MADADI Page 61 to 70

Yace.”A ina kika samo shi.”? Shuru tayi gabanta na faduwa! Tambayar ya sake maimaitawa babu rahama ko kadan a tare dashi!…..Halisa dake neman mafita tana kuka ta shiga fad’a masa cewa a gurin wata matane da Yaya Ramlatu take kaita gurinta….Jin ta kira sunan Ramaltu sai abin ya bashi mamaki yace.” Me yasa ko Yaya Ramlatu a cikin shirmen ki? ko dama ita take saki kina shaye shayen maganin mata bana son kiyi mata sharri dan ganin matsala na kokarin afkuwa dake.”
Tace”Wallahi tunda nake ban san hanyar gidan boka da malami ba sai ta hanyar ‘Yar uwarka Ramaltu kome nakeyi itace take d’ora ni a hanya.” Abbah Abbas bude bakinsa yayi kawai yana kallonta yace.”Halisa da bakinki kike fad’a min kina zuwa gidajen bokaye.”? Wani irin kuka ya kwace mata tace”Abbah Mufida ka gafarce ni wallahi ba laifina ne ni kad’ai ba Yaya Ramaltu itace take sani a gaba muyi komai tare ni yanzu babbar matsalata wannan matsalar data tunkaro ni!
Girgixa kansa kawai yake yana mamakin al’amarin! ikon Allah ‘Yar uwarsa uwa daya uba d’aya itace ke cutar dashi da iyalinsa yanzu meye amfanin d’ora Halisa a turba mara kyau da Ramlatu keyi! menene amfanin cutar dashi da takeyi? me yayi mata a rayuwa da har zata bada goyan baya a cutar dashi idan halisa tayi masa asiri matarsa ce zata iya aikatawa amma ita saboda k’arfin zumunci da ‘yan uwantaka bai kamata tayi masa haka ba
Ya jima yana kallonta gabadaya kansa ya kulle ya rasa wane irin tunani zaiyi dangane da wannan mummunar maganar da yaji daga bakinta wai Ramlatu ‘Yar uwarsa uwa daya uba daya itace take jagorantar matarsa domin xuwa gurin bokaye a asirce shi….Halisa ganin yanda ya zuba mata ido yana mata wani irin kallo yasa takasa tsayar da hawayen dake zubo mata sai yanzu ta fahimci wautar da ta tafka gabadaya bata cikin hayyacinta shiyasa tayi su’butar baki ta fad’a masa abinda suke shukawa shin yanzu idan yayi bunkice ya tabbatar da gaskiyar maganarta da wane ido zata kalleshi na farko dai ita da kanta ta fad’a masa tana zuwa gurin malamai da bokaye babu wanda yayi mata sharri ballantana ta kare kanta…Sunkuyar da kanta tayi ta cigaba da kuka tana murza yatsun hannuwanta!….
Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke ya Mi’ke tare da duba agogon dake daure hannusa yace.” Idan kina iyawa ki tashi muje asibiti domin a duba a ga abinda keda akwai amma ki sani bani kika cuta ba kanki kika cuta wallahi idan kina zuwa gurin boka domin ki mallake ni ‘Karyar ki tasha ‘karya ni ba irin mazajen da mata ke kaiwa gurin bokaye bane wai ko kunyata baki ji ba da bakin ki kika fada min cewar kina zuwa gurin malamai! shin me na rage ki dashi? meye bana miki a rayuwa zaki dinga biye biyen bokaye me kike nema a duniyar nan wanda bana miki? Halisa tayi shuru sai kuka take….Ya girgiza kansa yana jin wani irin takaici da mugun haushinta yace.”Kada kiga na rabu da Naja’atu ki dauka zan zauna dake ke kadai ‘Karya kike koda baki kaini gurin malamanki ba sai na sake aure kuma budurwa zan aura in yaso sai ki sake d’aura d’amarar kai sunana gurin bokayenki. Sannan kuma maganin banza da kike sha a kaina kada ki daina kanki kike cuta bani ba.” Halisa kuka kawai take tana bashi hakuri wai wallahi tsautsayi ne ita bata kaishi gurin malami dan a cutar dashi ba!
Cikin tsawa mai tafe da hantara yace tayi masa shuru domin kwata kwata shi ba zai saurari maganarta ba da bakinta ta fada ba wani shege ne yayi mata qazafi ba. Shuru tayi kamar ruwa ya cinyeta hawaye sai tsiyaya yake a kuncinta tana jinsa yana ta zabga mata cin mutunci tayi ‘kus! da bakinta addua ma take ka da yace ya saketa!! Da zai fita daga dakin a fusace! yace.”Idan kinga dama kina iya fitowa na kaiki asibiti ba dan halinki ba.” Yana gama maganarsa ya fita daga dakin rai a ‘bace!
Sosai Dr Sa’adatu ta shiga tsananin tashin hankali ganin abinda ya zazzago daga cikin matuncin Halisa dake kwance a wani hado kafafunta a bud’e! Dr Sa’adatu kasa aikin tayi ita kadai sai da ta kira ‘Yar uwarta suka zo suna ta wagewa Halisa kafarta suna haska headquarter d’inta da wata ‘yar ‘karamar fitila irin tasu! Dr Na’ima ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Halisa da cinyoyinta suke rawa tsabar tension hawayen ma sun daina zuba sai zazzare ido kawai take…..Dr Na’ima tace”Gaskiya Hajia Halisa kin bani mamaki wallahi! yanzu da girmanki da shekarunki kike aikata aiki irin na matasan yara kefa uwace ke zakiga yara na aikata abu mara kyau ki hanasu Fisabillilahi yanzu abinda kikayi ya kamata? ina amfanin cushe cushen maganin mata da kukeyi? kullum maganar da mukeyi kenan a kafafan sadarwa kancewar mata su daina irin wannan kwamacalar saboda muhimancin virginal d’insu ya wuce ace su had’a shi da komai! Guri ne mai muhimanci a jikinki mace da ya kamata ta mutuntuna shi amma saboda cutar kai kawai sai kuje ku dinga siyan maganin da baku san da wace tsiyar aka had’ashi ba kuzo ku cusa a matuncinku wai duk dan ku mallaki namiji humm! wannan zalintar kaine dan a yayin da wata matsala ta afku dake shi wanda kikeyi dominsa bazai saurareki ba karshe ma kina zaune ya dallo miki amarya sabuwa dal kuma baki isa ki hanashi ya aikata abinda yake so da ita ba….Yanzu dan Allah wa gari ya waya? Hajia Halisa kin dade kina sake saken maganin mata a gabanki ba tare da kina tunanin wata matsalar ba sai gashi kuma lokaci guda matsalar ta afko miki a sanda bakiyi tsammani ba……Dole na sanar miki da abinda ke faruwa dake hajia cikin tsokokin naman dake gabanki wani bangare ya samu nakasu sakamakon cushe cushen maganin da kike yasa naman gurin ya zazzago ya fito wanda idan ba’ayi da gaske ba to ruwan dake a fita a gurin zai iya janyo miki shiga matsala babba dan gurin zai iya fitar da tsutsa ba tare da kinyi tsammani ba! amma yanzu munyi kokarin mayar da tsokar data fito insha Allah akwai magungunan da zamu rubuta miki mutukar an siya kuma kina amfani dasu a kan ‘ka’ida wannan ruwan dake fita a jikinki zai tsaya kuma wannan abun daya fito zai koma mazauninsa amma akwai sharad’i kan cewar maigida zai daina kusantarki har sai mun tabbatar da cewar gurin ya daidaita sannan sai ku koma mu’amular aure kamar koda yaushe! Sai kuma shawarata karshe da zamu baki dake da masu aikata hakan dan Allah ku daina ba lallai sai ta wannan hanyar bane zaku mallaki mazajenku kuma ku daina yarda da rantse rantse da dik wata mai magani za tayi muku akan ko wane irin maganin da zata baku tace kusa a gabanku. duk macen da tayi sabo da cushe cushen magani a gabanta to babu shakka tana tattare da dana sani anan gaba.
Halisa kunyar duniya ce ta isheta Yara ‘kananu sun gane mata sirrinta suna farfada mata maganar da suka ga dama! kai gaskiya bata ta’ba nadamar rayuwa ba irin ta yau! tayi data sani yafi sau dari a cikin zuciyarta kuma sai yanzu tagane wautarta ta kuma gane mugunta Yaya Ramlatu take mata ai itama macace me yasa koda wasa bata ta’ba yarda ta siyi magani tayi amfani dashi ba, sai dai ita tayi ta ingixata tana siya da kudi mai tsada gashi yanzu matsala mai muni ta afkar mata ita tana gefe guda babu abunda ya dameta….Cike da kunya ta mike zaune tana gyara daurin zaninta gabadaya ta kasa had’a ido dasu sabida kunya su kuwa da yake akan aikinsu suke sai bayani suke mata suna gargadinta akan ta daina abinda take aikatawa domin cutar da kanta take..