MADADI 1-END

MADADI Page 81 to 90

Koda ya duba cikin motar yaga bata ciki bai damu ba saboda yasan bai kulle motar ba zata iya budewa ta shiga cikin gida……sai kawai ya nufi gidan Alhajin dan nan yake tsammanin samunta. 

Lokacin Naja’atu da yaran suna sama gurin hajia dan bayan tayi sallar jansu tayi domin suyi mata jagora zuwa gurin hajian masifar kunyar had’a ido take yi da ita shiyasa taja yaran domin su zame mata garkuwa.

Magana yaji ‘kasa-‘kasa a cikin dakin dasu Halisa suke, sai kawai ya nufi dakin dan yaji kamar muryar Zainab na magana…….”Nifa aunty Halisa jikina yay sanyi wallahi anya kuwa Abbansu Mussadiq ba mayar da Naja’atun nan zaiyi ba? Kinga ni mahaifina malami ne amma ba malamin zaure ba malam ne mai fad’a akan abi sunna gami da dokokin ubangiji mu ba ma asiri da tsafi! amma tun kafin na auri mijinki muka samu labarin abinda ke faruwa ance shi wannan Baba malam din asiri yake yi ya asirce Alhaji dashi Abbansu Musaadiq din sannan kuma baya bari ‘ya’yansa su wulakanta kullum cikin aiko musu da asiri yake shiyasa da waccar matar tasa ta rasu aka dauki qanwarta aka maye gurbin ta! wallahi ganin yanda kowa yake rawar jiki akan Naja’atun nan yasa jikina ya mutu wani irin tsanarta nake ji a cikin raina.”

Halisa ta ajiye carbin hannunta tana wani irin murmushi kai da ganinsa kasan na takaici ne tace”Zainab kenan to ni kam bansan abinda zance miki ba, tunda kin yarda da cewar Baba malam asiri yake sai kiyi takatsantsan da kanki kowa ya iya allonsa ya wanke ni yanzu duk ba wannan ne a gabana ba, maganar wai Abban Mufida zai dawo da Naja’atu gidanshi, ban sani ba, idan ma ya dawo da ita ni babu abinda ya dame ni ko wacce tata ta fishsheta.”

Zainab tace”Aikuwa mu bama boka bama malam Allah kad’ai muka dogara dashi saboda haka banga asirin da wani boka zaiyi yayi tasiri a kaina ba.”

Duk wannan maganganun a kunnansa, gaskiya yayi mamaki sosai! wai me yasa mutane suke hakane? duk wanda akaga babu ruwansa da duniya yana bin Allah sau da qafa sai a takura masa , tunda ya taso a unguwar kofar na’isa bai ta’ba jin wani yayi mummunar kalma akan Malam Sani ba, sai Halisa itace kullum ke kiransa da boka ko dan tsubbu to yau gashi an wayi gari itama Zainab tana kiranshi da wannan sunan duk kuwa da cewar ta fito daga cikin gidan da ba’a yarda da shirka da asiri ba gashi kishi yasa tana gazgatawa! duk akan ya tsaya a cikin al’amuran Naja’atu suke wannan surutan har suna zargin ko zai mayar da ita dakinta hmmmm! baya tunanin zai sake zaman aure da Naja’atu a yanzu duk wani abu da yake a kanta yanayi ne domin Allah da manzonsa da kuma lalurar cikin da take dauke dashi,

 Gyaran muryarsa ne ya dawo dasu hankalinsu, ya shiga dakin da sallama a bakinsa, Zainab da sauri ta riga Halisa magana tana wani irin murmushi na iyayi da kissa tace”Habibi sannu da zuwa ina fatan ka dawo lafiya.” ? Ba tare da yayi mata cikakken kallo ba ya amsa yana kallon Halisa da tayi qasa’ke tana kallon ikon Allah…Zainab ganin yanda ya amsa mata a banzace sai jikinta yayi sanyi tunda take dashi bai ta’ba yi mata irin hakaba.

Halisa ta gaisheshi a nutse tana tambayarsa hanya ya amsa babu kyakkyawar walwala a tare dashi yace.”Waye ya baku izinin zuwa nan gidan ku kwana.”? Sai sukayi tsuru tsuru suna kallonsa domin duk cikinsu babu wacce take da hujja.” Halisa da yake tasan halinsa idan yana fushi ba’a katse masa hanzari sai taja bakinta tayi shuru…..Ita kuwa Zeey sarki karambani tace”Habibi Hajia ce tac…….Hannu ya d’aga mata da fad’in “Rufe min baki sarkin magana! Hajia ce tace me? kina so kiyi mata karya ko.”? shuru tayi tana girgiza kanta, Yace.”Dama ai so nake na dawo na tambayeki dalilin daya sa kika fitar da hannu kika mari Yaya Ramlatu ashe dama baki da kunya da tarbiya.”? Halisa cikin zuciyarta tace ” Anzo gurun.

Zainab ta fashe da kuka tana kallonsa tace”Waye ta fada maka na mareta wallahi ni sharri akayi min yaushe ma zan mareta ba haba sai kace mara hankali itace fa kawai ta shigo gurina tana zagina amma ni ban mareta ba sai dai itace ma ta dokeni iya son ranta.”

Yace.”Bakin daya fad’a min ba zaiyi min karya ba kin mare ta ko baki mareta ba.”? Zainab ta dinga rantse ranste ita bata mareta ba sai kuka take tana neman mafita…..Yana ‘kokarin yin magana hajia tare dasu Naja’atu suka shigo dakin…Ganin Zainab na kuka yasa hankalinta ya tashi tace”To me yake faruwa haba kai kuwa daga dawowa sai ka aikata abunda bai dace ba .” Yace.”Hajia yarinyar nan bata da kunya wallahi wai sun samu sa’bani da Yaya Ramlatu shine ta fitar da hannu ta mareta.”

Hajia tace”Subahanallahi yaushe akayi hakan.”? Ya kalli su Saddiqa da fad’i! Saddiqa Zainab ta mari Yaya Ramlatu ko kuwa.”? Saddiqa da sauran yaran suka sunkuyar da kansu saboda basu iya karya ba.”

Yace.”Yanzu kin tabbatar da ba sharri akayi miki ba ko, a gabansu kika tsinkawa uwarsu mari sabida baki da kunya ko me tayi miki ai sai ki bari na dawo ki fada min aa sai ki ka shirya karya da gaskiya kika kira ni a waya kika fad’a min to jiya Salim ya sheda min duk abunda ya faru a tsakaninku.”

Zainab bakinta ya mutu murus sai hawaye dake zubo mata ta kasa magana ma ballantana ta kare kanta, Hajia tace” Idan ya kasance Zainab ta mari Ramlatu sai mu kira al’amarin da sunan hakkin wasu ne ya kama ta! Shin Ka tambayi dalilin zuwanta gidanka? Ramlatu ni na haifeta amma nafi kowa sanin halinta taje gidanka domin ta ‘bata maka iyali da mugun halinta ni banga laifin Zainab ba sabida hausawa nacewa(Idan babba ya zubar da girmansa sai na qasa dashi ya hau kai ya taka) sabida haka idan za kayiwa yarinyar nan fada kayi mata akan wani abu daban ba’akan Ramlatu ba wacce idan ta samu damar da take so ba zata bari ma ka zauna da iyalin ka ba.” Jikinsa ne yayi sanyi kuma dajin maganganun hajian, Hakane tabbas Ramlatu ta samu damar da take so a kansa zata iya hanashi zaman aure da mugun halinta abinda yasa yake wa Zainab fada yana so ya nuna mata girma da mutuncin ‘Yan uwansa kodan gaba zata kiyaye aikata abinda ta aikata.

Fita yayi daga dakin…. Hajia kuwa sai da ta tsaya ta rarrashin Zainab din kafin ta fita daga dakin.

Abbah Abbas yana zaune a kan kujera yana jiran fitowar mahaifiyar tasa su gaisa, a fakaice yake satar kallon Naja’atu dake zaune da yara suna magana, tayi wanka har ta sanja kayan jikinta sabuwar atampa hajia ta bata tasa a jikinta duk sai ta dawo hayyacinta, ya dinga satar kallonta ta’kasan idonsa yana mamakin uban haske da tayi a ganinsa hasken yayi yawa kuma baiyi kama dans ciki ba na rashin jini ne dan haka koda hajia ta fito suka gaisa yace yana ganin ko za’a kaita a asibiti a dubata dan yana tunanin akwai karancin jini a jikinta…..Hajia ta shiga duban Naja’atu tana nazarinta itama taga haskenta yayi yawa mussaman hannayenta da kafafunta, tace”To hakan ma nada kyau sai a bari sai zuwa gobe ko hajia Rabi sai ta kaita a dubata naga cikin nata ma yayi kwari.” Yace.” To babu laifi Allah ya kaimu goben lafiya……A nutse ya kalli Mussadiq yace.”Jeka kira Mommy da auntyku zamu tafi gida.”Yaron ya miqe da sauri ya nufi dakinsu…………….Yaya Ramlatu ce ta shigo gidan tana kuka sai kace ‘kan’kanuwar yarinya ta wani fad’i gaban mahaifiyarta tana sheshsheka da fad’in “Hajia na shiga uku na lalace! Ayuba ya cuce ni ya sake ni.” Sai ta fito da takardar sakin dake hannunta ta jefar da ita kusa da kafafunsa….Da sauri ya dauki takardar ya warware ya soma karantawa……Da gaske Ayuba ya saki Ramlatu saki daya amma bai fadi dalili ba yace sai yazo yayi bayani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button