MADADI 1-END

MADADI Page 61 to 70

 51

 Naja’atu Kasa fitowa palon tayi har sai da ta tabbatar da cewar ya tafi sannan ta fito da sanyayyan jiki ta zauna kan kujera tana sake duba text din data tura masa….Hajia ta kalleta a tsanake tace” Naja’atu ki kwantar da hankalinki kinji ko kada ki damu da yanayin rayuwar da Allah ya shirya miki mu bamu dauki al’amarin da zafi ba ki saki jikinki a nan gidan komai kike bukata ki fad’a min insha Allah zan share miki hawaye da nan gidan da gidan Malam Sani duk d’aya ne zaki zauna a hannuna har sanda Allah yasa kika ‘kare iddarki sai kiyi aure ga dukkanin mijin da Allah ya za’ba miki gabad’ayanmu muna yi miki fatan alkairi da adduar za’bi nagari.” Kasa daurewa tayi ta kalli Hajian tana share hawaye tace”Hajia nagode sosai da karamcin da kukayi min nima ina neman afuwarku a bisa abinda da ya faru kuma inaso in tabbatar miki da cewar wallahi ban zubar da ciki da kaina ba tsautsayi ne ya ritsa dashi koda can da nake ikirarin zubarwa bazan iya ba kawai dai ina fad’a ne amma wallahi bani na zubar ba wahala ce tasa ya zube.” Hajia Abu tayi murmushi tana girgiza kanta tace”Kada ki damu Naja’atu kinji na amince da maganarki kan cewa baki zubda ciki ba, idan Allah ya qaddara zamansa a jikin ki komai abu sai kin haifeshi sannan kuma zaki iya haifarsa ya d’auke abinsa sabida haka ki kwantar da hankalinki dama can Allah bai nufa abinda ke cikin naki zai taka kasar duniya ba muna rokon Allah ya mayar muku da alkairi gabadayanku. Cikin shehshekar kuka ta amsa da ameeen..Hajiya tace”Ga abinci can yanzu Magajiya mai aiki tazo ta ajiye yana da kyau kije kici ki kwanta ki samu nutsuwar zuciya.” A sanyaye ta mike ta nufi inda kololin abincin suke a ajiye.

To har tayi shirin bacci ta kwanta ba taga amsar sa ba, sai taji rashin dadin abin tana tunanin ko bai yarda da maganar ba koda yake dama tasan da kyar idan zai yarda da cewar ba ita ta zubar da cikin ba ita dai Allah yaga zuciyarta bata zubar da ciki ba duk wanda ma zai zargeta ya zalince ta( Magana zarar bunu naja’atu ke kika furta sai kin zubda ciki dan haka da yawa mutane zasu karyata maganarki ta cewa bake kika zubda shi ba)

Video call d’in da Bash yayi mata ne yasa ta manta da damuwar dake damunta suka shiga soyewa ita da masoyinta, Tana kallon Bash daga shi sai gajeran wando faffadan kirjinsa mai dauke da gashi ba’kikikirin na kara d’imautata sha’awa da sonsa na ‘kara ninkuwa a zuciyarta, to shima Bash din nasa ‘bangaran hakane dan shi al’amarin nasa ya fi nata tsanani jijiyarsa wacce ta mi’ke a cikin gajeran wandonsa ya shiga nuna mata yana lumshe mata ido wai ta taimaka masa ta tu’be kayanta ya dinga kallonta a haka ko zai samu satisfaction! a tsorace! ta kashe wayar gabanta na fad’uwa! Gaskiya Bash yana da katuwar jijiya ta tsorata mutuka da ganin girmanta jikinta ya shiga kyarma tana tunanin ranar da zai burma mata ita a jikinta…Bash kuwa ganin ta kashe data ne yasa a gigice ya shiga kiran wayarta kin d’agawa tayi sabida tsoro anya kuwa ba zata taka masa burki ba kuwa kamar abinda yake yi yayi yawa bashi da kunya ko kadan…Maganar Munira ta tuna inda take ce mata sai tayi da gaske a kan bash din saboda idan ta tsaya wasa to ‘yan matansa dake rububinsa zasu kwace mata shi, tana son Bash mutuka amma kuma bata so ya dinga nuna mata zulamarsa a fili sai taga kamar sha’awarta yake ba sonta yake ba, amma kuma a duk sanda ta tuna da kalaman soyayyar sa da al’kawarikan da yake mata sai taga tamkar tafi kowace mace dace da samun masoyi mai sonta da kaunarta dan Allah….Pillow ta rungume tana sauke numfashi a hankali a hankali bacci ya dauketa mai cike da mafarkin Bash da soyayyarsa.

Kamar dai yanda ya saba zama a palo duk daran duniya ya duba loptop to yauma hakane yana zaune a palon shi kadai da loptop a cinyarsa yana dubawa akwai sa’konni da yawa sabida ya kwana biyu bai duba ba shiyasa hankalinsa ya dauke sosai ko tunanin Halisa bayayi wacce take can tana jiran shigowarsa dan a matse take da sha’awa dalili koda suka je saudia tsayin sati biyu da sukayi sau biyu kacal ya kusanceta al’amura suka rikice shikkenan ta rasa gane kansa idan ta ganshi a kwance taje ta nema shi baya bata had’in kai sai yace ta rabu dashi da abinda ya dameshi idan ta tsananta sai yace shifa yazo garin ne domin ya kad’aice da Ubangijinsa ba jima’i ne ya kawo shi ba. Hakuri takeyi ta kyaleshi amma gaskiya tana cutuwa, to ganin sun dawo gida ne yasa ta bankad’i magungununta na mata ta tsumu sosai da sosai tana adduar Allah yasa ya bata had’in kai ta fito daga dakinta cikin ‘yar mitsitsitar riga cinyoyinta duk a waje ta fesa turaran da yake saurin dauke masa a hankali…Kusa dashi tazo ta zauna tana shafa gadan bayansa had’e da sumbatar gefan fuskarsa….Ko gezau beyi ba hankalinsa na kan loptp dinsa..Sai kawai ta shiga kokarin dauke masa loptop din daga cinyarsa, tsawa! yayi mata da fad’in ta matsa daga kusa dashi ta kyaleshi aiki mai muhimanci yake.” Halisa ta shiga mamakin abunda yayi mata! A fusace! tace”Wai dan Allah me kake nufi dani ne? Na lura ka tsiro da wasu halaye wanda ban sanka dasu ba shin ni me ya shafeni kuma da kake kokarin huce fushinka a kaina? tunda yarinyar nan Naja’atu ta aikata maka abu kake jin haushina sai kace nice nayi maka kana kokarin danne min hakkina haka akeyi ? kafi kwana goma baka neme ni ba ko na nema ka baka kulani ya kake so nayi.” Murya na rawa ta karasa maganar.

Shuru yayi mata ya cigaba da dube dubensa…Halisa ta sha’ka sosai da sosai ta dinga sakin maganganun da ranta yake so tana kuka amma d’an tahalikin nan ko kallonta baiyi ba cike da tsantsar tashin hankali ta bar gurin, ta shiga dakinta ta zabga uban tagumi tana tunanin masifar data rikito mata, to wai shin me hakan yake nufi ne?? Zuciyarta tace Asirin da ki kai masa ne ya karye sai kin sake wani!!! Idan haka ne kuwa tabbas ba taga ta zama ba! za tayi iya hakura da duk wani hukunci da zaiyi mata amma banda horon hana ta hakkinta gaskiya ba zata iya da wannan ba a halin da take ciki tana ji tamkar taje ta janyo shi dole yazo yayi mata dan yanda take tsiyaya Allah ne kawai zai mata magaji…Kwanciya tayi tana kuka takaici kamar ya kasheta, da dai ta kasa hakura sai ta mike kamar bugaggiya ta koma polon nan ta tarar babu shi a gurun ya kashe fitila yayi shigewarsa dakinsa yasa key…bugu ta dinga yi yana jinta ya shareta dan mugun haushinta yake ji yana ganin kamar itace tayi masa laifi ba Naja’atu ba!( Humm! Halisa ashe tsugune bata kare miki ba koda yake hausawa nacewa idan zaka gina ramin mugunta ka gina daidai misali dan watarana kaine zaka fada ciki)….. Tsaf yayi shirin baccinsa ya kwanta kan bed da wayarsa a hannunsa yana kokarin kashewa ya lura da text din Naja’atu, a nutse ya shiga yana dubawa, Ya jima yana nanata karanta text din yana mamakin hakurin da take bashi, to meye ma’anar hakurin da take bashi….? Ciki dai yasan ita ta zubar masa saboda ita da kanta ta tabbatar masa da hakan lokacin yana saudia sai yanzu kuma da bukatarta ta biya tazo tana bashi hakuri! Baya tunanin zai iya zama da kowace irin mace mutukar zata salwantar masa da albarka da Allah ya bashi komai son da yake wa mace zai iya rabuwa da ita har abadah…Najaatu tayi nasara a kansa sai dai kawai yace Allah yasa ka masa….Numbar yabi ya rubuta mata amsa kamar haka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button