MADADI 1-END

MADADI Page 81 to 90

 *****

‘Bangaran ‘Yar Sa’adu kuwa sai da tayi sati a barikin sojoji suna azabtar da ita sannan suka saketa ta dawo gidanta a mutukar galabaice jikinta duk yayi rud’u rud’u da shatin bulala abinka da farar mace ko’ina yayi tabo a jikinta, haka ta kwanta ciwo duk a cikin matan dake mata fadanci a kara rasa wacce zata zauna tayi jinyarta, sai da ta dan samu sauqi ta tattara komatsanta ta tafi garinsu tana ganin ba zata iya cigaba da zama ba haka kawai tana zaune wata ta sake janyo mata masifa gwara ta koma garinsu ta cigaba da harkokinta a can.

****

To kwanaki na tafiya wattani na shiga suna mutuwa, komai na tafiya ne da ikon Allah da kuma amincewarsa Naja’atu al’amuranta sun tsananta dan dab take da haihuwa cikinta ya shiga wata na tara har yayi kwanaki! gabadaya hankalin wanda yake kusanci da ita ya tashi saboda tunda cikin ya shiga wattanin haihuwarsa ta kumbura mussaman qafafunta, duk da Likita ya dubata ya tabbatar musu da cewar babu matsala hankalinsu bai kwanta ba. Abbah Abbas da hajia sunfi kowa tada hankalinsu a kan al’amarin….Baba malam da baba talatu kawaici da alkunya yasa duk damuwar da suke ciki game da ‘Yar tasu sun kasa nunawa gabad’aya ma Baba talatu d’auke kanta tayi da kanta sai dai kullum cikin yi mata addua take……B’angaran Abbah Abbas kuwa gudun zargin da mutane ke masa yasa yake boye damuwarsa akan halin da Naja’atu take ciki amma zahirin gaskiya yana cikin tsanani da damuwa mussaman idan yazo gidan ya ganta a jibge a kan kujera! sai dik jikinsa ya mutu kullum haka yake yini ya kwana cikin alhini da jiran tsammani yanda ma ya damu da haihuwar Naja’atu kamar bai damu data Zainab ba su kansu matansa sun fahimci hakan sai dai kowacce na kokarin dauke kanta akai amma hakikanin gaskiya abun yana damunsu mutukar aka cigaba da tafiya a haka to suna cikin matsala gwara ya dawo da ita gidan hankalinsu zaifi kwanciya akan ya dinga shiga halin damuwa akanta.

Ranar Alhamis da daddare ta farka da ciwon haihuwa mai tsanani dama tun sanda cikin nata ya tsufa Yaya Ramlatu take kwana da ita a daki, jin motsinta yasa ta tashi da sauri tana tambayarta, Naja’atu na zufa tana kiran sunan Allah tace”Watakila haihuwa zanyi dan ciwon da nake ji yafi na kullum.” Ya Ramlatu tace”To ikon Allah bari na kira hajia sannu kinji ko.” Fita tayi daga dakin da saurin gaske……….Tare suka dawo dakin da hajia da sauri ta d’ago ta ta rungumeta a jikinta, tana mata sannu! Yaya Ramlatu ta shiga hada kayan haihuwa! Hajia t”Ta kalli Ramlatu da fadin”Ki sanar da hajia Rabi Naja’atu na kan gwiwa.” Ya Ramlatu da sauri ta futa daga dakin…Hajia ta rike ta sosai tana tofa mata adduoi…. lokacin ita Naja’atu, ciwon ya tsananta dan dab take da haihuwa, shiyasa ta kasa tsugunawa sai kawai ta silale a gurin ta kwanta tana wani irin kifkif da idanunta! hannunta tasa ta janyo na hajian tana jan salati! Hajia ta shiga tashin hankali ganin irin abinda Naja’atun takeyi sai hawaye ya soma zubo mata addua take Allah y yanke mata wahala…..Hajia Rabi da Ramlatu na shigowa faya ta fashe! sai yunkuri kawai sukaji tana wani irin nishi!! da sauri suka rufu a kanta kowanne na iya bakin kokarinsa…..Naja’atu Ganin Yaya Ramlatu itace mai kwari a cikinsu sai kawai ta d’amko ta ri’keta gam! gam! a tare suka dinga nakud’ar suna nishi! tare! Sosai Ramlatu taji jiki ta kuma tabbatar riqon bana Naja’atu bane na mala’iku ne…….Cikin ikon Allah da hukuncinsa yaro ya fad’o a cikin zanin da suka rufa mata, sai kawai kukansa sukaji….Ajiyar zuciya suka sauke dukkaninsu suka had’a baki gurin fad’ar “Alhamdullhi.”

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button