MADADI 1-END

MADADI Page 81 to 90

Vip gruop #600 normal group #300 account numbar….0542382124…Binta umar gtbank…..Wahasap number…. 07084653262

*BINTA UMAR ABBALE*

68******Salim har yamma yana police station a gar’kame hankalinsa yayi masifar tashi ganin duhun magariba ya gabato sai kawai ya fara zubar da hawayen nadama! babu shakka wannan al’amari daya faru dashi hakkin Kawunsa daya zalinta ne, yasa hannu ya dauko hankici a cikin aljihunsa ya goge idanunsa tare da sake ri’ke ‘karfen da yayi masa katanga da ma’aikan gurin, zare ido kawai yake yana fad’in “Oga dan girman Allah ka saurari maganata wallahi ni ba ‘barawo bane inaso kazo kaji uzirina ni abun a tausayawa ne qaddara da tsautsayi ne suka afka min.”

‘Daya daga cikinsu ya doki! tebur din dake gabansa yace.”Rufe mana baki munafiki kai har kasan qaddara irinku ai ba imani ne daku ba kazo sata sai Allah ya tona maka asiri dama irinku muke nema duk muyi maganinku yanzu D.P.O muke jira yazo mu zartar da hukuncin da zamuyi maka.”

Salim ya sake rikicewa cikin tsantsar tashin hankali yace.”Wallahi wallahi bana daya daga cikin wa’yan nan mutanan da kuke magana a kansu, ku taimakeni kamar yanda Allah ya taimake ku wallahi ban shiga gurin nan da sunan sata ba Atm dina naje nema a gurin kasancewar kwanaki uku da suka wuce naje na cire kudi a gurun………Tiryan tiryan ya fad’a musu abinda ya faru, yace”Idan kuna so ku tabbatar da maganata to ku duba waya ta zaku ga text din da banki suka turo min cewar gabadaya kudin dake account d’ina babu.”

Da sauri wanda wayar ke hannunsa ya shiga dubawa, aikuwa da text din yaci karo cike da mamaki ya shiga nunawa ‘yan uwansa sai duk jikinsu yayi sanyi, wanda key din cell din ke hannunsa ya miqe da sauri yaje ya bude shi yace.”Kayi hakuri kaji ko Allah ya mayar maka da alkairi.”

Cikin tsananin damuwa da tashin hankali ya kar’bi wayarsa da key din motarsa ya kama hanya ya futa daga gurin, sai suka bishi da kallon tausayi kud’i kimanin miliyan daya da rabi an kwashe masa ai dole su jajanta al’amarin……..Salim na fita daga station din kai tsaye gidansu Salimat ya nufa, yayi parking a kofar gidan cikin damuwa ya kira wayarta……Salimat ta fito cikin shiga ta alfarma kamar yanda ta saba ta bude mota ta shiga, ganinsa a burkice yasa tasha jinin jikinta, ya kalleta dan jan ido yace.”Salimat ‘barayi sun kwashe min kudin accont dina yanxu bani da ko kwabo Atm dina ya fad’i a lokacin dana kaiki shopping ban ankara ba sai da naga bank sunyi min alert sannan na duba naga abunda ke faruwa…Hakika ina cikin tashin hankali mai tsanani.”

Cikin alhini tace”Innalilihi wa’ina ilahi raji’un Salim yanzu ya zamuyi da wannan qaddara sai kawai ta fashe da kukan munafurci……Naburago ne ya fito daga gidan, yasha shaddarsa harda hula kamar mutumin kirki kai tsaye motar ya durfafa. Dama sun riga sun gama shirya plan dinsu tun a gida. hannu yasa ya kwankwansa gilashin motar. Da sauri Salim ya sauke gilas din ganin Naburago a tsaye yasa da sauri ya miqa masa hannu suka gaisa Naburago ya gyara tsayuwarsa yana kallon Salim din yace.”A matsayina na wakilin wannan yarinya Salimat na yanke shawara kancewar mun fasa baka auranta dan sabida munyi kyakkyawan bunkice a kanka mungane kai d’in azzalimi ne macuci maha’inci mun samu labari daga bakunan mutane da yawa kancewa kaine ka kunnawa ubangidanka wuta a cikin dukiyarsa wannan dalilin yasa muka yanke shawarar dawo maka da kudin auranka.” Yana gama maganarsa ya kalli Salimat din cikin tsawa! yace.”Maza ki fito daga motar nan ki shiga gida babu ke babu wannan macucin.”

Salimat ta bude mota da sauri ta nufi gida tana kuka kamar gaske, Naburago yasa hannu aljihu ya dauko kudin Salim dubu Hamsin yasa masa a jikinsa yace “Ga kudinka nan babu mu babu kai kada ka kuskura na sake ganin kafarka a kofar gidan nan.” Yana gama maganarsa ya bar gurin.

Salim jikinsa ji’kewa yayi da gumi! tsabar tashin hankali makogwaronsa bushewa yayi qamas ya rasa ma wane irin tunani zaiyi sai kawai ya kifa kansa akan sitiyarin mota yana zubar da hawayen nadama.

****

*’Yar Sa’adu* ta jangwalowa kanta masifa, matar wani babban soja za’ayi mata kishiya sai ta samu labarin *’Yar Sa’adu* da magungunanta sai kawai ta wanko kafarta ta ciko jakarta da kud’i taje ‘Yar Sa’adu ta had’ata da magungunan mata iri iri………Matar ta tafi gida ta dinga shan magani babu qa’ida ta dinga cusa maganin matsi wai ita lallai sai gabanta ya matse dan saboda kada amarya ta fita a gurin miji…

Aikuwa matsalar data afku da Halisa irinta ce ta afku da ita, Soja mazan fama ya bud’e mata wuta danshi har da duka ma ya had’a mata dashi yace sai tayi masa bayanin yanda akayi al’amuranta suka kasance a haka! Ganin rufa rufar da take bashi da amfani sai kawai ta fad’a masa yanda al’amarin ya kasance, takaici yasa shi yayi mata dukan tsiya da blet kuma ya daina kulata, ashe duk hukuncin da yayi mata bai hakura ba mota ya cika da sojoji ya sata a gaba suka nufi gidan *’Yar sa’adu me kayan mata*…..’Yar sa’adu na tare da baki kawai sukaji ihun yara ga unguwar ta cika da kururuwar motar sojoji ai babu shiri ita da matan da take a gidan suka fito waje, ganin zaratan sojoji sun durfafo kofar gidanta yasa ta kusa sakin fitsari a wando! a tsaroce tayi nufin komawa cikin gidan gabanta na wani irin faduwa ganin matar sojan data zo ta hada mata magani makwanni biyu da suka wuce babu shakka akwai abunda ke faruwa, takalmin kafarta ne ya gurde ta tsaya zata gyara matar soja da sojojin dake bayanta suka karaso gurin ba tare da jin tsoron komai ba matar ta nuna ‘Yar Sa’adu da fad’in “Gata nan itace matar da siyar da magunguna kan kudi masu yawa.”

‘Yar sa’adu ta diririce ta hau inda inda, Sojan dake kusa da ita ya taska mata mari da fad’in “Kece kike cutar mata ko kin zama ‘yar damfara ki tara mata ki dinga kar’be musu kudi kina siyar musu da abunda zai cutar dasu ko to yau sai kin gane kuranki.” doguwar bundigar dake hannunsa ya dora mata a wuya a tsawace! yace.”Wuce muje yau kin fad’a komar mu sai kin gane baki da wayo.” Yar Sa’adu kuka ne ya kufce mata jikinta ya shiga kyarma! sai ta shiga d’aga hannunta sama tana basu hakuri….Kafin kice kwabo gurin ya cika da jama’a, su kuwa matan da suke tare da ita ganin an shigar da ita mota yasa da sauri kowacce ta fece! tsoro da tashin hankali duk ya cika musu zuciya.

 ****

Watannin Naja’atu biyu da dawowa gida inda ya kama wattanin cikinta shida kenan yanzu cikin nata ya fito ana d’an ganinsa amma ba sosai ba kasancewarta doguwa yasa cikin bai bayyana kansa ba sai dai amma ita kadai ta san abinda take ji a jikinta, kusan kullum sai ta ‘buya a daki taci kukanta ta koshi haka kawai Bash ya had’ata da wahala ya gudu ya bar mutane da jigilar d’ansa duk sanda ta tuno wannan al’amari takan kwana ta yini cikin kunci da damuwa, mussaman idan taga yanda Abbah Abbas ke hidima da ita da cikin jikinta duk sai hankalinta ya tashi ta shiga nadamar abinda tayi masa a baya, itace ta zama sanadiya gurin lalacewarsa cikinsa gashi ita taje ta dauko ciki ta kawo masa wahala, yanzu saboda ita kullum da safe kafin ya tafi harkokinsa sai yazo ya kofar na’isan sannan bayan ya dawo daga kasuwa ya sake dawowa gabad’aya jama’ar gidan sun fahimci saboda ita yake wannan sintirin dukkaninsu su gane ya damu da yarinyar da cikin jikinta, sai hankalinsu ya kwanta mussaman hajia da Alhaji burinsu kawai yarinyar ta haihu lafiya sai ai maganar kome domin su a ganinsu yanda yake nuna damuwarsa a kan yarinyar suna ganin kamar yana so ya mayar da ita gidansa ne. wanda shi kuma kwata kwata ba haka bane a cikin zuciyarsa haka kawai take bashi tausayi da ita da abinda ke cikinta shiyasa ya mayar da hankalinsa a kanta duk da bashi ne keda alhakin kula da itaba , a yanzu dai cikin zuciyarsa bai dauki Naja’atu a matsayin komai ba face ‘Yarsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button