MADADI Page 61 to 70

*Littafin na kudi ne..!*
Koda zaki ganshi a gruop to na sata ne idan kina bukatar karanta book din ga yanda abin yake…Vip gruop#600 normal gruop#300 account 0542382124…Binta umar gtbank…Idan kati zaki turo kiyi min mgn ta whasap da wannan numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*MANZIR _ALWAFIR ABUJA????????*
_*Sun tanadarwa da mata kayan gyaran jiki masu kyau da inganci magungunansu babu almundahana a ciki mutukar kika fara amfani da ingantattun magungunan company manzil alwafir to ba zaki daina ba saboda ingancin magungunansu ko wace matsala kike fama da ita mutukar ta shafi zamantakewar auranki manzil alwafir zasu share miki hawaye da akwai gruops na mussaman da suka bude domin taimakon mata masu fama da matsaltsalo a gidan auransu idan kanki na cikin duhu mutukar kinyi rijistar dasu to kukanki ya ‘kare idan kina bukatar kiyi rijistar sai kiyi magana.*_
53
To koda Halisa ta kira Yaya Ramlatu a waya ta sanar mata da halin da take ciki, Ya Ramlatu sosai ta shiga tashin hankali mutuka domin a yanda Halisan take kuka tana fad’a mata abinda ya sameta ko waye dole ya tsorata sannan kuma hankalinsa ya tashi…Da yake mijinta ya dawo kuma itace da girki yasa ba taje gidan a ranar ba sai dai kullum tana kiranta a waya tana tambayar ta yanayin jikin nata……..To da sauki dai za’ace dan Halisa ta shiga taitayinta sosai da sosai kuma bata wasa da shan magani da wanda akace ta dinga sawa a cikin headquarter din nata kullum sai tasa sau uku a rana shiyasa al’amarin yayi sauki dan ruwan dake fitowa ya ragu sannan kuma abinda yayi tsiro fito ya koma amma dai duk da haka idan tasa hannunta tana ta’boshi sai dai ba kamar kwanaki uku da suka wuce ba….
Gabad’aya Halisa tayi sanyi a gidan kullum tana daki a kwance tana tunane tunane tana zubda hawaye! Baba larai da yaran sai da suka fahimci cewar matar gidan na cikin damuwa dan duk irin iko da isar da takeyi a gidan ta rage ko magana za tayi musu cikin sanyin murya take…Shi kuwa Maigidan sabgar gabansa kawai yake yi dan a cikin kwanakin al’amuran sa suka sake bunkusa Ya samu wasu manya manyan kwangila daga gomnati shiyasa gabadaya baya samun lokacin kansa ballanatana na wani amma dai duk da haka yana kokarin shiga dakin halisan ya dubata kafin ya fice harkokinsa…….Kofar na’isa ma tun ranar da yaje bai samu damar sake zuwa ba sai dai idan ya dawo gida yakan kira iyayen nasa a waya su gaisa da juna.
Yaya Ramlatu bata samu damar zuwa duba Halisa ba sai da mijinta ya tafi tukkuna dan Kishiyarta Sakina zaunar da mijin nasu tayi ta sheda masa duk irin abunda Ramlatun takeyi idan baya gari! Aikuwa ya fusata sosai dan sabida yasan halin sakina ba zata ta’ba fada masa karya ba, ya bud’ewa Ramlatu wuta sosai sukayi ta babu kyau babu dad’i! wanda har sai da Salim d’ansu ya shiga tsakani jin mahaifin nasa na yunkurin sakin mahaifiyar tasa hankalinsa ya tashi ya dinga bawa mahaifin nasa hakuri da kyar ya hakura ya kyaleta amma yayi mata tas tas! kuma jikinta yayi sanyi mutuka dan tunda taji furucinsa a kanta ta shiga hankalinta idan ya saketa ai ya cuceta da girmanta da komai yasa ta zawarci! sai ta hakura ta kyaleshi har ya gama hutunsa na sati uku ya tafi , a ranar kuwa da ya tafi ta dauki mayafi ta yafa ta fice daga gidan tana yar da habaici! Sakina girgiza kanta tayi tana mamakin taurin kai irin na kishiyar tata
Halisa ta warware samul! sai dai rashin walwalar maigidan a tare da ita ya sanya duk wani kuzari da karsashinta ya dakushe a gidan, al’amarin da ya dameta mutuka gaisuwa kawai ke had’ata dashi da safe……idan kuwa ya dawo daga kasuwa da daddare ya zauna a palo yana dube dubensa a loptop to ta sake ta tunkari inda yake sai tayi nadama dan sai ya farfad’a mata munanan maganganun da zasu sanya zuciyarta bugawa….Dalilin da yasa kenan take kaffa-kaffa dashi amma dai duk wata kyautatawa tana yi masa domin ta wanke kanta a gurinsa.
Ga’badaya Halisa ‘kin kar’bar uzirin Yaya Ramlatu tayi ta nuna mata fushinta sosai akan abinda tayi mata ace tayi ciwo irin wannan amma ba zata zo ta dubata akan lokaci ba sai da ta samu sauki sannan zata zo gaskiya ba taji dadin wannan abunba.
Ramlatu ta fad’a mata cewar maigidanta ne ya dawo shiyasa bata samu damar zuwa ba kuma ina laifi tunda kullum tana kiranta a waya suna gaisawa! Jin haka yasa Halisa ta sake karatun ta nutsu ashe itace mara kishin kanta wacce take wulakanta auranta tana daukar mayafi ba tare da mijinta ya sani ba tana fita! gaskiya bata ta’ba tsammanin haka halin Ramaltu yake ba sai yanzu dole ne kuwa tayi taka tsantsan da ita dan ba zata sake yarda da ita ba tana ingizata inda zata ta kaita inda zata cutu ita kuma tana gefe guda babu abinda ya dameta………
To haka al’amura suka cigaba da tafiya tsakanin ‘bangarori guda kowanne ‘bangare yana yin abinda yake ganin shine daidai da rayuwarsa’ Bangaran Naja’atu sai abinda yayi gaba dangane da soyayyarta da Bash kullum suna ma’kale a waya suna soyayya sunyi wani irin sabo na ban mamaki! Naja’atu ba tajin kunyar yin ko wace irin magana da Bash mutukar ta shafi soyayyarsu! Ta daina jin kunyarsa yanzu ko wace magana ya fad’a mata da wacce ta dace da wacce bata dace ba sai ta mayar masa da martaninta sosai ta zama mara kunya saboda alqarta da Bash wanda take ganin shine dadai da rayuwarta……..A tsakanin wattani uku da tayi a gidan Alhaji tayi wani irin qiba da kyau na ban mamaki komai nata ya ciko ta bunkusa ta kai ta kawo babu abinda take bukata sai namiji ita kanta tasan tana da sha’awa a kusa shiyasa take Allah Allah ta ‘karasa iddarta a daura musu aure dan ita dashi duk a matse suke da junansu Bash yace tana kammala idda da sati biyu za’a daura auransu dan ba za’a ja dogon lokaci ba.
‘Bangaran Abbah Abbas kuwa tuni ya cire wata Naja’atu cikin zuciyarsa a da da farko ne al’amarin yake damunsa daga baya kuma da yaga yanda rabuwarsu ya janyo masa kwanciyar hankali a gidansa dashi kankin kansa da kuma cigaba ta fannin harkokinsa sai kawai ya cireta a ransa ya godewa Allah gami da adduar Allah yasa hakan shine alkairi! Yanzu babban burinsa ya samu nutsuwa ayyukan dake gabansa suyi sauqi ya shiga duba wacce zai maye gurbin Naja’atu da ita dan tunda ya saba zama da mata biyu yana ganin ba zai iya bari ba, mussaman yanzu da Halisa ta zama hoto a gurinsa dan tsoron tunkararta yake da bukatarsa saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo an samu da kyar ta samu lafiya yana jin tsoron yaje ya zunguro mata ciwon ya dawo shiyasa tsayin wattani uku da faruwar al’amarin bai tunkareta da wata maganaba, ba wai dan baya jin sha’awa ba kawai yana daurewa ne domin a zauna lafiya.
Misalin karfe hud’u da da kwata na yamma Salim yayi parking din dalleliyar sabuwar motarsa da Kawun nasa ya siya masa ya fito daga motar cikin shigar ‘kananun kaya kamar koda yaushe yasha gayu kana ganinsa kaga dan burni….Daya bangaran ya nufa ya bude mata ta fito….Wata matashiyar budurwa ce ta fito daga motar mai matsakaicin tsayi! babu laifi tana da kyau daidai gargwado sai dai kuma bleecing din da takeyi ya soma lalata mata fatar jikinta kana kallonta zaka gane idanunta a bude suke! Tana sanye da atampa super dinkin doguwar riga mai falmaran da madauri a baya, tayi wani katon a cuci da yayi tsayi a kanta tayi rolling da karamin gyale kafafunta na sanye da takalmi mai tsayin dunduniya da madaurai! lebenta kuwa yaji jan jan baki tana da fara’a sosai dan data fito daga motar ma sai dariya take tana haske shi da hakoran makkan dake bakinta Salim sai murmushi yake yana jin dadin samun Salimat a matsayin matar da zai aure Salimat ta ture hamshakan maza masu kudi da muqami tace shi take so! shiyasa yau ya dauko ta ya kawo ta ta gaisa da kakaninsa Hajiya da Alhaji! Gefe guda kuma yana so ya cizgunawa zuciyar Naja’atu dan ba karamin jin haushinta yake ba dangane da nuna halin ko in kula da take masa gabadaya ta watsar dashi tana nuna masa dashi da babu duk daya tunda ta samu wanda ya fishi! shine shima yau ya dauko Salimat ya kawo musu ita su ganta..