MADADI Page 81 to 90

Vip gruop#600 normal group #300 account.. 0542382124.//Binta umar gtbank …..WhatsApp number…. 07084653262
*MADADI*
70Zainab na zaune tana sa’kawa da kwancewa ya fito daga toilet yanda taga fuskarsa a had’e! shine yasa jikinta mutuwa gabanta ya dinga fad’uwa, tana kallonsa har ya kimtsa jikinsa ya kama hanya ya fice daga dakin ba tare da ya tanka mata ba…Jikinta a mace ta miqe salo salo tabi bayansa falon gurin cin abinci ta sameshi a zaune yana duba karamar wayarsa Saddiqa na kokarin zuba masa abinci.
Da sauri ta karasa gurin, cikin kokarin wanke kanta ta kar’bi plate din dake hannun Saddiqar tace taje ta zauna.
Abbah duba wayarsa kawai yake yi bai kalleta ba har ta gama zuba masa abinci ta ajiye masa a gabansa, ya ajiye wayar a nutse ya dan yanyo plate din gabansa yayi bisimillah kamar koda yaushe ya fara cikin abincin.
Ta kalleshi a sanyaye tace”Abban Mussadiq naga kamar maganata ta ‘bata maka rai dan Allah kayi hakuri wallahi ni haka nake bana iya ajiye abu a raina.”
Yayi mata wani kallo mai kama da harara yace.”Surutu da fad’i ba’a tambaye ki ba shine yake damunki ba abinda kika fad’a ba, Okey zan kira Halisa yanzu itama naji ta bakinta akan maganar da kika fad’a min tunda kun dauke ni munafiki wanda ke ‘boye muku tsakaninsa da Naja’atu.”
Da sauri tace”Wallahi ba haka nake nufi ba shiyasa fa tun farko kafin na fad’i maganar nan sai da nace ka fahimceni amma meye sai an kira anty Halisa dan Allah kada ka kirata.”
Yace.”Ai a inda ba qasa nan ake gaddamar kokawa tunda kince keda ita kuna cikin wasiwahsi kullum kuna tunani da zargina kan na ‘boye muku wani abu to dole itama tazo ta fad’a min da bakinta kamar yanda kika fad’i naki.”
Zainab idonta ya ciko da kwalla! Tunda suke basu ta’ba zancan Naja’atu da Halisa ba, tunda ta ta’ba yi mata maganar a gidan Alhaji Halisan ta nuna bata son maganar bata qara tunkararta ba ita kadai abun ke damu kawai ta sako sunan Halisa a cikin maganarta ne wai ko zai dauki abun da muhimanci ya fad’a musu abunda ke zuciyarsa.
Yana kammala cin abincinsa ya barta a gurin yaje ya zauna kan kujera yana kiran wayar Halisa…..Zainab kasa motsawa tayi tana zaune a inda take har Halisa ta shigo falon…..Umartar su Saddiqa yayi dasu je su kwanta, yaran suka miqa da sauri suka nufi dakinsu.
Halisa ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa itama tunda taga yanda yasha kunu sai tasha jinin jikinta, barka da dare tayi masa taja bakinta tayi shuru.
Ba tare daya juya ba yace.”Zainab zo nan.” Ta miqe a hankali taje ta zauna nadama da dana sani kawai takeyi data san tozartata zaiyi a gaban kishiya da ta daure ba tayi masa maganar ba…..Ya kalli Halisa a kaurare yace.”Ashe idan bana nan munafurcina kukeyi? Har kuna zargina akan ina ‘boye muku tsakanina da Naja’atu shin idan nace zan dawo da ita akwai wacce ta isa ta hanani dawo da ita a cikinku.”!
Halisa ta bud’e bakinta cike da mamaki da tsoro tace”Yaushe akayi hakan Abbah Mufida wallahi duk wanda ya fad’a maka maganar nan karya yake ni meye nawa a ciki idan ka dawo da Naja’atu gidanka gaskiya ka ‘kara yin bunkice a kan maganar nan..”
A tsanake ya kalleta ya kalli Zainab da tayi tsuru tsuru nan ya tabbatar da cewar ‘karya yarinyar tayiwa Halisan, yace.”Ba wani ne ya fad’a min ba Zainab ce gata nan tana jinki abunda yasa kuma na yarda da maganarta saboda ina ganin zaki iya aikata hakan tunda kema ba qaunar Naja’atun kike ba.”
Halisa tace.”To ikon Allah idan da ranka kasha kallo ina zaune anyi min sharri yanzu ke dan Allah dan annabi Zainab yaushe mukayi wannan maganar dake ashe kin manta maganar da mukayi dake a gidan alhaji, haka kawai zakiyi maganarki sai kisa sunana.”!
Ganin yanda Halisan ta hasala! ne yasa ya daga mata hannu yace.”Ya isa! kina nufin ba kiyi ba kenan.”? A fusace! tace”Wai dan Allah wace irin magana kakeyi? da da yanzu ba d’aya bane kai kanka ka san yanzu na gyara kuskurena sannan naji kana wata magana wai bana qaunar Naja’atu shiyasa zan zauna da Zainab mu zageta! a kan wane dalili ni Naja’atu da iyayenta basuyi min komai ba wallahi saboda haka ko yau ka dawo da ita gidanka ina maraba da ita.”
Tana gama maganarta ta miqe rai a ‘bace! ta fita daga falon……..Maganganun da Halisa tayi ya nuna masa gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta, kuma yaji dadin hakan Halisa ta daina adawa da Naja’atu ta barwa Zainab, a nutse ya juya yana kallonta tayi tsilli tsilli kunya da nauyi duk sun rufeta sai yanzu ta gane itama wauta da kuruciya na damunta to idan ba haka yaushe ma zata turkeshi da irin wannan maganar.
“Zainab.” Ya kira sunanta tare da tsira mata idonsa, ta amsa murya na rawa. Yace.” Saboda ina yiwa Naja’atu hidima kike ganin kamar zan dawo da ita gidana.” Fashewa tayi da kuka tace”Aa wallahi.” Yace.”Hakane mana! kina kishi da Naja’atu alhalin zama bai ta’ba had’aki da ita ba, to ki kwantar da hankalinki kinji ko dik wata hidima da kika ga inayi mata inayi ne dan Allah da manzonsa da kuma tausayawa abinda ke cikinta, amma babu maganar na sake zaman aure da ita! saboda haka ki samu nutsuwa ki daina wasiwahsi kamar yanda kika fad’a! Sai dai da kowane lokaci zan iya kawo muku abokiyar zama dalili ni mutum ne meso ya cikasa sinnar ma’aiki Annabi Muhammad (slw) inaso kafin Allah ya dauki raina na had’a mata hudu a gidana su haifa min tarin yara masu albarka saboda haka kisa a ranki cewar akwai sauran abokanan zamanki da zasu zo mutukar Allah ya qaddara min hakan.”
Zainab shuru tayi tana goge hawaye itakam wauta da rashin dubara na damunta amma daga yau tayi alqawari zata dinga kiyaye harshenta domin gudun abunda ka iya zuwa ya dawo, dan gaskiya itama ba laifinta bane kishin naja”atu ne ya tunxura mata zuciyarta amma dai za tayi kokarin ganin ta dauke kanta akan dukkanin abinda zata gani ko taji labarin yayiwa Naja’atun..
To kamar yanda yayi mata alkawarin zai siya mata waya hakan ya faru dan Abbah Abbas waya mai kyau da tsada ya siya mata sabuwa dal a kwalinta, ranar da ya bata wayar tayi ta murna da farin ciki tana masa godiya. babu wanda ta fara kira da wayar sai Mmn Sajida. suka shafe mintina da dama suna hira A gaskiya Naja’atu tayi farin ciki da samuwar wayar a hannunta dan sabida tasan ba qaramin kewa zata d’ebe mata ba.
******
“Kaga Salisu ina jin tsoron ranar da asiri zai tuno ni dai da zaka bi ta shawarata da kaje ka samu mutumin nan kayi masa bayani watakila ma yace mu rike kudin tunda nasa ne .” Mahaifiyar Naburago ce take wannan maganar
Gyara zamansa yayi yana kallonta yace.”Haba Mama ki daina tsoro mana babu ta yanda zaayi asiri ya tuno kudi sun riga sun shigo hannuna.” Tace.”A’a ni daina nafi so kaje kayi masa bayani wannan kudin ba zasuyi maka albarka ba tunda na sata ne kaga kenan sata ta saci sata kaima idan da tsautsayi wani sai ya damfare ka tunda dai kasan inda zaka samu mutumin nan to kaje kayi masa bayani ka bashi hakuri ni na fada maka ba zaice komai ba watakila ma yace ka rike kudin.”
Naburago yace.”Mamma wannan shawarar taki gurguwa yace yama za’ayi na samu kudi a sama kice naje fad’awa wanda yake dasu ni ba zanje ba wallahi, na riga na shirya tsaf akwai sana’ar da nake so na fara dasu sana’a ce mai inganci kuma ina da ya’kinin zata kawo min kudi dan lokaci guda zan zama multi mollonia.”.. Girgiza kanta kawai tayi tace.”Shikkenan ai tunda kaki daukar shawara.” Miqewa yay ya kama hanya ya fita, kai tsaye ya hau sabon babur dinsa wanda ya siya dubu dari biyu da hamsin, sannan yayi sabbanin d’unkuna ya kuma bibbiya bashin da ake binsa, daga haka sai kawai ya cigaba da facakarsa da kudin, dan ita kanta wacce tayi sanadiyar samuwar kudin da kyar yake bata wani abu, Naburago ya tattare kudin yayi bukatarsa dasu yanzu saura dubu dari takwas dasu yake so ya fara sanar cah-cah dan yana ganin yanda sana’ar take sanya mutane da yawa suyi mahaukanta kud’i to shima dama rashin kudi a hannu ne yasa bai fad’a harkar ba tunda yanzu ya samu dama to zai shiga a dama dashi, babur dinsa ya hau ya nufi mahad’arta su.