MADADI Page 81 to 90

Yau asabar yana zuwa da wuri dalili kenan daya sa takasa komawa baccinta na safe ta fito palo ta zauna tana jiran zuwan nasa, lokacin daya shigo hajia na sama ita kadai ya samu a zaune tana kallon tashar sunna tv Malam Aminu Daurawa na gabatar da shirin tambaya mabudin ilimi, a nutse ta amsa masa sallamarsa ta dan gyara zamanta a hankali tana gaishe shi….Ganin yanda take ya mutsa fuska ne yasa ya mayar da hankalinsa kanta a nutse yace.”Ina fatan kina lafiya ya jikinki.”?
Kamar za tayi kuka tace”Da sauki inasu Mussadiq.” Yace.”Suna gida lafiya lau ina hajia.”? Tana sama.” Tafada tana kallon kasan kafafunsa, kai tsaye saman ya nufa sai ta bishi da kallo tana girgiza kanta ita kam a duniya akwai mutumin dake sonta irinsa kuwa? gaskiya babu.
Ya kai mintina goma sha biyar a saman ya sakko da sauri yana duba agogon hannunsa, dan kallon gefan da take zaune yayi ba tare da yace wani abu ba ya kama hanyar fita…..Da kyar ta kira sunanshi, tsayawa yayi yana kallonta….Murya na rawa tace.”Ina so mu gaisa dasu Mmn Sajida matar nan data taimaka min.”
Jim! yayi kafin yace.”Yanzu dai sauri nakeyi ana jirana idan nazo da yamma sai ayi yanda kikace.” tace.”To Abbah Allah ya bada sa’a.”Ya amsa yana kokarin futa daga falon.
Sai bayan futarsa ne ta shiga tunanin yanda za’ayi ma tayi magana dasu Mmn Sajidan tunda lokacin data barsu daga ita har Mmn Ladin babu me waya a cikinsu , wannan dalilin ya sanya jikinta yay sanyi taso da hanyar da zata sadata dasu da sun gaisa da juna ta ‘kara yi musu godiyar abinda sukayi mata.
To koda ya dawo gidan da Yamma batai masa maganar ba shima al’amuran dake gabansa sun mantar dashi, sai kawai ya ajiye mata abubuwan da ya saba siyo mata ako wace rana yay tafiyarsa gurun iyalinsa.
Bayan kwanaki biyu da faruwar hakan…..Yana tsaka da shiryawa domin tafiya kasuwa kira ya shigo wayarsa, Zainab yasa ta miqa masa wayar ya daga tare da karawa a kunnansa…….Mmn Sajida dake d’aya bangaran ta sauke ajiyar zuciya tana godewa Allah da sauri tace”Sannu ina kwana sunana Mmn Sajida daga jos.” Sai yayi saurin duba number yana so ya tabbatar, ya mayar da wayar kunnansa yace.” Lafiya kalau Mmn Sajida na gane ina fatan kuna lafiya.”? Ta amsa da lafiya lau Alhaji muna fatan kunje gida lafiya.” Yace.”Lafiya lau alhmdullhi.” Tace.”Dama na kira ne idan da dama inaso a bani Naja’atu mu gaisa wallahi har yanzu alhinin rabuwa da ita bai sakemu ba.” Yace.”Ayya! kada ki damu insha Allahu anjima kad’an idan naje Inda take zan bata wayar ku gaisa.” Tace.”To Alhaji mungode sai anjima.” Yace.”To masha Allah.” Kashe wayar yayi ya ajiye kan drowar dake gefansa, Zainab tunda taji ya ambaci sunan Naja’atu ta sanja fuska dan har sai da ya fahimci sauyawarta alhalin labari take bashi amma lokaci guda yaga ta ‘bata rai! kwanciya ma tayi ta juya bayanta kishin Naja’atu naso ya dargagaza mata zuciya. Sai da ya gama shiryawa tsaf ya juyo yana kallonta a nutse yace.”Zainab lafiya dai ko.? ba tare data jiyo ba tace.”Lafiya lau bacci zanyi shiyasa na kwanta.” Yace.”Okey ni zan fita.” Tace”A dawo lafiya.” ya amsa a nutse ya bude kofar dakin ya fita, mikewa zaune tayi tana jan tsaki! kai gaskiya ta gaji da wasiwahsi gami da takurawa zuciyarta dole yau idan ya dawo ta tambayeshi tsakaninsa da Naja’atun nan da ya damu da ita idan mayar da ita zaiyi gwara ya fad’a musu su ya daina wani ‘boye-‘boye………..
*Littafin na kudi ne…..!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar karanta littafin ga yanda abin yake…..Vip group #600 normal group #300 account…. 0542382124…Binta umar gtbank…Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
69*******Lokacin daya isa gidan Alhajin Naja’atu na daki tana baccinta na qa’ida dama idan tayi sallar asubahi komawa take ta kwanta tayi ta bacci watarana hajia da kanta take shiga dakin ta tashe ta sannan fa tayi break fast…. tunda cikinta yayi kwari take wannan bacci mara qa’ida daddare ma tana idar da sallar isha’i take kwanciya, hajia da taga abun yayi yawa cewa tayi aje asibiti a dubata, Yaya Ramlatu tace” Lafiyarta lau kawai yanayin cikin nata ne yazo a haka dama ana samun ciki mai sanya baccin tsiya ta ce ta kwantar da hankalinta bacci lafiya ne. bana cuta ba to wannan maganar da Yaya Ramlatu tayi itace tasa hajian ta kwantar da hankalinta amma dai duk rintsi da daddare bata barinta ta kwanta sai ta tabbatar ds taci abinci ta koshi tukkuna.
Koda ya shigo gidan bai samu kowa ba, wai ashe sun tafi jana’izar ‘yar ‘kanin Hajia Rabi dake mandawari, da yake mutuwar ta dare ce shiyasa bashi da labari sai daya ya shigo gidan tukkuna maigadi ke fad’a masa………. Juyawa yayi da niyyar fita daga gidan sai kuma yayi wani nazari, yana tunanin ko zasuje gidan mutuwar bai zama lallai suje da ita ba shima yasan a daidai lokacin take baccin data saba, dan wani lokacin idan yazo baya samun ganinta sai dai kawai ya tambayi hajia lafiyarta.
Shuru falon lokacin daya shiga, bai jira komai ba ya nufi dakin da take……….Kallon sharia yayi mata yayi saurin kauda kansa, yanayin kwanciyar da tayi taso ta saka shi cikin wani yanayi yayi saurin kawar da abun daga cikin ranshi…Ya karasa bakin gado tare da tsayawa saitin kafafunta yana kallon fuskarta dake kallon rufin dakin, da yake irin kwanciyar da ba’a masu ciki suyi ita tayi (rigingine) ta tayar da kafafunta sun taka gadon kana ta d’ora dukkanin hannayenta a saman cikin nata……Sunanta ya shiga kira yana korar shad’en d’in da yake ra’barshi….idan da baiyi wa Mmn Sajida al’kawari ba da yana ganin tafiyarsa zaiyi dan tsayuwarsa a dakin na nema ta haifar masa da matsala.
Kamar a mafarki taji muryarsa na kiran sunanta! ta bud’e idonta da sauri! shi take gani dishi dishi a idonta, shi kuwa yanayin yanda yaga idanunta sun sauya yasa ya dauke kansa yana kallon gefe guda, yace.”Tashi ku gaisa da Uwar dakin ki ta jos dazu ta kira waya tana so ta dubaki.”
Da sauri ta miqe zaune jin cewar Mmn Sajida ta kira waya…Wannan gaggawar miqewar da tayi yasa yaron dake cikinta ya kai mata wani irin naushi! yayi fushi! ya samu guri guda ya dunkule mata! Rintse! idonta tayi murya na rawa tace”Wayyo cikina.”! Kafin kice me zufa ta tsatstsafo mata a saman goshi!
Rikicewa yayi yay saurin ajiye wayar a kan drowar dake gefan gadon, be san sanda ya zauna kusa da ita ba yana kokarin kamo hannunta…….”Wayyo Allah cikina ya ‘kulle a guri d’aya.”Abinda take fad’a kenan tana janyo zanin gadon da hannayenta……Kamota yayi yasa a jikinsa yana shafa bayanta a hankali a hankali duk ya rasa nutsuwarsa ita kuwa sai kokarin cire jikinta take tana kiran cikinta! Yace.”Me yasa kikayi irin wannan kwanciyar bayan kin san masu ciki ba’aso suyi sannan me yasa kike gaggawa a cikin al’amuranki kin jima a kwance rigingine gashi kin tashi cikin gaggawa dole shima yayi fushi! ya zauna miki a guri guda, sannu ki dinga kula kinji ko.”
Wannan maganganun yake mata yana dan shafa bayanta a hankali a hankali! Shuru tayi a jikinsa, tana jin yanda yaron ke motsi inda ya d’aure yana saki a hankali a hankali cikin nata ya koma daidai ta daina jin ciwo…..A sanyaye ta cire jikinta a nasa ta sunkuyar da kanta tare da kokarin gyara botiran rigarta….Daidaita nutsuwarsa yayi ya dauki wayar daya ajiye yana kallonta yace.”Ina fatan cikin ya daina ciwo.” Kanta ta d’aga tana jin nauyin abinda ya faru…Yace.”To sai ki kiyaye gaggawa kuma ki daina irin wannan kwanciyar cikinki yayi kwari yanzu kiyi hakuri kina kwanciyar da yaronki zaiji dadi kema ki inganta lafiyarki.”