MADADI 1-END

MADADI Page 61 to 70

Hajiya da Naja’atu suna zaune a palo su Salim suka shigo! Hajia na ganin Salimat jikinta yayi sanyi ikon Allah a ina Salim yaje ya samo wannan tsohuwar ai ta girmeshi! Daurewa tayi ta kawar da abinda ke zuciyarta ta karbi Salimat hannu biyu suka gaisa a mutunce.”

Naja’atu na dan mirmushi tace”Salim wannan itace antyn nawa.” Yace.”Eh ya kika ganta.” Yar dariya tayi tace”Wallahi tayi kuma kun dace Allah ya nuna mana lokacin yasa zaayi damu.”

Salim baiyi tsammanin haka da gurinta ya dauka za taji haushi sai yaga akasin haka sai ma jan Salimat din take da hira……..Da zasu tafi hajia tayi wa Salimat kyauta sabulai da turaruka masu kamshi, Naja’atu har bakin mota ta raka Salimat din tana daga mata hannu…..Wannan al’amarin da ya faru ya sanya salim jikinsa yayi sanyi ashe dai da gaske Naja’atu ta daina sonsa….Koda yake shima yasan Bash yafi shi komai da komai na rayuwa amma dai duk da haka yasan shine yake da nasara a kanta tinda har ya samu damar ruguza zamantakewar auranta da Kawunsa.dama babban burinsa kenan.

Bayan Sati hud’u….Naja’atu ta ‘kare iddarta alhamdullhi Mahaifin Bash tare da ‘yan uwansa guda biyu sunzo da sadakinsu an tattauna maganar daurin aure…cikin wad’anda suka kar’bi sadakin sun had’a da Alhaji Sama’ila Abbas Abbas ‘Kanin Baba Malam mai suna Ya sayyadi Nazifi! Abbah Magaji kam koda ya samu labarin zuwan iyayan Bash din cewa yayi yana da uziri a kasuwa ba zai samu zama ba babu wanda ya tursasa shi akan dole ya zauna a karbi sadakin dashi ya kama hanya yayi tafiyarsa kasuwa…..Abbah Abbas kuwa sai bayan sun kar’bi sadakin sun tsayar da ranar daurin aure sati biyu masu zuwa ya sami sukunin tafiya harkokinsa…..Naja’atu a ranar yini tayi cikin farin ciki da annushuwa burinta zai cika na auran muradin zuciyarta idan ta tuna da cewar harda Abbah Abbas a cikin wa’yanda suka kar’bi sadakinta sai taji wani farin ciki ya lullu’beta tasan komai ya wuce a gurinsa kamar yanda ya fad’a mata a text dinsa tunda har ya tsaya a cikin al’amuranta to tasan da cewar tuntuni ya yafe mata shiyasa ta saki jikinta take harkokinta cikin kwanciyar hankali.

*Massalacin Juma’a na b.u.k*

Kamar yanda muka sani cewar mafi akasari malaman addini gami da limamai na da wani irin tsari da a’kida a kan ‘ya’ya yansu na aurar dasu ga wanda suke ganin yana da yanayin aqidar su da d’abi’arsu to hakane ya kasance da *Malam Sharif Bala* wanda ya kasance fitaccen malamin da yayi fice a jahar kano, wanda kuma ya kasance limamin babban massalacin juma’a dake b.u.k….mutumi ga Abbah Abbas wanda suke da kyakkyawar alaqa mai kyau a tsakaninsu to yau bayan an idar da sallahr juma’a ya tsayar da Abbah Abbas din domun ya sheda masa irin kyautar da yayi masa saboda ganin cancantarsa da kuma yanda yake tsaye a kan addininsa da kuma hidimtawa addinin musulunci yaga dacewar ya bashi ‘Yar sa Mai suna Zaibab yar kimanin shekara goma sha biyar 

To lokacin da Abbah ya gama sauraran uzirin Limamin sai yayi wani murmushi mai ma’ana yana godewa da Allah a zuciyarsa, a lokacin da yake yunkurin dubawa kansa macen da zai aura sai gashi lokaci guda anyi masa kyautarta babu shakka ba zai watsawa mutumin qasa a ido ba, dik da cewar bai san yarinyar ba bai kuma ta’ba ganinta ba hakan ba zai hanashi kar’barta ba a matsayin matar auransa ba, yana adduar Allah yasa auranta ya zama alkairi a rayuwarsa.

Malam Sharif yaji dadi sosai da Amincewar da ya samu daga gurin Abbah Abbas d’in inda a nan take yace Juma’a mai zuwa za’a a daura aure a ka kawo masa yarinyar gidanshi….Anan shi kuma Abbah Abbas din ya kawo masa uzirinsa kan cewar yayi hakuri ya d’an bashi lokaci kadan zai yi wasu shirye shirye, malam sharif ya amince da uzirinsa amma bai yarda a ja dogon lokaci ba.

 ****

Bayan sati daya da zuwan iyayen Bash ranar Alhamis Sai gasu Munira ita da ka’wayen mommynta da ‘Yan uwanta sunyi mota biyu suna tafe da setin akwatina mai shida shida goma sha biyu kenan! Ko wacce akwati sha’ke da kaya tamkar za’a bude dan karamin kanti! akwai wani dan kit dake dauke da gwala gwala manya manya masu masifar nauyi da tsada! Al’amarin da yayi masifar firgita Baba talatu ita da ‘Yan uwanta irin wannnan uban kaya da uban gold sai kace ana hauka!!! kafin ‘yan kawo kaya su tafi zance ya soma tashi a unguwa cewa ashe Naja’atu mai kudi ta gani shiyasa ta fujirewa auran Mijin ‘Yar uwarta kai kowa dai d irin abunda zai fad’a akan al’amarin da yawa daga cikin mutanan unguwa sai suka dawo ganin laifin Baba Malam a ganinsu ai shine bai tursasa yarinyar ta zauna da Auran madadin da akayi mata ba suna ganin shima kamar kwadayin abin duniya ne ya sanya ya amince da rabuwar auran to idan ba hakaba mutanan da sukayi maka hallaci ai bai kamata ya watsa musu qasa a ido ba…….Haka dai rukuni rukunin mata suka dinga shigowa wai sunzo ganin lefa!Baba talatu ita da ido kawai take binsu dashi tana mamakin sanya ido da bindiddigi irin na mutane……Ya Ramlatu data samu labarin abinda ke faruwa bata zauna ba sai da taje ta kashe kwarkwartar idonta aikuwa ta dinga addua Allah yasa d’an yankan kai yarinyar ta daukowa kanta….Ita kam Naja’atu ko a jikinta al’amarin bai firgitata ba saboda tasan a irin kaunar da bash yake mata zai iya narkar da gabadaya kud’ad’ansa akanta.

Ana ya gobe daurin auran da yamma Naja’atu ita da Salimat budurwar Salim dan yanzu sun zama qawaye tun salim na jin haushi har ya hakura ya kyalesu…Salimat ita ta kai Naja’atu gurin gyaran jiki aka gyara mata jikinta sosai sannan akayi mata kitso da lalle wanda yayi masifar yin kyau! Naja’atu ta fito amarya sai wani murmushi take tana jin nishadi….Bayan sun dawo ita da Salimat din gidan Baba malam suka shiga, nan suka tarar da Aunty maryam da Baba talatu a zaune suna tattauna al’amuran da suka shafesu…Naja’atu koda taga aunty maryam kunya ce ta rufeta sai ta sunkuyar da kanta kasa tana yar dariya gami da gaisheta 

Aunty maryam tace”Ai dole kiji kunyata naja’atu abubuwan da kikayi baki kyauta ba koda yake dawo da abinda ya wuce bacin rai ne saboda haka ina miki fatan alkairi da adduar Allah yasa gidan zamanki ne Allah ya baki zaman lafiya da nutsuwa zaman aure da mijinki.” Baba Talatu ta daure fuskarta sosai da sosai tace”Dama inaso na aika a kira ki domin akwai maganganun da nake so nayi dake! 

Naja’atu tayi shuru gabanta na faduwa Baba talatu tace”Babu abinda zance a cikin wannan auran naki sai dai nayi shuru da bakina amma bana yi miki fatan nadama a rayuwarki ammafa ki sani duk wanda kika zalinta a cikinmu idan bai yafe miki ba sai hakki ya kama ki! Gobe za’a daura miko aure da wanda kike so kuma goben dai zaizo ya daukeki ku tafi can inda yake…Ina so na fada miki cewar ki zauna a dakinki duk rintsi duk wuya kada wata wahala tasa kiji sha’awar dawowa gida domin ki ‘karasa zubar mana da sauran mutuncin da muke dashi a cikin unguwa! Babu maganar kawo kara ko kuma yaji ki zauna komai wahala tinda ke kikaji kika gani zaki iya! Daga karshe nake miki fatan alkairi da samun nutsuwar da kike bukata.”

Kuka kawai takeyi ta kasa cewa komai! shin me wad’annan maganganun na mahaifiyarta suke nufi a kanta? Idan ta fahimta kenan Baba talatu na nuna mata cewar tunda suka dauketa suka bawa Bash sun yafeta daga zuriarsu kome.? Aunty maryam ce kawai ta rarrasheta amma baba talatu sabgar gabanta kawai takeyi….Jiki a sanyaye suka mike suka nufi gidan Alhaji….Suna shiga gate din gidan Abba Abbas na kokarin fitowa daga mota Salim yayi saurin rufe motar bayan fitowar tasa…..Salimat kasancewar tasan matsayin sa a gurin Salim yasa da sauri cikin ladabin karya ta tsuguna har kasa tana gaisheshi! ya amsa cikin kulawa gami da kokarin ratse su ya wuce!! Naja’atu ta bisa da wani irin kallo gabanta na fad’uwa, gwiwa a sage suka shiga palon.. …….Nan suka sameshi shida mahaifiyarsa suna maganar data shafesu, hajia Abu ganin sun shigo yasa ta saki fuskarta da fad’in” Naja’atu kun dawo ai ina nan inata fad’a kan cewar wannan irin gyaran jiki ne ace tin safe ku fita babu ci babu sha ai dole ku galaibata! A sanyaye ta zauna kan kujera da fadin.” Wallahi hajia guraran La’asar muka dawo mun shiga gidan baba malam ne kuma munci abinci a can.” Hajia tace”To alhamdullhi dama tunani na inda zaku samu abinci kuci.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button