MADADI 1-END

MADADI Page 81 to 90

A hankali tace”Wallahi bana sanin sanda nakeyi nafi jin dadin irin kwanciyar.” Dan murmushi yayi yace.”Baki damu da lafiyarki ba shiyasa kike biyewa son zuciyarki kisa a ranki kin daina irin kwanciyar sai kiga kin zauna lafiya.” Tace”To shikkenan insha Allah.”

Dakin ne yayi shuru Abbah na traying din number Mmn Sajida tana fara ringing ta dauka yay saurin miqa mata, gani yay ta fad’ad’a fuskarta da fara’a tana dariyar farin ciki tace.”Mmn Sajida ina kwana ina Mmn Ladi.”? Mmn Sajida cikin da walwala da farin ciki ta amsa da fad’in “Ga Mmn Ladi a kusa dani muna tare Naja’atu ya kuke je gida? Ya kuma jikinki muna fatan duk komai lafiya.” Tace”Wallahi alhmdullhi Mmn Sajida gaskiya naji dadin jin muryarki ina nan ina kewarki ki bani Mmn Ladi mu gaisa insha Allahu idan na haihu zanzo nayi muku kwanaki.”

Mmn Sajida tace.”Muma muna nan duk kewarki ta ishemu dan Walid ma sai da yayi zazzabi Sajida kuwa kullum sai ta kira sunanki tayi kuka.” Najaatu murya na rawa tace”Ayya Allah sarki Walid dan Allah kice ina gaishi da kyau Sajida kuma kice mata idan zanzo zan zo mata da kayan wasa irin wanda take so.

Mmn Sajida tace”To insha Allah zan fad’a mata ga Mmn Ladi ku gaisa.” Mmn Ladi na washe bakinta ta kar’bi wayar da fad’in “Naja’atu ‘yar albarka mai gyara sinnar ma’aiki ai ni kam babu abinda zance miki daba dan keba da tuni na dade da rabuwa da Saleh wallahi yanzu zaman lafiya muke da juna yanzu ina hakuri da duk abinda ya bani kuma na daina yi masa rashin kunya yanzu Saleh daidai gwargwado yana kyautata min muna zaune lafiya da ‘ya’yanmu.

Naja’atu tace” Amma gaskiya naji dadin wannan labarin naki Mmn Ladi Allah ya qara muku zaman lafiya sannan kuma inaso in tuna miki cewar kada ki manta da al’kawarinmu insha Allah idan nazo garin zan tallafa miki ki fara sana’a kema.”

Mmn Ladi tace”To nagode kwarai da gaske Naja’atu Allah ya saka da alkairi Allah kuma ya sauke ki lafiya.” Ta amsa da amin tana jin wani irin farin ciki a cikin ranta.

Abbah na zaune yana kallonta sai dariya take Mmn Sajida ce take bata labarin halin da Dantalle ya shiga bayan tafiyarta harda kuka ya dinga yi…..Naja’atu ta dinga kyalkyala dariya tana fad’in “Lallai Dantalle to ki bashi hakuri yaje ya rungumi matanshi ya kyautata musu shine abinda ya dace yayi”………Kallon agogon hannunsa yayi yaga lokaci yaja a qallah sun dauki minti ashirin suna wayar gyaran mirya yayi tayi saurin kallonsa, hannunsa ya miqa alamun ta bashi wayar….Da sauri tace” Mmn Sajida nagode da karamci Abbah zai kar’bi wayarsa insha Allahu idan na haihu lafiya zaku ga nazo muku.” Mmn Sajida tace”To Naja’atu Ubangiji Allah ya raba lafiya sai anjima.” Sallama sukayi cike da farin ciki da kewar juna.

Tana miqa masa wayar tace”Abbah don Allah kayi serving number ta Mmn Sajida ce.” Wayar yake dubawa a tsanake ba tare da ya dubeta ba yace.”Waye Dantalle.”? Sai tayi saurin kallonsa….Hankalinsa nakan wayar yana kokarin serving din number Ya sake maimaita tambayarsa……A sanyaye tace”Wani mutumi ne a garin tun zuwa na na farko yake naci wai sona yake.”

Miqewa yayi tare da mai da wayarsa aljihu Yace.”Okey na fahimta to Allah ya tabbatar da alkairi a tsakaninku Wannan number kuma nayi serving insha Allah gobe ko jibi zan kawo miki waya sai ku dinga gaisawa idan kin haihu sai ki fad’a musu dan na fahimci matar tana kaunarki sosai.”

Maganar Allah ya tabbatar musu da alkairi da Dantalle itace duk ta ragargaza mata duk wani farin ciki da annushuwar da take ciki! sai ta shiga tunani gami da nazarin inda maganar tasa ta dosa! Me yake nufi ne?? Bayansa tabi da kallo har ya fice daga dakin bata samu damar yin wata magaba ba 

Jiki a masifar sanyaye ta koma ta kwanta ai sai hawaye suka ‘balle mata suka dinga fita tamkar wanda aka kwance famfo yanzu idan yace ba zai mayar da ita ba to wa zata aura? waye zai riqe mata d’anta? Waye zai tallafa mata kamar yanda yake mata, gaskiya idan yaqi mayar da ita gidansa ya cuceta dan ta riga ta gama sa rai ganin irin wahalar da yake mata shiyasa ta sakankance da cewar yana jira ne ta haihu ya bijiro da maganar da kowa yake tunaninta a kansa

Shi kuwa yana fita motarsa ya shiga a gurguje ya nufi gidan mutuwar domin yayi gaisuwa ya wuce harkokinsa, gabad’aya bai sanya lamarin Naja’atu a cikin ransa ba ballantana ya dameshi yana fitowa daga inda take ya ajiyeta a gefe guda ba zaije ko’ina da damuwarta ba bare ta hanashi gudanar da abubuwan da suke gabansa.

Koda su hajia suka dawo kasa gane kanta sukayi, hajia ta dinga tambayarta ko wani abu na damunta, girgiza kanta kawai takeyi tace”Babu komai baccin data yini tanayi ne ya sanya yanayin ta ya sanja to hajia dai taji ne amma bata amince da maganar ba, haka yamma tanayi data fahimci ya kusa shigowa gidan sai kawai ta shige daki ta kwanta bata so ta ganshi saboda gudun abunda ka iya zuwa ya dawo tana ganin zata iya fashewa da kuka mutukar zata kalli fuskarsa.

To shima a nasa ‘bangaran bai damu da rashin ganinta a falon ba bayan sun gaisa da mahaifiyarsa sai kawai ya ajiye ledojin hannunsa wanda ita tasan ko na menene kayan ciye ciyen Naja’atu ne wanda yake siyo mata kullum ta Alla…..Sallama yayi mata yace.”Idan ya fito daga massalaci gida zai wuce ba zai dawo ba. Hajia tayi masa fatan alkairi tare da bashi saqon gaisuwarta gurin su Saddiqa, ba tare da damuwar komai ba ya bar gidan.

Koda ya isa gidan nasa kai tsaye gurin Halisa ya nufa duk da cewar ba itake keda girki ba, sai da ya duba ta sosai sannan ya fito ya nufi gurin Zainab….Ita da yaran suna zaune a falo gwanin sha’awa sukayi masa sannu da zuwa ya amsa a sake, yana kallon Zainab yau tayi kwaliya sosai sai dai babu walwala a tare da ita, bece mata komai ba ya nufi dakinsa, ta mike tabi bayansa tana wani cika da batsewa.

Ya tu’be kayan jikinsa yana kokarin shiga wanka ta shigo dakin sai ya tsaya yana kallonta har ta qaraso ta samu guri ta zauna tare da fadin.” Abban Mufida sannu da zuwa.” Ya amsa yana sake nazarinta yace.”Da alama yau akwai abunda ke damunki na karanci rashin walwala a fuskarki ina fatan ba yaro na bane yake takura miki.”

Girgixa kanta tayi tana dan ta’be bakinta tace”Idan shine yake takura min ai da sauqi Abban mufida zuciyata ta kasa nutsuwa kwana biyu sai tunani nake da wasiwahsi dan Allah kada ka dauki maganata da wata manufa naga kamar kana so ka dawo da Naja’atu gidanka saboda dawainiyar da kake mata har taso tayi yawa wani abun ma sai dai mu samu labari, nida aunty Halisa kullum cikin tunani muke idan dawo da ita za kayi gwara kawai ka fad’a mana mu sani dan ina ganin kamar ‘boye-‘boyen da kake mana sam bashi da wani amfani.”

Tunda ta soma maganar ya zuba mata ido yana kallonta mamaki yana kasheshi! shi dai tunda Allah ya had’ashi aure da qananun yara yake ganin rashin kunya iri iri….Wai Zainab ce ta turkeshi take kokarin sai ta ‘kure shi a ganinta yana ‘boye musu abinda ke tsakaninsa da Naja’atu, idan tunaninsu kenan to babu shakka zai basu mamaki! Dauke kansa yayi daga kanta ba ta tare da yace mata komai ba ya nufo toilet cikin d’umbun mamakin yarinyar.

*NA DAWO????????‍♀️*

*’Kawata matso kiji wata magana mai muhimanci???????? nasan kin san da cewar yanxu muna lokaci na sanyi jiki na bushewa kammani na sauyawa????????‍♀️ to bari kiji wata magana maza a irin wannan lokacin jaraba da fitinarsu take tashi, me ya kamata kiyi domin ganin kin gyara kanki da kowane lokaci mijinki na samun nutsuwa dake???? Kada ki mayar da hankalinki kacokan kan gyaran fatar jikinki baki inganta ni’imarki ba???? Ina amfanin fatar ki tayi luwai luwai kina gayu da tunkawo kuma sai dare yayi maigida yaji guri a bushe????????‍♀️ kada ki sake haka ta faru ‘Kawata! kamar yanda zaki kula da fatar jikinki to ki kula da Ni’imar ki ya kasance kullum idan maigida yazo yaji zam!zam???? kada kiyi wasa da shan ruwan kaninfari had’e da shan kayan marmari ina ganin koga wannan kika tsaya zaki gamsar da maigidanki……..Wannan itace tsarabar da nake tafe da ita????????‍♀️*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button