MADADI Page 81 to 90

Wannan tone tone da akeyi yayi masifar sanya shi cikin d’imuwa da tashin hankali……
*Ke duniya!!!* ina zaki damu? wai shin me mutane suka dauki duniya ne? duk yanda fa ka tafi da ita haka zata tafi da kai! Jama’a su sakankance a duniya suyi ta shirya mugun abu kamar sun samu madawwama! me yayi wa mutane da dama da suke cin dunduniyarsa ba’a gida ba ba’a waje ba, Yanzu ashe dama da sanya hannun Salim gurin fujirewar Naja’atu gurin rashin so zama dashi, meye ribar abinda Salim yayi masa gashi nan da yake bashi da hakkin kowa tun ba’aje ko ina ba daga shi har uwar tasa asirinsu ya tuno shi kam me zaice da wad’annan bayin Allah.”
Alhaji ya kalli Ayuba da fad’in “Banji ciwo da takaicin sakin da kayiwa Ramlatu ba, shi aure anayin sa ne bisa amana da yarda da juna, kayi kokarin ma tsayin shekaru kana zaune da ita bayan kana zarginta! nima yanzu zargin nata nake saboda dukkanin abinda ka fad’a jama’ar gari suke a fad’a a kanta zata iya aikatawa saboda ba tsoron Allah take ba saboda haka kada ka sanya a ranka cewar ni Sama’ila zan qullace ka dan ka saki Ramlatu nayi maka farin cikin rabuwa da ita.”
Ramlatu na kuka ta rarrafo gaban Alhajin tana kuka tace”Alhaji ka gafarce ni dan darajar annabi ka ro’ki Ayuba ya mayar dani wallahi duk abinda na aikata kuskurene da son zuciya hakika nasan nima ban kyautaba zuciyata ta tunzurani na cutar da dan uwana, sannan wallahi zargin da jama’ar gari suke min ba haka bane! ban ta’ba zina ba nasan dai kullum bana zama a gidana ina yawace yawace amma ba bin maza nake ba
*( qalubale gareku matan dake yawace yawacen banza da wofi haka kurrum ki kulle gidanki kiyi ta shige da fice a unguwa to wallahi yanzu kiwon mutum ake ba dabbah ba, shashahar mace itake yawon bid’id’i! fakal fakal ko wane namiji na qarewa tafiyarki kallo ke idan aka samu ‘yan iska ma kiji wani yay miki magana idan kince ke matar aure yace ya raina miki hankali yace ai ya dauka bazawara ce! hattara mata mu mutunta kanku sai Allah ya mutuntamu)*
Alhaji miqewa yayi ya kama hanya zai hau samansa dan zamansa a gurin yana kallon fuskar Ramlatu zai iya sanyawa jininsa ya hau dama ba lafiya gareshi ba……Ramlatu ta rarrafa gurin Dan uwan nata ta rike masa kafafu tana kuka tace”Abbas ka gafarce ni wallahi sharrin zuciya ne ni kaina na rasa me yasa nake maka hassada duk da cewar babu abinda zan nema a gurinka ba kayi min ba, ka dauki d’ana ka ri’ke tamkar kai ka haifeshi kayi masa komai na rayuwa amma na kasa kyautata maka zuciya na ingixani akan na cutar da kai nima yanzu na gane zuciyata bata da kyau! kayi hakuri ka gafarce ni ka yafe min ka yafewa Salim abunda mukayi maka.”
Abbah ya ciro hankici a aljihunsa ya goge zufar goshinsa hularsa ya dauka yasa cikin wani irin yanayi na damuwa da alhini yace.”Na yafe miki sai ki cigaba da neman gafara gurin Allah ina rokon Ubangiji yasa wannan tuban da kikayi na gaskiya ne.” yana gama maganarsa ya miqe! Salim cikin borin kunya gami da nadama Yace.”Kawu ka duba darajar Annabi Muhammad ka gafarce ni wallahi shedan ne! ya tunzurani cutar da kai yanzu na gane qarya da yawancin wasu abubuwa na mugunta basa lasting Idan mutum naso ya zauna lafiya a wannan duniyar to ya kad’aita Allah shi kad’ai kuma ya ri’ke gaskiya d’aya mutukar yayi haka to zai zauna lafiya kuma koda mutum ya nufe shi da mugun abu to Allah zai kareshi.”
Abbah Abbas ya jima a tsaye yana kallon Salim din dake hawaye kansa a kasa kunya ta hanashi ya dago kai ya kalleshi, yace.”Salim kaima na yafe maka Allah ya yafe mana baki daya.” Ya kalli Hajia cikin wata iriyar murya da bata fita sosai yace ”Zamu tafi.” Hajia ta goge hawayen idonta cikin tausayi da jin kai irin na uwa da d’anta tace” Ina rokon Ubangiji Allah ya ji’banci al’amuranka Abbas Allah ya kare ka ga miyagun mutane da aljanu, duk wanda ke nufinka da sharri Allah ya maida masa kansa, Allah ya daukaka darajarka daukaka mai amfani Ubangiji Allah ya shi maka albarka Abbas hakika ina alfaharin haihuwarka Allah ya albarkaci zuriarka.” Wannan adduar da mahaifiyarsa tayi masa itace ta wanke masa zuciyarsa tayi wasai gabadaya ma yaji ya daina jin takaicin abinda akayi masa……..sai ya kasa ‘boye farin cikinsa ya dinga amsa adduar mahaifiyarta sa yana jin wani irin dadi yana ratsa shi.
To bayan tafiyar Abbah Abbas da iyalinsa Hajia ta kalli Yaya Ramlatu cikin bakin ciki da takaici tace” Ramlatu bana tunanin zan zauna dake a gidan nan sabida haka tun wuri ki nemi inda zaki je ki zauna, Idan ya kama dole sai kin zauna to ni ina iya bar miki gidan dan ni wallahi sharrin ki tsoro yake bani.”
Ramlata cikin sarewa da al’amarin ta nufi mahaifiyar tata murya na rawa tace”Hajia dan darajar Allah kada kije ko ina a kaina kiyi zamanki a dakinki wallahi na tuba nabi Allah na gane abinda nayi ban kyauta ba insha Allah ba zan sake ba ki yafe min Naja’atu kema ki yafe min abubuwan da nayi miki.” Naja’atu ta goge hawayen idonta ta kalli hajia murya na rawa tace”Hajia dan Allah ki yafe mata tunda ta gane kuskuranta kin san adan adam ajizi ne kowa yana kuskure a duniya kinga shima wanda akayi wa laifi kafin ya tafi sai da ya yafe mata tukkuna.” Hajia tace”Humm! Naja’atu kenan har yanzu ke yarinya ce kina ganin kamar abinda take fada har zuciyarta ne nafi kowa sanin halin Ramlatu da rantsuwa kan karya.”
Hajia Rabi dake kokarin shigowa dakin tace”Ke kuwa Hajia ki daina wannan maganar mana, kiyi addua kan Allah yasa tuban Ramlatu na gaskiya ne ni a jikina ina jin cewar karshen matsalarta ne yazo akwai mutane da dama da suke aikata mummunan abu wanda yafi nata su tuba su nemi gafarar Allah ya gafarta musu, kema don Allah ki yafe mata tunda shi Abbas din ya nuna komai ya wuce kuma dan Allah ki daina fad’in zaki fita ki bar mata gida wannan maganar bata dace ba.” Hajia tace”To shikkenan tunda kunce haka na hakura na barku da ita gatanan ta zauna idan halinta ne zaku gani ni tuntuni na dawo da rakiyar Ramltu shiyasa nake so tayi nesa dani da zuria ta.”
Ramlatu tace”Hajia ashe har kin cire ni daga cikin zuriarki me yayi zafi hajia ki duba halin da nake ciki nice fa babbar ‘yarki.” Hajia taja tsaki gami da miqewa da fad’in “Kece babba kuma kece fitinanniya wacce bata kaunar zaman lafiya Allah dai ya shiryeki.” Tana kare maganarta ta mike tare da kallon kishiyarta tace”Hajia gobe idan Allah ya kaimu da safe zakuje asibiti da Naja’atu a dubata.” Hajia Rabi tace”To Allah y kaimu goben lafiya.” Hajia sama ta nufa ba tare da ta saurari magiyar da Ramlatu take mata ba…..Hajia Rabi ta kalleta a nutse tace”Hakuri zakiyi Ramaltu ki cigaba da rarrashinta har ta sakko amma hakikanin gaskiya ke da d’anki kun aikata mummunan aiki sai dai kawai ace Allah ya kyauta ya kuma kiyaye gaba.”
Ramlatu tasa gefan zaninta ta share hawayen idonta jingina tayi jikin kujera tare da tsirawa kasan kafet ido tana tunanin yanda rayuwa ta juya mata baya…..Naja’atu kuwa miqewa tayi ta shiga daki ta kwanta tana zubar da hawayen bakin ciki, tana kallon Abbah Abbas ya tattara iyalinsa suka tafi banda ita wannan al’amarin yayi masifar tsaya mata a rai! sai ta shiga tunanin ita yanzu mecece makomarta.