MADADI Page 61 to 70

_”Babu komai kada ki damu magana ta wuce a gurina.”_
Yana tura text din ya kashe wayar tare da gyara kwanciyarsa ya rufe kafafunsa da bargo yana addua a cikin zuciyarsa.
Halisa da kyar ta iya samun bacci a daran koda asubah ma da ya shigo dakin so tayi ta ri’keshi ta karya masa alola yayi gaggawar yaki ce ta daga jikinsa ya fita daga dakin, shifa gabad’aya sha’awar sex din a ka cire masa daga cikin ranshi tunda abun nan ya faru ya daina jin sha’awar komai na rayuwa abinci ma dan ya zama dole ne yake tsayawa yaci…..Halisa ba tare da tayi yunkurin tashi taje tayi alwala ba ta dauki wayarta ta shiga kiran Aminiyartata Ramlatu…..Yaya Ramlatu na kokarin tada sallah taji ringing din wayarta sai da gabanta ya fadi kafin ta dauki wayar tana dubawa cikin zuciyarta tana fadin”Allah yasa ba mutuwa akayi ba kiran waya da asubah….Ganin numbar Halisa yasa gabanta ya sake faduwa da sauri ta kara wayar a kunnanta tare da zama a bakin gadonta.
Halisa sai da taci kukanta ta koshi tukkuna ta warwarewa Ramlatu abinda ke faruwa!!! Ramlatu tace”Ni wallahi na dauka wani gagarimun abune duk kin sa gwiwata ta sage.” Halisa tace”Ni kam gagarimun abune a gurina Yaya Ramlatu ke naga dama ai wannan al’amarin kamar be dame ki ba kina kallonmu muna fad’i tashi gurin shaye shayen magani sai da kiyi ta ingiza mu kina zaune a guri daya ni yanzu na kira ki a waya ne muyi shawarar yanda za muyi dan wallahi gabakid’aya d’an uwanki ya rikice min na rasa gane kansa da gindinsa tunda al’amarin nan ya faru shikkenan ya sanja hali sai kace ni nayi masa laifi…..Ramlatu tace”Ni kam wannan masifa ta Abbas ta isheni wallahi haba jama’a ayi tayi masa magani ana jifansa da asiri kamar ba’a jikinsa ba daga zarar aiki yayi kyau sai warware shin yanzu ya kike so ayi dan wallahi gabadaya tunani na ya kare kan al’amarin nan.”
Halisa tace”Nifa babban abinda yake da’ga min hankali kin had’a shimfida dani da yake idan babu wannan harkar ina tunanin zan iya bin maza.” Yaya Ramlatu tace”Subahanallahi!( Duk macan dake yawace yawace na bin bokaye da malaman tsubbu watarana sai tayi tunanin aikata zina koda kuwa mijinta na dauke mata dukkanin lalurarta akwai sanda wani bokon zai bukaci kasantuwa da ita domin biyan bukatarta Allah ya tsare mu ya kare mu daga sharrin duniya) Yaya Ramlatu ta cigaba da cewa” Haba Halisa kada laifukan naki suyi yawa mana ki daina maganar aikata zina zaki zubar mana da mutunci abinda za’ayi yanzu idan ya fita kasuwa ki fito da wuri muje gidan ‘Yar Sa’adu ko za’a dace ta baki maganin da zaki dinga sa masa a abinci yana ci wanda zai dinga tayar masa da sha’awa kinga dole idan sha’awa ta dameshi ya kusanci inda kike.”
Halisa ta share hawayenta tace”To wannan shawarar taki tayi ma’ana aikuwa yana tafiya kasuwa zaki gan ni a gidanki.
Sallama sukayi da juna Halisa ta d’an ji sassauci a zuciyarta ta mike ta nufi toilet domun daura alwala lokacin garin hr yayi haske.
‘Bangaran Naja’atu kuwa bayan ta idar sallahr asubahi kamar yanda ta saba sai ta kunna wayarta tana kunnawa kuwa text ya shigo hannu na rawa ta shiga tana dubawa, wani irin farin ciki ne ya lullubeta ganin amsar da ya bata, sai taji hankalinta ya kwanta sosai dan dama bata so kwata kwata ya ‘kullace ta ko kuma ya dinga kallonta a matsayin wacce ta aikata masa mummunan ta’addanci.
To kamar yanda Halisa ta fad’awa Yaya Ramlatu hakane ya kasance maigidan da yara na fita itama ta kintsa jikinta a gurguje ta fito ta samu baba Larai na goge a palo tace mata za taje unguwa, Baba larai tayi mata fatan dawowa lafiya ta juya ta cigaba da aikinta.
Ba suja wani dogon lokaci ba suka nufi gidan ‘Yar sa’adu yau ma kamar koda yaushe ‘Yar sa’adu na zaune a gurin zamanta mata sunkewayeta suka shiga gurin da sallama a bakinsu suka nemi guri suka zazzauna ana gaisawa….’Yar sa’adu na murmushi tace”Lallai yau tunda na ganki nasan akwai bayani da kwana biyu kinyi min yaji kin daina zuwa ina fatan dai ba wata matsala kika kawo min ba.”
Halisa tace”Matsala babba na kawo miki wallahi kuma inaso ki share min hawaye na.” Yar sa’adu tasa dariya tare da bawa ta gefanta hannu suka tafa tace”Lallai to ina sauraranki nasan dai zance gizo baya wuce na ko’ki hummm! maza kenan maza mutanan mu idan babu ku babu mu hahahaha.”! d’akin ya d’auki dariya jin irin kirarin da ‘Yar sa’adu tayi wa maza!
Halisa ta shiga zayyanewa ‘Yar sa’adu abinda yake tafe da ita, ‘Yar sa’adu murmushi tayi tace”Rabu dashi zanyi miki maganinsa dama wani sa’in ai haka suke idan iskancinsu ya motsa! humm! babu komai Allah ya taimake ki kinzo akan ga’ba! akwai wani *’Dan anace* dana samo shi daga Garin *Jega* wannan maganin ba kowa nake siyarwa dashi ba kema dan mun saba dake ne tsohuwar costomar ce ke shiyasa zan siyar miki dashi amfani d’aya zakiyi dashi ki gigita masa tunani wallahi sai ya zama tamkar mahaukaci ke zaki sha mamakin aikin da maganin nan zaiyi miki mutukar kin fara amfani dashi a kan tsari.” Halisa da sauri tace”Na amince da maganarki ‘Yar sa’adu dan duk maganin dana ke siya a gurinki babu na banza ki fada min kudin maganin ko nawa ne zan biya.”
Yar sa’adu tace”zaki bani dubu dari da hamsin hakan ma sauki nayi miki wallahi.” Halisa babu neman ragi tace”Bani accont numbar naki sai na sa miki kudin dan yanzu kudin jakata basu kai haka ba.
‘Yar sa’adu ta bata accont numbar dinta a take a gurin tasa mata kudinta ita kuma taje ta dauko mata maganin cikin wata ‘yar mitsitsiyar kwalbar fiyafiya maganin ba’kikkirin dashi. Yar sa’adu tayi mata bayanin yanda za tayi amfani da maganin sannan sukayi mata sallama suka tafi.
A daran ranar Halisa ta dinga binsa a jiki a jiki tana marairaice masa tana kuka da bashi hakuri wai idan laifi tayi masa ya gafarce ta bai kamata ya dauki fushi a kanta ba tunda ba ita tayi masa laifi ba, to shima ganin ta damu yasa ya ji tausayinta ya kuma yi tunanin abinda yake mata bai kamata ba tunda ba ita tayi masa ba to yana da kyau ya daina shiga hakkinta….biye mata yayi suka nufi dakinta anan ta baje kolin iskancinta dama already ta tusa *’Dan anace* wannan bakin maganin na gurin ‘Yar sa’adu a can cikin matuncinta ta turmutsa maganin….Abbah Abbas ya afka suka dunga suburbudar juna Halisa taji masifar dadin maganin dan har matseta yayi kuma ta lura shima mijin nata yana nishadantu wa kwarai da gaske…..sai bayan sun samu gamsuwa ne ya zare jikinsa domin zuwa ya tsarkake kansa anan ne ita kuma Halisa taji tamkar an barbad’a mata barkono a gabanta, hannu tasa a gurin cikin wani irin jin radad’i ta sanya ‘yar ‘kara tana kokarin yunkurawa ta mike zaune nan ma taji tamkar an caccaka mata allurai cikin gabanta da wani irin sauri ta koma ta kwanta tana zazzare ido gabanta sai wani irin fad’uwa yake………………
*???????? WAI!!! NI FAD’IMATU !!! YAU HAR SAI DA NA RASA VOICE D’IN WANDA ZAN SAURARA AMMA DAI NAFI SAURARAN VOICE DIN ‘KAWATA MC
ALLAH YASA NA FADI SUNAN DAIDAI???????? SISTAR AISHA ABDULLAHI ???????? NA SAURARI VOICE DINKI HAR YANZU BAMU SAUKA DAGA MAUDI’IN DA MUKE KAI BA MUNA CIKIN MAUD’UIN LITTAFIN MADADI???? GASKIYA NAYI DARIYA SOSAI DA SOSAI JIN COMMMENTS DIN KI NA KUMA KARA TABBATAR DA CEWAR ABBAH ABBAS NA DA MASOYA MUTUKA MOMMYNA TA NIJAR ITAMA TUN SHEKARAN JIYA MUKE FAFATAWA DA ITA KAN AL’ AMURAN DA SUKE FARUWA TSAKANIN NAJA’ATU DA ABBAH TO YAU MOMMYNA DA DUK WANI MA’KIYIN HALISA PEGE NAKU NE KUYI RAWA KU JUYA DOMIN KUWA HALISA ZATA SOMA GIRBAR ABINDA TA DADE TANA SHUKAWA………….*