalli Mussadiq da fadin”Oya ku tashi mu tafi.” Mussadiq da Mufida suka mike sai ya kalli Saddiqa yace”Baby kefa?” Tace”Ciwo naji a hannuna.
Abbah Abbas yace “Yau saddiqa bata zuwa skull ta samu rauni a hannunta saboda haka idan kaje ka shedawa ancle dinsu abinda ke faruwa.
Yace.” Insha Allah Kawu.” Lokacin daya kama hanyar fita tare da yaran Naja’atu binsa tayi da wani irin kallo mamaki take sosai wai yau ita Salim ke kira da Aunty lallai Salim gaskiya ya bata mamaki.
Mi’kewa tayi jikinta a sanyaye ta nufi daki ta kwanta! ganinsa yanzu ya sake tayar mata da hankali sai taji duk ta tsani komai na duniya Abbah Abbas din ma taji bata son kallon fuskarsa….Saddiqa ce ta shigo dakin, ta zauna tana kallonta tare da fadin” Yaya Naja’atu Abbanmu yace.”Wai ki bani magani na.” Harararta tayi tace”Kamar baki san inda maganin naki yake ba duba dan Allah da girmanki da komai ake cewa a baki magani kamar wata kankanuwar yarinya.”