MADADI Page 61 to 70

Baba talatu ta mike tana goge hawaye da gefan zaninta ta shiga kicin ta dauko kunu cikin kofin silba ta ajiyewa mussadiq a gabansa tace”Dauki kunu kasa kaji ko ko zaku ci awara.” Mufida ta d’aga kanta tana share fuska, kicin din ta koma ta dauko awara me yawa a cikin silba ta ajiye musu a gabansu ta nufi dakinta ta rarraso saddiqar suka fito tare….Baba malam na kokarin fita su Naja’atu suka shigo gidan sai ya koma ya zauna..Baba talatu kauda kanta tayi daga inda suke Baba malam ya nuna musu gefan tabarmar da yake zaune….Naja’atu kamar ba’kuwa taje ta zauna munira ta zauna a kusa da ita suka shiga gaishe dashi…..Cikin kulawa ya amsa musu suka juya suna gaishe da baba talatu ciki ciki ta amsa hankalinta na kan mussadiq tana gyara masa awarar dake gabansa
Shuru gurin yayi naja’atu sai kokawa take da zuciyarta dan kuka ne yake kokarin kwace mata ganin yanda iyayenta nata keyin baya baya da ita sai kace basu santa ba….Abbah magaji ne ya shigo gidan da shirin tafiya kasuwa….Naja’atu tunda ya shigo gabanta ke faduwa ta kasa hada ido dashi saboda tsabar tsoro murya na rawa take gaishe shi ba tare daya kalleta ba ya amsa kana ya shiga gaishe da iyayensa…Baba malam yace”Dama inaso mu tattauna maganar yaron nan bashir da kai.” Kai tsaye yace.”Malam bana cikin wannan al’amarin sabida bana so nan gaba wani abu ya faru sunana ya fito idan Naja’atu ta za’bi Bashir ya zama abokin yaruwarta to ina mata fatan alkairi.” Baba malam ya ‘bata rai yace.”Wannan wace irin magana ce ka keyi meye aibun yaron? kai tsaye yace”Bashi da hali mai kyau ni na gani da idona kuma na sheda shiyasa nace babu ruwana.” Malam yace.”Komai munin halinsa muna masa fatan shiriya akwai matasa da yawa wad’anda suka zama wani abu a duniya bayan a can baya sunyi gagara Allah ya shiryesu sun koma salihai masu tsoron Allah saboda wannan dalilin naka ba zai hanamu mu dauki naja’atu mu bawa yaron nan ba domin ita shiriya ta Allah ce muna addua Allah yasa sanadiyar auran nan ya gyara kusakuransa.” Abbah magaji ya sauke ajiyar zuciya had’e da mikawa da niyyar tafiya yace”To Allah yasa haka shine yafi alkairi ni zan wuce kasuwa.” Baba talatu tayi masa fatan dawowa lafiya baba malam ya mike suka fita suna sake tattauna maganar………To Bash bai zo gidan ba sai bayan sallahr azuhur tukkuna sai da ya gama yawace yawacen sa tukkuna ya shiga unguwar lokacin Munira ta shirya tsaf shi take jira ita kuwa naja’atu cike take da alhini da damuwa dan har kusan rungume juna sukayi ita da Bash din sabida tsabar shau’ki da sha’awar junansu da suke….Bash ya dauki daya daga cikin manya manyan wayoyinsa ya bata tare da sa mata sabon sim card tayi ta masa godiya kana ta rakashi har cikin gidan alhaji yayi musu sallama suka fito suka shiga gidan malam…Bash gurin malam kawai ya samu cikakkiyar kulawa baba talatu kam kin fitowa tayi tana daki ta amsa gaisuwarsa har suka fita daga gidan bata fito ba.
Naja’atu yini tayi a kwance dan bayan tafiyarsu Bash din kasa zama tayi gidan malam sabida babu fuska gurin matar gidan sai ta tattara ta bar gidan ta nufi gidan alhaji dama duk wani kayanta na gidan, ta shiga daki ta kwanta cike da damuwa gabad’aya halin ko in kula da baba talatu take nuna mata shine ya tsaya mata a rai.
Sai yamma can ta fito palo ta zauna kusa da hajia suna d’an ta’ba hira hajia Abu macace mai mai da d’an wani nata kwata kwata bata ‘kullaci naja’atu ba wai dan ta’ki zama da d’anta gabad’aya ta dauki a’lamarin a matsayin qaddara.
Kamar koda yaushe hakane ya kasance bayan sun taso daga kasuwa kofar na’isa suka nufa shida Salim dake driving dinsa, kasancewar lokacin sallar magariba yayi yasa basu shiga gidan ba sai bayan da suka gabatar da sallar tukkuna suka nufi gidan harda Alhaji wanda suka hadu a massalacin….Naja’atu ce kad’ai a palon hajia ta shiga sallah! Alhji gaba yayi Abbah Abbas da Salim suka tsaya a gurin Hajia Rabi suna gaisawa…Naja’atu na ganin shigowar Alhaji cike da ladabi ta gaishe shi ya amsa cikin kulawa had’e da kokarin hawa samansa……..gyara zamanta tayi ta cigaba da latse latse a wayarta ita da Bash suke hira sai zantukan soyayya yake mata tana jin dadi….Hancinta ne ya shaqo mata kamshin turaransa, tayi saurin dago kanta, wayar ce ta kusa faduwa tayi saurin ri’kewa gabanta ya wani fad’i! shaf ta manta yana zuwa gidan da irin wannan lokacin da tuntuni ta bar palon dan bata kaunar abinda zai had’a fuskarta da tasa…Kallo d’aya yayi mata ya kauda kansa yana bin palon da kallo babu hajia a gurin…Ya juya bayansa yana kallon Salim daya shigo yace.”Haura sama kacewa hajia gani nazo zamu gaisa ba zama zanyi ba.” Salim da sauri yace”To Kawu.” Saman ya nufa yana dan satar kallon inda naja’atu take zaune.
Kujera ya samu ya zauna ba tare da ya kalleta ba, ita kuwa gabadaya ji tayi ta muzanta simi-simi ta mike da wayar ta ta nufi dakin da take jikinta duk ya mutu ta rasa me yasa Abbah Abbas keda kwarjini mutukar yana guri takan rasa karsashi da nutsuwar zuciya…Daf da zata shiga dakin taji gyaran muryarsa hade da kiran sunanta, Gabanta na faduwa ta juyo amma bata yarda ta hada ido dashi ba, Yace.”Baba Larai ta kawo miki kayanki ko.” Kanta ta d’aga masa, Yace.”Okey ki duba da kyau abinda baki gani ba naki sai kiyi magana a kawo miki.” A sanyaye murya na rawa tace”To.” ta juya da sauri ta shiga dakin, zama tayi gefan gado tare da tsirawa fuskar wayar hannunta ido! shin wai shi Abbah Abbas din nan wane iri ne? tayi masa laifi amma sai tausasa mata yake kamar ma yana nuna abunda tayi bai dameshi ba, tausayinsa taji ya kamata sai ta kwanta tana hawaye tasan dai daurewa kawai yake a yanda yake da son ‘ya’ya dole yaji ciwon lalacewar cikinsa aikuwa tunda taga bai dauki abin da zafi ba zata yi masa text ta bashi hakuri ta kuma tabbatar masa da cewar ita bata sha komai ba dan ta zubar masa da cikinsa cikin ya zube ne sakamakon irin ‘bakar wahalar data sha lokacin zuwanta jos…..Da yake tana da numbarsa a kanta sai kawai tasa a sabuwar wayar tata tayi serving ba tare da tunanin komai ba ta shiga rubuta masa text kamar haka.
_Assalamu alaikum Abbah Kayi hakuri da abubuwan da suka faru tsakanina da kai wallahi nima ba’a son raina ba hakan ya faru kayi hakuri ka yafe min. sannan inaso in tabbatar maka da cewar wallahi ban sha komai ba domin na zubar maka da ciki ba Allah ne ya aiko da tsautsayi a kansa kayi hakuri da abunda Allah ya qaddara a tsakaninmu ina mana fatan alkairi tare da fatan Allah yasa haka shine yafi alkairi.”_
Tura text din tayi ta ajiye wayar a gefanta tana adduar Allah yasa idan ya karanta yayi mata kyakykyawar fahimta kuma yace ya yafe mata
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_