MADADI 1-END

MADADI Page 81 to 90

Hajia ta shiga rud’ani sosai! to wai wace irin masifa ce ta rikito musu a cikin lokaci guda, Allah ta shiga kira a cikin zuciyarta tana ro’konsa ya kawo musu mafita……Abbah Abbas ya miqe a fusace! yace.”Wane irin sakin wulakanci ne wannan kawai babu laifin komai sai ya sake ki ai kamata yay yayi mana bayanin abinda yake faruwa.”…….Ramlatu za tayi magana sai ga Alhaji da Ayuban da Salim sun shigo palon kallo d’aya yayi musu yasha jinin jikinsa ganinsu yayi wani irin kamar wasu marasa lafiya suka nemi guri suka zazzauna, Ramlatu ta sake fashewa da kuka! Da fad’in “Wallahi tallahi bani na tura shi ya aikata wannan aika aikan ba. Ya ma za’ayi na had’a baki da d’ana a cutar da d’an uwana.”…………

*Littafin na kudi ne…!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin ga yanda abin yake….Vip group #600 normal group #300 account….0542382124…..Binta umar gtbank..Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number…

*07084653262…BINTA UMAR ABBALE*

65 Gabakid’ayansu hankalinsu ya koma kan Yaya Ramaltu dake wani irin kuka tana sake nanata maganarta ta farko na cewar ita ba itace ta tura Salim yaje ya aikata abinda ya aikata ba….

Alhaji ya buga mata tsawa da fadin.”Rufe mana baki.mutuniyar banza mai ba’kin hali Ramlatu nayi nadamar haihuwarki tun kina yarinya kike bani wahala na rasa a wane guri kika dauko wannan mummunan halin naki yanzu ki rasa wanda zaki cuta sai dan uwanki wanda kika sha nono kika bashi kike wa qeta shin me Abbas yayi miki a duniya wanda zai sanya ki had’a bakinki da d’anki ku sa masa wuta a cikin dukiyarsa.”

Abbah da hajia sukayi saurin kallon alhjin jin maganar da yake, hankali a tashe hajia tace”Wai shin me yake faruwa ne ku fad’a min na rasa gane inda maganarku ta dosa.

Alhaji ya kalli Ayuba da fad’in “Yana da kyau ka fad’i maganar data kawo ka a gaban kowa yaji cewar wad’annan mutanan ba mutanan arziki bane.” Yafada yana nuna Ramlatu da Salim dake zaune duk sun muzanta.

Ayuba yace.”Hakika na jima ban shiga tashin hankali da mamakin abinda kunnena yaji min ba a yau .Na dawo daga sallar asubah nazo gifta dakin Salim sai naji maganarsa da mahaifiyarsa sama sama nayi mamaki sosai dan na dauka yaron yaje sallah kamar yanda na shiga na tashe shi kafin na fita, ashe bayan fita ta mahaifiyarsa ce ta shiga dakin ta hanashi zuwa massalacin……..Lokacin da naji maganar da suke tattaunawa akai sai da na kusa fad’uwa sabida tsananin mamaki da al’jabi Salim na shedawa mahaifiyarsa cewar shine ya kunna wuta a cikin rumfar dan uwanta dake kasuwa, sai nayi shuru ina sauraran naji abinda zata ce. Kawai sa naji tana fad’in “Ya kyauta mata hakan da yayi dama saboda dukiya Abbas ke wulakantata har da dauko mata police yazo har gida yaci mutuncinta saboda haka idan ma da akwai wata hanyar da yaron zai sake bi yaga ya kassara dan uwanta to ta bashi goyon baya yaje yayi ya kuma cigaba da nuna masa cewa shi mai kaunarsa har dai bukatarsu ta biya suga sun kai Abbas d’in k’asa! wannan al’amari ya d’aga min hankali mutuka dan ban san sanda na fad’a dakin ba, suna ganina duk sai suka diririce alamun rashin gaskiya ya bayyana a idonsu.

Cikin takaicin da tsananin bacin rai da damuwa nace musu duk naji abinda suka aikata ashe dama sune silar faruwar gobarar data cinye dukiyar Alhaji Abbas? sai dukkaninsu suka shiga rantse rantse cewa basu bane gabadaya ma ba maganar suke ba…..Alhaji ku yafe min a lokacin ji nayi ina nadamar auran Ramlatu ina kuma nadamar hada zuria da ita! hakika tunda na auri wannan baiwar Allah na kasa samu nutsuwar zuciyata kasancewa ta matafiyi duk sanda zan dawo sai jama’ar unguwa makusantana sun kawo min magana a kanta, cewar kullum a kan hanya take bata zama gida itace shiga can fita can! tun a wancan lokacin zargi ya shiga tsakanina da ita sabida kowa akwai maganar da zai kawo min a kanta……Allah ya had’ani da mace tagari Sakina kullum itace ke hanani na aikata abinda nayi niyya akan Ramaltu Sakina mutuniyar arziki ce kuma tana kaunar zama da Ramlatu da shiriyarta shiyasa ta juri cin mutuncin da take mata…..Ban ta’ba jin tsanar Ramlatu ba irin yau! jin mummunan aikin data tunzura d’anta yaje ya aikatawa d’an uwanta wannan dalilin yasa naji kamar naje na dauko musu hukuma a tafi dasu dan gabadaya zama dasu annoba ne tunda sun zama ‘yan ta’addah gwara suje su fuskanci hukunci sai kuma nayi tunanin cewar ai bani da hurumi yin hakan, wannan dalilin yasa ni na yanke shawarar rabuwa da ita dan gaskiya dama can zama hakuri kawai nake da ita, idan ina gurin sana’ata hankali kwata kwata ba a kwance yake ba saboda ina tunanin abubuwan da suke faruwa a gidana, jama’ar gari da abokaina gabadayansu babu wanda yake wa Ramlatu kallon mutuniyar kirki harda masu kiranta karuwa! wannan kalmar na daga min hankali mutuka! shiyasa na gaza samun nutsuwar zuciyata da ita gurin mu’amular aure……….Ina rokon ku afuwa kan hukuncin dana yanke a kanta kamar yanda na rubuta mata saki daya jikin takarda hakane na sake ta saki daya idan ta samu miji tayi aurenta kai kuma Salim babu ni babu kai na yafe ka a duniya tunda ka zama butulu maci amana.” Ayuba ya kare maganar muryasa na wani irin rawa.

Gabad’aya palon shuru yayi kowa na mamaki da Tu’ajibun wannan al’amarin….Hajia Kuka take tana Kallon Ramlatu tana so tayi magana amma tsabar damuwa da ‘bacin rai ya hana ta iya cewa komai………Wani sabon kukan suka ji da sauri suka kalli inda kukan ke tashi…Halisa dake tsaye a bakin kofar daki ta karaso cikin palon tana hawaye cikin tsananin damuwa gami da nadamar abinda suka aikata a baya, ta kalli Ramaltu tace”Nima babu abinda zance dake sai dai na had’aki da Allah ya saka min kin cuce ni kin cutar da d’an uwanki sannan kin cutar da baiwar Allah Halimatu wacce ba taji ba bata gani ba! wallahi tunda uwata ta haifeni ban ta’ba zuwa gurin wani boka ko malami ba wai dan yayi min duba ko yayi wa wani asiri sai da kika shigo rayuwata kika lalatani da zuwa gurin bokaye! wane gari ne baki jani kin kaini ba, har tsutsa sai da kika kaini gurin bokan da ya bani naci! a matsayinki na ‘yar uwar mijina bai kamata kiyi mana hakaba kin cutar damu Allah zai saka min gashi garin biye biyen bokaye gami da shaye shayen maganin mata kinsa na had’u da lalura mai wahalar magani ni kuwa me zance miki a rayuwata wallahi Yaya Ramlatu kinci amanar zumunci.”!

Yaya Ramlatu ta dinga kuka tana had’a hannuwanta guri da fad’in “Ku gafarce ni nima ba laifina bane sharrin shedan ne wallahi kuyi min addua Allah ya gafarta min laifukana.”

Gabad’aya palon suka zuba mata ido jin maganganun da takeyi tana kuka….Naja’atu murya na rawa tace”Salim idan ban manta ba ka ta’ba fad’a min wata magana a kan Abbah cewar a kwai lokacin da kake so ka rabu dashi bayan bukatarka ta biya a kansa! ashe wannan ne lokacin kana so ka cutar dashi ko? yanzu meye ribar abinda ka aikata masa? kada fa ka manta Abbah yayi maka abinda iyayenka da suka haifeka ba suyi maka ba me yasa kake cin dunduniyarsa? kana nufin dan kasa masa wuta a kan dukiyarsa ya gama arziki kenan? lallai ashe baka da hankali kuma baka san waye Ubangiji ba! a lokacin da hassada da ganin kyashi sukayi yawa a kan mutum a lokacin shi kuma Ubangiji ke qara daukaka darajarsa! wallahi wannan abun da ka aikata a banza domin duk zakaran da Allah ya nufa da cara sai yayi, daga karshe nake so in sake jaddada maka cewar ka samu nasarar raba tsakanina da Abbah ta hanyar zuga ni da nuna min aibunsa tare da tunzurani nayi masa rashin kunya to bukatarka ta biya amma ka sani duk abinda kayi mana mutukar muna da hakki sai Allah ya saka mana sannan kuma insha Allahu sai na koma dakina sai dai ka mutu da bakin ciki.” Cikin kuka mai wahala take maganar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button