MADADI 1-END

MADADI Page 81 to 90

To washe garin ranar da wuri Naja’atu da hajia Rabi suka shirya direba ya daukesu suka nufi asibiti da yake pravite ne basu sha wahalar ganin likita ba………Dr ya tabbatarwa Da hajia Rabi cewar Naja’atu ita da babyn dake jikinta lafiyarsu lau, hasken da fatar tayi ba matsala bane mafi akasari masu karamin ciki nayin irinsa, har scanning sai da yayi mata ya nuna musu tare da tabbatar musu da lafiyar babyn magunguna masu kyau ya rubuta a takarda sannan yace suna fita zasu ga gurin saida magani sai su siya………..Hajia Rabi taji dadin bayanin da Dr yayi kan lafiyar Naja’atu da cikin jikinta, dan haka kafin su nufi gida sai da suka tsaya a Pharmacy (gurun siyar da magani) suka siya kana suka shiga mota direba yaja suka nufi gida.

Koda suka isa gida hajia rabi bata bari direba ya shiga da motar cikin gidan ba ta umarce shi daya saukesu….Suna fitowa ta kalli Naja’atu a nutse tace”Zamu shiga gidan Baba malam ku gaisa ko.”? Naja’atu tayi kwal kwal tana shirin yin kuka tace”Hajia ina jin tsoron haduwata da Baba Talatu.” Hajia Rabi tayi murmushi tare da girgiza kanta tace”Ki saki jikinki kada ki damu bazan bari tayi miki fad’a ba! Baba Talatu macace mai ilimi tasan qaddara daidai gwargwado saboda haka ki kwantar da hankalinki nayi niyyar kaiki gurinta ku gaisa ba da wata munufa ba.” Naja’atu ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace”Nagode hajia.” Hajia rabi tace”Babu komai ai.” Hannunta ta riqe kai tsaye suka nufi gidan baba malam d’in………

*Wayyo hannuna???? Ayi hakuri da typing error babu editing???? Nagode????????*

*Littafin na kudi ne….!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake….Vip group #600 normal group #300 account… 0542382124…Binta umar gtbank idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number…. *07084653262…..BINTA UMAR ABBALE*

66****Baba Talatu na zaune a kan tabarma da karamar redio a kusa da ita tana sauraran shirin barka da hantsi wanda tashar redio freedom ke gabatarwa a daidai irin wannan lokacin Baba Talatu ma’abociyar jin redio ce shiyasa kullum kanta yake a waye ta iya mu’amula da mutane bayan hakan kuma tana zuwa isilamiyya irin ta matan aure duk ranakun asabar da lahadi( sauraran redio nada mutukar tasiri a rayuwar d’an adam akwai muhimman shirye shiryen addini da wasu tashoshin gidajen redion ke gabatarwa wanda idan mutum na saurara zai qaru da wasu abubuwan masu amfani, redio tamkar makarantar ce ta wanni fanni domin suna ilimantarwa )

Tunda suka shiga gidan Naja’atu take ra’be ra’be ta kasa sakin jikinta sai ‘buya take a bayan hajia Rabi tana jin tsoron had’a idonta da mahaifiyartata……Baba Talatu ta gyara zamanta fuskarta da fara’a takewa Hajia Rabi sannu da zuwa, redion kusa da ita ta dauke daga gurin ta sanja mata guri tana fad’in” Hajia bisimillah zauna ga guri nan.”

Hajia Rabi ta zauna a nutse Naja’atu ta zauna kusa da ita sai sunkuyar da kanta takeyi…………Bayan sun gaisa da juna Hajia Rabi ta kalli Baba talatu tace”Naja’atu na kawo miki ku gaisa da juna.” Baba Talatu tace” Au ita bata da kafafu har sai anyi mata jagora.”? Hajia Rabi tace” Haba ba dai haka bane wallahi munje na kaita asibiti ne nace lallai sai na kawo ta ku gaisa da juna.

Baba Talatu ta ta’be bakinta taja bakinta tayi shuru har yanzu tana jin ciwo da takaicin abinda naja’atu tayi musu…..Naja’atu ta dago kanta a hankali ta kalli gurin da mahaifiyar tata take a sanyaye tace”Baba ina kwana kunanan lafiya.”? Ba tare data kalleta ba ta amsa da “lafiyarmu lau.” A sanyaye ta mayar da kanta qasa jikinta duk ya mutu da yanayin kallon da mahaifiyar tata ke mata….Hajia Rabi tace”Baba don Allah ki yafewa yarinyar nan magana ta wuce nasan ke mai ilimin addini ce kin san qaddara daidai gwargwado dan haka ki sassautawa naja’atu taji da abu guda.

A sanyaye tace”Ai bani tayi wa laifi ba da kike wannan maganar ita tasan wanda tayi wa laifi shi zata nemi afuwarsa bani ba.”

Hajia Rabi tace”Wallahi tuntuni Alhaji Abbas ya yafe mata da bai yafe mata ba ai ba zai tsaya a kan al’amuranta ba nasan kina sane da cewar shine yaje har can garin da take ya daukota ko.”

A sanyaye tace”Duk inada labarin komai wallahi ni kam na rasa wace zuciya ce da mutumin nan hajia Rabi ki duba kiga irin rashin arzikin da yarinyar nan tayi masa amma bai duba ba ba tare da yayi shawara da kowa ba yaje ya daukota daga wahala ai naso ya barta a can ta gane duniya ba rigar sanyawa bace.”

Hajia Rabi tace”Haba Baba ya kike wannan maganar babu dadin ji idan rai ya ‘baci hankali ake sawa ya nemo shi, kuma a duniyar nan babu wanda baya kuskure saboda haka dan Allah ki daina wannan maganar Baba kiyi hakuri da duk wasu abubuwa da suka faru a baya tunda shima wanda akayiwa laifin maganar ta wuce a gurinsa sai mu taru gabadayanmu muyi wa yarinyar nan adduar rabuwa da cikin jikinta lafiya shine babban abinda ke gabanmu

Baba Talatu ta share guntun hawayen idonta tace”Wallahi tuntuni magana ta wuce a gurina kuma na yafe mata har abadah sai dai duk sanda na tuna al’amarin nakan ji rashin dad’i a zuciyata nida malam munso yarinyar nan ta zauna zaman aure da Alhaji Abbas amma ta watsa mana qasa a ido duk sanda na tuno wannan al’amarin nakan shiga ‘bacin rai mai tsanani.”

Hajia rabi tace”Gaskiya da akwai rashin dadi a cikin al’amarin amma bakya tunanin rabo ne ya fitar da ita daga gidan Alhaji Abbas din, dukkaninmu fa bamu san gaibu ba sai Allah wannan cikin dake jikinta ya ishemu ishara gabad’ayan mu.”

Baba Talatu tace”Eh nima bayyanar cikin jikinta yasa na jingina al’amarin a matsayin abinda kika fad’a yanzu babu shakka idan rabo ya rantse to babu mahalukin da ya isa ya dakatar dashi, san nan kuma wani baya ta’ba haihuwar d’an wani koda da akwai sauran zama a tsakanin Alhaji Abbas da yarinyar nan to tilas sai taje ta auri wani ta haihu sannan ta dawo hannunsa.” 

Hajia Rabi tace”Yawwa nima abinda nake taso ki fahimta kenan watakila akwai ragowar zaman aure a tsakaninsu shiyasa Ubangiji ya yanke alaqar auranta da Bashir bayan ya saukar da ikonsa na samuwar cikin jikinta.”

Baba Talatu tace”To Allah yasa dan wallahi nafi mata sha’awa ta koma dakinta akan ta sake wani auran.” murmushi hajia Rabi tayi a zuciyarta tace akwai yiwuwar hakan dan ganin irin kulawar da Abbas keyi wa yarinyar alamu sun nuna har yanzu yana muradinta.

Mi’kewa tayi da niyyar tafiya ta kalli Naja’atu da kanta ke sunkuye tace”Zaki zauna ku sake gaisawa ko? bayan sallahr azuhur rana tayi sanyi sai ki shigo gida.” ” A hankali ta d’aga kanta tare da fad’in “To shikkenan.” Hajia tace”Ga magangunanki nan idan kinci abinci sai kisha insha Allah idan na shiga gida zanyiwa hajia bayanin abinda dr ya fada sai ta kwantar da hankalinta.” 

Murmushi ta d’anyi tana sake sunkuyar da kanta da tunanin yanda hajia ta damu da ita da cikin dake jikinta ita kam babu abinda za tace da Iyalan gidan Alhaji sama’ila sun nuna mata zahirin kauna gami da kulawa a cikinsu babu wanda ya kyamaceta duk kuwa da cewar ita din mai laifi ce a gurinsu, amma sun kauda kansu suna tattalinta gami da bata dukkanin kulawar data dace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button